Tushiya
Alhaji Sadik Ahmad, fitaccen mutum ne a jihar Gombe, ya rike mukamai da dama a zamaninsa, wanda daga bisani ya yi kaura daga garin Gombe ya koma Kano da zama. A maganar shekarun da suka gabata. Sauya mazauninsa bai wuce akan ɗiyarsa ɗaya tilo Rumaisa ba wacce matarsa Hajiya Yasmin Mohammad ta haifa mishi, adalilin ta yi aure a kasar waje daga bisani ta rabu da mijin ta dawo gida. Sai dai ko kadan Rumaisa ba ta da walwala a tun bayan dawowarsu, ya kasance babu wanda ta ke kulawa, ta koma shiru-shiru, kusan koyaushe tana cikin kuka da zubar hawaye. Wannan ya tashi hankulan iyayenta inda daga bisani Mahaifinta ya yanke komawarsu Bauchi. Ainahin garin mahaifiyarta Yasmin kenan. A haka ta ci gaba da rainon cikinta, cikin ikon Allah da kuma yawan shiga ƴan uwan mahaifiyarta da irin kulawar da take samu, ya sanya ta soma dangana da hakuri akan mijinta na farko wanda aka ce ta ci burin kara sanyashi a idanu da kuma gudanar da rayuwa tare da shi.
Ranar farko da ta soma zuwa ganin likita an tabbatar musu cewar cikinta na da mugun hatsari, sai anyi taka tsantsan wajen kula da ita da duk damuwarta idan kuwa ba haka ba za’a iya rasa ɗaya yayin haihuwa. Wannan ya tashi hankalin iyaye da yan uwa aka kara ƙaimi wurin lallaɓata da bata kulawar da ta dace. Itama adalilin ganin irin so da kaunar da ake mata ya sanya ta sassautawa ranta.
Cikin ikon Allah ta haifi diyarta mace, ta ci wuya ba kaɗan ba don a karshe ma aiki akai mata. Ranar suna yarinya ta ci sunan Rasheeda. So, kauna da kulawa babu irin wanda ba ta gani.
Tana da shekara biyu a duniya Rumaisa ta yayeta. Alokacin ta soma zuwa aiki a Kamfanin RUM Limited.
Ba jimawa masoya ta ko’ina suka soma fitowa neman aurenta sai dai ko sau daya ba ta ba kowa fuskar da zai tunkareta da zancen aure ba. A haka wani babban Manager a bankin Gold Bank, Jafar Isyaku, ya fito yana sonta. Matarsa daya da yara biyu, ta ce sam ba za ta aureshi ba. Kasancewar Allah Ya ƙaddara shi zai zama mijinta a wancan lokacin, sai iyaye suka shiga maganar, bayan nan kuma mai ɗa wawa, da irin yanda yake son Rasheedat da bata kulawa kamar mahaifinta ya sanya Rumaisa saukowa ta dangana aka yi aurensu.
Matsalar farko da ta soma fuskanta shi ne akan Rasheedat. Mahaifiyarsa da matarsa, suka bi suka tsangwameta, abu kadan za ta yi a goranta mata, yarinya karama da bata san komai ba. Wannan ta sanya Rumaisa tattarata ta maidata hannun iyayenta.
Shekara daya da aure ta samu cikin ƴan biyu, aka ciromata su ba rai. Likitoci sun bata tabbacin mahaifarta ta samu matsala wannan ta sa dole aka ciremata. Wannan ne silar da ta sanya Jafar ya dage akan karɓar Rasheedat daga hannun iyayen Rumaisa. Ba don sun so ba suka bar mishi ita.
A wannan tsakankanin ya samu sauyi na wurin aiki, daga branch din da yake zuwa wanda ke Kano. Ya tattara ya koma Kano tare da iyalinsa, Rumaisa a dole ta hakura ta ajiye aiki, tana kuka hakanan iyayenta suna yi, suka rabu.
Ta samu saukin tsangwama daga mahaifiyar Jafar, sai dai da sauran rina a kaba, don kuwa abokiyar zamanta Yusra, sai ta kara bada ƙaimi gun azabtar da Rasheedat da kuma ita. Rumaisa sam ba ta da faɗa, ba ta iya ba, a dole ta koya. Tun Jafar ba ya daukar sharri da maganganun da yake ji akanta daga bakin Yusra, har ya zo ya soma dauka.
Wataran haka zai kama Rasheedat yarinya kankanuwa mai shekaru uku a duniya, ya jibgeta son rai a dalilin ta yi mishi ɓarna. Tun Rumaisa na ganin kamar a hayyacinsa yake ta soma jin tsoro, take gani bai san me yake ba ganin yanda yake bala’in tsoron Yusra. Idan ba satar ƙafa ba, to ba zai taɓa takawa sashin Rumaisa ba alhalin Yusra na gidan. Sai ko idan ta fice zai zo ya lallaɓa ya biya bukatarsa ya kara gaba.
Rayuwa ta ci gaba da tafiya a haka har suka shekara biyu da aure, sa’ilin Rasheedat nada shekaru biyar a duniya. Ta soma fuskantar irin zaman da mahaifiyarta ke yi a gidan, sai ya kasance ta fi kaunar hutu ya zo ta tafi Bauchi wurin kakanninta har ba ta kaunar dawowarta Kano. Sai dai Jafar da zarar hutu ya cimma ƙarewa da kansa yake zuwa ya ɗaukota. A ransa yana jin so da kaunar yarinyar, a gefe guda bai san dalilin kiyayyar da yake garesu ba da zarar ya taka ƙafarsa cikin gidan. Sai ya soma jin haushin kansa, ya rasa dalilin da ya sanyashi ɗaukota daga Bauchi. Haka zai dinga goranta mata yana ambatonta da Agola ko marar asali. Anan ne suka yi fata-fata da Rumaisa, ta rantse ba za ta kara zama da shi ba muddin zai ci gaba da kiran diyarta da Agola ko marar asali. Rasheedat yarinya mai kaifin basira, ta haddace kalmomin sosai a kwanyarta duk da cewa ba ta san manufarsu ba. Takan yawaita tambayar Rumaisa sai dai ta nunamata ba komai bane.
Dakyar Jafar ke shawo kan Rumaisa a duk sadda ta botsare da cewar sai ya saketa, sai ya ji kamar ana rura wutar kaunarta a zuciyarsa, ya ji ba zai iyaba.
Cikin wannan hali labarin mutuwar iyayenta adalilin gobara da ya ci sashinsu a gidan ya risketa, nan take ta fadi ta suma. Ta yi kuka na fitar hayyaci bisa rashin iyayenta ababen kaunarta. Sai da ta yi watanni uku a Bauchi kafin ta tattara zuwa gidan aurenta. Dangin Mahaifinta suka danne hakkinta, ko kwandala basu ba ta na gado ba, abin ya daure jama’a da dama kai, daman zasu iya cin dunduniyar Alhaji Sadik a bayan idanunsa? Mutumin da ya daukesu kamar ciki daya suka fito, yake hidimtamusu da jiki da aljihunsa?
Har kotu dangin Yasmin sun yi niyyar shiga sai dai Rumaisa ta dinga mafiya akan su yi hakuri su bar zancen gudun lalacewar zumunci. A dole ba don ransu ya so ba suka hakura aka bar su da halinsu.
Wannan ya kara zubar da ƙimar Rumaisa a wurin dangin mijinta, aka dauketa wata marar daraja, nan ta kara fahimtar da yawa a dangin suna kaunarta ne adalilin abin duniyar da mahaifinta ya tara. Hakanan idan sun zo ba ta rasa abin ba su.
Ba ma a dangin miji kadai ba, da yawa a dangin Yasmin sun sauyamata sai dai wadanda suke uwa daya uba ɗaya da mahaifiyarta.
Ita da Rasheedat suka kara zama shara a gidan Jafar. Matsi ta ko’ina, Jafar sai ya ga dama yake kashe musu kwandalarsa.
A haka rayuwa ta ci gaba da tafiya har Rasheedat ta shekara goma sha biyar a duniya, da taimakon aljihun Rumaisa wacce ta koma aiki, ta samu ta kammala Sakandire, zuwa lokacin ta gano Baban Hasiya da Maaruf daban ne da nata mahaifin. Takan kallesu a masu gata tunda har sun san asalinsu, sun san tarihin rayuwarsu a yayinda ita har zuwa lokacin fama take da Rumaisa akan ta bata labarin inda za ta ta samu mahaifinta ko ta huta da gorin mutane. Sunan Jafar take amfani da shi a dukkan takardun makarantarta, shi ya soma daukarta ya kaita makaranta, ya sanyata a aji, ya kuma yi mata rajista da sunansa. Koda Rumaisa ta nuna a’a, ya hau ɓacin ran zata bambanta Rasheedat da yaransa, za ta nunamasa ba shi ne mahaifinta ba. Da wannan ta dangana ta yi hakuri.
Manema suka soma ɓullo wa Rasheedat, sai dai duk wanda zai soma zuwa, labari zai riskeshi kan cewar ba ta da asali, wannan ke korarmata duk wanda zai zo. Rumaisa ta gargaɗeta akan kula kowane namiji, burinta ta yi irin karatunta mai zurfi. Ita kuwa har a ranta ba ta da burin dogon karatu.
Cikin ikon Allah miji ya fitowa Rasheedat, Adam Zannah, Maraya ne kuma Malamin makarantar Sakandire na gwamnati. Yana da rufin asiri daidai gwargwado, duk yanda aka kai ga tsegunta mishi rashin asalin Rasheedat wannan bai sanya ya gujeta ba. Ya tsaya tsayin daka akan lallai sai ita. Farin ciki ya cika zuciyar Rumaisa, ta san kudi ba shi ne jin dadin rayuwa ba, tana da yakinin ɗiyarta ta samu miji mai kaunarta domin Allah. Ko faduwa ta yi ta mutu, ba ta da kaico.
Babu wani dogon bincike a wurin Jafar, ya karɓi kudin auren Rasheedat, aka sanya rana shekara daya a lokacin ya kammala ginin gidansa.
A daren suna hira da Rumaisa suna tattaunawa game da yanda za ta siya mata kayayyakin aure, Rasheedat ta yi shiru sai hawaye. Rumaisa ta dubeta da kyau. Ta san damuwarta. Kawai itama sai ta soma share hawayen, duk sadda za ta ga hawayen diyarta ba abinda ke zuwa ranta sai irin rabuwar da suka yi da Bello. Ta tabbatar har abada Bello ba zai zo gareta domin ɗiyarsa ba wannan ne dalilinta na zaɓar ɓoyewa ɗiyarta komai dangane da shi. Ta zaɓi ta ci gaba da bata kulawa har karshen rayuwarta sai dai kuma kamar hakan ba mai yiwuwa bane.
“Ki fito ki fadamin Mama, ki fadamin koda sunan mahaifina ne na ji sanyi a raina. Na yarda ina da mahaifi kuma ni yar sunnah ce, ki taimaka don Allah ki fadamin sunansa ko raina zai yi dadi.”
Yanda ta yi maganar a raunane ya kara sanyayawa Rumaisa jiki, ta share hawayenta.
“Bello shi ne sunan mahaifinki, haifaffen Nijeriya ne sai dai yana zama tare da iyalinsa a London. Shi ne mahaifinki, ina kara yi miki rantsuwa da Allah, mun samar da ke a karkashin inuwar aure. Ke yar halak ce kamar kowane ɗa. Ki yi hakuri Rasheedat, ki yi hakuri.”
Ta karasa jikin Rumaisa ganin yanda take kuka sosai, ta rungumeta suka hau yi tare, tausayin kansu da kansu kawai suke yi, a karshe suka rarrashi juna suka ci gaba da hira mai dadi tsakanin ƴa da uwa. Tun lokacin Bello da kuma London suka samu wuri na musamman a zuciyar Rasheedat. Da ta tuno sunan mahaifinta Bello sai wani dadi ya ratsa ta ko ta ina.
Bayan auren Rasheedat da watanni uku, Rumaisa ta kwanta rashin lafiya mai tsanani. Tashi daya likita ya tabbatar ta kamu da ciwon zuciya ga kuma hawan jini. Hankalin Rasheedat ya yi masifar tashi, a wannan lokacin Jafar karfinsa ya ja baya sosai ba kamar a baya ba yanda ya yi tashen kudi. Ya soma gani bambanci tsakanin Yusra da Rumaisa, Rumaisa koda bai bata na cefane ba to zai samu abinda zai sanyawa cikinsa a wurinta. Yayinda Yusra babu ɗaya a hakkokinsa da take ba shi. Wannan dalilin ya sanyashi saukowa ya bar musguna wa Rumaisa.
A wataranar Juma’a ciwon ya tashi gadan-gadan har aka kwantar da ita a asibiti na tsawon sati biyu, ranar da aka sallamota Rasheedat na wurinta cike da farin cikin ganin yanda ta samu sauki sai uban rama.
Ta sharemata dakin tas, ta girka mata abinci ta ajiye. Za ta mike don dauko ruwa Rumaisa ta dakatar da ita da hannu.
“Rasheeda.” Ta juyo da sauri don duk a zatonta bacci ya ɗauketa, ta karasa gareta tana mai amsawa. Murmushi Rumaisa ta sakarmata gami da yi mata nuni da gefenta alamun ta zauna. Ba musu ta zauna tana mai riƙe hannunta.
“Ba zan daina ba ki hakuri game da ɓoyemaki asalin mahaifinki da nayi ba, ki yafemin, watarana idan da rai da rabo za ki ganshi. Tashi ki daukomin wannan tsohuwar Adakar tawa.”
Kirjin Rasheedat na bugu ta mike ta dauko, Rumaisa ta bude ta fiddo wani ƙaton enbelope ta mikamata.
“Bude.”
Hannu na rawa ta bude ta ciro hotunan da suke ciki. Ƙuri ta yiwa hoton da ido, duk da cewar da kuruciya sosai a fuskar, ta gane mahaifiyarta ce sai kuwa wani dogo fari da ba ta san sunansa ba. Hakan yasa ta ɗago da zummar tambayarta. Rumaisa ta katse hanzarin.
“Shi ne Bello, mahaifinki ne.”
Ƙuri ta yi mishi tana fidda hawaye, karshe ta fashe da kuka sosai, wani irin kauna da soyayyarsa na ratsa ta, duk yanda mahaifinka ya kai ga lalacewa, naka ne. Rumaisa ta sharemata hawayen tana murmushi.
“Keda ya kamata ki yi dariya na gani, shi ne za kimin kuka?”
Ta girgiza kai tana dariyar gami da share hawayen.
“Ki adanasu a wurinki, ko ba raina, zasu zame maki tsanin neman mahaifinki. In sha Allah.”
Ta ji maganar banbarakwai sai dai ba ta fassara da komai ba sakamakon tunaninta bai je ko’ina ba. Ta tattara ta adana, burinta ta je ta nunawa Adam da surikarta mai kaunarta kamar diyarta, burinta ya cika ta yi tozali da hoton mahaifinta. Yanzu kam ta kara gaskata cewar tana da mahaifin.
A daren suka riski labarin mutuwar Rumaisa, Rasheedat ta ji duniyar ta fita a ranta, ta ji wani kadaice, ta kara tabbatar da maraicinta. Jafar ma ya yi kuka ba kaɗan ba, yana tuna irin hakurin da ta yi da shi a kowace gaɓa ta rayuwa.
“Rumaisa ki yafemin, ki gafarceni.” Shi ne abinda kawai ke fita daga bakinsa, hatta da Yusra sai da jikinta ya ɗan yi sanyi na lokaci.
Rasheedat ta rungumi kaddarar rayuwarta, ta ci gaba da tafiyar da rayuwar a yanda ta zo mata. Ta koma shiru-shiru fiye da baya, ba ta da aiki sai zubar hawaye. Iya, mahaifiyar Adam kan yawaita rarrashinta gami da ban baki, takan yawaita nunamata akan ta yi hakuri rayuwar duka-duka ba komai ba ce. Takan yawaita sanya hotunan iyayen a gaba tana kallo tana hawaye, addu’a kam tana yi akai-akai duk domin Allah Ya nunamata mahaifinta.
Ta haifi yaranta biyu duk maza, Bello wanda suka kira da Abba sai kuma Mujahid. Haka take hakuri da duk yanda rayuwa ta zo mata, cikin ikon Allah ta kara samun wani cikin, a sannan Allah Ya yiwa Iya rasuwa, ta haifi diyarta mace wacce ta ci suna Maryam.
Ba ta da matsalar komai sai na tunani a koyaushe, takan ɓata lokaci wurin tunanin Iyayenta, da kuma inda za ta ga mahaifinta. Wannan tabon ba ya barinta ta runtsa.
A sanadin Abba, sunan Anna ya bi ta, shi ya soma sanyamata sunan wannan ta sa har makwafta da Anna suke kiranta. Da taimako na Ubangiji Adam ya samu budin rayuwa bayan haihuwar Maryam. Ya zama babban lakcara a makarantar B.U.K.
Kyakkyawar kulawa ta ko’ina yaransa suke samu, Maryam ta taso cikin gatan iyaye ta ko’ina.
Ganin irin samun da yake yi, ya sanya danginsa wadanda a baya basu damu da shi ba suka soma sanya mishi idanu. Yayarsa wacce suke uwa daya uba ɗaya, Dije, ta zamewa Rasheedat kamar uwar miji. Ta uzzurawa rayuwarta. Gori da habaice-habaice kala-kala. Tun abin ba ya samun Rasheedat har ta soma damuwa ganin ko a gaban waye yi mata take. Wannan ya sanya ta rage shiga sabga dangin mijinta. A hakan ma ba ta tsira ba. Tun yaran basu fahimta har ya kasance Abba ya soma ƙullatar Dije, shi kuwa Mujahid ba shi da hayaniya, Maryam mai shekaru bakwai a sannan, sai dai su yi shiru suna kallon Dije idan ta zo gidan tana masifa. Abba Sarkin zuciya shi ne kan miƙewa ya ce zai ramawa mahaifiyarsa. Dakyar Rasheedat ke tsawatar mishi. Adam dama ba ya magana, kusan komai akai yakan ba ta hakuri da hujjarsa ta cewa ba ya don zumunci ya lalace. A dole take shiru sai dai ba ta jin dadin yanda yake bari ana taka ta son rai.
Please is she still waiting the book because this is not complete if she finished how will I get the complete?