Skip to content
Part 7 of 59 in the Series Rigar Siliki by Maimuna Idris Sani Beli

Duk wannan iqirari nata, washegari haka ta wuni sukuku cikin tsananin damuwa, babu wanda ta ke tausayi ko kuma kunyar gani irin Nabila, har ba ta qaunar qarshen mako ya zo Nabila ta zo gidansu, ba ta san me za ta ce mata ba.

Babu kuma wanda ta ke jin haushi kuma ta ji ta yi mugun tsana irin Mujahid, wai har yaushe ne ma zai ce yana sonta? Ita mamakin wannan shegen son mara dacewa ta ke.

An kwana biyu ita da kanta ta kira Nabila a waya.

“Ya ya ku ke Anti?”

Nabila ta tambaye ta cikin murna da ladabi.

“Lafiya mu ke Nabila”.

“Ranar lahadi ai zan zo na gaishe ku”. In ji Nabila.

Dole Binta ta qirqiro murnar dole.

“Da ma tambayar da na kira in yi ke nan, laifin me muka yi aka yi mana yaji?”

Nabila ta qyalqyale da dariya.

“Yaji kuma Anti? Kin san muna tunkarar jarrabawa, dole na dinga zama a gida na yi karatu”.

Binta ma ta yi dariya.

“Haka ne, amma kiin manta musamman ina da laburare a dakina? Sai in tura ki can, ni dai buqatata kawai na ganki a gidanmu. Ina sonki Nabila”.

Nabila ta yi dariyar jin dadin kulawar da Binta ke ba ta, tuni da ma ta san yadda Binta ta damu da ita ko ciki daya suka fito iyakacin yadda za ta damu da ita ke nan.

Cikin siririyar murya ta ce.

“Na gode Anti”.

“Ni ma haka”. In ji Binta.

Suka dan ja fasali dukkansu kafin Binta ta tsinka shirun.

“Nabila kin san wani abu?”

Cikin nuna rashin fahinta tun daga zuciya Nabila ta ce.

“A’a ban sani ba Anti”.

Binta ta dan ja doguwar dariya, ta ce mata.

“Amma dai kin san kina da kyau tamkar zinare ko?”

Nabila ta yi dariya cike da jin kunya, da kuma mamakin wannan yabon.

“Ni din Anti, kuma kamar zinare?”

Binta ma tana dariya ta ce.

“Wallahi za ki iya shiga sahun farko na mata masu kyau Nabila”.

Har yanzu Nabila na dariyar da ta ke bayyana cikin kunya ta ke.

“Kar ki kumbura min kai Anti, don Allah mene ne dalilin wannan zugar?”

“Ba zuga ba ce, kina da kyawun ne kawai, a kan batun mutuminki ne”.

Gaban Nabila ya fadi, sai dai cikin basarwa ta ce.

“Wa?”

“Mujahid”.

Binta ta amsa mata kai tsaye.

Nabila ta ji wani dum, amma ba ta san dalilin da ya sanya ta ji takaici da karaya na neman dame ta ba, ta yi kuma qoqarin ta tanka ko ya ya ne ta kasa har ita Binta ta gaji ta dora.

“Kyanki ne ya sanya shi shakkarki, wai zato ya ke kin fi qarfinsa,  so gabadayansa a rude ya ke…”

Ko kadan labarin nan bai faranta wa Nabila ba, yanzun ma daurewa ta yi ta amsa.

“Sai ka ce ba namiji ba?”

“Ai ke ce kin yi zarra Nabila, kuma mazantakar ke nan, haka mazan ke shan wuya farkon yada manufa”.

Binta ta amsa mata.

Nabila ta jima cikin shiru tana yaqi da takaicinta, tsakani da Allah ta zargi kawai shirin Binta ne wannan waqar da ta karanto mata, waqar ma mara tura kowane irin saqo ba ya ga nishadantar da zuciya ko fada mata abin da ta ke son ta ji.

Suka dinga kokawa ita da numfashinta domin hana wasu qananan nishe-nishen da ke tasowa daga can qasan zuciyarta bayyana a muryarta.

“Anti, don Allah mu rufe maganar Yaya Mujahid”.

“Don me?”

Binta ta tambaya ba tare da ta shirya ba, da alama dabarunta nema suke su kunce, ko nabila ba ta ramfo ta ba, to da alama ta shirya dawowa daga rakiyar Mujahid, idan kuwa haka ta faru ita haqanta ba zai cimma ruwa ba, don Nabilan ba za ta ba ta hadin kan da ta ke buqata wajen jona su soyayya da Mujahid don ita ya manta da ita ba.

Kai tsaye cikin nutsuwa Nabila ta amsa mata tambayarta.

“Duk abin da bai zo ba bai kamata mu dinga salwantar da lokacinmu wajen jiransa ba. Jiya ta wuce, yau ce tamu, gobe kuwa ba mu san ya ya za ta zo mana ba. Saboda haka ban zabi komai akan yadda Mujahid zai zo min gobe ba, don haka na ke cin moriyar yau na”.

Iyakacin hangen Binta ta rasa da kafar da za ta qalubalanci Nabila duk da kuwa in ta dage za ta iya samo qalubalen, sai dai inda matsalar ta ke ita ce, ita kanta ba gaskiya ta taka ba, bare qarya da gaskiyar su yi mata sauqin samuwa. Da qyar daga qarshe ta sauke nishi.

“Hmn! To bari dai na yi shiru, lokacin da ya gama bilinbituwarsa ya furta, sai na shigo sahun ‘yan iza wuta”.

Dariya kawai Nabila ta yi ba tare da nuna alamun za ta tanka ba. Dole Binta ta yi mata sallama ta ajiye wayar a gajiye cikin sauke tashoshin nazari da saurare iri-iri.

Da alama daga yanzu yadda ta ke shan taurin kan Mujahid haka za ta koma shan na Nabila mai azanci da hangen nesa.

Ta ina za ta kubuta? Ta dinga jero wa kanta wannan tambayar amma babu amsa, sai ranta da ya dinga taruwa yana jagulewa yana kuma baci.

Har qarfe sha dayan daren ranar ba ta runtsa bacci ba, kuma da ya ke ma’abociyar son chatting  ce, haka ta dinga hada lissafinta da leqewa kafafen sada zumunci.

Ta haka Mujahid da bai da lokacin zaman leqa kafar sadarwar sai dare ya hango ta online, nan da nan ya tura mata saqo ta whatsapp.

“Salam”.

Ta yi niyyar share shi, amma kasancewar ya zamar mata dankali sha kushe dole ta tanka shi.

“W/salam, muna amsa sallamarka daga sakatiri hosfital”.

Ya aiko mata dariya da tambayar.

“Ke da su wa?”

Ta tura masa.

“Ni da haukana da rashin imanina tare da  matsalolina duka”.

Ya turo mata  amsa mai nuna karsashi.

“Allahu akbar, ai da na ji shiru kwana biyu na zaci kin warke wasu daga ciki, musamman hauka da rashin imanin, don na san da wuya ki rasa matsala”.

Ta ji haushi da kyau, amma haka ta daure ta amsa.

“Babu abin da ya warke, sai ma dai ka zuba ido ka ga qari”.

Ya sake aiko dariya da dori a kai.

“Na bude fallen zuciyata da qwallon kaina, komai ma ya zo in dai daga gare ki ne zan shanye”.

Ta cije maqaqin da qirjinta ya ke, ita ma ta tura alamar dariyar.

“In kuma daga Nabila ne fa?”

Ya turo alamun fushi sannan ya amsa.

“Shi ma in ta hanyarki ne ai dole na yi fuska na cinye”.

“Ina so mu yi maganar gaskiya don Allah Yaya Mujahid”.

Ta tura masa haka lokacin da ta fahinci in ta ci gaba da laqaqi zai furta mata ita ya ke so.

Ta dan jima tana sauraron amsarsa, sannan ya turo mata.

“In kina san gaskiyar ko?”

“Ni dai ba wasa na ke son yi da kai ba, da gaske maganar gaskiya na ke son mu yi”.

Ta hada alamar roqo ta tura masa.

Ba jimawa ya amsa mata.

“Ina sauraronki, Allah ya sa da gaske gaskiyar ce ba ra’ayinki ba, kin san cewa ra’ayi ba lallai shi ne gaskiya ba”.

Ya shiga sauraron cewarta da yaqinin maganar Nabila za ta yi masa, shi ya rasa dalilin wannan jarabar tata na neman yi masa auren dole tamkar wanda ya rasa mashinshiniya. Ilai kuwa sai ga saqonta.

“Kar ka yi saken da za ka rasa auren Nabila Yaya Mujahid, in an yi hakan ba qaramar asara za a yi ba”.

Ya jima yana nazari kafin ya sami abin ce mata.

“Me ya sa in na ce ba ki da imani ki ke jin haushi?”

Ta qara turnuqewa da wani jin haushin, amma haka ta yarda su ci gaba da buga wasan.

“Yaushe na ce na ji haushi? Ai na ga karba na yi rashin imani da haukan da ka goga min har ma da zamowata matsala”.

Ya turo murmushi, sannan ya biyo da cewa.

“Wadannan maganganun naki su suke nuna kin ji haushin, ai wani lokacin kin iya siyasa ba sai lallai kin furta kalma ta ke zama aiki ba”.

Ta ce masa.

“Ko? Tunda na karbi tambarin rashin imani ai kamata ya yi mu wuce wannan gurin, mu dora kan tayin da na yi maka”.

Ya share maganarta da cewa.

“Da ni ne aka ce min ba ni da imani sai na bi ba’asi kafin na karba”.

“Da ma Fatima Binta daban, Muhammad Mujahid daban”.

Ta amsa masa kai tsaye.

Shi kuma ya turo.

“Ba ki sani ba”.

Ta turo masa gatsine.

Bai damu ba ya amsa.

“Da kin tambaye ni qila amsar da zan baki ta jefi tsuntsu biyu da dutse daya, wato ta hado da tayinki gare ni ta amsa”.

Tana ganin wannan rubutun nasa da sauri ta amsa saboda muhimmancinsa.

“In haka ne, yanzu na tambaye ka”.

Ya jima kafin ya turo  cewarsa.

“Kin taba dandanar shauqin so? Da kin taba za ki san cewa duk wanda ya zo da ta’addancin sauya wa zuciyarki akala daga abin da zuciyarki ta ke marari zuwa wanda ba ki taba mafarkiin so ba, ba shi da imani kuma ba shi da tausayi, qila in aka barshi zai iya kisa”.

Wannan karon ita ta jima tana juya maganganunsa kafin ta samo lagonsa.

“Don me za ka yanke hukuncin ban taba dandanar shauqin so ba? Na taba mana, yanzu ma a cikinsa na ke”.

Ba don jarabar dora idonsa a kanta ba, tabbas sai ta ci lagonsa da wannan maganganun nata, amma ya santa ciki da bai a mu’amala da shige da fice, qarya kawai ta ke don ta shatile kafarsa ne, amma ba ta son kowa sai nasa son da za ta fara nan gaba, don haka kai tsaye ya amsa mata.

“Qarya ne ba kya son kowa, so irin wanda na ke nufi, ina dai dab da sa ki a hanya”.

Yanzu kuma ta dauke wuta dif ba ta da niyyar sake tanka masa don duk abin da ta ke gudun ya fada dangane da nuna ita ya ke so ya fada a yau wadannan kalaman nasa. Babu abin da ya rage yanzu sai jiran ya fito fili ya fada, ita ma kuma ta fito kai tsaye ta fada masa ba ta sonsa.

Ganin ta jima ba ta turo masa ba ya haqiqance ba za ta tanka shi ba, tunda yana ganinta online, don haka ya qarasa fashe mata cikinsa duk da bai warware ba.

“Tunda ki ka fara kwaso min maganar Nabila na ke miki kallon ‘yar ta’adda, wadda  ke son sanya kaifin takobi ta fille ran soyayyar da ban fare ta ba sai da na gauraya ta da nawa ran.

Kwatsam a wannan hanyar dai sai na ci karo da wani irina mai soyayya da jinin jikinsa, wato Yaks. Haba Binta, laifin me mu maza muka yi miki da ki ka qi jininmu har za ki hada mu ki yi mana kisan kiyashi irin wannan? Na sha sanar da ke ban fara sona don na daina ba, kuma zan iya komai don na tsira da shi”.

Binta ta dinga juya maganganunsa cikin jin kala-kalar kuka da yunqurin ba shi amsa ko da uwa danya ce wadda za ta yi masa rauni a zuciya, amma sai wani irin in girma da isa ya cunkushe ranta, ta dinga jin shirin qalubalantar wannan  banzan son na Mujahid yana shigarta ko ta ina.

Ba ta yi nisa ba sai da ta tsinci kanta cikin jin matsanancin fushin da ya kai ta rataye lambarsa (blocking) daga farfajiyar sada zumuntarta (whatsapp), ta wurgar da wayar sannan ta rarumi filo ta boye kanta ciki ta fara runtuma kukan da ita kanta ba ta san dalilinsa ba.

Cikin abin da bai gaza minti daya ba, Mujahid ya fahinci abin da ya faru, Binta ta rataye lambarsa, abin saka sanyin gwiwa ne da tararradi, amma shi sai ya ji wani sabon qarfin gwiwa ya shige shi, Binta ta gane manufarsa, ke nan daga yanzu za su bude nasu shafin ko ya yi musu dadi su duka, ko ya yi wa dayansu, ko kuma su dukan su ji a jikinsu, ko ma ya ya ne shi yana maraba don tun daga qasan zuciyarsa ya ke jin qamshin sai ya yi nasara.   

<< Rigar Siliki 6Rigar Siliki 8 >>

1 thought on “Rigar Siliki 7”

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×