“Meke faruwa?” Humaira ta karanta rubutun Mamarta, kafin ta soma ba ta amsa.
“Dan uwan Malam ne ba shi da lafiya. Yanzu haka ma ya na asibiti.”
Jin haka Maryam ta girgiza kai cike da tausayi. Ta kara daukar takardar da Humaira ta kara yin wani rubutun.
“Zamu je duba shi?”
Maryam ta gyaɗamata kai. Da zumuɗi Humaira ta kara rubutun ta mika mata.
“Na faɗawa su Baba Yaha idan zasu su yi mana magana?”
Nan ma Maryam gyada kai ta yi tana dan murmushi. Humaira da saurinta ta mike, dama tana son zuwa dubiyan. Zama na dan lokaci ta yi da su amman tsohon ya shiga ranta yana da jan wasa da kuma fara’a.
Ita kuwa Maryam tun ganinsa ba ta da nutsuwa sosai, kirjinta yakan yawaita bugu. Ba ta da masaniyar ko su na da dangantaka ko babu, kawai ta san tana jinsa kamar wani na kusa da ita.
Humaira ta samu Yaha ta sanarmata cewar zasu je duba Engineer.
“Ai kuwa zamu je yanzu don za’a kai abinci ma. Ku shirya ku fito mu wuce kawai.”
“Toh.” Ta koma ta sanarwa Maryam, dogon hijabi kawai ta sanya a saman doguwar rigarta. Humaira da ke sanye da baƙin wando na riga fara mai adon duwatsu na ƴan Pakistan, ta yi lulluɓi da mayafin kayan fari mai ratsi-ratsin baƙi. Ta yi kyau sosai. Suka fita gaba daya gidan.
*****
Wuraren la’asar suka iso Yobe. Lokacin Malam bai jima da dawowa daga asibiti ba tare su Kawu Lawwali. Suna zaman jiran ruwan alwala suna tattaunawa game da yanda za su ɓullo da lamarin ɗan uwansu, suka ji tsayuwar motar Adam.
Gaba daya suka dakata ganin Adam da baƙin fuska. Adam ne ya soma ƙarasowa kafin Fu’ad ya zagaya ya buɗewa mazauna bayan motar ƙofa.
Wanda ke fitowa ya sa Malam Kabiru miƙewa. Shekaru sun ja, ƙuruciya ta kau hakanan tsufa ta bayyana, wannan ba zai sa ya kasa gane fuskarsa ba.
“Malam Buhari?”
Shima tuni ya ganeshi. Idanunsa cike da kwalla ya ce.
“Malam Kabiru?” Suka rungume juna su na kuka, kukan farin ciki da tunawa da iyayensu maza. Kawu Lawwali ya basu baki akan su yi sallah tukunna. Ba musu suka shiga ɗaura alwala. Fu’ad jikinsa ya kara sanyi, gaba daya suka burgeshi, ya lura ba abinda ya kai zama cikin dangi dadi. Rayuwarka kai ɗaya ba ta taɓa cika sai da ƴan uwa. Ba ta da dadi.
Bisa jagorancin Baharu, Baraka ta shige cikin gidan Malam don Gwaggo Kubra ta dawo tare da Malam.
Da hannu bibbiyu itama aka karɓeta jin cewa baƙuwar Malam ce. Ta yi sallah ta ci abinci.
Bayan sun samu nutsuwar kai aka shiga bangaren Malam aka zauna a falonsa. Nan kuma aka hau hirar yaushe rabo. Buhari ya soma magana.
“Bayan tahowarmu daga Yobe zuwa Kano, tun a hanya jikin Malam ya ƙara rikicewa har ya suma, daga karshe ya farfaɗo. Har zamu fasa tafiyar Malam ya nuna sam a’a. A cewarsa idan ma mutuwar ce ya fi kaunar ya mutu gaban ƴan uwansa kuma a asalinsa. Sai da burin Malam bai cika ba sakamakon mummunan hatsarin da muka yi inda motarmu ta bugi wata mota na tankin ruwa wanda hakan ya yi sanadin da motarmu ta faɗa gefe ɗaya muka kife kaina ya bugu da wani abu da ba zan iya tantancewa ba. Banda salatai da kuma ihu ba abinda ka ke ji. To nidai Malam na kusa da Ni ya rike hannuna yana salati tun ina iya sauraronsa har na daina.”
Malam Buhari da hawaye ya ce.
“Wallahi tun daga hakan da akai bani da labarin komai saboda mantuwar da ta same ni. Na manta komai na manta asalina.”
Su Malam Kabiru suka sanya salati, kanin mahaifin Baraka shima ya fadi yanda ya zo hannunsu da kuma irin kulawar da ya samu wanda hira karshe suka aura masa Baraka suke zaune tsawon shekarunnan lafiya kalau. Ya kuma fadi sanadin da yasa ya dawo hayyacinsa.
A karshe Adam ya dora da bayanan likita da kuma irin wannan matsalolin.
“Allah Hakeem! Buwayi gagara misali.”
Cewar Kawu Lawwali. Nan dai Malam ya ba shi labarin Inno da kuma yanda suka zo suka kara haduwa daga baya. Malam Buhari ya yi murna da jin cewa yar uwarsa tana nan lafiya, yanzun ita kadai ta ragemishi da suke uwa daya kuma uba daya. Ya yi ta godiya ga Allah. Ya so zuwa a ranar sai dai aka ce ya yi hakuri zuwa gobe.
Da wannan ya hakura ba don ya so ba.
“Bari mu leka asibiti mu dawo.”
Faɗin Adam yana duban su Malam.
“Nikam wannan abokinka ne?”
Cewar Kawu Lawwali wanda tun zamansu yake dan satar kallon Fu’ad din cike da tambayoyi kala-kala a zuciyarsa.
Murmushi Adam ya yi.
“Fu’ad ne, ɗan wajen Sal..ɗan wajen Matar ɗanku.”
Daƙuwa Malam Kabiru ya mishi sanin da ya yi Hayat yake nufi. Shi kuwa Fu’ad ɗan harararsa ya yi da wasa jin daga farko sunan Mum dinsa ya so kira. Shi duk sai suka ba shi dariya don haka sai ya murmusa kawai. Fu’ad ya kara gaishesu, su na tambayar lafiyar iyayennasa.
*****
Hannu yake miƙomata wanda ta jinkiri ta karasa ta miƙa nata hannun tana kyakkyawan murmushinta da har dimple dinta ke lotsawa.
“Allah Ya ba ka lafiya Baba.” Fadin Humaira tana duban Engineer wanda ya kurawa Maryam ido. Maganarta ta dawo da shi hayyacinsa yake dubanta. Murmushi ya yi ya amsa da cewa
“Amin ɗiyata.”
Maryam ta ɗan matso ta durkusa gami da gyaɗa kai da matsa hannu wuri guda tana murmushi. Ya gane gaisuwa ce ta ke da fatan samun lafiyarsa.
“Ta ce Allah Ya ba ka lafiya.” Humaira ta furta. Aka yi dariya kadan. Dakin daga su Amir da Amira sai Anti Khalisat da su Shuraim. Su Gwaggo Hannatu duk sun tafi. Umma da Hashim na hanya sun taho da abinci.
Zama suka yi gaba daya saman tabarmar da ke shimfide a gefe. Humaira da Amira sai kuskus suke suna ba juna labarin makaranta. Idan ka gansu sai ka rantse sun shekara a haka. Shuraim ya wurgowa Humaira tuffa har sai da ta tsorata. Ta dubeshi tana tsuke fuska.
“Me nayi?”
“Kin janyemin hankalin mata, har ina magana ina kallonta ba ta san ma ina yi ba.” Amira ta ɗago ya kuwa ɗagamata gira ta zabga mishi harara, Allah shaida ba ta taɓa jin wani abu dangane da Shuraim ba sai dai ta daukeshi matsayi guda da yayanta Adam.
“Oh Allah, nikam Shuraim na gaji da wannan rashin kunya taka. To tashi ka fita ka bamu wuri.”
Anti Khalisat ta fadi tana zare mishi ido.
“Ina zai je? Ai lokaci ne, ki kyaleshi ya zaɓa ya darje.” Fadin Baba Hindu da ke zaune gefen Mijinta tana yi mishi damun fura.
Maryam ba ta ji sai dai murmushinsu ke ba ta tabbacin abin na dadi ne suke tattaunawa hakan yasa ta murmusa. Ba ta san dalili ba su na burgeta sosai.
Haka suka ci gaba da barkwanci, karshe Amira ta mike tsaye ta ja hannun Humaira wai su fita. Humaira ma ta mike bayan ta yiwa Maryam alamar tana zuwa suka fice daga dakin ganin Shuraim din ya ƙi ficewa. Zai bi bayansu Anti Khalisat ta yi mishi kan ido ya koma ya zauna suka sa dariya.
*****
“Wai ina muka nufa?” Fadin Humaira da ta gaji da zagaye cikin asibitin. Amira ta gyara zama farin gilas din da ta sanya wanda ya kira fito da tsantsar kamanninta da Adam da kuma kyawunta. Yamutse fuska ta yi.
“Ai gwara mu ga gari da na zauna wancan yana karemin kallo. Bana son yawan surutu. Allah kuwa ana yin hutun makaranta zan gudo gidanku na zauna. Ya takuramin.”
Dariya sosai Humaira ta sa.
“Ke sonki fa yake.”
Taɓe baki Amira ta yi.
“Shiyasa yake ban haushi.”
“Wallahi kuma kinga fa ya haɗu.”
“Eh na sani amma ni bana sonsa. Wata cousin dinsu ce ke sonsa sosai. Diyar yayar Anti Khalisat, gobe za ta zo daga Abuja. Cewa yake wai idan ta zo ko kallo ba ta ishe shi ba. Wai shi dama kada ta zo. Ni kuma ba ruwana, Umma ta ce ni yarinya ce har yanzu. Duka-duka fa Ss1 nake.”
Suka yi dariya.
“Ki godewa Allah ma kina Ss1, nifa cikin kannena nake kuma fa su na girmama ni, Anti suke cemin.”
Nan ma dariyar suka yi.
“Ƴan mata adon gari.” Muryar da suka ji ta sanya suka maida hankali ga inda ta fito. Da murnarsu suka mike suka nufeshi.
“Lah, Yaya Adam.” Kusan a tare suka furta. Yana murmushi ya amsa.
“Na’am. Me kuke yi a waje?”
Humaira ta nuna Amira, itama ta nuna ta. Sai ma abin ya basu dariya.
“Allah kuwa ita ce ta jawoni wajen.” Fadin Humaira a shagwaɓance. Ya ji saƙon tun daga tsakar kansa har zuwa yatsa.
Ya kasa amsawa sai murmushi da dan lumshe ido da ya yi.
“Ba magana? Shi kadai ku ka sani ko?”
Fu’ad ya furta cikin zaƙuwa na son ganin sun haɗa ido da Amira, fatansa ta yi mishi magana. Ya samu yanda yake so kuwa, suka dubeshi. Ita Humaira kokari take ta tuna ko waye shi. Ita kuwa Amira tsai ta yi tana murmushi kafin ta gaidashi.
‘Ɗan gayu da shi.’ Ta furta a ƙasan ranta.
“Lah, ƙanin ɗan biyutiful ko?”
Humaira ta furta tana nunashi da yatsa. Ya yi dariya shima.
“Yes, ni ne, Fu’ad.”
Jin sunan Fu’ad ya ankarar da Amira ko waye, sai dai ba ta ji ta sauya daga yanda ta ji a kansa a farkon gani ba. Wato kauna ta yan uwantaka.
Adam yana amsa wayar Huzaifah yana sanar da shi shima gashinan ya shigo asibitin. Ba jimawa sai ga Huzaifa da Amaryarsa Nuriyyah, ta yi kyau ta yi jiki. Fatar kamar ka taɓa jini ya fito. Humaira na ganinta ta fice a guje ta rungumeta itama ta ba ta kyakkyawan runguma. Amira sau daya ta taɓa ganinta sadda suka je gidan Uncle Hashim gaisheshi. Don haka ba su yi sabon da sukai da Humaira ba.
“Wow ƴar Kanwata kin yi kyau abinki. Ina Mama? Ya jikinta?”
Cikin yanayi marar dadi ta amsa.
“Mama da sauki. Kema Anti kin yi kyau sosai wallahi.”
Suka yi dariya. Huzaifa na can su na musabaha da su Adam. A karshe dai gaba ɗaya suka dunguma zuwa ciki bayan Nuriyyah ta gaida su Adam.
Ranar kam Engineer ya sha baƙi, aka yi ta hira sosai kamar ba a asibiti ba, shi kuwa wannan ya fi komai yi mishi dadi, murmushi kawai yake zabgawa ganin wurin duka don shi aka zo. Fu’ad ba ya daukar kansa bare kuma ba wanda ya nunamasa wani abu don haka sai ka rantse an shekara tare da shi dama a hakan. Zuwan Uncle Hashim da Umma ya sa duk aka nutsu.
“Haba, kun maida asibiti sai ka ce gidan biki. Kun manta ba Baba me kaɗai a asibitin ba? Kuma ma ai hutu aka ce ya samu ba a zo a cikashi da kowace irin hayaniya ba.”
Yana maganar daga tsaye sai dai da tausassan murya. Mazan daga mai shafa kai sai mai murmushi yayinda matan suka yi ƙus.
Umma ta dubi inda Maryam take, Yaha ke sanarmata ita ce mahaifiyar Humaira.
Ta gaisheta. Humaira ta taɓa ta gami da yi mata alamar da za ta gane, da murmushi ta haɗe hannu ta ɗan russuna kai alamar gaisuwa. Tausayi ta basu, Adam dama tun ganin da ya yi mata ya tausayi da kaunarta matsayinta na musulma yar uwarsa. Haka ma a ɓangaren Fu’ad. Nuriyya ta kauda kai ta share hawayen da ya cikamata idanu. Ina zata manta mutuncin Maryam? Kamar wata ɗiyarta haka ta dinga daukarta a ranar bikinta. Suka haɗa ido da Huzaifa ya yi mata alama da kai cewa a’a.
“Mun ga wannan.” Fadin Shuraim saitin kunnensa. Ya kuwa ba shi mintsili ya gantsare suka yi dariya.
Amira ta soma gajiya da kallon da Fu’ad ke mamayarta da shi don haka ta kara jan Humaira akan su fita. Ganin zasu fita Umma ta ce.
“Ai da dukkanku ma fitar ku ka yi don naga Baba ya soma gyangyadi. Ku tashi ku fita kar a dameshi.”
Aka dara sannan duka matasan suka kama hanya. Humaira ta waiga ta kalli mahaifiyarta, kai ta gyaɗamata alamun ta je. Ta yi murmushi sannan ta fita. Abin ya burge su Umma matuka sannan sun ba su tausayi.
“Nayi fushi da ke, ba ki zo kinga gidana ba har yanzu.” Fadin Nuriyyah ga Humaira kamar mai magana da wata babbar budurwa sa’arta. Humaira ta yi dariya.
“Yi hakuri don Allah Anti, dagaske ina son zuwa. Rannan ma Mama sai da ta yi zancenki wai ba ki zo ba kuma ba ta je ba. Na ce mata ai zamu je wataran.”
Murmushi Nuriyyah ta yi,
“Shikenan zan yiwa Habibina magana ko ran juma’a ne sai a kawoku ku wuni.”
Humaira na murmushi ta gyaɗamata kai.
“Anti kinsan ina zuwa makaranta ko?”
“Eh, Mummy ta fadamin da muka yi waya cewar za’a sanyaki. Mun gaisa ai da Inno.”
Nan fa Humaira ta shiga magiyar ta kiramata Inno a waya. Ba musu ta kira ta miƙamata. Suna tsaye gaba dayansu, Amira na magana da Yayanta Adam da Amir sai ganinta su kai ta yi can gaba tana waya da Inno. Kamar wata budurwar arziki sai malkwaye baki take tana rangwaɗa kai tana ba Inno labarin makarantarsu. Sosai Inno ta ji dadin wayar don har da Malam suka gaisa. Anan ta ke jin cewa Umar ma ya yo waya daga Madina sun gaisa. Ta kara jaddada mata idan ya kira a fadamasa ya tahomata da kayan larabawan da ya yi alƙawari zai kawomata ita da Jamila. Inno dariya kawai ta yi kafin ta katse kiran.
Itama a nishaɗance ta ke duban wayar kafin ta maido hankali wurin da suke tsaye. Kafafunsa a harɗe, kusan duk abinda suke cewa bai ji ba. Hankalinsa kacokan yana kanta, murmushinta, kallonta, dariyarta da duk wani motsinta yana jinsa daidai da ra’ayinsa. Daidai da yanda yake son matarsa ta zama. Ta karaso garesu fuskarnan cike da fara’a, motsi kadan da bakin sai dimple dinta ya fito.
“Gyara dai.” Ya ji muryar Huzaifa saitin kunnensa. Suka dubi juna, Adam ya harareshi shi kuwa da murmushi ya kara matsawa kusa da kunnensa.
“You Are in love.”
“No.” Fadin Adam kafin ya ja guntun tsaki.
“Kamar Amira nake kallonta. So don’t take me otherwise.”
Dariya kawai Huzaifa ya yi ba tare da ya ce komai ba.
Sai bayan sallar Magriba tukunna suka bar asibitin gaba daya. Maryam da Humaira suka hau motar Adam. A harabar asibitin Fu’ad ya dubi Amira da kallon da take jinsa wani iri. Take jin ya girmi shekarunta.
“Kanwata sai gani na biyu?”
Tana murmushi ta gyada kai.
Ya ɗan ɗagamata yatsunsa uku itama ta maida martani. Suka haɗa ido da Shuraim, kallon da ya yi mata kawai sai ta tsargu don haka ta janye yatsunta ta juya zuwa wurin motarsu.
*****
“Kasheta zamu yi!”
Faɗin Hayat cikin gigicewa.
“Idan da hakan zai yiwu zan fi kowa farin ciki! Sai dai ka sani hakan ba mai yiwuwa bane.”
Fadin Salma ta wayar tana fidda huci.
“Ai wannan ma ba mafita bace!” Halima ta amsa kasancewar conference call Salma ta haɗamusu duk don a samu mafita akan baiwar Allahn da ba ta ji ba kuma ba ta gani ba.
Cikin daga murya yake fadin.
“To wai ya kuke so mu yi? Zuba ido zamu yi wancan tsohon najadun ya ci gaba da ba ta magani tana warkewa? So kuke wataran Maryam ta zama dole dakushewar farin cikinmu? Idan fa kwai ya fashe, ba wanda ba zai shafa ba cikinmu. Kun riga da kun san da hakan.”
Shiru ya biyo baya kafin Halima ta ce.
“Me zai hana mu ƙulla mata sharri wanda zai sa a tsaneta a gidan kuma a koreta?”
“Ta yaya?” Fadin Hayat da Salma kusan lokaci guda cikin son sani.
Ta koro jawabi, Hayat tun yana jin kansa ya dauki zafi har ya ji wani sanyi da farin ciki. Tuni ya koma ya zauna, sai a sannan ya ke jin gudun na’urar fankar na bugarshi. Itama Salma wata nutsuwa ta ji ta samu ta musamman.
“Shiyasa aka ce kaidinku mai girma ne. Kinga lokaci guda kin warwaremana ƙullin da muka kasa warwarewa.”
Dariya Halima ta yi.
“Ba ka da dama Hayat, ka manta wacece Halima kuma?”
“Mtsww, ya isa haka. Yanzu wa za’a samu ya yi aikin?”
Fadin Salma cikin son katse hirar da zasu dauko.
“HANAN.” Faɗin Halin daga can ɓangaren.
“Hanan?” Salma da Hayat suka maimaita sunan lokaci guda.