Sai kawai ta kawar da kai tana kallon windo mota tana qoqarin shanye hawayenta.
Ya kamo hannunta yana qoqarin juyo da ita don ta fuskance shi ya cigaba da more kallon kyakkyawar fuskarta mai sanya shi nishadi,
Da sauri ta janye jiki cikin dariya da farin ciki,
“Malam mai zance ai zaka saba qa’ida”.
Yana dariya ya shiga karkade hannu,
“Ayya! Uffararan, na sha’afa ne”..
Tana samu dariya ta fanshe mata hawaye.
“Mu dawo maganar mu, me ye ra’ayinki ga haifar mana yara? Ina son yara turmis, ina son masu sa ni farin ciki irinki.
Wannan karon ma ta kasa tankawa, zuciyarta da kwanyarta ba sa tsinana komai sai karrama Mujahid da qirqira masa manyan matsayi tare da hango kyakkyawar rayuwar farin ciki tare da shi, ya iya ciyar da mace abincin zuciya, ya iya gwada wa mace cewa so ne gaba da komai a muhimmanci cikin abinda ke tsakaninsa da ita. Da ba ta aure shi ba da ta yi asarar wannan nasarar, Binta da ta samu ba ta san darajarsa ba ko ta halin yaya yakamata a bi ta da Jaje.
“Ke fa ba zubin zancen qauye na kira ki mu yi ba Nabila, ba jikin darni muka manne kina kawar da kai ina satar bin ki da kallo ba, zancen birni na zo mu yi domin sonki yayi min nauyi a qirji ina son na yi ta fitar da tsoho ina nuna miki don kullum zuciyata qirqirar sababbi take.”
Wannan karon ta qoqarta ta amsa cikin nauyin qirji da raunin murya mai nuna tsantsar gaskiya,
“Zuciyata tana da rauni tabbas, in zata yi zata hada sauraron labarin taka soyayyar da qoqarin bayyana tata ina jin darewa biyu zata yi Yaya Mujahid, ba komai ba ne farin ciki kai ne, ba komai ba ne kyau kai ne, kai ni son ma kai ne, in ana kwatance ni duk wani abu mai daukaka na qawa ina ganinsa kai kawai, duk wani alkhairi kuma ina yi fatansa daga gareka duniya da lahira… shiruna ya fi, don ba ni da azancin iya bayyana sonka wallahi tallahi…”
Ya kasa jurewa sai da ya jawo abarsa ya rungume.
Duk da suna neman shidewa don jin qauna ba ta fasa yunqurin qwacewa tana fada masa,
“In ka yi haka zancen yan duniya zamu yi?”
Ya girgiza kai da sauri yana nemo kunnenta,
“Bar ni na yi wa kaina murna na kuma yi wa masoya irin mu jaje da ba su sami damar hallacin shaqar zazzaqan numfashin juna ba, Na godewa Allah da ya rataya min qaunarki a lokacin da komai daga gareki ba zai nesance ni ko ya zama haramiyata ba, ina sonki Nabila… don Allah ke ma ki cigaba da sona don in kin rage min so zaki dauki haqqi”
Tana neman rasa numfashin shaqa take jaddada masa,
“Ina yi maka albishir din qarin so duk bayan shaqar ko wanne numfashi, ai sonka ne ma numfashin nawa, ta yaya zan dakatar da shi?…”
Binta ta gaji da dauriyar yi musu hasashen inda zasu je ko ta yi zamanta a daki har su je su dawo din, sai da ta biyo su da leqe, amma ba ta jima ba ta ji tsaiwa na neman gagararta kawai sai ta ja qafa ta koma daki ta cigaba da rasgar kukanta har qarfe goma da rabi ta gota, ba ta ji motsawar motarsa da barin gidan ba sai motsin shigowarsu da mota gidan ta ji.
Tana tsaye tana kallonsu ta windo suka shigo manne da juna yadda ko a duhu aka hango su za a gane yadda gangar shauqin soyayya ke goga musu take.
Da sauri ta saki dan labilen da ta riqe ta koma da sauri kan kujera ta zauna cikin rashin hayyaci tana cewa,
“Wadannan sakarkarun mutanen a make suke, sai ka ce sun shawo giya, ko ma ita suka shawo oho musu”.
Ta san ta fadi wannan maganar ne domin ta bawa kanta qarfin gwiwa, amma gaskiyar magana ji take kamar zuciyarta zata kama da wuta.
Sun fara hawa matakalar bene ta ji Nabila ta ce,
“Au! Ban yi wa Anti Binta bankwana ba”.
Ta jiyo Mujahid a make ya rage murya ya ce mata,
“Ki share, ina jin fa ta yi bacci”
Cikin kulawa Nabila ta ce,
“A’a Yaya Mujahid, dazu ma da na je tana sallah fa.”
Ya sake yin qasa da murya ya ce,
“To Babu laifi, ki je, amma don Allah ki yi sauri ki zo kar ki bar ni da kadaici”.
Da sauri Binta ta shiga kintsawa kanta zama da hadiye hawaye tana kuma ta faman goge wanda tuni ya riga ya bayyana kansa, lokacin da ta ji Nabila ta doso qofar falonta tana cewa,
“Na yi alqwari.”
Da ta shigo babu ko wacce irin alama da ke nuna ta fita da Mujahid ko ta yi wani abu ba daidai ba, a sake ta yi sallama ta shigo. Ita kuma Binta ta tsaya saroro tana kallon wannan qarfin hali da nuna halin ko in kula.
“Anti Binta zan kwanta, ba ki buqatar komai?”
Binta ta dube ta da kyau cikin janyowa kanta jar zuciya, ko yaya ne dai Nabila na ba ta girma kuma duk runtsi ba ta hadiye mata haqqi, wannan ne abin kirki daya da zata ce tana iya riqe kanta ta aikata shi, wato ta ga karamcin Nabila da girman da take ba ta, duk masifar son da Nabila ke wa Mujahid wanda ba tun yau ba Binta ta san da zamansa, amma ko sau daya Nabila ba ta taba zaqewa ta nuna shi a gaban Binta ba, tana matuqar qoqarin wajen riqe kanta da kammale rayuwarta a zuwan kanta kawai take wakilta ban da Mujahid.
Binta na dariyar qarfin hali ta ce,
“A haba, sai ka ce ni ce Mujahid? Ba zaki kwanta ba sai kin tabbatar ba ni da matsala?”
Nabila ta amsa da iyakar gaskiyarta,
“Haqqin zumunta ko na auratayya ke janyo kulawa Anti, in mace na tabbatar da nutsuwar miji kafin ta kwanta, kamar haka ne in qanwa ta bi ba’asin lafiyar yayarta kafin ta kwanta, yaya zan saki baki in yi bacci in kina cikin matsala?”
Binta ta kawar da kai cikin shanye hawaye saboda tuno kashedin da Mujahid ke wa Nabila, na cewa, kar ta dade ta bar shi cikin kewa, gashi nan duk da ta dauko masa alqawari sai ba ta ji ba ta zo tana neman karya alqawarin saboda ita.
Wannan dalilin ya sanya ta fara jin qarfin gwiwar sadaukarwa irin nasu, wato yin abu don saka juna farin ciki,
“Ki je ki kwanta ki yi bacci cikin kwanciyar hankali, ba ni da wata matsala Nabila”.
Cikin bayyana farin cikinta ta ce,
“To Allah tashe mu lafiya Anti”
Sannan cikin hanzari ta wuce, Binta na kasa kunne tana jiyo ta tana hayewa Bene cikin sauri, wannan saurin nata kawai sai da yayi wa Binta rauni a qirji don ma ba ta san Mujahid ya jira Nabilansa a qafar benen ya dauke abarsa don rage mata dawainiyar hawa suka shige cikin farin ciki ba.
Kwanukan da suka biyo baya duk tunanuwan Binta sun tafi ne a kan yadda zata samawa rayuwarta sauqi duniya da lahira, don a yanzu dai duniyar a quntace take gareta kuma tana ganin alamu idan ta cigaba a haka ma zata je lahirar ta sha wuta.
Bisa wannan hasashen ta dauki shawarar Sani qanin Mujahid, wanda ya taba ce mata ko yaya ne ta rataye qiyayya gefe ta kalli Mujahid, zata tarar sonsa ba zai ba ta wani wahala ba wajen shigar mata zuciya, in ma ba ta yi hakan ba, ko yaya ne ta yarda ta karbe shi a amatsayin miji, yana da tabbacin shi Mujahid din da kansa zai wa kansa gurbin zama a qahon zuciyarta.
Ta fara gwadawa, kuma a guje zuciyarta ta fara karbar wani sabon saqo tare da mijinta, duk da ba ya bata kulawa amma in ta kalle shi tana farin ciki. Da tafiya ta qaru ma sai ta fara jin alfaharin aurensa, musamman in ta kalle shi a matsayinsa na kyakkyawan gaske ita kuma mara yabo mara fallasa, sannan Qaniyancinta bai sa ya danne mata ko wanne irin haqqi ba ko kuma ya zo mata da salon cin zarafi, wanda shi ne jaroran qiyayyar aurenta da shi.
Dayake ya riga ya cire hankalinsa daga kanta sai sam bai kula da wani canjinta ba, ba wai haqura yayi da sonta ba, dena neman son da qarfi yayi don ya ga yana da halin nan da ake cewa zafin nema ba ya kawo samu, sannan idan ma yana kawo wa to dai ya kasa samo masa Binta, sai ya dauki matakin nan na cewa abinda ka san ba zaka samu ba to bi shi da ba na so.
Wata safiya ya shiga mata cikin shirin fita kamar yadda ya saba fuskarta babu yabo babu fallasa,tana kwance tana bacci ya farkar da ita da daskararriyar murya,
“Binta, Binta…”
Ta yaye bargo ta juyo ta dube shi kawai, shahararriyar kyakkyawar fuskarsa take qarewa kallo wadda a yanzu ta fi koma taba mata zuciya.
Yayi fuska ya isa bakin durowar gadonta yana gyara fitilar gefen gadon da ya ganta a gicciye,
“Ke dai ban taba ganin raguwa kamarki ba, wai ke ba kya gajiya da bacci ne”?”.
Ta fara yunqurin tashi zaune, muryarta a sarqaqe ta ce,
“To ina da wani abu da ya fi baccin da zan yi ne?”
Dayake ba ya dubanta, hasalima hankalinsa na can kan Nabila wadda jiya ta yi wuni zazzabi da amai, kuma don taurin kai irin nata ta ce sai an boyewa Binta, a jiya bai san dalilinta ba amma a kwanan da yayi zullumin ciwonta da yawan buga mata wayar da yake ya gane inda maganar ta dosa, Nabila na da ciki tana boye musu su duka, farin cikinsa ya hana shi neman dalilin boyewar, murna ya ke kamar zai hau tsani ya sanar.
Wadannan dalilan ne suka sa bai bawa maganar Binta muhimmanci ba bare yayi mata fassara, yana duban agogo ya ce mata,
“Wannan dalilin ya sa wani lokacin kike ba ni tausayi gaskiya, yakamata ki nemi wani aikin ki yi ban da aikin bankin, bai kamata na yi ta takura rayuwarki ba”
Ta gane bai fahimci inda ta dosa ba don haka ta sake zunguro shi,
“Ko wanne aikin zan nema dai ai dole zan yi bacci da dare, ba a can zan dinga kwana ba”
Ya tare ta ba tare da ya fahimci abinda ta so ya fahimtar ba,
“Ai dai an rage, a qalla kin wuni cikin walwala yadda kike so, ki gafarce ni ban hana ki aiki don na zalunce ki ba, in kina buqatar aikin zan ba ki dama”
Binta ta yi tsuru tana kallonsa, alamunsa na nuna lallai da gaske yake, sai ta rasa bakin magana.
“Ni zan wuce, anjima kadan dai zan dawo na kai Nabila asibiti, ba ta ji dadi ba”
“Haka ne, jiya na kama ta tana zazzabi ta boye min”
Ya dan yi dariya,
“Wai na kama ta tana zazzbi”.
Ga mamakinsa sai ga shi ita tana dariya.
Bai dai dada kansa da qasa ba ya fara qoqarin ficewa, sai ga shi ta biyo shi falo da katinan gayyata biyu a hannunta, tana nuna dan tsoro da shayi lokacin da take masa bayani,
“Jiya Hajiya ta aiko mana da saqon gayyatar dinner murnar auren Yaks, jibi ne”.
Ba qaramin jarumta yayi ba wajen boye tashin hankalinsa da jin dacin ransa, yayi fuska kamar babu komai ya ce mata,
“Wai ke da wa?”
Kai tsaye ta amsa a takaice,
“Nabila”.
Ya jima cikin shiru kafin ya daure ya amsa,
“Gaskiya Nabila ba zata ba”
“Don me?”
Ya bata rai,
“To don me ma zata je wani bikin Yaks? Ke dai ki je kawai, amma ita da Yaks ai sai hange daga nesa”
Tana nacewa yi masa kallon nazari, sannan ta qoqarta ta ce,
“Amma dai ko Yaks din ne ya gayyace ta ba mahaifiyarsa ba bai kamata ka ce ba za ta ba…”
Ya tare ta cikin alamun tuhuma,
“Don me?”
“Don kai ka yi nasara shi ya fadi, Game dinsa bai hana ka auren Binta ba hakazalika kai ka sami Nabila shi ya rasa ba, bisa adalcin saka kai in ka rage gaba da shi ba aibu ba ne”
Ya juya kai yana huci,
“Gara da kika ce adalcin saka kai”
Ba ta yi Magana ba.
Ya jinkirta yana kamar yana tunani amma tsabar jin haushin Yaks ke yakushinsa a zuci, haka dai ya danne ya basar ya ce,
‘A yi haquri ba zan iya barinta ba, kin fi kowa sanin ina da kishi, duk abinda na sassautawa rashin iko ne kawai ya katange ni, ni ban yarda a min qwallo da mata ba, ke ki je kawai, bugu da qari ma ba ta da ishasshyar lafiyar da zan bar ta wani gararin biki”
Ya tunkari qofa kai tsaye yana shirin fita, ta ji takaicin ma ko ya tambaye ta wa Yaks zai aura ta ce masa Saratu, don ya ji dadin cewa Yaks ya qare da auren ragowar shedancinsa, saboda tana jin labarin zai iya faranta masa rai ita kuma yanzu tana son abinda zai faranta masa rai komai qanqantarsa, sai dai bai ba ta wannan damar ba har ma ya fice ya bar ta.
Tana jin sa yana hayewa sama cikin sauri, sai ta ji tana neman karaya amma kasaitar jaririn son da ta fara samun kanta ciki ya sa ta ji cewa cikin jarrabawa take, zata ci ne idan ta zama mai sadaukarwa kamar yadda Mujahid da Nabila sauka zama. da sauri ta doshi bandaki domin ta dan kintsa kafin Mujahid ya sakko, ba sai an fada mata ba ta san dole ne ma ya dade.
Ilai kuwa sai da ta yi wanka ta kintsa sannan ya sakko daga saman wai kuma cikin azama yana nuna alamun ya makara.
A bakin qofar dakinta ya same ta tsaye, bai wani dube ta sosai ba, don haka bai kula da annurin da ke fuskarta ba.
“Yaya jikin nata?”
Yayi fuska ya nuna mata qafar benen,
“Da sauqi, zaki iya zuwa yanzu ta samu ta yi wanka”
Bai jira cewarta ba ya nemi hanya ya fice abinsa.
Dole cikin kasala ta kama qafar bene da hawa.
Allah ya saka