Wani katafaren gida ne wanda ya sha fentin fari da ruwan toka. Gida ne da kallo daya za ka yi mishi kasan an kashe maƙudan kuɗaɗe wurin ginashi.
Babban mutum mai kimanin shekaru Arba’in da uku ne tsaye yana faman safa da marwa a cikin kayataccen falon wanda ya tsaru iyakar tsaruwa, falo ne mai girma da yalwa, an yi mishi ado daidai misali wanda ya kara fiddoshi. Zaune saman kujera mai zaman mutum uku, wata baƙar mace ce wadda kallo daya za ka yi mata ka fahimci Kanuriya ce sakamakon irin suturar dake jikinta da kuma yanayi na adonta.
Daga matar har namijin fuskokinsu babu ko digon walwala. A haka Maigadi ya yi sallama a kofar shiga falon. Da sauri Dattijon nan ya amsa gami da yi mishi iznin shigowa. Ya ƙaraso, cikin girmamawa ya ce.
“Ranka ya dade kana da Baƙo. Yace a fadamaka Gwask…”
Ai bai karasa ba Mutumin ya saki fuska gami da fadin.
“Maza ka ce ya shigo.”
Jin haka Maigadi ya juya ya fita, Mutumin ya dubi Matar fuska cike da fara’a.
“Alhamdulillah, yanzu zamu ji kyakkyawan labari.”
Itama cike da murna ta gyaɗa kanta tana dariya. Kafin ta samu abin cewa Gwaska ya shigo da sallamarsa. Suka dubeshi ba su ko damu da amsawa ba.
Mutumin ya karasa gareshi.
“Gwaska! Ina fatan kwalliya ta biya kudin sabulu?”
Jin haka Gwaska ya yi shiru ya sunkuyar da kai, nan da nan annurin fuskokinsu ya dauke. Matar ta miƙa tsaye a rikice itama ta matso.
“Kana nufin akwai matsala kenan?”
Ta furta cikin rawar murya. Gwaska ya dubesu.
“Oga an samu matsala, mun nemi matarnan sama da ƙasa mun rasa.”
Jin wannan ya sa Mutumin shaƙar wuyan Gwaska, kusan hankali tashe ya soma magana.
“What do you mean?! Kar ka soma bani labarin wanzuwarta a doron ƙasa! Ban biyaku maƙudan kuɗaɗe ba don ku tseratar da ita ba. Na baku domin ku kasheta! Ku kasheta da abinda ke cikinta!”
Ganin dagaske Mutumin ya fice a hayyacinsa, ya sanya matar daka mishi tsawa.
“HAYAT! Ba ka da hankali ne?! So kake kaima a kashe ka za ka yi kisan kai?”
Jin haka Hayat ya saki Gwaska gami da hankadashi. Ai Gwaska yana ganin ya kuɓuta ya hau tari ba ƙaƙƙautawa. Matar da saurinta ta ƙarasa saman tebur ta dauki ruwa ta miƙa mishi. Ya karɓa kuwa ya kwankwaɗe yana maida numfashi.
Wanda aka kira da Hayat ta dubi Matar hankali a matukar tashe.
“SALMA! Ya kike ganin zamu yi? Maryam fa bata mutu ba kenan! Tana nan da rai. Kada allura ta tono garma!”
Ya karashe yana mai cire hular kansa ya yi cilli da ita wata kusurwar. Salma ta dubi Gwaska.
“Kana iya tafiya, sannan ina mai gargadinku da ku kama bakinku. Kar ku kuskura wata magana ta fita ta wajenku.”
Gwaska ya gyaɗa kai.
“Ba ku da matsala, tuba nake.”
Ba wanda ya kulashi cikinsu har ya fice daga falon, a rayuwarsa ba abinda ya tsana irin ya ɓatawa Ogansa rai, ko ba komai ya yi mishi abinda iyayensa basu yi gareshi ba. Ta maida dubanta ga Mijinta wanda gaba daya ya ruɗe.
Kama hannunsa ta yi ta zaunar tana murmushi wanda ya ba shi mamaki.
“Kar ka damu Hayat.”
Ya gushe hannun yana mai zaro mata idanu cike da hargagi ya ce.
“Kar na damu? Kin san me kike fada kuwa? Abu yana barazana da rayuwarmu za ki ce kar na damu? Kanki daya kuwa?”
Ta dan daure fuska.
“Na fi ka damuwa da abinda zai ta6a zaman lafiyarmu. Ka tuna kai fa ba kai rabin abinda nayi ba, Ni ya cancanta na yi wannan samuwar ba kai ba. Na riga da na rufe wannan babin. Bamu da matsala kwata-kwata domin kuwa na shiryawa hakan.” Ta karashe da kwantacciyar murya.
“Dama kinsan hakan zai kasance ne?” Ya nemi ba’asi.
Wata shu’umar dariya ta yi.
“Malam Bulama ya fadamin kwanaki, ya tabbatarmin ba zamu ta6a iya kashe Maryam ba. Tun a lokacin na tsorata, nace to menene mafita? Nan da nan ya bani shawarar ɓatar da ita ta yanda za a nisanta ta daga garemu, ta kasa tuna komai na rayuwarta. Da wannan shawarar na bar wurinsa inda na tabbatar mishi zan koma na biya dukkan abinda ya dace idan ya so sai ya yi aikin.”
Hayat jin hakan ya numfasa, a sanyaye ya ce.
“Amma meyasa kika barni na wahala? Da bamu sa Gwaska sun wahala ba.”
Salma ta murmusa.
“Na bari ne naga gudun ruwansu, nayi zaton za’a iya kasheta sai yanzu na tabbatar da maganar Malam Bulama. Tunda anyi haka yau ba gobe ba, zan je na sallameshi don ya soma gudanar da duk abinda ya dace kafin mu wayi gari mu ganta a garin nan.”
Jin wannan sai Hayat ya murmusa gami da kwantar da kai saman kujera yana murmushi.
“Har na samu nutsuwa.”
Sukai dariya. Daidai lokacin aka banko kofar falon, gaba daya suka maida dubansu ga wurin a firgice, fuskarsa babu alamun fara’a, bai ko kallesu ba ya soma tafiya yana taka matattakalar bene.
“FU’AD! FU’AD!”
Hayat ke kiransa sai dai inaa, ko alamun juyowa bai yi ba. Ganin haka Hayat ya dubi Salma bayan ya mike tsaye,
“Yau ma an taba ɗannaki a makaranta ga dukkan alamu, aiki ya sameki.”
Murmushi ta yi.
“Kar ka damu, wuyarta ya ji batun komawarmu London.”
Suka yi dariya.
Rumfar Malam
Malam hamdala kawai yake yana ƙarawa sa’ilin da Matarsa Fatima ta ɗora kyakkyawar jaririyar saman hannunsa. Cikin natsuwa ya dubi Fatima.
“Ki tambayoyin mahaifiyarta, wane suna take son a sanyawa diyarta.”
Fatima ta amsa sannan ta koma ciki da sauri inda Maryam ke zaune tana jiran Safiyya matar Aliyu ta gama hada ruwan wanka. Cike da raunin zuciya ta amsawa Fatima yayinda ta gama sauraronta.
“Mahaifinta zai ji dadi idan na kirata da A’isha Humaira.”
Da murmushi Fatima ta koma ta sanarwa Malam. Nan da nan ya yiwa jaririyar huɗuba da A’isha Humaira. Kulawa sosai Maryam ta samu daga bayin Allahn nan. Yanda suke mata ji take kamar tana gaban iyayenta ne. Kuka kam duk sadda ta keɓe sai ta yishi. Tana ganin irin yanda suke gudanar da rayuwa a wahalce, amman hakan bai sa sun fasa bata kulawar da ta dace ba.
Kwananta shida da haihuwa ta gama karantarsu, dagaske suna fama da rashin kuɗi sai dai hakan bai sa musu mutuwar zuciya ba. Koyaushe cikin fita nema suke yi. Fatima saƙa take yi, sai ta yi huluna da riguna masu kyau ta ba babban ɗanta, Yaron Malam ya fita can kasuwar garin da ke makwabtaka da su, Garin Shanu, anan zai siyar da duka. Hakanan Malam yake sana’ar ƙira yana fitarwa duk ranar kasuwa. Daidai gwargwado suna samun abinda zasu ci safe da dare. A gefe guda ga kiwon Tinkiya da zabbi. Rayuwarsu dai Alhamdulillah. Duk yammacin juma’a matan aure Fatima da suke kira Inno, ke koyarwa a gidanta. Yayinda sauran ranaku idan an cire Alhamis da Juma’a to yara kananu ne mata da wasu cikin ƴanmatan Rumfar Malam.
Ta yi nisa cikin tunani har ba ta ji sallamar Inno ba. Sai da ta ta6a ta kafin ta yi firgigit ta dubeta, kunya ta kamata ta sunkuyar da kai ta maida hankali ga ba diyarta nono.
Inno ta ajiye Akushin tuwo a gefe kafin ta dubeta cike da kulawa.
“Haba Maryam, meyasa haka? Ki daina wannan yawan tunanin domin tunani bai ta6a zama mafita ga damuwa ba. Ki sani babu abinda ya fi karfin Ubangiji. Ki godemiShi a duk yanayin da kika tsinci rayuwarki. Maza ga tuwo nan, ki samu ki ci don Allah. Rashin cin abincinki ba shi zai ɗaukemaka dukkannin damuwarki ba.”
“Toh Inno, na gode Allah Ya biyaku da aljanna mafificiya.”
Da murmushi Inno ta amsa ta kara da fadin ai ɗa na kowa ne hakanan musulmi dan uwan musulmi ne a ko’ina.
Cikin salasainin dare suna tsaka da bacci ta ji kamar an kwadamata guduma a kai, ba shiri ta mike zaune a firgice tana ambaton Allah. Kan nata ya ci gaba da sara, ta rikeshi gam tana addu’a a hankali har ya soma daidaita sannan ta nemi wuri ta kara kwanciya, ba ta san dalili ba, hawaye ta shiga zubarwa tana yi tana duban ɗiyarta da ke bacci. Ji tayi kamar komai na kwakwalwarta an kwashemata, ta yi- ta yi ta tuna wani abu da ta sani cikin tarihin rayuwarta amman ko sunan mutum daya ta kasa tunawa balle akai ga sanin kusancinsu. Da ta gaji ta runtse idanu, haka har bacci kakkarfa ya dauketa. Kusan ba ita ta tashi ba sai da kukan Humaira ya cika dodon kunnenta. Kasancewar tana jinin biƙi, ya sanya Inno ba ta matsamata ba. Tashi ta yi dakyar, a hankali kuma ta bar jin wannan ciwon kan, cike da kasala ta sanya hannu ta dauki Humaira ta soma shayar da ita. Sai da ta ƙoshi kafin ta sanyata a kafaɗa tana shafa bayanta kamar yanda Inno ta koyar da ita, har sai da ta ga ta yi gyatsa sannan ta kwantar da ita a cinyarta tana dubanta. Sai alokacin ta lura da sauyin suturar dake a jikinta wanda hakan ya tabbatar mata Inno ta wanketa tas. Idanun yarinyar a rufe tana sauke numfashi a hankali, wani sanyi ke ratsa zuciyar Maryam. Ta shiga murmusawa tana dubanta, so da kauna ta uwa da ɗa ke ratsa dukkan kofofin jikinta.
Sallamar Inno ce ta sanya ta kauda kai a kunyace, ta shimfidar da Humaira ba ta ko kara kallonta ba ta shiga gaida Inno. Murmushi Inno ta yi don ta gama karantar kunya irin ta Maryam, wanda hakan abu ne mai kyau a Musulunci.
“Lafiya kalau Maryam, ya karfin jiki?”
“Da sauki, Alhamdulillah.”
“Haka ake so, tashi ki wanka sai ki zo ki sa abu a cikinki. Kishiyata dai ta rigaki wankan, da yake bata da rigima, ina gama wanketa kafin ma mu kammala shiri bacci ya yi awon gaba da ita.”
Ita dai Maryam banda murmushi ƙasa-ƙasa ba ta ce uffan ba, ta mike cikin bin umarnin Inno ta fice daga dakin bayan ta sanya hijabi.
Da yammacin ranar, Maryam ce zaune gaban Malam Haruna wanda ya aika Inno ta kirata. Bayan sun gaisa yana rike da Humaira ya maida hankali gareta.
“Maryam, hakika duk bawan da Ubangiji ke so, shakka babu yana zama cikin jarrabawarSa a koyaushe. Ki sanya a ranki ko menene ke dawainiya a rayuwarki to ba daga gareki bane, ba kuma sai don kin yiwa Allah wani laifi ba zai jarabceki, a’a. Duk abinda ya ƙaddara to ba makawa sa ya afku garemu mai dadi da akasinsa.”
Shiru ya biyo baya, zantukan Malam sun samu mazauni mai girma a zuciyarta. Ta numfasa tana jin wani sanyi na ratsa ta har zuwa sadda Malam ya dora da zancensa.
“Ni haifaffen ƙauyen Cinnaku ne a wannan jaha tamu ta Yobe, asalin iyayena mabiya addinin Dodo ne, haka muka taso, sai dai kuma wani ikon Allah, zuciyata ba ta ta6a bada gaskiya ga Dodo ba. Asalima a duniya babu abinda na tsana kamar zuwa wurin bautarsu tun da ƙananun shekarunta har zuwa sadda na soma zama matashi. A wannan lokacin ne Allah Ya yiwa mahaifiyata rasuwa ta barni daga ni da ake kira da Gatari a baya, sai Mahaifina da ƙanina Tanko. Sai da mahaifiyata tayi kwana har uku bayan an wanketa, kamar dai yanda al’adar wannan yankin take, idan mutum ya rasu, dole sai ya kwana uku, a wannan kwanakin danginsa na kusa da nesa zasu zo a hadu ana waƙe-waƙe, shan giya da ma sauransu. Sai a kwana na ukun za’a dau mutum a kai shi makwancinsa tare da kayan Noma su fatanya da sauransu domin a ganinsu mutum ba mutuwa ya yi ba, sabuwar rayuwa zai shiga. Nan ma dai abu bai ƙare ba saboda a kan kabarin za’a yi kiɗe-kiɗe da sauran sha’ani na rayuwa daga bisani bayan kwanaki bakwai a komai a bi mutum da kayansa a ƙone. A zuba tokar saman kabarin a na fadin, “Idan ka je ka ce kai kaɗai ne ya rage ba saura.”
Malam ya ɗan tsagaita yana ƴar dariyar takaici wanda har Inno da Maryam sai da suka murmusa.
“Duk wannan buduri da aka sha ban leka wajen ba a karshe ma da Mahaifina ya matsamin sai na fito nan inda kike ganina yanzu bayan gari, a lokacin ƙorama ce babba a nan ta ruwa, nan nake zama na yi kukan rashin Mahaifiyata. Bayan gama makoki Bokansu ya tsawatarwa Babana akan rashin zuwana wajen Bauta. Ƙarshe ya kuma ce dole ayi biyu cikin daya, ko na bada gaskiya na dinga zuwa bauta ko kuwa na fice a garin. Ba irin duka da faɗan da Baba bai yi ba, har hanani abinci ake ace sai naje wurin bauta, amman wallahi ban ta6a ji a raina zan iya aikatawar ba. Haka kurum nake zaune bana bautar komai cikin rashin sanin me zan bautawa din. A haka Baba ya fitar da ni daga gidansa ya tura ni can cikin garin Yobe hannun kakata ta wajen Babana, a tsauri ta fi shi tsauri wajen bautar Dodo don har mutum-mutumin Dodo take da shi a ɗakinta wanda kullum cikin bauta take. Cikin ikon Allah shigata birni, sai ya zamana na hadu da wani aboki kuma amini mai suna Bukhari. Na lura akwai lokuta da dama wanda idan muna tare da Bukhari zai mike ya cemin zai je sallah, har yakan tambayeni ko ba zan je ba, to bansan mene ma’anar sallar ba, wannan ta sanya kullum zan ce mishi a’a. Watarana da ya matsa akan kodai bana sallar ne, sai na tambayi ma’anarta. Ya sha mamaki sosai domin duk abotarmu a kasuwa ce idan na yiwa Kawuna rakiya. Anan yake tambayar addinina. Budar baki nace bana bautawa komai amman ga abinda iyayena ke bautawa sai dai ban yi imani da shi ba. Alhamdulillah.”
Malam ya furta fuskarsa na cike da murmushi saboda tunawa da lokaci can baya mai dadi gareshi.
“Shigowar Bukhari rayuwata wanda bana rabo da yaba sunansa a baya tunda lokacin ni sunana Gatari, nakan sha tambaya wurin jama’a akan ma’anar sunana, wasu da suka san gidan Kakata sukan yi shiru kawai sanin dawar garin. Sanadin Buhari na karɓi musulunci, a ɓoye nake gudanar da ibaduna saboda Kawuna kanin mahaifina, Danliti da Kakata. Wajen mahaifinsa Malam Zubair muke daukar karatu duk bayan Magriba zuwa isha’i. Shi ya sauyamin suna zuwa Haruna. Tun ina ɓoye Musuluncina a gida har wataran ina cikin sallah da Asubahi, Kakarmu ta kamani. Ranar Allah kadai Yasan azabar da na sha.”
Ya dan yi shiru sannan ya cigaba da magana da alamun rashin don tuna bayan.
“Maryam, a hankali Allah Ya bani iko akan Kakata da Baffana suka musulunta. Na kwashi tsawon shekara guda muna abu daya, duk wannan buduri Babanmu ya sani a wani zuwa da Kakata suka yi bikin shekara na Dodo. Lokacin na rabu da gidan gaba daya na koma zama hannun Malam Zubair. Cikin ikon Allah a sannu Allah Ya taimakeni na dasa son musulunci a zuciyar Baffana da kuma Kakata. A hankali suka karɓi shahada, ranar har kukan murna nayi. Wani zuwan da Babana ya yi tare da Tanko, ya tarar da sauyi mai yawa. A hankali ya soma gaskata abinda yake gani kuma yake ji, Allah Ya taimakemu daga shi har Tanko suka kar6i shahada. Sai zumunci mai karfi ya kullu tsakaninmu da zuriar Malam Zubair har aure ya shiga tsakanina da Fatima diyarsa kuma kanwa ga Buhari aminina. Gobara ce ta yi sanadiyyar mutuwar Kakata da Baffana da matarsa Sadiya. Wannan ne dalilin tattarawata na komo Kauyen Cinnaku tare da Fatima wajen Baba. A wannan lokacin Malam Zubair ya samu matsalar gocewar ƙashin baya, ya kasance gaba daya baya tafiya. Asalinsu ba ƴan Yobe bane, zama ya kawo Malam Zubair. Faruwar wannan lamari suka soma shirin komawa Kano, ban mantawa Buhari ya taɓa cemin su din mazauna garin Dambatta ne a Kanon. A daidai sadda mu kuma muka wuce Kauyen Cinnaku tare da Fatima sakamakon labarin mutuwar Babana da Tanko da ya riskeni ta hanyar wani dan garinmu da ke zuwa Yobe sarin kaya. Tashin hankalin da muka shiga ba a magana. Na so komawa Yobe da zama sai dai kuma na duba naga babu ta yanda za’ayi na bar gidanmu tunda can din zai yimin wuyan zama saboda rashin kuɗi da kuma muhalli mai kyau. Muhallin da Kakata ta ke, na bukatar gyara don ba karamin ta’adi gobara ta yiwa gidan ba.
Sai da na tabbatar na bar Fatima a kyakkyawan hannu, wani makwafcin Babana mai amana wanda ya tabbatarmin ba zai bari a cutar da iyalina ba, sannan na koma Yobe don ganin Malam Zubair. Abin takaici na tarar sun wuce zuwa Kano. Ban yi ƙasa a gwuiwa ba na dawo Kauyen Cinnaku na dau Fatima muka wuce Kano. Allah Ya taimaka ita din ta san mazaunin iyayenta a Dambatta, da wannan muka isa. Abinda Allah Ya riga ya tsara ba yanda muka isa mu yi, duk bincikenmu a Dambatta an tabbatarmana ba su zo ba. Wannan tasa Fatima har da suma da kwanciya rashin lafiya, a karshe dai wani dan uwansu ya ja ni muka bar Fatima a Dambatta muka komo cikin Birni muka huta lalube a asibitoci ko Allah zai sa mu dace da ganinsu sai dai babu su ba ƙurarsu. Bayan sati muka juyo zuwa Kauyen Cinnaku, ba mai taimakamana sai Mahaliccinmu. Da karfin IkonSa, Ya ban iko wanda da yawa daga cikin mutanen Kauyen suka karɓi shahada ciki har da Aminin Babana da iyalinsa. Muka soma samun matsi daga mutanen Kauyen, basu iya sun cutar da Ni da almajiraina ba saboda karfi na addu’a da kuma kwarjinin musulunci. Ƙarshe suka ce ai talaucina yana da nasaba da saɓawa umarnin Dodo. Daga baya akai masalaha, na fice daga Kauyensu muka kafa mazauninmu anan wanda muke kira da Rumfar Malam. Koyaushe ina musu fatan alheri da kuma fatan samun haske da ikon kar6arsa da hannu bibbiyu kamar yanda Allah Ya bamu wannan ikon, yaranmu biyar da Fatima, kuma duk a wannan kauyen muka haife su, duk maza ne, Yaron Malam mai sunan surukina Malam Zubair, sai Aminu, Usman, Haidar da karaminsu Umar.”
Yana zuwa nan ya numfasa, Inno hawaye ta ke fitarwa sakamakon sosamata inda yake mata ƙaiƙayi, an tunomata da iyayenta wanda har yau babu wani labarinsu. Ga Maryam kuwa, kanta ke wani irin sarawa, ga tausayin wannan bayin Allah ga kuma na kanta.
“Maryam, wannan shine tarihinmu, na fadamaki domin ki kara sakin jiki da mu ki kara fahimtar mu ba zamu cutar dake ba da yardar Allah.”
Daga haka ya miƙawa Inno Humaira da ke faman tsotsar hannu. Ya kara duban Maryam.
“Kiyi hakuri da tambayar da zan maki sai dai kuma ya zama dole Maryam. Mun shaida ke din musulma ce kuma Hausa Fulani, sai dai bamu san asalin Maryam ba. Ga kuma albarkar haihuwa kin samu, wannan ya zama dole mu san tarihinki domin mu san matsayinki a Shari’a. Mu kuma san taimakon da zamu yi gareki.”
A hankali gudun hawayenta ya ƙaru, kanta da ke sarawa ya ci gaba da bugu kamar ana saramata. Ta dago Kai ta dubi Malam, ya tsorata ainun da yanda idanunta suka sauya launi zuwa ja. Ta hau girgiza kai, baki na rawa ta ce.
“Wallahi..wallahi na manta wacece ni. Haka kawai na tsinci kaina..”
Sai ta fashe da kuka. Gaba daya sai ta basu tausayi musamman Malam Haruna wanda kallo daya ya yi mata ya ji kaunarka tamkar diyarsa ta cikinsa. Inno na dubanta zuciya a cunkushe. Muryar Malam ce ta katse su.
“Ba komai Maryam, dauki hakan a matsayin kaddararki. Ki sa a rai kowane bawa ba ya wucewa tasa kaddarar ta Ubangiji. Kar ki fasa addu’a, kar ki fasa kai kukanki gareShi. Shi ne Mai yaye dukkan baƙƙan ciki, da ace duniya zasu taru don su cutar dake, ina mai miki rantsuwa da Allah ba zasu iyaba, idan kuwa Allah Yay niyyar afkuwar lamari gareki marar dadi domin Ya jarabta imaninki, nan ma ba wanda ya isa ya tseratar da ke. Don haka ki yi hakuri, ki miƙa lamarinka gareshi, komai kaddarawarSa ce. Watarana zai zama labari, In sha Allah zamu tayaki da addu’a. Zamu rike ki kamar ɗiyarmu ta ciki. Tashi ki je.”
Dakyar ta iya bude baki tana magana cikin muryar kuka.
“Na gode Baba, na gode Allah Ya saka da alkhairi. Ba abinda zan ce muku banda addu’ar Allah Ya muku sakayya da aljanna, Ya haɗaku da ƴan uwan Inno.”
Sosai sun ji dadin addu’arta, a haka ta mike ta koma ciki. Bayan tafiyarta Malam ya maida dubansa ga Inno.
“Fatima, Allah Yay miki albarka. Kamar yanda kika saba, ki tayani riƙon Maryam, ina jinta kamar diyar da na haifa.”
Murmushi Inno ta yi.
“Allah Ya tayamu riƙo Malam. Nima ina jin yarinyar a raina, lokaci daya Allah Ya sanyamin kaunarta, yarinyar da duka-duka ba za ta fi shekaru ashirin da uku ba, ba ta wuce sa’ar Yaron Malam ba.”
Daga haka ta maida dubanta ga Humaira tana murmushi. Shima murmushi ya yi bai ce uffan ba, kaunar matarsa da tausayinta na ratsa shi. Kullum addu’arsa bai wuce akan Allah Ya bayyana Malam Zubair da iyalinsa ba.
This is a really different and great book, I’ve never read anything like it before, it’s usually cliche love stories but this is different!