Ya sake nisanta tunani a cikin lamarin Binta, yanzu ne kuma ya fara fahimtar lallai da gaske Binta take ba ta sonsa, kuma ba zata taba son nasa ba, don haka ya ji sanyin gwiwar cigaba da duk wani yunquri da zata so shi, ya riqe kansa da damuwarsa a zuci ya bar zolayarta, ya bar yin abu don ya bata haushi, ya shiga tafiyar da ita tamkar qanwarsa ta da can.
a daina biyo Nabila dakinta idan ta shiga ranar girkinta, sannan ya daina ko wacce irin walwala gaban Binta, to da alama wannnan sauyin ne zai sauya masa. . .