Skip to content
Part 50 of 59 in the Series Rigar Siliki by Maimuna Idris Sani Beli

Ranar juma’a da safe tana shirin fita aiki ya dube ta da fuskar shanun da tun da suka yi rigimar nan take ganin irinta a fuskarsa, ya ce mata,

“Ina son ki rubuta takardar barin aiki yau, na zabi baki damar ki rubuta ne don na cigaba da mutunta ki, da zan yi ta jahilai cewa zan yi kar ki sake fita aiki daga yau din nan.”

Ta zagaye fuskarsa da kallo babu alamun wasa sam, kuma babu qofar wargi bare ta zo da shi,

Amma duk da haka sai da ta kwatanta,

“Amma dai ka san ba da ni muka yi maganar aiki ba ko…?”

Ya tare ta har yanzu babu wasa a fuskarsa,

“Eh da Alhaji muka yi magana, sai dai ba dan shi karan kansa na bar ki aikin ba don karan naki kan na bari, domin na baki wata dama da kike jin da ita zaki iya muzguna min ko kuma ki sa na sake ki, na zaci wannan qwantaragin ya qare tun da kin je aikin ban saki ba?”

Kallonsa kawai take tana ganin kamar ma ba shi ne Mujahid ba, komai ya canja babu rahama babu annuri sannan babu ragayya, duk kururuwar soyayyar da yake mata.

Bai bar ta ta qare nazarinta ba ya cigaba,

“Na ga zaki balle wani sabon kwantaragin ne, na kwasar sirrin gidanmu ki yi waje da shi, ki dinga wucewa gidajen mutane daga wajen aiki kina yawo tsegumi, wannan ba zan iya hana ki ta dabara ba gaskiya, sai dai na qarfi, zuwa yanzu ma yakamata ki san ina da shi”

Cikin rashin hayyaci ta ce,

“Me?”

Da isa ya ce mata,

“Qarfin”

Ta jima kafin ta tanka,

“Gaskiya babu wanda ya isa ya hana ni aiki…”

Ya fara qoqarin kaucewa ya bar mata gurin,

“Shikenan, don Allah kar ki rubuta takardar barin aikin ki gani, na ba ki sati guda”

Tuni ta sha gabansa,

“Gaskiya yau yakamata ka amsa min wata tambaya, shin don ka ga kowa ya kasa fahimtata ne ana kuma hukunta ni bisa rashin fahimtar ya sanya kake amfani da wannan damar kake quntatawa rayuwata?”

Ya dan ja fasali kafin ya amsa,

“Ni ba na son dogwayen zance, maganar yanzu ita ce, na hana fita aiki saboda kar ki dinga fitar mana da sirrin gida, tunda na fahimci ke kanki babu saiti”

Ta daure ta ce,

“Wannan tsohuwar magana ce”

‘To ai ke sai ana yi ana tuni, matsalar taki ai da yawa”.

Yayi wucewarsa ya bar ta.

Tana nan tsaye cikin tsabar takaici ko yatsanta ta kasa motsawa bare ta yi alamar barin wajen sai ga shi ya dawo da waya a kunnensa yana cewa,

“Bari na ba ta ki yi magana da ita.”

Ta ji kayan cikinta na qara saboda fargabar ko mahaifiyarta ya sanarwa ta ce a bata wayar, cikin karkarwar hannu ta karbi wayar sannan a jigace ta dube shi ta ce,

“Wacece?”

Abinda ya ba ta takaici sai ya ce mata,

“Nabila ce.”

Ta ji kamar ta kashe shi da mari ta kuma yi cilli da wayar, amma dai ta daure ta kai wayar kunnenta lokacin da ta jiyo muryar Nabila cikin rauni tana ambaton,

“Anti”

Ba qaramar dauriya ta yi ba ta tanka da dadin murya hawaye na fado mata a fuska,

“Nabila yaya aka yi?”

Nabila ta fara hado kayan kuka tana cewa,

“Anti ki yi haquri”

Yanayin shauqin kukan Nabila ya tuna mata qaunarsu, sai ita ma ta ji kukan na neman qwace mata, amma dai muryarta ta yi rauni sosai ta ce,

“Nabila wai meye?”

Nabila na kuka ta ce,

“Ni dai ina sake ba ki haquri, kina fushi da ni ba na jin dadin rayuwata na rantse miki da Allah, in ba ki bari ba Anti komai ma zai iya faruwa da ni”.

Tausayi ya dami ran Binta, ta ji da yawan haushin Nabila da take ji ya tafi, tunaninta na cillawa can tuno shaquwarsu da damuwarsu da juna, ta tabbatar in ba mai irin damuwoyinta ba dole manta wannan shaquwar ba zai zo masa da sauqi ba.

Tana ta faman dauke nata hawayen ta ce,

“In sha Allah komai ya wuce, kar ki damu Nabila na rantse miki komai ya wuce”.

Mujahid na tsaye yana kallonta har ta gama wayar ta miqa masa, ya kara a kunnesa ya fice yana cewa Nabila,

“Amma ba cewa kika yi na hada ki da Binta a waya zaki yi mata kuka ba”.

Nabila na qoqarin kama kanta ta ce,

‘Ayya wallahi Yaya Mujahid ni har ma na manta dalilin wayar”.

Ta tari numfashinta,

“Eh na fahimci haka, ke babu wani abu muhimmi a wajenki yanzu sai Binta na fishi da ke, ni da nake muhimmi na sha fada miki ki share komai zai wuce amma kin qi yarda da ni”

A raunane ta ce,

“Yi haquri Yaya Mujahid na daure na manta, ba zaka sake kama ni da wannan laifin ba”.

Da sauri ya ce,

“Kin yi alqawari?”.

Kai tsaye ta amsa,

“Na yi, In sha Allah”

Cikin kawa ya ce,

“To kin biya ni”.

Nabila ta nisa,

“Sai ka mayar mata da wayar na roqe ta ta zo kamun.”

“Zan fada mata da baki”.

Bayan sun gama wayar ya koma daki ya sami Binta na goge hawaye tana qoqarin yafa mayafi,

Ya kawar da kai kamar bai gane tana hawayen ba, yayi fuska ya ce mata,

“Nabila ta zaci ina da wani matsayi a wajenki, wai cewa ta yi na roqe ki ki je kamu yau, ga katin.”

Ya ciro katin gayyata mai dauke da adireshin wajen da za’a yi taro ya miqa mata, sannan bai jira cewarta ba ya zarce da cewa,

“Idan kin ga zaki je kuma kina buqata zan iya kai ki, amma in ba ki da sha’awa zaki iya zamanki”

Ta rude dalilin batutuwa biyu, bikin Nabila ake amma wai tana cikin ‘yan gayya, sannan Mujahid ne ya dauki nauyin biki me tsada haka idan ta yi la’akari da wajen da za’a yi kamun da kuma dinar da za’a yi gobe.

Wannan karon cikin hawayenta ta dube shi a raunane,

“Me yasa baka jira wannan lokacin an shafa maka lalle kamar yadda za’a shafa mata ba? abin zai fi armashi, ka ragewa soyayyarku da bikinku armashi dalilin aurena”.

Ya so ya cigaba da da wasa da hankalinta, amma yanayinta na wannan lokacin ya nuna lallai in yayi mata zolaya zai mata rauni a zuci, don haka ya fada mata iyakar gaskiya kuma cikin dadin furuci,

“Ni ba na tauyewa mutum haqqi sai wanda ya tauyewa kansa Binta, hakan kika kasa fahimta tuntuni,  ke baki yarda ki saurare ni ba bare ki yi wata hidima a aurena, na sani Nabila ma ni na matsa mata ta yi hidima a aurenta, dalilina shi ne, tana gudun yin hidimar ne sabo da ni da ke da take ganin kamar takura mana ta yi ta shigo rayuwarmu, ba na son ta tafi da wannan tunanin don haka nake son yi mata abinda har ta mutu ba zata taba jin ni na muzguna mata babu haqqi ba, sannan ni mai kare mata baya ne ta sami abinda duk wata diya mace take samu.”

Daga wannan bai sake ace mata komai ba ya fita.

Ta bi bayansa tana tsakiyar jin wata kururuwa a filin kanta, yayin da sashin editing na kwanyarta yana ta faman gyara wasu kalmominsa don su yi mata dadi a zuci, amma duk da haka sun gaza iyawa.

“…ba na son ta tafi da wannan tunanin don haka nake son yi mata abinda har ta mutu ba zata taba jin ni na muzguna mata babu haqqi ba, sannan ni mai kare mata baya ne ta sami abinda duk wata diya mace take samu.”

Duk inda kalmar yabo da nuna qauna take kalmomin nan sun bayyana na Mujahid ga Nabila, tana jin kishi a qirjinta amma ba ta yarda kishin ba ne.

Da ya kai ta wajen aiki yana shirin juyawa ta ce masa,

“Qarfe nawa zaka zo ka kai ni?”

Ya ji wani farin ciki a ishe shi, har muryarsa ta kasa boye farin cikin inda ya ce,

“Qarfe nawa kike son zuwa?”

Ta ce,

“Qarfe hudu”

Ya ja motar ya wuce yana cewa,

“To ki zama cikin shiri”.

*****

Bai sami dawowa da wuri ba sai bayan biyar, kusan shidda saura ma, ya sami Binta ta shirya tsab, ta ci kwalliya bai taba ganin kwalliyar da ta yi kyau kamar haka ba, sai ya ji ta burge shi, don ba ya so kowa yayi mata kallon raini a wajen, duk da shi yake ganin yana girmama ta amma ita ba ta son ta girmama kanta.

Ganin fuskarta babu yabo babu fallasa ya sa ya dan kalle ta a kaikaice yayi murmushi,

“Kin yi kyau Binta.”

Ta dan yi gatsine sannan ta basar, shaidar ba ta ji komai a ranta game da yabonsa ba, bai damu ba ya wuce yana cewa,

“Ba ni minti goma mu shirya, ai ba wani makara muka yi ba, yanzu Nabila ke ce min ita ma ba ta yi mintuna goma da isa wajen ba”.

Ta bi shi da kallo a sarare, a ganinsa kalaman da yake bayani ne da zai ragewa zuciyarta nauyi don ta yi jira, amma qarin ciwo ne ga zuciyarta don yana nuna lallai fa Nabila muhimmiya ce gare shi, yadda har ba ya mintuna sai ya kira ta a waya ya ji halin da take ciki.

Mintuna goman ba su cika ba ya fito cikin shadda Senator grade A, ruwan kunun kanwa an mata qaramin aiki dinki yayi matuqar kyau kamar wani kyakkyawan fure,  har a idon Binta, kansa babu hula sai kwantacciyar sumarsa baqa wuluk tana qyalli. baqaqen takalma da agogon hannunsu sun qara wa kwalliyar tasa armashi.

Satar kallonsa kawai Binta ta ke har suka shiga mota suka tafi, babu mai tanka kowa.

Ta yi ta kintacen abinda zai faru a wajen mai dadi da mara dadi saboda haka ta dinga danasanin ma amsa gayyatar da ta yi, sannan data sani ba ta yarda da cewa shi zai kawo ta ba, gara ta kai kanta in yaso in ta hangi abinda zata ji bacin rai a wajen kawai ta samfe.

Duk ta gama wannan saqe-saqen ga farin cikinta ya tsayar da motar a wajen fakin sai ya ce mata,

“Ki shiga, in kin gama sai ki kira ni, zan jira ki”.

Ta dan dube shi saroro,

“Au ba zaka shiga ba?”.

Ya girgiza kai da sauri,

“Ba na sha’awa”.

Ta dan yi dum,

“Da ka san zaka takura ai da ba ka gayyato ni ba”.

Ya tare ta da sauri,

“Na fada miki sha’awa ce ba na yi, ba don zuwanki ba ne ko ba don ba na son taya Nabila farin ciki ba”

Da ta ji zai tsokano mata damuwa sai ta yi saurin bude motar tana cewa,

“Ai da na ga ma ka ciyo gayu na zaci ka zo ku aje hoton tarihi ne”.

Ya daidaita murya ya kira ta a tausashe,

“Binta”

Ta riqe murfin mota tana kallonsa da qoqarin cusawa kanta jar zuciya, ya fara daukar hankalinta a yau, amma ta fi tsammanin kawai tausayin kanta ne ya sa take jin motsin wani abu cikin ranta game da shi.

“In zaki ba mu hadin kai na zo mu yi hoton?”

Ta runtse ido ta bude ta kalle shi,

“Ni meye nawa a ciki?”

Ya kada kai,

“Ina da tabbacin idan Nabila ta gan ki ba cikin walwala ba sai hakan ya bayyana a idonta da tata walwalar, ni kuma na san ki da kyau, ba ki da walwala idan ina guri, wannan ne naki a ciki”.

Ta jima kafin ta tanka, cikin rawar murya,

“Yau daya dai ka zo zan baku aron walwalar, kar na shiga kundin tarihin ranar aurenku na hana ku farin ciki.”

Ta rufe motar inda ya fito da sauri,

“To ki tsaya ni mana”.

Ba don ta so ba ta tsaya ya zo suka jera, suka doshi harabar da kade kade ke tasowa.

<< Rigar Siliki 49Rigar Siliki 51 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×