Firgigit ta farka daga dogon baccin da ta yi, ta kurawa wanda ke riƙe da hannunta idanu. A hankali ta mike gami da kiran sunansa baki na rawa.
“Yaya?”
Ya shiga gyaɗa mata kai kamar kadangare. Hawaye na zuba kamar famfo saman fuskarsa.
“Ni ne ‘Ƴar Baba, ni me Buhari.”
Inno ta fashe da kuka jikinta har yana rawa.
“Kai ne wallahi, kammaninka ba su ɓacemin ba. Yaya ina Baba?”
Malam Buhari ya girgiza kai.
“Baba ya rasu Fatima. Ya rasu.”
Ta gyada kai tana salati.
“Allahumma ajir nuni fee musibatii. Jikina ya jima da bani hakan, na gani ba sau daya ba a mafarkaina.”
Tausayinta ya ratsa zuƙatan mutanen wurin, Maryam duk da ba ta ji takan fahimci wasu abun daga motsawar bakunansu. Hawaye kawai take tana mai tausayawa nata kaddarar. Fu’ad kuwa gaba daya ya sha jinin jikinsa, idanunsa a take suka kaɗa daga launi masu haske zuwa ja. Tausayi ne irin wanda bai san a duniyarsa yana da shi ba sai yanzun. Ya kara ganin dadin yan uwa da dangi, zama da rayuwa kai ɗaya cikin dauka ba shi ne rayuwa ba. Mutane ma rahma ne.
Tiryan-tiryan Malam Buhari ya bada labarinsa, ɗan uwan Baraka ya dora da wanda ya sani na tsintarsa da suka yi sannan Baraka ta gabatar da kanta matsayinta na matarsa sama da shekaru ashirin. Inno banda kuka da yin kirari ga Ubangijin sammai da ƙassai babu abinda take yi.
Adam ya kara da saninsu na likitoci game da irin wannan matsala da ta samu Malam Buhari duk don hankalin Inno ya kara kwanciya. Karshe Malam Kabiru ya rufe zancen da nasiha da kuma addu’a.
A karshe mazan suka yi sallar azahar a jam’i, mata sukai nasu.
“Maryam? Kinga ikon Allah? Maryam Allah Ya haɗani da Buhari, kema Allah Ya haɗaki da baki dangin kamar haka.”
Inno ke wannan sumbatun suna zaune saman abin sallah hannunta riƙe cikin na Maryam din. Maryam banda murmushi ba abinda take yi.
“Kayya Inno, murna ta sanyaki mance wacce kike yiwa maganar bebiya ce kuma kurma.”
Fadin Yalwa da wani da nishadi, ita fa tun ji da ta yi ba yan uwan Maryam ne suka bayyana ba ya sanya wani dadi da annashuwa ya cika zuciyarta.
“Au, Allah Sarki. In sha Allah za ta samu sauki itama.”
Aka amsa da Amin banda Yalwa da ta taɓe baki.
Jamila har da hawayenta jin Humaira ba ta zo ba. Kamar ta san tunaninta, ta mike ta shige dakin Inno kafin ta dawo da rubutu ta mikawa Inno. Fatan alheri ta yi mata da kuma tayata farin cikin ganin ɗan uwanta, a karshe ta sanarmata da dalilin rashin zuwan Humaira da fadin ciwon mara ta ke, ta girma kawai ta ce a karshe wanda ya sa Inno murmushi. A bakin Innon suke jin dalilin rashin zuwan Humaira sai dai b ta faɗi ga babban dalilin ba.
Sai wuraren karfe hudu sannan su Malam Kabiru suka yi musu sallama. Maryam har da kukanta yayin rabuwa da su Inno a karo na biyu. Kayan su rama da su zogale Inno ta haɗa a kaiwa Gwaggo Kubra. Sai alewar madara na Humaira da sauran yaran gidan.
*****
Juyawa kudaden ta ke yi yayinda ta kasa ɓoye annurin dake a saman fuskarta. Ta lula cikin tunanin sabuwar duniyar da za ta shiga idan yau ace mafarkinta ya tabbata na auren Fu’ad.
Hanan! Ba magana ake ba kin yi shiru.”
Cewar Halima cikin tsawa. Wanda ya yi sanadin dawowarta cikin hayyacinta. Tana murmushi ta maida dubanta garesu. Hayat ne sai kuwa Salma da Halima.
“Ina jinku mene aikin?”
Salma ta soma kora jawabi.
“Za ki shiga gidan cikin shigar ɓadda kama, ma’ana ki sanya nikaf da hijabi. Idan son samu ne har safar kafar da ta hannu.”
Yamutse fuska ta yi ta dubi Halima. Halima ta kifta mata idanu alamun kada ta ce komai. Salma ta dora.
“Za ki shiga gidan da sunan ke ƴar uwar Maryam ce. Kuma ta gudu ta bar gida sakamakon mijinta da ta kashe. Ki haɗa dukkan labarin da za ki haɗa domin su gaskata hakan. Idan har haƙanmu ya cimma ruwa suka amince da tahowarku tare da ita, mu kuma zamu san dabarar da zamu yi wajen ganin komai ya tafi daidai. Idan komai ya kammalu toh ki sani, zamu ba ki ninkin abinda muka ba ki a yanzu. Za ki je kasashe biyar wadanda kika zaɓa.”
Ta kasa magana tsabar mamaki da ruɗani, a gefe guda ji take kamar ta daka tsalle ta yi ta juyi da rawa tsabar murna da farin ciki. Ta kasa gaskata hakan gaskiya ne ko mafarki. Ita ce za’a mallakawa dukiya? Ta kasa yarda da hakan.
“Kin ji kin yarda za ki yi ba tare da kin bamu kowace matsala ba?”
Hanan ta shiga gyaɗa kai kamar wata kadangaruwa tana washe baki.
“Zan yi, zan yi. Sai dai ya za’ayi na san gidan?”
“Wannan mai sauki ne, Ni zan nunamaki. Burinmu kawai Maryam ta zo hannu.” Fadin Hayat yana murmushin mugunta. Salma da Halima suka tayashi.
“Toh shikenan, yaushe ne za’a yi?”
“Karshen weekend dinnan.” Faɗin Hayat wanda ke kokarin miƙewa don komawa bakin aiki.
“Ba ka ganin ya yi nisa? Idan ta bayyanamusu komai fa?”
Dariya Hayat ya yi jin maganar Salma.
“Cool down Darling. Hakan ma ba mai yiwuwa bane saboda babu ta yadda za’a yi wacce ba ta ji ba ta magana dare daya ta soma. Duk da na sani it is not natural, amman ba za yiwu ba. Ina da ayyuka ne, a bari zuwa Weekend din.”
Gyada kai Salma ta yi tana murmushi.
“Kuma fa hakane, na yarda da aikin mutumina, ko ba komai idan ya yi sai an ci wuya kafin a karya.”
Suka yi dariya banda Hanan da ke kokarin cusa kudadenta a jaka yayinda jikinta har rawa yake. Itama mmiƙewar ta yi ta dubesu.
“Shikenan, ni na wuce. Sai ranar, Halima kya basu lambar wayata.”
Daga haka ta yi gaba, burinta ta je ta yi ƙarya. A kwashi ƙawaye a tafi wurin shaƙatawa.
“Halima take kiranki ba Mama ko wani abin ba?” Fadin Salma tana yamutse fuska.
“What do you expect a zaman Bariki?”
Fadin Hayat yana dariyar rainin wayo sadda ya sanya kai ya fice. Tsaki Halima ta yi.
“Sai me? Ni ba damuwata ba ce. Salma kina sane da maganarmu ko? Wallahi kar ki min halin ƴan duniya don na fi ki iya bu…uba!”
Salma ta ji kamar ta shaƙeta sai dai ta danne gudun kada allura ta tono garma.
“Naji, kya bari dai a kashe wannan wutar. Don idan aka bar ta sai dai a zubar da tokarmu a ruwa.”
Gyada kai Halima ta yi tana mai miƙewa.
“Shikenan, ina jira. Zan turo miki lambar Hanan ta whatsapp.”
Daga haka ta yi gaba Salma ta bi bayanta da harara gami da jan tsaki. Sai a sannan hankalinta ya koma kan Fu’ad wanda kwana biyu ba ta ganshi ba. Wannan tashin hankalin ya rufemata idanu. Wayarta ta dauka ta danna kira sai dai har ta katse bai ɗaga ba. Tsaki ta ja ta yi jifa da wayar ta shige ɗaki.
*****
Kyakkyawa ce ta gaske don idan ba ta yi magana ba sai ka dauka wata buzuwar ce daga Agadez. Siririya kuma doguwa, a tsawo zasu yi kai ɗaya da Shuraim sai dai ba ta da dirin jiki kamar sanda haka ta tafi. Tana da yawan fara’a.
Tunda suka shigo ta ɗora idanu a kanta ta kauda kai ta ci gaba da yin aikin makarantarta. Hira suke da dariya yana janye da akwatinta. Salima Idris Zakariyya kenan, matashiyar budurwa wacce duka rayuwarta a ƙasar Egypt ta yi shi. Iyayenta haifaffun Kano sai dai zama ya maida su Misra kasancewar mahaifinta ambassador na Nijeriya. A can ta yi karatunta, wannan yasa ta ke jin larabci sosai. Iyayenta suka dawo Abuja da zama ita kuwa ta yi saura a Misra sakamakon karatun da ba ta kammala ba.
Zamansu a can ne ya jawo mata shaƙuwa da Shuraim, har ba ta ankara ba so da kaunarsa suka mamaye dukkan ilahirin jiki da zuciyarta. Tun tana ɓoyewa iyayen har suka gane, shi kuwa koda maganar ta zo gareshi, dariya kawai ya yi ya kuma tabbatarwa Mahaifiyarsa babu wannan a ransa. Ita kuma ta ce bai isa ya ba ta kunya ba za ta ba shi lokaci.
Khairat ta fice a guje ta rungumeta tana mata oyoyo. Wannan ya ja hankalin Umma da Anti Khalisat gareta.
“Lale marhabin.” Fadin Anti Khalisat tana mai sakin fuska. Salima ta karaso ta rungumeta cikin harshen larabci take fadin,
“Nayi kewarki Ammina.”
Dariya Anti Khalisat ta yi.
“Nima haka ɗiyata. Ya su Ummintaki?”
“Suna nan lafiya.” Ta amsa da Hausa.
Ta karasa ga Umma wacce ke mata sannu da zuwa ta gaisheta. Umma ta amsa tana mai yabawa da halayyarta. Amir ma ya gaidata. Shuraim ya sa hannu ya fisge biron dake hannun Amira wanda ya sanyata ɗago kai a dole, harararsa ta ɗago da zummar yi idanunta suka shiga na Umma da ta galla mata harara. Gane kurenta ta yi don haka ta gaida Salima fuska a sake. Salima ta karaso ta miƙa mata hannu gami da yi mata sallama, Amira ta amsa da murmushin da ba ta san sadda ya suɓuto mata ba, ba ta dauketa a mai saukin kai har haka ba.
Zama Shuraim ya yi gefen Amira bayan ya sa hannu ya ture litattafanta da hannu.
“A koyi tarbar baƙi.”
Ta saci kallonsa ta kauda kai ta shiga tattara litattafanta.
“Mami kinga yanda wannan yarinyar ta ƙara girma da kyau ko? Fari kuwa kamar ta san wa wasu.”
Ya ƙarashe yana mai satar kallon Amira. Anti Khalisat da murnar ganin Salima ya rufemata idanu ba ta wani tsaurara wurin tauna maganarsa ba balle ta firzar.
“Bari kai kam, Salima ta ƙara girma wallahi kamar irin an shekara ba’a ga juna ba.”
Salima dariya ta yi tana mai gyara zaman Jidda a saman cinyarta, idanunta a kan na Shuraim ta yi mai farr da idanu.
“Wallahi Laah, yanda kewarka ta dameni ina ni ina wani kyau?”
Ya basar gami da murmushi ya maida dubansa ga Anti Khalisat.
“Abba bai dawo ba ko?”
Ta harareshi kadan don ta gane.
“Bai dawo ba tukunna.”
Ya jinjina kai gami da miƙewa.
“Bari na dan je na runtsa kadan, na gaji.”
“Har yanzu kana nan da baccin rana?” Fadin Salima tana murmushi.
“Me za’a fasa? Wannan ai rago ne, idan ya tafi camp za ga yanda zai yi.”
Akai dariya, Amira ta dubeshi.
“Bani birona.”
Alokacin ya tuna da biron da ya karɓar mata.
“A’a Amira, shigar da jakarta ɗaki mana sai ki kawomata ruwa. Rubutun kya yi daga baya.”
Umma ta fadi kafin Shuraim ya karɓi maganar. Ta mike ba musu ta ja trolley din ta nufi dakin dake kusa da nasu a sama wanda tun safe Anti Khalisat ta gyarashi tas.
Ta ajiye ta juya kenan ta ganshi tsaye a kofar dakin ya harɗe hannu da kafa ya jingina kai da kafadarsa da kofa. Tsuke fuska ta yi gami da giftashi za ta wuce ya yi azamar tare hanya. Ta dubeshi.
“Mene haka wai?”
“Komai ma.” Ya furta ƙasa-ƙasa yana murmushi. Ta kauda idanunta sakamakon kallon da yake bibiyarta da shi ya mata tsauri.
“Ka matsa na wuce.”
“Anƙi, sai an fadamin dalilin da yasa aka kasa nutsuwa har sai da aka turomin wasikar ban hakuri.”
Ta ja guntun tsaki.
“Yarinyarnan kina sona fa, ganewa ne ba ki yi ba ko?”
Abin ma ya bata dariya har ta murmusa. Shima murmushin ya yi gami da nunata da yatsa.
“Kin gani ko? Na fadi gaskiya.”
Ta girgiza kai.
“Ina Amirar ne?” Suka tsinci muryar Anti Khalisat wanda hakan ya sanya ta saurin wucewa ta gefensa bayan ta tura hannunsa.
Ya yi dariya, ba karya shi kansa ya san ba karamin so yake yi mata ba. Ba kuma shi da burin da ya wuce na aurenta. Ba ruwansa da karancin shekarunta, tunda har ta wuce munzalin yarinta, ya tabbatar tana fahimtar dukkan zantukansa.
*****
Ta koma wata shiru-shiru, tun bayan da ta farfaɗo daga ciwon mara, sai tunani ya zame mata abin yi. Maryam ta sha tambayar damuwarta sai dai ta girgiza kai ta nuna ba komai. Sai ta bingire da wata hirar.
Kamar yau ma, labari aka ba ta akan zuwa gidan Nuriyyah da zasu yi da kuma na sallamar da aka ba Engineer a ranar sai dai ko a jikinta. Yaha ta rike haɓa.
“Wai kuwa Indon Maryam lafiyarki kuwa? Kwanakin nan na lura kin sauya kada dai duk girman ne ya sauyaki?”
Murmushi ta yi wanda ya fi kama da yaƙe.
“Ashe ba ni kadai na ankara da ita ba, na yi maganar duniyarnan amman yarinyarnan ta cemin ba komai. Bansani ba ko kishin ne ya motsa.” Faɗin Gwaggo Kubra cike da zolaya banda murmushin ba abinda Humaira ta yi. Karshe ta sunkuyar da kai ba ta sadda ta soma zubar hawaye ba. Salati suka sanya, suka buga suka raya sai dai ta ƙi ce musu komai. Wannan ta sanya Yaha miƙewa da zummar zuwa sanar da Maryam. Da sauri Humaira ta rike hannunta tana kuka gami da girgiza kai.
“Don Allah ki yi hakuri.”
Ganin abin na neman fin karfin Gwaggo ya sa ta umarci Yaha ta miƙa Humaira ga Malam ko za ta fadamasa. Yaha ta ja hannunta har gaban Malam Kabiru, ya yiwa Yaha umarnin barin wuri. Bayan sun fitarta ya dubi Humaira.
“Indo, jikata, fadamin meyafaru?”
Humaira da kanta ke a ƙasa ta girgiza kai. Murmushi Malam Kabiru ya yi.
“Ki sani babu abinda Allah ba Ya magancewa bawa. Babu abinda ya fi karfinSa. Ki yi hakuri, ko menene a ranki ki yi hakuri. Ki mika lamarinki ga Allah. Idan har kin ji ba za ki iya fadamin ba, ba zan matsa akan lallai sai kin fada ba amman ki sani wannan damuwartaki, za ta shafemu da kuma mahaifiyarki. Tana cikin wata damuwar ki taimaka kada ki sanyamata wata.”
Jin hakan ya sassauta zafin da take ji a zuciyarta. Sai a sannan ta samu damar firzar da abinda ke cin ranta.
“Baba Malam meyasa a makaranta bana amfani da sunan Babana? Mama ta cemin ya mutu, amman har yau ba wanda ya fadamin sunansa.”
Ta ba shi tausayi, ya yi mata nasiha akan ta yi hakuri. Ta kuma yi addu’a mahaifiyarta ta dawo cikin tunaninta ko mene za a ji. Ya ga ba amfanin ɓoyemata komai, don haka ya yi mata bayanin dukkan abinda ya sani game da Maryam da yanda ta zo hannun Malam Zakari. Ta ji abin kamar almara, ba ta taɓa zaton ba su Inno ne iyayen Mamarta ba. Ta ci kuka ta kuma jin tausayi da kaunar Mahaifiyarta, Malam Kabiru ya dora da yi mata nasiha akan ta kwantar da hankalinta ta kuma tsawaita addu’a, wataran labari zai sauya da iznin Allah.
Da wannan ya sallameta bayan ya ga murmushi saman fuskarta.
*****
Falon yake karasowa gami da karewa dattijuwar dake zaune cikinsa kallo, Inna ta kara gyara zama a cikin lumtsumemiyar kujera mai zaman mutum biyu. Ganinsa ta shiga washe haƙoranta.
“Lale da jikana.”
Fu’ad bai fahimceta ba, ya dai gaisheta ya nufi hanyar bangaren Salma. A hanya suka yi kiciɓus. Ta daure fuska gami da watsa mishi tambaya.
“Na yi maka magana jiya ka kyaleni, yanzu sai ka bani amsa. Ina kake zuwa?”
Ya yi murmushi hakan ya bata mamaki, da ace a baya ne watakila ma ya ja tsaki ya gifta ya wuce abinsa.
“Yi hakuri Mum, na yiwa ɗan uwana rakiya Yobe.”
Gabanta ya faɗi,
“Waye hakan?”
“Adam.”
Mutumin da ta tsana duk cikin yaran Hayat tsabar yanda ya ke daukarta a kaikace. Ta tsani alaƙarsu sai dai a gefe daya yanayin yanda Fu’ad din ya nutsu kan burgeta.
“Lafiya dai? Yauwa Mum, wace ce a falo ne?
“Uwar uwarka ce! Wato ni yawa uwar da yake ba ka dauketa komai ba ka kyaleta zaune ban ce ma ka gaisheta ba. Amman ka iya ka kwashi jiki ka je can wani garin wurin mutanen da ba dangin iya balle na Baba ko? Ya yi kyau!”
Daga haka ta yi kwafa ta wuce shi fuu zuwa falon, sam bai gane Inna ba ce. Bai taɓa ganinta ba sai a hotonta na aikin hajji da ta yi, shima tun da sauran kuruciya. Bai ma yi zaton ganinta haka ba, ya dauka family na Mum masu kuɗi ne duba da yanda sukan samu baƙi ƴan ƙarya kuma ta sha fadamasa cewar ƴan uwanta ne. Juyawa ya yi zuwa falon, ya zauna suka kara gaisawa da Inna har da janta da hira da dariya, sai kuma a sannan Salma ta ɗan sakarmishi daga bisani ya shige ya bar su nan. Inna sai da ta tabbatar ya wuce kafin ta fiddo wasu kullin layu ta miƙa mata. Salma ta karɓa ta duba kafin ta kalleta.
“Wai kuwa kin ji me na ce? Kakar Fu’ad ke kirana akan lallai suna don ganin jikansu, ni kuwa ba zan lamunta ba. Wannan layun me zan yi da su?”
“Kayya Salame, ba ki iya cin ribar zance ba. Kya jira dai ki ji inda na nufa ko?”
Salma ta yamutse fuska kawai.
“Karfe ukun dare, daren ma na ranar Lahadi kamar yanda Gagarabadau ya bukata, za ki tashi ki zagaya bayan gidanki, a cikin gidan kenan. Sai ki nemi tulu ki yi rami ki cusa tulun a ciki, daga nan kuma ki zura layun a cikin tulun ki kira suna surukar akan a haneta zancen shi yaron. Daga nan ki binne. Idan har kika yi nasarar binnewa kuma ko kukan karnuka babu a wannan lokacin to ki sani babu su babu ɗan nan. Ki tabbatar babu kukan kare ko ɗaya. Sannan ki tabbatar ba wanda ya ganki.”
Murmushi Salma ta yi.
“Shiyasa nake sonki, ai unguwarnan ma ban jin akwai kare. Ban ma taɓa jin haushinsa ba.”
Dariya Inna ta yi.
“Yauwa don an fi son hakan.”
Dadi kamar ya kashe Salma, ta tabbatar a ranar za ta yi. Inna ba ta tafi ba sai da abin arziki kala-kala da kudi. Takanas ta sanya direba ya maidata gida.
*****
Motar ta yi parking nesa kadan da kofar gidan, ya juyo ya dubeta. Sanye take da hijabi da nikaf kamar yanda suka bukata. Hayat ya dubeta gami da yi mata nuni da gidan.
“Ga gidan can. Kina iya zuwa, duk yanda ku ka yi kimin koda karamin saƙo ne ta waya.
Murmushi Hanan ta yi.
“Ba matsala.” Ta gyara zaman jakarta ta fita, kasancewar rana ce sosai, hakan ya sa babu mutane sosai, wannan tasa ba wanda ya ankara da su. Sai da ta kai kofar gidan kafin ta ɗaga nikaf dinta ta kalleshi su yi murmushi ya ja gilashinsa na mota ya rufe ya yi gaba. Ita kuwa ta cusa kai ciki da sallama.
I like the book
This is so interesting and I love the idea