Skip to content
Part 28 of 41 in the Series Rumfar Kara by Rufaida Umar

Da wannan kalar matsin Rasheedat ta ci gaba da rayuwa a gidan Adam. Kwatsam kuma sai Adam ya zo mata da zancen kara aure, tana daukar abin kamar wasa ta ga dai dagaske yake, ta nuna kishin ta yi fushin ta dauke hankalinta ga yi mishi komai karshe haka ta hakura ta dangana a ba yanda ta iya. Babu abinda ya kara tayar da hankalinta sai jin da ta yi diyar ƙawar Dije ce ake son ya aura. Ta tabbatar ita da kwanciyar hankali sun yi hannun riga. Ya yanke shawarar ajiye Amaryar a tsohon gidansa don acewarsa ya fi kaunar rabasu ko don kwanciyar hankalinsa. Rasheedat ba ta ce mishi komai ba. Ko da bikin ya zo, ta sake kamar ba ita ce mai fushi ba, ta yi karamin yininta, kowa ya yaba da yanda ta maida komai ba komai ba. Masu yada mata magana kuwa ko a gefen zaninta. 

Koda aka kawo Amarya gidanta don su gaisa, ta tarbe su da hannu bibbiyu, ba ta yi mamakin ganin Dije cikin masu kawowar ba. Ta shanye dukkan wani habaici da akai mata, Hajiya Yusra matar Jafar wacce a yanzu ta zame mata tamkar uwa, ita ta rarrasheta gami da yi mata faɗa akan ta maida komai ba komai ba. Da wannan ta shanye dukkan ɓacin ranta har aka rabu. Sai bayan tafiyarsu ta ci kukan bakaken maganganu da habaici da Dije ta fesamata, tun Hajiya Yusra na lallai har dai ta haɗa da faɗa-faɗa ganin abin na neman wuce gona da iri. Akan dole ta sanyawa zuciyarta dangana. Ta kuma rungumi ƙaddara. 

*****

Tun bayan auren sai ta samu sauki daga tsangwamar Dije. Ta ci gaba da gudanar da rayuwarta cikin walwala da farin ciki duk kuwa da cewar sau da yawa ta kan yi zaman kukan rashin ganin mahaifin da ba ta sanshi ba a rayuwarta gaba daya. 

Maryam ta taso ciki kulawa da soyayya ta bangaren yan uwanta maza da kuma iyayenta. Ta tashi yarinya ƴar shagwaɓa sai dai wannan bai sa sun bar ta kara zube ba ilimi ba. Tun tasowarta ta ke lura da karancin walwala a saman fuskar Anna, ta sha samunta tana kuka, har ta ji Abba da Mujahid na rarrashinta, Abba yana fadin In sha Allah ta silarsa za ta ga mahaifinta yayinda Mujahid ke fadin shima haka. Tun Maryam ba ta biyemusu har ta yi wayon sanin me suke nufi, tun daga lokacin ta sha alwashin sanya Anna a addu’a akan Allah Ya haɗata da mahaifinta. 

Tsakanin Rasheeda da Amaryar Adam, basu da kowace matsala. Sai ya kasance su na zumunci,takan zo gidan Rasheedat, hakanan su Mujahid kan je mata. Wannan ne ya rage karfin Dije sosai, sai itama ta sauko ta hakura da matsawa Rasheedat suka ci gaba da mu’amala kamar a baya sai dai Rasheedat ba ta sakar mata sosai ba.

*****

Maryam ta dubi taron mutan gidan da duk suka zuba idanu suna biye da ita. Ta ci gaba da magana.

“Inada shekaru goma sha biyu a duniya na yi haddar Alkur’ani mai girma, na sauke litattafan addini da dama haka kuma a tarihin rayuwata tun soma zuwa makarantar boko, ban taɓa haura ta uku ba a aji. Nakan zo ta ɗaya, biyu sai kuwa ta ukun. Wannan hazaƙar tawa ya sanya malaman makarantar ke ji da ni, da yawa kuwa sukan ce daga ni har yayyunta ba’a ƙasa muka ɗauka ba. Ilimin Babanmu muka yo. Dadi yakan ishemu mu ji nan duniya babu ya mu saboda muna da baiwar ilimin da wasu nema suke basu samu ba. A wannan lokacin tuni Abba yayana ya yi jami’ar Lagos inda anan zai karanci Computer Engineering. Mujahid kuwa a sannan yana shirin rubuta jarrabawar fita daga Sakandire. Ni kuwa duka-duka ina aji biyar a firamare. 

Tun muna kanana har girmanmu, muke fuskantar damuwa daga Anna, muka gane abinda take yiwa kuka, muka zama masu rarrashinta. Ni ce mai tayata kukan a duk sadda ya tashi, wannan abu kan ba Mujahid haushi don a cewarsa idan ban rarrasheta ba ai bai kamata na tsaya ina sanyata ba. A karshe ya biyoni zai daka, gudun da zamu dinga yi muna zagaye a gaban Anna ne sai ya sanya ta dariya har ta mance da abinda take tunani. Wannan ya fi komai faranta ranmu. 

Bana mantawa a ranar da muka yi jarrabawar karshe a ajin karamar Sakandire Jss3, na shiga dakin Anna bayan dawowata daga makaranta na sameta ta tisa hotuna a gaba tana kallo. Kafin ta ankara da ni har na isa gareta. A wannan rana na san Baba Engineer a hoto na kuma kara ganin hoton Kakarmu duk kuwa da cewar akwai babban lamination da akai mata na hoton Kakarmu wanda ta kafe a ɗakinta. 

Tun ganina da Baba Engineer naji ina son tsohon wanda aka kira da sunan Kakana, na roƙeta akan ta bani hoto daya ta ƙi dole na hakura sai dai ranar da zarar na tuno da hoton sai naji raina ya yi haske. Ina jin wani abu na jini yana zagaye da ni, nasan cewar na hoton shi ne ainahin kakanmu. 

Sadda na hadu da baban Humaira kuwa ina yar ajin karshe ta makarantar sakandire. Mun hadu a watarana a lokacin damina, hadari ya cika sararin samaniya, ni kuwa ina kofar makaranta a tsaye kasancewar ba makarantar cikin B.U.K na yi ba, wata tsohuwar  makaranta ce da ake kira Da’iman Science Academy. Wannan ta sanya dole sai na jira mai tasi din da ke daukata ya kaini gida, na ja tsaki ya fi a kirga, nan da nan kwalla ta cikamin idanu ganin yanda ake iska ga sama na kara haɗewa, ruwa ka iya sauka a kowane lokaci. Shi kuwa daga gidansa ya biyo daukar kannensa bisa umarnin mahaifiyarsa, ya fito daga motarsa ya tsallako, tun zuwansa ya lura da tsayuwata a wurin ni kuwa da zarar naji rayuwar motoci sai na baza idanu naga ko Jibril Mai Tasi ne. Kallo daya na mishi, muka hada idanu wanda daga bisani nayi saurin janye idanuna. Ya shige ciki can kuma ya fito da kannensa su biyu. Kallo daya na musu naga na sansu, akwai daya mara jin magana Sadik kuma ɗan ajinmu ne ba ma jituwa, sai kuwa wani yaro ɗan aji huɗu a Sakandire. 

Har sun shiga motar sai naga Sadik ya fito yana kwalamin kira da sunan da ake kirana da shi a makaranta.

“Gifted!” Nayi mishi banza ko kallon inda yake ban ba, sai kuma naji ya kirani da Maryam. Na dubeshi ya min alamar na zo, na kauda kai na gyara tsayuwata lokacin har an soma yayyafi, ina shirin komawa cikin makaranta naji an riƙe jakata. Na juyo a fusace don har ga Allah na dauka Sadik ne me wannan ta’asar. Wanda na gani ya sanya naji ba zan iya rashin kunyar da na yi niyyar yi ba, na sauke idanuna ƙasa don ba zan juri kallon nashi kwayar idanun ba.

“Will you please…” Sai kuma ya yi shiru, ya ci gaba.

“Kinga ba’a zo daukarki ba, ko za ki zo mu kaiki tunda naji Sadik ya ce nan cikin B.U.K kike, kusan hanyarmu ce.”

Na dubeshi kadan sai naji ba zan iya ja da shi ba, a dole na bi bayansa da sauri-sauri muka wuce, na bude backseat na zauna ya rufe kofar, Sadik dake mazaunin kusa da direba ya juyo ya harareni, nima na murguda mishi baki na kauda kai. Ya yi kwafa.

“Da kar ki zo din.”

Ban ce uffan ba adalilin na ɗaga kai da niyyar faɗa muka haɗa idanu da Yayansa, murmushi mai sanyi yake yimin na kasa cewa uffan dole na yi shiru.

“Yauwa Anti Gifted, don Allah bari ki dubamin wannan aikin. Wallahi dama ban gane ba kuma ina tsoron Malamar, Miss Jumoke, kin santa masifaffiya ce. Kada nace ban gane ba ta hukuntani.”

Fadin ɗan fulanin yaron, na dubeshi da murmushi. Ba musu na karɓi littafin, sai da na soma duba sunan na gani, Nura Zakariyya  sannan na soma yi mishi bayani yanda nasan za ta fahimta. 

“Dagaske you are gifted.”  Na tsinci muryar Yayansu, muka haɗa idanu ta madubi, na maida mishi martanin murmushin.

“Ai akwai ta da iyayi ga cin gyaran Malamai kamar ita ce Mangopark.”

Sadik ya furta da gatse, harararsa nayi, shi kuwa Yayansu ya ɗan kaiwa Sadik duka.

“Ba ka jin magana ko?” Ya shafi kai yana murmushi. 

Ni suka soma saukewa har cikin B.U.K  na yi musu godiya na karasa ciki. 

A bakin kofar muka yi kiciɓus da Babanmu, yana ganina ya riƙeni.

“Maryam, wa ya kawoki? Jibril ya samu karaya a ƙafa. Ina shirin zuwa daukarki, fadamin wa ya kawoki.”

Na labarta mishi komai, ya sauke ajiyar zuciya yana rungume da kafadata muka shiga ciki. Anna itama sai da ta ji labarin hankalinta ya kwanta. Na watsa ruwa na sauya kaya sannan na fito. Anan nake jin labarin komawarmu garin Maiduguri sakamakon sauyin wurin aiki da Baba ya yi daga jami’ar B.U.K zuwa UniMaid.  Ba da son raina ba saboda duk da ba wani fita muke cikin jama’a ba, mun san da mutanen kusa da mu. Babu kamar Maman Shuraim wacce suka saba da Anna hakanan muka saba da yaranta. 

Baba ne ya soma yin gaba don alokacin muna dab da soma jarrabawar fita daga sakandire. Muna kammalawa zamu tattara mu tafi banda Mujahid wanda ke ajin karshe a matakin karatunsa na Medicine. A sannan Abba yana India domin kammala Masters.  

Watarana muka kara kiciɓus da Yayan su Sadik, Ina shirin shiga tasi, naji ya kira sunana. Ina ganinsa na saki fuska muka gaisa, kuma yakan aiko saƙon gaisuwa gareni daga bakin Sadik, nikam Sadik bai taɓa shaidamin ba. Bai yi mamaki ba don ya san ba ma jituwa, nake sanar mishi da komawarmu Maiduguri. Naga fuskarsa ta sauya kadan, cikin damuwa ya ce.

“Kinsan sunana?”

Na girgiza kai don dama na ƙagu da na sani din. Tunaninsa kan hanani sukuni sai dai tun ranar da ya kaini gida ban kara sanyashi a idanu ya zo daukar su Sadik ba sai yau. 

“Haisam Zakariyya. Ma’aikaci ne a Federal insland Revenue. Ina zaune a unguwar Gyadi-gyadi. Inada mata da ɗa.”

Shiru nayi bisa rashin sanin dalilansa na faɗamin duka wannan bayanan a kansa. Murmushi ya yi. 

“Nasan za ki mamaki ko? Meyasa na fadamaki duk wadannan? Kar ki damu za ki sani nan gaba kaɗan in Sha Allah. Sai mun kara haduwa.”

Daga haka ya ɗan dagamin hannu sannan suka gaisa da Jibril ya ba shi hakurin ɓata lokacinsa da ya yi sannan ya bar wurin, na shiga motar ina murmushi sai dai da zarar na tuna yana da mata sai gabana ya faɗi ban kuma san dalili ba. 

Haka muka tattara muka koma Maiduguri da zama bayan kammala zana jarrabawar Waec da Neco ɗina. Tare muke gaba daya a gidan har Amaryar Babanmu, sai dai kowanne bangarensa daban. Babu wata matsala tattare da ita, zamu yi hira zan shiga sashinta. A sannan ta haifi diyarta mace, Fadila. 

Antina na dauketa, za ta ban shawara idan ta ga zan kuskure. Labarin Haisam kuwa babu abinda ba ta sani ba, takan ce nayi hakuri na fidda shi a raina, idan da rabon ya zama mijina don kansa zai tako zuwa garinnan. Kamar kuwa ta sani, watanmu daya a Maiduguri, sai ga Babanmu ya shigo yana fadin mun yi baƙo daga Kano. Ban taɓa kawowa shi bane, ya ce Anna ta ban ruwa na kai musu. Ina kaiwa na ga Haisam durkushe gaban Baba, sai da jikina ya dauki rawa da irin kallon da Baba ya watsamin. Na gaida Haisam sannan na fice. 

Ina ta fargaba, tsabar tsoro ma sashin Anti Amarya na nufa. Tana ganina ta san ba lafiya, na bata labarin wanda ya zo gidan. Ta yi murmushi.

“To mene na ruɗewa Maryam? Ke kila ce ya zo? Ai shi ya kawo kansa, idan da rabo kuma da alheri sai kiga an yi.”

Nidai ba baka sai kunni, nayi shiru ina addu’a a zuciyata. 

Baba ne ya shigo yana nemana, da sauri na fito falon Anti Amarya, muka yi kiciɓus. Ga mamakina murmushi ya sakarmin sai dai fuskar da ƴar damuwa kadan. Ya ce na biyoshi, muka koma sashin Anna muka zauna.

“Wannan bawan Allahn da ya zo sunansa Haisam Zakariyya ko? Ya cemin ya sanki a makarantarku, hakane?”

Na gyaɗa kai ba tare da na kalleshi ba, dakyar na iya buɗe baki na amsa.

“Eh.”

Ya jinjina kai.

“Toh madallah, Haisam aurenki ya zo nema, na nunamishi karatu nake sonki ki yi, ya nunamin ba shi da matsala, karatu za ki yi shi a gidansa idan har an mishi alfarmar aura mishi ke a yanzu. Ya nunan ko uwargidansa ma ta yi karatu, don haka shi ba shi da matsala game da karatunki. Auren dai naki yake so yanzun.”

Wani sanyin dadi ne ya cika zuciyata, na rasa abin cewa sai dai har lokacin shiru ne. 

“A bangarena na yaba da nutsuwar yaron, sai dai dole bisa yanda addini ya tsara, zan bincika can Kano na ji Asalinsa da kuma wani bangare na halayyarsa. Daga nan zan ba shi damar turowa a yi magana. Zan so kiyi auren ki karasa karatun a ɗakin mijinki Maryam, burin kowane mahaifi ya ga ɗiyarsa mace da ta kai munzalin aure a gidan miji. Sannan a bangarenki ki dage da addu’a, idan da alheri tsakaninku Allah Ya tabbatar. Yanzu kina iya zuwa ku gaisa. Allah Ya yi maki albarka.”

Na amsa ƙasa-ƙasa, bayan fitarsa na karasa ga Haisam. Mun yi hira sosai, wata shaƙuwa da kauna ta shiga tsakaninmu a wannan ƴan awannin da muka kasance tare, bayan tafiyarsa  Anna ta sanyawa abin albarka, ina zuwa sashin Anti Amarya na faɗa jikinta muka sanya dariya. Ta tureni.

“To ya isa haka, yanzu dai ki dage da addu’a kuma ki kwantar da hankalinki, idan da rabon aure tsakaninku da Haisam sai kiga komai ya zo da sauki.”

Na yi murmushi. 

Sati uku tsakani Abba ya dawo daga karatu bayan ya kammala, mun yi farin cikin ganinsa. A sannan ne kuma Baba ke sanar da mu cewarta kammala bincike akan Haisam, ba ya jin yana da matsala, zai iya turowa a sanya rana. Abba ya nuna shi fa bai ga amfanin yimin aure yanzu ba, acewarsa duka-duka nawa nake? Baba ya nunamishi wannan auren shi ne dai mutunci da cike kowane Ɗan Adam. Don haka shima ya soma shirin nashi auren. 

Dariya kawai aka yi. 

Kamar da wasa aka sanya ranar aurena da Haisam, ta Landline muke gaisawa da Haisam shima jefi-jefi. 

Watanmu Biyar a Maiduguri akai aurenmu da Haisam. Na yi kuka sosai na rabuwa da Anna da Anti Amarya. Nakan ji sauki idan na tuna Yaya Mujahid dake Kano, shima ya zo bikina. Shi da Abba kuwa har dakina a Kano suka rakani.Na shiga sabuwar rayuwar gidan Haisam, wanda na zauna tare da Uwargidansa Salma da ɗansa Fu’ad. Wanda a dalilin wannan zaman na shiga dukkan hatsarin da nake ciki a yanzu.

<< Rumfar Kara 27Rumfar Kara 29 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.