Mu muna tunani akan kowa, amma ke kanki kawai kike wa tunani, mu muna damuwa da burin kowa, amma ke naki burin kawai kike hange, mu muna haqura da farin ciki mu bawa juna, amma ke kanki kawai kike wa tanadin farin ciki, hatta da zuciyoyinmu ba sa aibata ki, amma ke taki zuciyar wani lokacin tana zundenmu, tana aiki don muzguna mana, in kin yi kuka muna ji a jikinmu, hatta da ni nan binne ki kawai nake da siyasa, amma ke kullum ke kike gadar mana da hawaye…”.
Ya miqe tsaye cikin zafin rai yana murza yatsu,
“Binta wannan haqqinmu ne, nauyinmu ne da in kika je da shi lahira Ubangiji zai bi mana kadi.
Lallai na sha fada miki cewa ke Rigar Siliki ce, abinda ba ki fahimta ba, ni ma ita ce, sai na so za’a sarrafa ni, kuma sai na so za’a ji dadina, haka sai na ga dama za’a san cikina, duk inda kika so da baudewa Binta na fi ki, bambancina da ke shi ne, duk hargitsina, ba na barin kafar da ma’abocina zai gaji da shaqiyyancina ya yaga ni ya watsar, ko qyallina ya gushe daga idon masu gani, sannan ni in zan yi tsiya ina waiwayen gaba da baya, haka zalika ina sadaukar da farin ciki ga kowa, ba sai abinda nake so ba, duk wanda ya cancanta sai na ba shi haqqinsa, duk wanda bai cancanta ba kuma sai na hargitse masa ko da shi ne abinda nake so”.
Ya sake tsagaitawa yana dubanta da kyau, ita ma haka take dubansa ko qiftawa ba ta yi, ya ce,
“Ke ke ce kika kawo Nabila rayuwata, tun farko ke kika koya min sanin muhimmancinta, har ma kika sha yi min tayin aurenta, ban karbi tayin ba don ba ita nake so ba ke nake so, amma dai kin yi nasarar hada mu zumuncin da ya ba ni damar sanin muhimmancinta, duk lokacin da zan yi kuka akan sonki Nabila ce ke share min hawaye, duk lokacin da zan fara jin karaya akan sonki Nabila ce ke qarfafa min gwiwa ta ce min zan yi nasara, in Nabila na da dama ko sau daya ba zan yi baqin ciki ba, na rantse da Allah na yi mata wannan shaidar, wannan shi ne haqqin Nabila a kai na, da zan biya shi har tsawon rayuwata, akan sa ne kuma nake tsaye gabanki yanzu nake roqon alfarmar cewa, qiyayyata kar ta shafi Nabila, shaquwar Nabila da ke na janyo ta shiga damuwa a duk lokacin da ta ga hawayenki, in ita ce ba zata bar hawayenki ya diga ba, amma ke kullum sai kin qirqiri kuka don ta cutu, yanzu an kai mata labarin kina kuka, kawai ta sami guri musamman ta share ta zauna tana kuka…”
Wannan lokacin ta tare shi, tana goge hawaye,
“Tun da ka fara magana yanzu ne kake fadar abinda ban gane ba, ban taba cutar da Nabila a fuskarta ba, don na zama karkatacciyar kukarka in na yi kuka sai ka ce don na cutar da ita na yi…”
Ya tare ta,
“To don me zaki dinga kukan? don ta auri mijinki? ke ba zaki iya sadaukarwa ba? In Nabila ce ta fara aurena na rantse da Allah babu abinda ba zata yi ba don ta nuna miki farin cikinta, me yasa komai na kirki sai ke ce zaki rasa shi? Me yasa in dai zamu yi kuka ni da Nabila sai ta silarki? ke sakamakonki kenan ga masoyanki ki dinga quntata musu? duk me sonki sai ya ga abinda ba ya so…?”
Ta dakatar da shi da hannun cikin kuka,
“Tsaya haka mana”.
Yayi shiru yana kallonta.
Tana kukanta ta tambaye shi,
“Ka ce, tun daga ranar da muka ganku a gidansu ni da Yaks kullum kuka hadu sai ka ba ta labarin son da kake min, har zuwa ranar da aka daura aurenku, me yasa ranar daurin aurenku ta zama ranar dena fada mata kana sona…”.
Ya tari numfashinta da amsa,
“Don lokacin in dinga bata labarin ke nake so ya wuce, in na cigaba ya zama cin fuska, adalci a lokacin shi ne in ta fada mata ina sonta, shi ne abinda na yi, daga ranar ban qara yi mata labarin sonki ba, illa ina yi mata labarin nata son…”.
Wannan karon ma ta tare shi,
“Yanzu dai me kake buqata?”.
Kai tsaye ya amsa,
“Nabila ta dena shiga damuwa, in zaki yi kukanki ban hana ki ba, yadda ban hana ki qina ba ban isa hana ki kuka ba, to ina roqon alfarmar ki dinga boyewa idonta don kar ta yanke qauna daga sanin da ta yi miki na mutuniyar kirki…”.
“Kuma don kar ka ga tana kuka”
Ta tare shi cikin share haweyenta tana murmushin yaqe, shi kuma bai damu ba ya amsa mata,
“Wannan dalilin na fara fada, tun dazu nake fada nake jaddadawa, ban ga dalilin da zai sa qaramar yarinya ce zata yi ta faman yi wa rayuwarmu halacci mu gundum gundum da mu ba zamu iya mayar mata ba”
Ta cigaba da share hawayenta tana cigaba da murmushinta,
“To shikenan an gama, zan yi ta kiyaye maka farin cikinta dama na iya, amma bisa sharadi”
“Ina jin ki”.
Ya fada hankali kwance,
Ta ce,
“Zaka cigaba da ririta son Nabila,ni kuma kar ka qara cewa kana sona…”
Kawai sai ya kada kafada,
“In kin zabi hakan zan gwada, dama can na dade da sonki a zuci ai kowa bai sani ba”.
“Yanzu za ka boye ne saboda Nabila”.
Ya tare ta,
“Ki bar wani maimaitawa, ko wanne iri ne dalilin naki ne ba nawa ba, ni dai kawai abinda zan sanar da ke shi ne, duk tsarin da zaki zo da shi ba zan yarda ya cutar da ni ba, in ramin mugunta kike tunani haqa min yakamata ki tuna wadanda kika sha haqa min a baya, duk wanda kika dana ke yake harba, su ne kuma suka yi ta cunkushewa har suka aura min Nabila, abinda ba ki sami me fada miki ba kenan, haka zalika su suka hana Yaks Nabila, don ba don kun kwashi sharri kun kai asibiti ba, babu yadda likita zai san Alhaji, bare har ya zama dalilin Alhajin zai je binciken qanjamau dinki aj nuna masa yarinyar da Yaks ya kawo zubar da ciki ta haife, abinda ya qara fito da rashin kyan halinku sarari har dai manya suka ji bari dai su hada mu masu kyawawan halin guri daya kar su yi mana wake da shinkafa”
Binta ta ji kanta na neman tarwatsewa, sai yanzu ta gane kan zaren, kawai ta shiga tare shi da borin kunyar cewa,
“Shikenan dai tunda ka riga ka amince, duk zantuka sun qare.”
Ya miqe tsaye,
“Za mu cigaba da buga Game kenan?”.
Kallonsa kawai ta yi, babu halin ta ce eh, ko a’a, don qwaqwalwarta ma ba a kammale ta ke ba.
Ya murza yatsu ya fara qoqarin tafiya,
“Har yanzu qofa a bude take, in kin ji kina buqatar canji ki yi magana”.
Tana ta kallonsa ya doshi qofa, ya riqe labile ya juyo ya sake dubanta,
“Kar ki manta da maganar rubuta takardar ajiye aiki saboda kwantaragin aikin nya qare”.
Ba ta yi magana ba.
Ya murza Handle ya ya fice ba tare da ya sake tankawa ba.
Da farin cikinsa ya komawa Nabila wadda motsin hawowarsa Bene ya sa ta kintsa kai, ta raba idonta da hawaye ta raba fuskarta da qananun damuwa.
A falo ya tarar da ita, yana shigowa ita da shi idanuwansu akan juna.
Ta yi saurin sauke kai qasa, saboda annurin da ke fuskarsa ya bugi muhallin sonsa a zuciyarta, suka shiga sassarfar kada mata zuciya.
Cikin kuzarin yake sosai irin wanda farin ciki yake haifa, ya isa gareta ya zauna a hannun kujerar da take zaune ya dafa kafadarta,
“Nabila dago ido ki dube ni.”
Da qyar ta sarrafa kanta ta iya daga idon ta dube shi, ba cikin qwarin gwiwa take ba saboda barin da jikinta yake sakamakon kusacin da ke tsakaninsu, ta dinga jin qanshin turaren jikinsa na shiga ta dukkan kafofin jikinta ba wai hancinta kawai ba, kai tsaye kuma yana isa har tsakiyar Kwanyarta da zuciyarta, sai take jin tamkar shi ne yake neman canja mata duniya.
Suka dubi qwayar idon juna kai tsaye, dukkansu suna jin wani canji a tare da su, canjin da Nabila ke jin lallai da ba ta auri Mujahid ba, ta yi gagarumar rasa aljannar duniya, canjin da shi Mujahid ke jin Lallai duk wanda bai auri matar da ke sonsa ba yayi gagarumar asarar farin ciki a duniya.
Ya qwaci kansa da qyar wajen shauqin da ke cilla shi sama yana cafewa, murya sarqe ya ce mata,
“Ki jaddada alqawarinki.”
Ita ta kasa qwato kanta a wajen shauqin, don haka ta kasa tankawa sai wata qwallar farin ciki da ke tarar mata a ido, Mujahid ya fahimce ta, don a cikin qyallin qwallar tata ya hango sonsa kwance, hakan ne kuma ya tuna masa dogon zangon da ta ja tana jin cewa ai sonsa da take boyewa ya boyu ga kowa ciki har da shi.
Da dabara ya lalubo tafukan hannunta ya shiga murzawa, tafukanta masu laushi fiye da atafa, masu santsi masu dumi, komai nasu mai kai saqo zuciya.
Niyyarsa ya rikitata ta bayyana son a fatar bakinta yanzu, amma ya fahimci idan bai wasa ba za’a sha shi basilla, don ba ta daga cikin matan da za’a rabe su a mallaki kai dari bisa dari, amma dai ya daure ya kai zuciya nesa, murya a sarqe ya ce mata,
“Ki yi min alfarmar so Nabila, zumunta ta jaza min sonki mai qarfi ya marabci zuciyata, ina neman raddi don Allah.”
Ta ji maganarsa a fatar kunnenta, ma’anarsa kuma ta kai zuciyarta, amma so da murna sun hana ta qarfin halin sarrafa kai, babu komai a zuciyarta da numfashinta sai Mujahid da sonsa, ba ta ma san haka sonsa yake da dadi a rai ba, sai ranar yau, kodayake da tana son ne cikin debe qauna, ta cire rai zata samu saboda haka ba ta tuna komai sai jin asarar so.
“Ki taimake ni Nabila, ina neman soyayyarki, don Allah kar ki zauna da ni bisa alfarma”.
Ya sake fada mata cikin rada a kunne, so yake ya ga da shauqin da zata bayyana masa sonsa.
Ta dago da kanta sosai ta kalle shi, hawaye na taruwa a idonta murya na rawa ta ce,
“Duk abinda kake so zan yi Yaya Mujahid, duk abinda kake so na zama, ko ya kake so na kasance iyakar iyawata zan kasance, ba bisa alfarma ba bisa cancantarka”.
Ya kada kai yana sake girgizawa,
“Ba buqatuna kenan ba, tunda ma can kin kasance min yadda na so ki kasance, duk wata karramawa kin ba ni, raddin so nake so ba na biyayya ba Nabila, ina sonki”.
Ta ji numfashinta na neman daukewa saboda murna da farin ciki, tana qwato kai da kyar ta kada masa kai,
“Ni ma haka?”
Ya jawo ta jikinsa ya rungume, yana jiyo sautin bugawar zuciyarta wanda ba sa jaddada komai sai nuna soyayyarsa, cikin sassarfar numfashi ya ce mata,
“Ke ma me?”
Ta kasa cigaba da boyewa,
“Ina sonka, ban taba jin son wani abu sama da naka ba, ban taba farin ciki da komai kamar naka ba, babu wani abu da ya taba burge ni sama da kai, ni ba zumunta ta raya min sonka ba, wayar gari kawai na yi na sami kaina cikin son ba tare da na san dalilinsa ba… in wannan ne buqatarka ka yi farin ciki Allah ya biya maka kafin ka ambata”.
Shi ma ya fara jin qwalla saboda so,
“Ba zaki taba nadamar sona ba Nabila, ni dan halak ne, duk wanda ya kyautawa rayuwata ba na juya masa baya, na gode.”
Tsakaninta da Allah ta kada kanta da ke kafadarsa tana cewa,
“Na sani”