“Dama hoto za ka ɗaukemu a wayarka” Ta faɗi tana ɗan murmushi da sunne kai. Ya yi dariya.
“To ku gyara.” Da sauri suka haɗa kai. Ya lalubo Camerar wayarsa ya shiga yi musu kala-kala. Ya yiwa kowacce ita kaɗai.
“Ɗan Biyutiful mu yi hoto.”
Da murmushi yake dubanta. Kawai yarinyar tana burgeshi yana jinta a rai. Ba musu ya juyo don lokacin waya ba Selfie. Ya rasa wa zai ba ya yi musu.
“Can I?” Ya tsinci muryarsa. Murmushi ne dauke saman fuskar mai haɗe da wani rauni na ban mamaki wanda ya zama sabon abu a fuskarsa. Kamar ba zai bayar ba sai ya miƙa mishi.
Hotuna har kala uku ya daukesu.
“Kai ma kana da kyau, taho mu dauka.”
Jamila wacce tuni ta hango su Mama da Hajjo, ta shiga kiftawa Humaira ido amman ko ta kanta ba ta bi ba. Sai dai ga mamakin Jamila, wucewa kawai suka yi da sauri sauri ba su ko lura da su ba. Ta sauke ajiyar zuciya tana mai jin dadin hakan don bata kawo komai a ranta ba.
Ya karɓi wayarsa, girgiza kai ya yi da ɗan murmushin dole ganin idon Adam a wurin.
“No, bana hoto.”
Ta hangame baki kafin ta jinjina kai.
“Hum um!” abinda ta fadi kenan kafin ta dubi Adam.
“Bai bai (Bye bye) ɗan Biyutiful, mungode.”
Yana murmushi ya ɗaga mata yatsu ta ja hannun Jamila suka yi ciki. Haidar wanda ya ji shiru ya fito saboda a cewarsa rainin hankali Fu’ad zai mishi da ya bar shi a baƙin fuska sai rarraba ido yake kamar shege a rabon gado. Cak ya tsayawa yana kallon ikon Allah, Fu’ad da wata yarinya ƴar figigiya, babu komai a kirjin ballantana ya ce shi ya ɗau hankalinsa. Ga dai kyan fuska amman yarinya ce. Har yarinyar ta fice sannan ya maida dubansa ga Adam wanda ke cin magani kamar ya ga kashi.
Adam shima ya bar wurin bayan ya furta kasar thank you.
Ganin haka Haidar ya ƙaraso ya dafa amininsa. Dubansa ya yi kafin ya ja guntun tsaki.
“Ya akai?”
Takaici ya kama Haidar.
“Ya akai? Ka bar ni cikin mutanen da ban san su ba ka cemin ya akai? Wannan ya zama gayyar soɗi. Ba wannan ba, meke samun kwakwalwarka ne kake yin abu kamar ba kai ba wallahi. Duk wani motsinka na nema ya sauya. Ban san Fu’ad da cusa kai inda ba kwarjini ba, ban sanka da kula kowace kashi ba. Mene a jikin waccan tatsitsiyar da ka tsaya kana wani murmushi gabanta, wanda ma kake yin dominsa ba burgeshi ka yi ba? Haba Malam! Wannan ai zubar da class dinmu kake yi.”
Waya kawai yake dannawa sai dai hankalinsa ba’a kam wayar yake ba, babu alamar zai amsawa Haidar, shima bai san me zai ce ba, abu kamar tsafi. Da zuciya daya yake jin kaunar Adam a ransa. A jikinsa yake ji koda Yayansa ne, to kaunar da zai mishi sai haka.
Nan da nan ya kwadaitu da son jin ko waye Adam din. Don haka ya nufi ciki gami da faɗin
“Naji, taho mu yi musu sallama mu tafi.” Nan ma ya kara kashe shi da mamaki, sai dai wannan karon bai furta komai ba.
Suna shiga ya ga Adam bai gurin ya na wajen iyayensu mata suna gaisawa. Wannan ya ba shi damar ƙarasawa mazauninsu ya zauna. Dr Ibrahim ya dubeshi.
“Ah, ai na yi zaton ka tafi.”
Ya na murmushi ya amsa.
“No, ban tafi ba.”
“Ok.” Ya furta kawai.
“Please ina da tambaya ne idan ba za ka damu ba.”
Dr Ibrahim ya gyara zama.
“Me zai sa? Yi tambayarka.”
“Ina son sanin full name na friend ɗinka da kuma address.”
Baki ya saki, sai kuma ya ce.
“Sunansa Dr Adam Hayat Bello. Amman nayi mamaki da ma kake maganar address sai kuma na tuna ba fa mazaunan garinnan bane mu, daga Kano muka zo. Don naga dai inda ka je jiya nan ne gidan kakanninsa.”
Tunda ya ji cikakken sunan Adam, ya yi turus. Sai yanzun yake tuna kamannin Adam din yana ƙarami da kuma yanzun. Ya kara kai kallo inda Adam yake. Shakka babu shi ne! Ta ina kuwa zai ganshi da ƙima? Ya sha zagin Adam din ya ce dukiyar ta ubansa ce Hayat ke juyawa son ransa. Ya sha tofamasa baƙaƙen maganganu, ya sanya Hayat dukansa ya fi a kirga, hakanan Mum dinsa ta sha zagi da aibatashi da mahaifiyarsa. Yanzu ya fahimci dalilin da ya sanya Adam shareshi, ba ya kaunar ganinsa. Shi kuwa tunda har ya ji kaunarsa kamar wani dan uwansa na jini, ba zai rabu da shi ba sai sun yi zumunta. Gani sukai kawai ya miƙa ya dubi Haidar.
“Muje.”
Kafin Dr Ibrahim ya samu abin faɗa har ya yi gaba, dole ta sanya Haidar mikewa ya mara mishi baya cike da rashin sanin taƙamaiman dalilin wannan rainin hankalin da Fu’ad ke mishi. Ya ji ma Yoben ta ishe shi tattarawa zai yi ya koma Kano abinsa.
Adam yana gaisawa da dangi caraf ya ji an riƙe gefen rigarsa. Ya juya don ganin ko waye. Fuskar da ko a cikin mata dari ne ba za ta ɓace mishi ba ya gani. Tana murmushi tace.
“Wai ɗana ne haka ya girma?” Cewar Salma.
Babbar diyar Gwaggo Rakiya, Abu. Ta bata amsa tana washe haƙora.
“Shi ne dai, Adamu.”
Ya watsamata kallo mai kama da harara sannan ya juya ya bar wurin ba tare da ta ci darajar ko gaisuwa ba. Wannan abu ya yi mata mugun zafi, ta ji wani bakin ciki ya tokare ƙahom zuciyarta. Ko su Amira basu ƙi gaisheta ba sai shi. Kwafa kawai ta yi ba ta ce uffan ba.
*****
Inno suna zaune a tsakar falon Hajiya Hafsatu, tare da su Hajiya Hamidah ana hira cikin nishaɗi. Sallamar Hajjo ce fa katsemusu hirar, suka juya.
“A’a, Hajjo kada dai an tashi?” Fadin Hajiya Hamidah, Inno miƙewa ta yi zaune sosai tana duban Mama cike da nazari. Sai a sannan suma suka lura da sauyin kwayar idanun Hajjo daga fari zuwa ja. Kukan kuwa ta kara fashewa da shi, ita kuwa Mama ƙarasawa ta yi ta rungume Inno ta shiga rera kuka. Gaba daya suka daskare ganin ikon Allah. Mama ta zaune ta hau kwatantawa Inno da hannu. Ta nuna kunnenta da baki ta girgiza kai. A rikice Inno ta mike tsaye ta kamo Hajjo.
“Ke, fadamin meyafaru da Maryam? Menene?”
Hajjo ta bada labarin abinda ta sani takara da fadin
“A hanya ma nayi-nayi ta ce wani abu ba ta yi magana ba, sai ta min alama da hannu bata ji bata iya magana.”
“Innalillahi wa inna ilaihir raajiun!” Duk suka dauki salati. Inno sai kuka, ba ita kadai ba sauran jama’ar wurin aka shiga kukan tausayawa Maryam. Ita kuwa baiwar Allah tun tana yi har ya zamana sai hawaye. Hajiya Hafsatu ta mike da sauri ta yi sashin mijinta. Jimawa kadan ta dawo tana duban Inno.
“Ku tashi muje Fatima, ga Alhaji nan zai kaimu asibiti.”
Inno ba musu ta mike tana jan hannun Maryam, sai da aka taimaka aka miƙomata hijabi ta sura suka tafi. Alhaji Lawwali ne ya kai su asibiti mafi kyau a garin. Duk iyakar binciken likitocin basu ga abinda ya jazamata wannan matsala ba. Karshe aka ce su dawo gobe. Da wannan jimamin suka nufo hanyar gidan.
Humaira basu da labari ba wanda ta fadamusu gudun yada hankalinta. An dai ce musu sun fita ne, wannan ta sanya kafin ma su dawo sun yi bacci. Maryam da Inno kam ba bacci su na zaune saman darduma. Inno ta yi niyyar kiran Malam sai dai Alhaji Lawwali ya hanata akan ko mene ta bari su koma asibitin a ji sakamako. Da ta kalli gefen da Maryam ke zaune saman darduma sai wasu sabbin hawayen su zubo kuncinta. Haka har bacci ya ɗauketa.
*****
Wurgi ya shiga yi da duk abinda hannunsa yakai kai, kafin can ya zauna ya nutsu yana huci. Hakan ya saba a duk sadda suka yi faɗa da Haidar. Yanzun ma kaca-kaca suka yi sai da Salma ta taushi Haidar ta ba shi wani ɗakin domin ya kwana. Koda ta dawo ba irin kwankwasawar da ba ta yi ba Fu’ad ya ƙi buɗe mata. Sigari ya ciro a dirowar gefen gadinsa ya kunna da lighter. Zuƙarta yake har ta hauka ga goshinsa na fidda jini alamar ya taɓa rauninsa. Zafi biyu ne ke nukurkusar zuciyarsa. Da na Haidar, da kuma Adam wanda ke wulakantashi akan abinda ya faru zamanin kuruciya.
Haidar ya matsa da zaginsa akan shishshiginsa, a karshe ya huce haushi a kansa ya zazzageshi, nan kuwa suka hau cacar baki ya kai su da soma bugun juna. Mum ce ta raba faɗan ta rabamusu makwanci.
*****
Ranta idan ya yi dubu ya ɓaci jin cewa wai duk akan tsinannan yaronnan ne Adam ake rikici a gidanta. Ta kuwa ji kamar ta kamo Fu’ad ta mishi duka.
“Ya zama tilas mu bar garinnan. Gobe gobennan zamu tattara mu koma Kano. Ba zan iya daukar wannan tozarcin ba.”
“Ya fi dai Mum, nima na gaji nawa iyayen su na jirana a gida. Ba yaronki bane da za ki dinga sanya ni a gaba sai na lallaɓamaki Fu’ad kamar ni na haifarmaki shi. Mtsww.”
Fadin Haidar yana yankwane fuska. Salma ta ɗan dafa kafaɗarsa da rarrashi.
“Sorry my son, ai gobe zamu tafi. Kada ka damu, ina mai ba ka hakurin abinda Fu’ad ya yi maka. Zan kuma sanya shi ya ba ka hakuri.”
Ya taɓa baki gami da ɗaga kafaɗa.
“Ok, tafi zan kwanta please, kaina ya yi nauyi.”
Maimakon ranta ya ɓaci, sai ta miƙe tana murmushi. Ta shafi kansa
“Goodnight my son, sleep well.”
“Thank you.” Ya faɗi da ɗan murmushi sannan ta fita.
*****
Zaune yake gaban Engineer Bello da Malam Kabiru ya je musu sallama akan zasu wuce Kano tare da Dr Ibrahim bakin aiki. Maganar aure suka yi mishi sosai.
“Idan ma ka yi kwantai ne, ka zo ka duba cikin ƴan uwanka.”
Engineer ya ƙarashe da dariya Malam na tayashi. Shi kam Adam murmushi kawai yake wanda bai kai zuci ba. Ba ya son maganar auren, har ga Allah bai ta6a soyayya ba saboda ba shi da budurwa. Shigowar Dr Ibrahim ta sanya aka bar zancen, gaishesu ya yi suka yi musu fatan alheri sannan suka fice. Tuni dama sun yi sallama da mutan gidan.
Ya bar Yobe cike da tunani kala-kala. A gefe guda ga wani irin kewa da yake ji na Baiwar Allahn da bai san ma takamaiman garin da take ba. Abu daya ya sani game da ita, dangin Amaryar Huzaifa ce. Banda wannan bai san komai ba. Asalima yarinyar ƙarama ce don haka ba zai ce kewarta da yake yi ba So ne.
“Ya dai? Naji shiru ina ta magana.”
Ya dubi Dr Ibrahim.
“Ba komai, kasan kuwa tsofaffinnan sun matsamin game da batun aure. Wai idan ma ban fiddo ba to a dangi na zo na zaɓa.”
Murmushi Dr ya yi.
“Daidai kenan ai. Nima na gaji da ganinka haka wallahi. Haba, haihuwa ta biyu fa za’a yimin amman kai kam aurenma ba ka da niyyar yinsa.”
Ya ja guntun tsaki.
“Auren ne tsoronsa nake wallahi. Bana son tashin hankali. Ba kuma na son na auri wacce bana so, kamar yanda bana kaunar na auri wacce ba ta sona. Duka biyun nan suna da matsala Dr.”
Dr ya jinjina kai.
“Hakane, ka faɗi gaskiya. Kowanne da nashi disadvantages din. Allah Ya zaɓamaka mace ta gari.”
“Ameen.”
“Ka ji yanda mukai da mutuminka ba ka ce komai ba.”
Murmushi Adam ya yi.
‘Dama ai rashin sanin waye ni ne tun a farko.’ Ya fadi a ransa sai dai bai ce komai ba a fili, karshe ya share zancen ya shiga wani.
*****
Yinin ranar sun yi zirga-zirgar asibiti har kusan uku amman ba maganar sauki a lamarin Mama. Alhaji Lawwali ya ce su je wani asibitin a gani. Girgiza kai Inno ta yi tana share hawaye.
“Um um Alhaji, wannan lamari na Maryam ba na asibiti bane. Ku bari dai na kira Malam don Allah.”
“Haba Fatima, kar ki karaya har haka. In sha Allah za’a dace.”
Hajiya Hafsatu ta tareshi.
“Um um Alhaji, da gaskiyar Fatima. Yanzu kam na yarda lamarin nan ba na asibiti bane. Ba ka ganin yanda duk wani gwaji da za’ayi cewa ake ba’a ga komai ba? Ka bar Fatima ta kira Malam din dai. Ko me zai ce shikenan.”
Da wannan damuwar suka dawo gida. Humaira wacce tuni labari ya risketa, ta ruga a guje ta rungume Mamanta tana kuka da sheshsheka.
‘Allah Ya ƙara.’ Fadin Ameena a ƙasan ranta.
Maryam wacce hawayen ma sun daina fita kawai tsintar kanta ta yi da ajiye kawaici ta rungume diyarta suka nufi ciki kanta a ƙasa. Tana jin kanta kamar wata bare a cikin masu dangi da iyaye. Ita kam ba ta san ko wacece ita ba.
Inno ta kira Yaron Malam ta wayar Hajiya Hafsatu, ya haɗata da Malam. Komai ba ta rufemasa ba, ta yi mishi bayani.
Ya yi salati, karshe ya ce kada su sake su taho, yana nan zuwa Yoben a gobe. Da haka suka yi sallama hankalinta ya ɗan kwanta.