Skip to content
Part 26 of 41 in the Series Rumfar Kara by Rufaida Umar

Babu kowa a tsakar gidan sai Humaira, ta bada himma sai dakan yaji take sakamakon wainar fulawar da Yaha ta ce za ta yi. Tsayar da dakan ta yi ta dubi mai sallamar. Hanan ta sakarmata murmushi, itama Humaira ta maida mata martani duk kuwa da cewar na ta da masaniyar ko wacece.

“Sannu da zuwa, Bismillah shigo, Gwaggon na ciki.”

Fadin Humaira wacce duk a zatonta baƙuwar ta Gwaggo ce.

“Toh.” Fadin Hanan, bisa jagorancin Humaira suka shiga ciki, Gwaggo ta yi saurin miƙewa zaune

“Indo, Maryama ce suka dawo?”

“A’a Gwaggo. Baƙuwa ki ka yi.”

“Tooh, ikon Allah, ce ne ta karaso. Ni na yi zaton ma Maryama ce ta dawo.”

Humaira ta girgiza kai ta fita waje don kawo ruwa kamar yanda aka koyamusu, idan baƙo ya zo abu na farko da za’a ba shi ya kasance ruwa. Hankalinta ya kasu biyu da tunanin ko wace shawara za’ayi da Mamanta da ta shiga meeting din iyalan Engineer? Takanas Yaha ta wuce da ita da zummar Malam Kabiru da yan uwansa na nemanta. Humaira ta so zuwa saboda ta rubuta mata sai dai Yaha ta ce ta bar shi suna tare.

Da wannan tunanin ta debi ruwan ta koma ciki da sallama. Har yanzu da shiru ba wanda ke magana tsakaninsu.

“Baiwar Allah ban shaida ki ba.”

Murmushi Hanan ta yi gami da gyara zama.

“Nima yau ne ranar farko da na taɓa ganinki Iya, na zo ne kuma domin don ganin ƴar uwata da naji labarin cewa tana hannunku.”

Humaira ta kasa fita ta yi tsai tana duban Hanan, Gwaggo na daga nata ɓangaren sai ta yi turus.

“Humaira! Humaira! Gwaggo!!”

Muryar Yaha suka tsinta tana rangaɗa kiran sunansu, cikin daga murya.

A gigice suka mike suka fito. Hanan kuwa ta mike ta yi jikin tagar ɗakin tana mai kasa kunne.

Mintocin Da Suka Gabata

Tun shigarsu falon take duban jama’ar wurin, kirjinta ya ci gaba da lugude sai dai duk da haka Allah take ta ambato a ƙasan ranta. Engineer ne sai kuwa yan uwansa maza da mata babu ɗansu ko ɗiyarsu ko guda. Ganin yanda kowannensu ya zubo mata idanu sai ta sunkuyar da kanta, jikinta har rawa yake ta samu wuri ta zauna, alama ta yi musu da kai da hannuwanta alamar gaisuwa. Suka amsa.

Malam Kabiru ya sa hannu ya dauki takardar da ya riga ya rubuta tun kafin zuwanta ya miƙamata. Karɓa ta yi ta shiga karantawa.

“Maryama kada zaman nan ya jefa zuciyarki cikin ruɗani, ki kwantar da hankalinki ba ma nufinki da komai sai alheri. Wasu hotuna kawai zamu nunamaki ki mana nazarinsu ko kinsan fuskar.”

Tana gama karantawa ta dubi Malam Kabiru cikin sanyin jiki ta gyaɗa kai tana ɗan murmushin da ya ɓoye fargabarta. Ya gyaɗa kai. 

“To Alhamdulillah.” Ya dauki hotunan ya miƙamata. Hannunta na rawa ta karɓa ta shiga dubawa. Cak ta tsaya, lokaci guda ta ji kamar an tsotse mata ruwa da jinin jikinta. Fuskar ba yau ta santa ba, fuska ce ta makusanciyarta.

Da wani irin sauri da rawar jiki ta yi jifa da hoton farko ta tafi na biyu, komai yana dawomata. Gumi ya tsastsafo daga goshinta.

“An…an…Anna! Anna!”

Muryarta ta karaɗe falon gaba daya, Engineer da ke a dan jingine bai san sadda ya mike tsaye da wani irin kwarin da bai san akwai sauransa a shekarunsa ba. Ba komai ya razana shi har haka ba illa muryar Maryam wanda ya yi ɗaya da na Rumaisarsa.

Toshe kunnuwanta ta yi wadanda suka soma zafi da radadin da ba ta san dalili ba, a hankali suka shiga fidda wani irin ruwa, ta ci gaba da salati ta kife a jikin Yaha. Nan da nan kowa ya yi kanta.

Malam Kabiru ya dubi Yaha,

“Yi sauri tafi gida ki karɓo rubutun da nake ba ta, ki tahomin da jarkar zamzam.

Wannban ne ya sanya Yaha da azama ta zame kan Maryam da ke a jikinta tana kuka ta fito zuwa bangaren Malam Kabiru kamar wata zararriya.

“Lafiya? Me yafaru Yahanasu?” Fadin Gwaggo zani na faɗuwa tana taku da kyar.

“Mamana ce ko?! Mutuwa ta yi?” Humaira ta furta a gigice. Kirjinta kamar ya tsage tsabar bugu. Daga daki Hanan kuwa ta yi tsuru tana jiran amsar da zai fito daga bakin Yaha.

“Ba lokacin dogon bayani bane, sai dai bakin Maryam ya buɗu. Gwaggo ina zamzam din Malam? Ke Humaira yi azamar daukomin rubutun da Mamanki ke sha wanda Malam…”

Tun bata karasa ba Humaira ta yi wuf ta faɗa ɗaki, ita kuwa Yaha jin Gwaggo na kiran daga ina Malam ya ajiye tsabar ruɗu da farin ciki a gefe guda, ya sanya ta bin bayanta. Ganin haka Hanan ta dauki jakarta da azama ta fito daga gidan takalmanta a hannu. Sai da ta kai kofa kafin ta sanya ta fice tana maida numfashi. Tun a hanya ta dau waya ta kira Hayat ta fesa mishi labarin da ta ji. Iyakar tashin hankali ya shiga karshe ya ce ta zo su yi maganar a nutse don kamar bai gama jin daidai ba.

Su kam babu wanda ya tuna da Hanan tsabar fargaba da kuma murnar abinda ya afku, Humaira har da kukanta, ji take kamar ta miƙewa yi wurin Mamarta sai dai an gargaɗeta da zuwa hakan yasa dole ta hakura.

*****

Ta farfaɗo tana mai sakin atishawa har uku a jere, karshe ta yi hamdala ga Mahaliccinta. Ta ci gaba da duban mutanen da ke a falon sai kuma ta fashe da kuka tana girgiza kai.

“Maryama, hamdalar dai za ki ci gaba da yi. Kuka ba zai magani ba. Ki yi hakuri kinji? Ki sanya a rai wannan ne jarrabawarki.”

Fadin Gwaggo Hannatu tana matse nata hawayen. Engineer ya bude baki zai watsamata tambaya Malam ya dakatar da shi da sauri ta hanyar girgiza kai. Dole ta sa Engineer shiru sai dai ko’ina a jikinsa banda rawa ba abinda yake yi. Hamdalar da aka ambatawa Maryam, shi ya shiga jerowa.

“Bansan me zan ce muku ba, na yarda dukkan iko da rahma na Ubangiji ne. Shi kadai ke mulkar ruhinmu. Ban ce ba’a warkewa daga irin larurata ba, sai dai nikam har na dangana da kalar rayuwar da Allah Ya zaɓamin.”

Tana kaiwa nan ta kara ɗaukar hotunan tana ƙaremusu kallo. Ta ɗago ta dubi Engineer.

“Hotonnan ya tunamin da Anna Mahaifiyata, a wurinta nake ganinsa, na kuma san kakata ce a hoton. Baba tun sadda idanuna suka soma ganinka naji gabana ya fadi sakamakon tsantsar kamannin da ku ka yi da Rasheeda, Mahaifiyata. Allah bai ban ikon tuna komai ba, wannan ta sanya na hutar da kwakwalwata daga ciwon kai na yakice tunanin da ke fin karfin zuciyata a koyaushe. Sai dai don Allah ya ku ke da Anna?”

Muryarta har rawa yake tsabar ruɗewa. Dakyar ta karasa zancen.

“Ban santa ba, sai dai ina tunanin wani abu game da ita.”

A gajarce  Engineer ya labartamata alaƙarsa da Rumaisa da kuma silar rabuwarsu.

Yada kai ta shiga yi kamar wata ƙadangaruwa tana kuka.

“Wallahi kai ne Anna ke nema, kai ne mahaifin Anna. Anna ba ta rabo da kuma da tunani, burinta ta yi tozali da mahaifinta, ba ta san inda za ta sameka ba saboda har Innarta ta rasu ba ta da cikakken bayani akanka. Ta dai san sunanka Bello, ta kuma san a kasar waje kake rayuwa da iyalinka. Amman ba ta da masaniyar dawowarsa Nijeriya balle ta san garin da kake da zama.”

Tana kaiwa nan ta yi shiru tana mirza idanunta wadanda suka yi ja su na kuma raɗaɗi tsabar kukan da ta ci. Kowa a falon sai da ya daku da jin mutuwar Rumaisa. Engineer kuma kuka sosai ya shiga yi yana salati gami da nemamata rahmar Ubangiji.

Sai da komai ya lafa kafin Malam Kabiru ya ba Maryam damar bada tarihinta garesu. Maryam ta dubeshi da alamar roko.

“Malam da za ku yimin wata alfarma da naji dadi.”

“Fadi kanki tsaye jikata, kar ki shakkar komai.”

Fadin Gwaggo Hadiza. Murmushi Maryam ta ɗan yi gami da russana kai.

“Baba da Inno, sun min taimakon da ba zan iya fadin tarihina alhalin ba sa wurin ba. Da ace za’a yimin alfarmar gayyatosu kafin..”

Ta kasa ƙarasawa hakan yasa Malam Kabiru murmusawa.

“Na fahimceki, hakika kuma kin yi tunani mai kyau. Duk ɗa na halak, ba ya mance halacci. In Sha Allah, a yau zan sanarmusu da zuwanmu ta waya idan ya so gobe sai mu dunguma. Amman me ku ka ce?”

Ya waiwaya ga yan uwansa, kowannensu ya yi na’am da hakan ba don ransu ya so ba sai don a ba Maryam damarta. Kuma ta fi su gaskiya. Da wannan abin farin cikin ta mike tare da Yaha suka fito. Sai da suka karasa cikin gidan Engineer kowa na mata barka da samun lafiya, ita kam sai matsar kwallah da gyaɗa kai kawai take gami da amsawa. Wani abu ne tokare a ƙasan ranta, tun farfadowarta ta ke tuna rasuwar mijinta kuma mahaifi ga ɗiyarta. Ba ta jin har ta gushe a duniya za ta iya mancewa da abinda kunnuwanta suka tsinkaya a kwanaki hamsin da rasuwarsa. Har abada fuskokin mutanen ba zasu taɓa ɓacemata ba.

*****

Kawu Lawwali ya dubi yan uwansa bayan fitar Maryam.

“Ba kwa ganin ya dace maganarnan a yi ta gaban yarannan? Saboda ko bamu ji sauran bayanai ba, zai iya kasancewa Maryam tsatsonmu ce. Ko ya ku ka ce?”

Girgiza kai Gwaggo Hadiza ta yi.

“Gaskiyarka Lawwali, sai dai kuma dole zamu bi komai a sannu mu soma jin cikakken tarihin Maryam. Daga nan idan ya so sai a ga abinda ya kamata.”

“Hakane Yaya, nima ina bayan maganarki. Zai fi.”

Fadin Gwaggo Hannatu. Kowa ya yi na’am da hakan. Karshe aka fito aka ba Engineer wuri don ya kara hutawa ganin ya soma haki.

*****

A bangaren Maryam kuwa, su na shiga gidan Malam Kabiru, Humaira ta taho a guje ta rungumeta sai kuka. Ganin hakan itama Maryam ta ajiye kunya ta rungumeta tana kukan. Tausayi biyu take a kanta, na maraicinta da kuma irin karɓar da ta ke ganin ba lallai ta samu ba daga dangin mahaifinta. Bai kuma zama lallai su aminta da cewa ita din jininsu ba ce.

“Haba Maryama, ai kuka ba zai miki ba. Ki share hawaye ki yi ta godiya ga Mahaliccinki da ya kawo karshe kukanki. Wannan ranar ta farin ciki ce.”

Wani daɗi ya ƙara ratsa ta jin yanda ta ji kalaman Gwaggo raɗau cikin dodon kunnenta. Tana murmushi ta gyaɗa kai gami da janye Humaira daga jikinta. Humaira banda kallonta da washe haƙora ba abinda ta ke yi. Tana murnar soma maganarta, ta tabbatar ko ya ya za ta fidda ita daga duhun da take ciki game da mahaifinta da sunansa.

Ranar kusan wuni aka yi hira tsabar murna da farin ciki.

*****

Ba ya fatan ya runtsa, ba ya fatan ya tuna abinda ya faru a daren jiya. Wannan na ɗaya daga dalilin da ya sanyashi barin gidan gaba ɗaya zuwa gidan su Haidar.

*****

Awanni Takwas Da Suka Gabata

Al’ardarsa, zai wahala ya kwanta bacci ba tare da ya farka da niyyar rage mara ba. Kamar koyaushe cikin baccin ya dinga jin alamar fitsarin a mararsa, sai dai kwuiya da wani irin baccin wahala ya hana ya iya buɗe idon balle ya kai ga miƙewa. A dole ba don ya so ba ya miƙe tsaye yana jin kamar a duniya fitsarin kan shiga rayuwarsa. Yakan katse mishi daddaɗan bacci, ya yanke dole ne ma ya samu likitan mata (Yaya Adam) ya ji ko akwai abinda zai iya mishi. Don kansa kuma ya murmusa ganin haɗin gwamutsin da ya ayyana.

Tun yana ciki ya ke jin kamar karar tona wani abu a bayan bandakin, sai dai ya kawo shawagin tsuntsaye ne kawai. A karshe ya ji bai gamsu ba wannan ya ba shi damar ƙarasawa ga faɗaɗɗan windon bandakin, har zai ja igiyar labulen ya zugeta, sai ya yi shawarar kashe fitilar bandakin gudun abinda zai gani din kada ya aje baƙin dare ne.

Dawowa ya yi ya zuge labulen sannan ya ƙurawa wurin ido. Mustsike idanun ya kara yi domin a ganinsa ba su nunamishi daidai ba. Mum dinsa ce durkushe cikin harshen dinsu, ba ta shakku akan yanda fitilun wurin suka haska ta, ta dage sai haƙar rami take ga wani tulu a gefenta. Girgiza kai yake kirjinsa na wani irin bugu. Ya kasa hakuri sai da ya sauko ƙasa, a gaggauce yake tafiya har ya ƙaraso inda take.

“Mum?”

Ya furta da alamun mamaki zagaye da shi. Ta yi saurin kai duba gareshi a gigice ta mike gami da sakin fartanyar ta faɗi saman tulun ai kuwa ya bada kara tus! Tare da shi suka dubi tulun kafin ya daga kai yana dubanta cike da matsanancin tsoro da fargabar ganin layun da ke gefen tulun a ajiye. Bai san hawaye yake fitarwa ba sai da ya ji su na kokarin shiga bakinsa.

“Mum me kike yi? Tsafi? Tsafi kike yi?!”

Salma gaba daya ta ruɗe, ta shiga girgiza kai ga wani fitsari da ke shirin suɓucemata, gumi kam ba’a magana. Ta karaso gareshi tana magana kamar mai raɗa.

“No son, ba abinda kake tunani bane. Yimin akai shi ne na zo tonowa.”

Za ta riƙe hannunsa ya yi azamar ja da baya.

“I hate you!” Ya furta kansa tsaye sannan ya juya a gaggauce ya bar wurin. Babu damar kiransa kasancewar dare ne tana tsoron wani a gidan ya ji. Wannan ta sanya jiki na rawa ta tattare layun da suka zame mata asara da kuma bala’i ta bar wurin gaba ɗayansa. Koda ta koma ciki a tsakar ɗakinta ta yi ciki da su ta faɗa banɗaki da gaggawa. Kafin ma ta kai ga karasa zama ta soma malala fitsari, ashe wai har da zawo ba ta da masaniya akai. Abinda ta riga ta sani shikenan karshenta ya zo, asirinta ya tonu wurin Fu’ad, ya san komai game da halayyarta da ta yi nasarar ɓoyemishi shekara da shekaru, tasan yanzu ko za ta haɗiyi Kur’ani, yaron ba zai aminta da duk wata ƙaryarta ba. Sai da ta gyara jikinta kafin ta dawo tsakar dakin a saman kafet ta zube. Kuka ta ke har da sheshsheƙa, ta tsinci kanta da ja wa Innarta Allah Ya isa ta fi cikin kwando, a cewarta ita ta jazamata wannan bala’i na binne-binne a tsakiyar dare wanda ya yi silar tonuwar asirinta wurin tilon ɗanta.

CI GABA…

Haidar ya shigo dakin hannunsa riƙe da gorar ruwa yana sha. Ya kara kai dubansa ga inda Fu’ad ke kwance ya ja tsaki gami da karasawa ya zauna gefen gadon.

“Wai kai don ubanka ba za ka bude baki ka yi magana ba? To da ka ƙi faɗamin damuwarka a tunaninka shiru zai magance maka? Haba mana! Tun zuwanka ka wani jibge a gado, sallah ma ba don ta zama dole ba nasan ba tashi za ka yi dominta ba. Ka fadamin damuwarka.”

Fu’ad ya ja tsaki, idanunsa suka kaɗa lokaci guda, me zai ce? Sai ya bude baki ya faɗawa Haidar cewar Mum dinsa ya gani cikin dare tana tsafi ko me? No, ba zai iya ba.

Ganin tsakin da ya ja ya sanya Haidar taɓe baki gami da ɗaga kafaɗa.

“Do as you wish! Idan ka ga dama ka fito mu yi Lunch if not wallahi yanzu zan turomaka Dad ko kuma na kira Yayanmu na kai ƙararka.”

“Oh shit!” Fu’ad ya furta gami da wani irin zabura ya miƙe har sai da ya ba Haidar tsoro. Meyasa ma bai tuna da Adam ba? Shi kaɗai ne zai iya ba shi shawara ko kuwa nasihar da hankalin sa zai kwanta kuma ya samu nutsuwa. Da sauri-sauri ya faɗa banɗaki, Haidar ya bishi da kallon taɓaɓɓe kafin ya miƙe ya fice.

A gaggauce ya shirya cikin ƙananun kayan Haidar sannan ya fice. Sai tashin motarsa suka ji. Mahaifiyar Haidar ta dubeshi.

“Wai meke damun Fu’ad ne?”

Taɓe baki ya yi gami da ɗaga kafaɗarsa bai ce uffan ba. Ganin haka ta share zancen.

*****

Kansa tsaye ya faɗa ofishinsa ba tare da ya ƙwanƙwasa ba. Adam ya dakatar da shi da hannu gami da faɗin.

“Please ka jira, ina aiki.”

Sai a sannan ya hankalta da mace mai juna biyu a kujerar ganin marasa lafiya. Cikin rashin kuzari ya fita gami da tura kofar. Adam ya ja numfashi, ya tabbatar akwai wata damuwar babba a saman fuskarsa, sai dai dole ya jira ya kammala. Ba ya kaunar abinda zai shiga hurumin aikinsa.

Sai da ya kammala duba marasa lafiya da suka yi mishi saura har uku, kafin ya nemi Fu’ad a waya sai dai a kashe.

Yana yunkurin miƙewa ya fita wurinsa ya shigo. Zama ya yi ɗabas saman kujera yana maida numfashi. Adam ya koma mazauninsa yana dubansa a nutse. Ruwa ya zuba a kofi ya miƙa masa. Ba musu ya kwankwaɗe, ya ƙara zubawa ya miƙa nan ma ya shanye.

“Meyafaru haka? Meke damunka?”

Ya dubeshi idanunsa sun kaɗa, kamar ya yi magana sai kuma ya shiga girgiza kai. Uwa uwa ce duk lalacewarta kuwa, ba zai iya yi mata tonon silili ba. Adam ba bare bane, sai dai akwai tabon kiyayyarta a zuciyarsa. Ba lallai ya kara ganinta da kowane irin ƙima ba.

“Shiru.” Adam ya furta har sannan nazarinsa kawai yake yi.

Ya share maganar, duk yanda Adam ya so jin ko mene amma babu dama hakan yasa tilas ya rabu da shi kawai gami da mishi nasiha akan koma mene ya miƙa wa Allah.

*****

Da sauri-sauri ta shigo gidan da sallama, Baraka da Inno wadanda ƙarar tsayuwar motocin ya katsemusu hira, suka bi Jamila da kallo su na amsa sallamarta. Bakinta ya ƙi rufuwa tace.

“Inno, su Mama ne wallahi. Na hangota a motar.”

Jin haka farin ciki ya cika zukatansu, Inno ta mike tsaye tana gyara zaman dankwalinta.

“Maza je ki faɗawa Malam yana can kofar gidan Na Allo.”

Jamila ta fice cikin bin umarninta. Nan suka yi kiciɓus da Maryam, dadi da mamaki ya cika ta ganin ta ambaci sunanta, ai sai ta kasa tafiya aiken Inno suka dawo tare.

Sallamar da Inno ta ji da muryar da ta jima tana fatan sake sauraro ya sanya ta yi azamar kallon hanya. Ta yi kasaƙe tana dubanta don ta kasa ko motsi sai uban murmushi da take zabgawa. Tana a haka har sai da ta ji Maryam a jikinta ta rungumeta tana kuka. Sai a sannan ta samu damar rungumeta itama tana kuka da dariya lokaci guda. Har su Gwaggo Hannatu suka shigo ba su lura da su ba sai da Baraka ta yiwa Inno magana. Inno ta saki Maryam tana dubanta.

“Alhamdulillah, yau burina ya cika. Alhamdulillah ɗiyata ta warke. Oh ni Fati. Me zan ce wa Allah banda na bauta maSa gami da godiya gareShi?”

Aka yi ƴar dariya, dakyar Inno ta samu nutsuwa suka zauna, nan aka shiga gaisawa. Jin cewa tare suke da su Malam Kabiru ya sanya Inno ankara da Jamila wacce ta sanya kiran Malam.

“Au, ba ki tafi  kiransa ba?”

Da sauri Jamila ta mike ta fice ana dariya. Ba jimawa Malam ya zo tare da Buhari, bisa jagorancin Malam din gaba daya suka shigo cikin gidan. Aka zauna aka fara sabon gaisuwa. Anan shima Malam ya ji muryar Maryam garau, har da kwallarsa ta murna musamman da ya ji daga bakin Malam Kabiru cewar  ta dawo hayyacinta har ta tuna asalinta.

Bayan an nutsu Malam ke fadin ai da sun zo sun tarar basu garin don zasu je can Dambatta Kano, wurin yan uwan Inno. Daga bisani hankali ya koma kan Maryam bayan an sha ruwa.

Ta gyara zama kanta a ƙasa ta soma magana tana mai jin saukar wani irin dafi a ranta. Za ta so ayi komai agaban Humaira, za ta so a yau ta san mahaifinta, sai dai bisa umarnin su Malam Kabiru, sun ce ta yi hakuri har sai sun dawo. Da wannan ta hakura.

<< Rumfar Kara 25Rumfar Kara 27 >>

1 thought on “Rumfar Kara 26”

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×