Ya ji maganar tamkar saukar aradu a kunnuwansa, a gigice ya yi miƙewar da bai zata ba.
“Ba ki da hankali!”
Daga ɗaya ɓangaren Halima ta kwashe da dariya kafin ta nutsu.
“Matsoraci ba ya zama gwani Yallaɓai. Wannan ai umarni ne ba wai alfarma nake nema ba ko wani abu. A’a Hayat, ya zama dole ka aureni nima naji abinda Salma ta gani har ku ka iya kashe ALHAJI HAISAM ZAKARIYYA saboda cimma burinku.”
Yanda ta furta maganar har sai da ya tsargu ya ƙarewa ofishinnasa kallo wai ko wani yana tsaye yana sauraronsu sai dai ba kowa sai shi din. Tsabar rudewa ma ya manta a waya suke, dodon kunnensa kadai ke jin sautinta.
“Look Halima, ya kike neman wasa da hankalinmu? Ina ce mun kashe magana da ke? Mene naki na dawo da hannun agogo baya? Please don’t.”
“Hum, Hayat ba ka sona ne? Ko ban kai a so Ni ba? Kasan dai Salma ba ta kama rabin ƙafata ba a kyau. Hayat zan jiyar da kai abinda Salma ba ta ta6a…”
“Ya isheni! Kamar kin manta wace Salma a wurina ko? Salma rayuwata ce! Akan Salma na aikata abubuwan da ko a mafarki ban zaci zan aikata ba, don haka ki kiyaye harshenki akan Salma.”
Ta yi ƴar dariya.
“Koma mene, auren Magaji ba zai hana na Magajiya ba. Ya zame maka dole ka aureni Hayat, wannan shi ne matakin karshe na rufin asirinku. Idan kuwa ka bijirewa umarnina, ba sai na faɗamaka abinda zai biyo baya ba. Na ba ka nan da kwana uku, duk abinda ka yanke ina jira.”
Tana kaiwa nan ta katse wayar tana huci, HANAN wacce ta ci uban kuka ta dubeta.
“Wai Halima mene haka? Na zo miki da maganata kin wani watsar a bola? Damuwarki kadai ce damuwa?!”
Halima wacce gaba ɗaya a tunzure take ta lailayo ashar ta narkamata tare da fadin.
“Don ubanki ni ba uwarki bace?! Bariki ta bude miki ido da yawa da har bakya ganina da gashi ko Hanan? Kin manta dole sai kin bini za ki shiga aljanna?”
Dariyar rainin wayo Hanan ta yi.
“Hakayake Halima Badar! Ni Hanan haihuwar bariki rainon barikin kike cewa aljannata na karkashinki? Kin taɓa koyamin koda harafin A ballantana na saka ran na iya karatun Fatiha? Aikin banza kawai!”
Maimakon ta tsawatar sai ta yi kwafa ta zarce da maganar da ke cin zuciyarta.
“Hayat sai na aureka koda kuwa duk abinda na mallaka zai ƙare. Ai karen bana shi ke maganin zomon bana! Idan ka san wata ba ka san wata ba!”
Jin haka Hanan ta matso kusa da ita.
“Me za ki yi mishi Halima? Nima fa akwai tawa matsalar. Ki haɗa ki mana gaba ɗaya. Nima auren nake so”
Halima ta ja tsaki.
“Banda abinki Hanan nawa kike da za ki kashewa kanki kasuwa da zancen aure yanzu? Kar ki ƙara tada zancen ma. Ni ki dubeni, yanzu Bariki ta daina yayina, na zama wata gyatuma a Bariki, ba wanda ke yi da ni kinga kuwa idan ina son samarwa kaina lafiya toh nayi aure kawai.”
“Lallai me kike nufi toh?! Sai nima na zauna na tsufa a bariki yanda ki ka yi? So kike na shiga bulayin neman mijin aure idan na kawo shekarunki? Toh wallahi ba ki isa ba! Yanda za ki yi auren nan nima haka zan yi shi. Ba za ta saɓu ba bindiga a ruwa ehe!”
Jin haka Halima ta janyo jakarta gami da dauko sigari ta kunna sai da ta bisa hayaƙin sannan ta dubeta dakyau.
“Waye shi wanda ku ka haɗu? A ina yake?”
Da zumuɗi ta labarta mata duk yanda suke da Fu’ad. Jin ba ta ma san gidansu ko wani kwakkwaran bayani game da shi ba ya sanya Halima jan tsaki.
“Ba son shi kike ba, kawai kina kashe gobarar da ke ƙasanki da shi ne. Ba ki biyo halina ba sam! Domin ni ba kowane shege ne abokin tarayyata ba.”
“To wallahi wannan ma ɗan babban gida ne don ko makaho ya shafa ya sani. Bari ma kiga hotonsa.”
Jiki na rawa ta bude wayarta ta nemo hoton Fu’ad da tayi mishi ba tare da ya sani ba ta miƙa wa Halima. Halima tana ganin hoton Fu’ad ta saki baki.
“Ke! Wannan ai Fu’ad ne ɗan Hayat da muka kammala waya yanzu.”
Hanan ta yi ƙasaƙe tana dubanta. Sai kuma suka yi wata shewa suka cafke kamar wasu sa’annin juna.
“Tabɗijan! Za’a yi tsiya anan! Ai ki kwantar da hankalinki, muddin na shiga gidan Hayat kamar kin auri Fu’ad kin gama. Wallahi ba boka ba malam, don mu shegun kanmu ne. Muna da makamin da ya fi wannan!”
Hanan tsabar murna sai ta rungume uwar suna jin kamar duniyar don su kaɗai aka yi.
*****
Shiru ya yi yana duban wayarsa, yanzun ba jimawa suka gama waya da Uncle Hashim yana bukatar ganinsa a karshen satinnan. Kuma ya san tatsuniyar gizo ba ta wuce ta ƙoƙi. Batun dai na aure ne za’a yi mishi. Ya zai yi toh? Har yanzun bai ga wacce yake da ra’ayin auren ba, babu soyayyar kowace mace a ransa.
‘Har ita?’ Cewar wani ɓangare da zuciyarsa. Ya dauki wayarsa ya shiga sarrafata har ya isa kan hotunansu. Kallonta yake, duk da karancin shekarunta, ba karamin matching ya ga sun yi ba. Wushiyarta ya burgeshi. Ga dimple dinta wanda sak irin nasa. Yana jin kamar yana sonta sai dai ya san soyayya ce ta domin Allah yake mata kamar irin wacce yake yiwa Amira. Kallo sosai yake yana murmushi, ya shagala da har bai ji sallama ba sai wayar da ya ji an zare daga hannunsa. A ɗan firgice ga dubeshi, Dr Ibrahim ne. Zai warce ya yi azamar kauda hannunsa yana dariya.
“Soyayya? Yau soyayya ce ta samu gurbi a zuciyar Dr Adam?” Unbelievable.”
Ya dafe kai gami da jan tsaki.
“Soyayya da yarinya sa’ar Kanwata? Kasan dai da ace aure ne ma irin na kauye da ka haifeta.”
Dr Ibrahim ya sa dariya gami da ajiye wayar.
“Kai fa ɗan iska ne, wannan na haifa? We are just 31yrs fa. Oops! Ashe ƙauye ka ce.”
Murmushi Adam ya yi.
“Amma fa kyakkyawa ce. Za’a yi mace anan daga..”
Adam ya fisge wayar da sauri yana harararsa. Dariya sosai ya sanya Dr Ibrahim.
“Ashe har kishi ya aureka.”
Ya kuma ji kamar hakan ne amman sai ya yi ta maza.
“Ba gurbin wannan a raina. Na fadamaka kamar Amira nake kallonta.”
Dr Ibrahim ya gyaɗa kai yana taɓe baki.
“I see.” Daga nan ya kauda maganar suka faɗa zancen da ya shafi aikinsu.
*****
Ta shirya tsaf cikin riga mai gajeran hannu ruwan ƙasa, sai ta ɗora dark brown riga a samanta mai tsawo har kaurinta. Farin hijab ta sanya karami sai Safa da Takalmi. Tana yi idan bai yi daidai ba Maryam na cin gyaranta. Murmushi kawai take tana kallonta, yarinyar ta yi kyau ta yi ƙiba abinta. Itama kallon Maryam take har bata san sadda kwalla ta ciki idanunta ba. Ta rungume Maryam tana fadin.
“Mama yau zan soma zuwa makaranta. ” Sai da ta furta sannan ta tuna da cewa ita kadai ta ji abinta. Maryam ta dafa kanta ta yi mata adduar da Annabi s.a.w ya koyar nemawa yara tsari.
“U’idhukuma bi-kalimati l-lahi t-tammati min kulli shaytanin wa hammatin, wa min kulli aynin lammatin.”
Ta fadi a kasan ranta sannan ta ɗagota ta share mata fuskar. Juyawa ta yi ta dauki littafi daya da Humaira ta bata a litattafanta don su dinga communicating.
“Kar ki manta da addu’a. Ki je ki gaida su Gwaggo da Malam.”
Ta gyada mata kai, sannan ta fice. Kowa ya yi mata fatan alheri. Malam har kudin kashewa ya bata sannan Baharu ya shigo suka tafi.
Ranar farkon zuwanta makaranta sai ta ji ta kamar a wata sabuwar duniya, sai ɗari-ɗari take. Yarinya ta farko da ta soma kulata sunanta Fauziyya Habib. Sai ta biyun Maimuna Naseer wacce aka fi kira da Meema. Tun daga ranar suka dinke kamar dama can sun san juna.
*****
Sai da ta cinye sati tana zuwa makaranta kuma Alhamdulillah tana fahimta. Ranar Asabar tana zaune ta tisa littafin da aka bata aiki a gaba, ta rasa gane ta inda za ta soma, ta dauki littafin zuwa sashin Gwaggo don ba ta son tashin Mama da ta sha maganin wurin Malam tana bacci.
“To yanzu ni Indo ina ni ina sanin wannan bokon naku? Ki shiga can wurin su Haulatu ko za ki ci sa’ar ganin Yusuf sai ya gwada yi miki.”
Yusuf jikan Gwoggo Hannatu ne wanda ke zaune wurin Engineer. Tun zuwanta ba ta ta6a shiga ko’ina ba a gidan banda bangaren Malam ba. Ita Yusuf din ma ba ta sanshi ba.
“Humaira, ajiye littafin ki fita daga wannan kofar ki shiga kofar da ke jikinsa, ki ce Yusuf ya zo inji Gwaggo.”
Yaha ta faɗi tana aikin tsinkar zogale. Humaira ta koma ta sanya hijabi saman doguwar rigar atamfarta ta fita.
Kai tsaye ta shiga gidan Engineer ba tare da ta lura da motar dake fake a kofar gidan ba. Shi kuwa daidai lokacin ya kashe motarsa ya fito, bayanta kawai ya gani ta shige gidan Engineer bai kawo komai ba ya nufi bangaren Malam Kabiru.
Da siririyar muryarta ta yi sallama aka amsa. Su Baba Hindu dake tsakar gidan ta gaida, kallon baƙuwar fuska suke mata.
“Kamar yarinyar baƙuwar gidan Malam.”
Fadin wata Abulle kanwar Baba Hindi, itama ta ta6a shiga ta ganta ne a gidan take jin labarinsu. Humaira ta kai dubanta gareta. Nan take ta gane fuskar. Ita ce mai kitson da ta yiwa Yaha kwanaki.
“Eh ni ce, Gwaggo ce ta aiko ni na kiramata Yusuf.”
“An aikeshi, idan ya zo za’a fadamasa.” Ta amsa da toh sannan ta kama hanya za ta fita. Idanun Engineer a kanta, itama haka kawai sai ta ji tsohon ya burgeta. Ba ta san ya akai ba sai tsintar kafafunta ta yi sun doshi inda yake. Tana zuwa ta durkushe ta gaidashi. Ya amsa fuska a sake.
“Yarinya daga ina?”
Sai ta ɗan yi jim don ta rasa ma ya za ta kwatanta, Allah Ya taimaketa Baba Hindu ta shigo. Nan ta mishi bayanin da ta tsinta a bakin Abulle.
“Sannunki kinji, Allah Ya ba mamanki lafiya.” Ta amsa da ameen tana murmushi kafin ta tashi ta fita.
Kanta na ga kallon takalma kafarta sabbin dal silifas wadanda Baba Hashim ya siyamata. Ba ta yi aune ba ta ci karo da mutum. Ja ta yi da baya gami da ɗaga kai. Suka dubi juna, ta saki baki da mamaki. Shi dinma bakin ya saki.
“Gorgeous, me kike a gidanmu?”
Ta tabbatar shi dinne.
“Dan biyutiful, dama gidanku ne?” Ta ƙarashe tana wangale haƙora, shima sai ya ɗan murmusa har lokacin fuska cike da mamaki. Ya tuno hirarsu da Umma ta waya, ya nuna gidan Malam Kabiru da yatsa.
“Wai kada ki cemin ke ce Mamanki ba lafiya a gidan Malam?”
Ta gyada kai fuska a raunane. Tausayinta ya kamashi, tarihinsu dama sosai ya girgizashi. Yanzun kuwa da ya san cewar Gorgeous dinsa ce sai abin ya ƙara sosa zuciyarsa. Ba ta san hawaye take fitarwa ba sai da ta ji tattausan hannunsa a saman fuskarta yana sharemata su. Ta dubeshi, ya yi durkuso a gabanta.
“To mene na kukan? Ba fa ya miki kyau. Sai ki koma kamar wata horror.”
Murmushi ta yi ganin ya kashemata ido daya.
“Allah Ya bata lafiya. Naji kina zuwa makaranta ko? Ki dage toh da karatun.”
“Toh.” Ta amsa itama tana bin shi da murmushin.
Ya mike tsaye.
“Oya, tafi ki jira yanzu zan zo sai na tayaki homework din.”
Da murnarta kuwa ta amsa sannan ta fice. Ya bi bayanta da kallo yana jin wani irin farin ciki da bai san iyakarsa ba. Da wannan farin cikin ya karasa ciki suka gaisa. Nan ma magana ɗaya aka kara yi mishi kan aure har ana kiransa tuzuru. Haka ya toshe kunnuwansa ya fice.
Yana komawa ya dubi Humaira dake zaune tana jiran zuwan Yusuf da kuma shi.
“Taso ki rakani wurin Umma.”
“Toh karatun fa?” Fadin Gwaggo.
“Zan koyamata a can. Yaha ga amanar Mamarmu zamu je mu dawo.”
Tana murmushi ta amsa
“Ai ko baka faɗa ba ɗana. A gaidamin yan biyuna.”
Ambaton ƴan biyun da ta yi ne ya ankarar da Humaira gidan da zasu je, wato wurin su Amira. Nan da nan fuskarta ta cika da farin ciki. Koda ta leka Mama ba ta farka ba don haka ta sanya silifas dinta suka fice. Gaban motar ya bude ta zauna kafin shima ya shiga su kama hanya.
Dan biyutiful, kaine Yaya Adam ko?”
“Ba tare da ya dubeta ba yana murmushi ya amsa.
“Um.”
“Amira ta cemin tana da Yaya likita, sunansa Yaya Adam. Kuma na tuna a wurin party naji an ce maka Adam.”
Murmushi sosai yake.
“Ni ne, amma kar ki sauyamin suna daga ɗan biyutiful.”
Ta yi dariya tana ɗan lilo da ƙafa duk cikin rawar kan za ta je unguwa.
“Ai nima Mama ta ce Likita take so na zama. Idan na zama likita ita zan soma yiwa aiki ta dawo tana magana da ji.”
Tausayinta ya sanyashi kallonta, gaba daya ta yi narai-narai da fuska. Iyakar gaskiyarta take maganar. Ya kauda kai.
“Za ta warke in Sha Allah, addu’a zamu yi ta yi. Ba kuka ba kinji ko?”
“Toh.” Don ya ɗaukemata hankali, ya dau wayarsa ya lalubo hotunansu ya miƙamata. Karɓa ta yi tana gwalalo idanu.
“Lah, wallahi mu ne. Kaga mun yi kyau.”
Ta ba shi dariya.
“Yes, mu ne. Mun yi kyau sosai ko?”
“Eh wallahi, amma ka fi ni hanci da kyau. Ji fa, kumatunmu iri daya, har lotsawa suke saboda girma.”
Adam me zai yi ba dariya ba har da gyara zama. Ta ji ƴar kunya don ta gane kamar ta yi katoɓara. Baki ta ɗan turo kamar zata yi kuka.
“To me nace?” Ta furta a shagwaɓance. Ya girgiza kai yana mata kallon da kwanyarta da karancin shekarunta sun yi kaɗan su fassara don haka ta kauda kai tana maidawa kan hoton.
“Ba ki ce komai ba Gorgeous, amma ba yawa suka yi mana ba. Halittarmu ce haka. Idan muka yi dariya ko motsi da bakinmu sai ya fito.”
Ta saki fuska gami da faɗin.
“Au, na tuna ma haka Inno ta cemin. Kaga har wannan ma ta ce halitta ta ce haka.”
Ta ƙarashe tana washe haƙora gami da nuni da wushiyarta.
Ya lumshe ido yana mai kauda kai da sakin murmushi. Wata kasala na saukar mishi, Humaira na zagaye ra da zuciyarsa a hankali tana zamowa farin cikinsa.
Har suka isa bai ƙara cewa uffan ba, ita kuwa sai kallon hotunan take, sau ɗaya ta ja ta ga ya yi gaba sai ta ci gaba da kallo har da wanda ba’a sanyata ba.
Yes