Skip to content
Part 32 of 41 in the Series Rumfar Kara by Rufaida Umar

“Wai ke Amira meke damunki?” Fadin Humaira tana duban yanda walwalarta ta yi ƙaranci tun zuwansu. Amira ta girgiza kai.

“Ba komai fa.”

“Wallahi ban yarda ba akwai, saboda ba haka kike ba ai.”

Murmushin yaƙe Amira ta yi, to sai ta ce mata tana kishin Shuraim? Tun zuwan Salima bai damu da harkarta ba, ko abu za ta yi idan nashi ne zai ce kada a sanyata daga wurin Salima yake so. Ita dai tasan ba sonshi take ba amman ta rasa dalilin wannan damuwar. Don ko Fu’ad da take tunanin ya kwanta mata a rai, ba ta jinsa kamar yanda take jin Shuraim da lamuransa. Ko wuri ya shigo sai ta ji faɗuwar gaba.

“Kin gani ko? Kin gani? Ina magana ma kin kara tsunduma cikin tunani? Wai meke damunki haka?”

Dariya Amira ta yi ganin yanda Humaira ke fidda huci kamar wacce ke shirin dambe.

“Allah Ya huci zuciyarki. Kefa yar uwata ce, ya zamemin dole na faɗamaki damuwata. To me zan ce ma? Abu ne da ban tabbatar ba, ki bani daga nan zuwa muje Maiduguri mu dawo, In sha Allah zan faɗamaki kin ji tawan?”

Murmushi Humaira ta yi.

“Naji toh.”

“Eh kisa Fu’ad, don su kai ni lahira ba komai bane a wurinsu.”

Fu’ad ya haɗiyi wani miyau mai ɗaci. Tiryan-tiryan ta soma ba shi labari tana shafa jikinsa, hatta da yanda suka yi da Halima a mota bata ɓoyeshi ba duk don son ta ƙara burgeshi ya aminta cewar tana bayanshi a kowane hali. Ta kara da fadin.

“Nidai ina sonka wallahi, koma ɗan wanene kai ni ba zan fasa nuna so da kauna gareka ba.”

Sumbatu take tana kara shafashi, sam bata lura da tashin hankalin da ke kwance a kwayar idanunsa ba. Kansa sarawa yake yayinda jijiyoyin kan suka miƙe lokaci guda. Idanunsa kuwa sun kaɗan matuƙa, wani wawura da ya kai mata ne ya maidota hayyacinta ba tare da ta shirya ba.

“Kin tabbatar babu karya a zantukanki?”

Jiki na rawa ta gyada kai, ta m kasa motsa lebbanta har sai da ya kira jijjigata, cikin tsawa ya ce.

“Hanan! Kin tabbatar babu karya a abinda kika fada?”

Ta hau girgiza kai tana magana a rarrabe.

“E..h…wall..wallahi babu.”

Ya wancakalar da ita ya dau mukullin motarsa ya fice.

Gudu yake tamkar zai tashi sama, hawaye kuwa zuba suke kamar mai yankan albasa.

“Kuma ba ita ta haifeka ba. Wanda kake tunanin mahaifinka ne ba shi ya haifeka ba. Amman ta cemin kai ba shege bane.”

Wannan kalaman su suka fi tsayawa a ransa, tunaninsa kuma ya tafi akan me Maryam baƙuwar gidan Malam Kabiru ta yi musu? Wane sirri ta sani a kansu da har suke yunƙurin kasheta?

Bugu ya kaiwa sitiyarin, zuwa Yobe ya kamashi, yau kan dare ne kaɗai zai hanashi zuwa. Yanzu zuwa zai yi ya ji asalinsa daga bakin Salma. Idan kuwa ta yi kuskuren yi mishi ɓoyo to kuwa zai kasheta ne!

Kansa ne ya yi mugun riƙewa wannan ta sanyashi dole ya faka motar ya kunna ƙira’ar Alƙur’ani, zafin da ke kirjinsa ya soma raguwa, ya shafe kusan awanni biyu a wannan hali kafin ya karasa gidansu sai dai ya tarar ba kowa ta fita.

Shiga ya yi don ya rantse a yau ba zai bar gidan ba sai sun hadu da ita. Ko shi ko ita za’ayi.

***

Hanan kuwa saurayinta Sidi Oscar ga kira ta ba shi kwatancen inda take don tana da tabbacin muddin ta fita a haka akwai matsala. Ita kadai tasan yanda take ji a jikinta.

Sai bayan ta dawo hayyacinta ta kara fahimta irin rainin wayon da Fu’ad ya yi gareta.

Jiki na rawa da gaggawa ta maida kayan jikinta, Oscar ya dubeta.

“A haba yarinya, ai ban gama ba. Yanzu aka fara, irin wannan abu? Me da me kika kwankwaɗa ne?”

Wani wawan tsaki ta ja gami da fiddo bandir din ƴan ashirin ta cilla ya cafe gami da sumbata. Mayafi ta yafa ta fice, tasan yau ta yiwa su Salma laifi.

Tun a hanya ta kira Halima ta labartamata yanda suka yi da Fu’ad, Halima ta kunduma ashar ta afkamata.

“Kina neman ɓatamin shiri, wa ya fadamaki yanzu na so Fu’ad ya ji komai? Mtsw. Ya zama dole na sanar da Salma don na tabbatar ita zai soma tunkara.”

Ita ta kira Salma ta labarta mata abinda ke faruwa, Salma ba kalar tsinuwar da ba ta yiwa Halima ba har da cin alwashin sai ta hallakata. Anan ne suka yi baram-baran ta waya. Salma na kuka, ga ruɗewa ta sanar da Hayat, shi ya sanya ta haɗa abinda za ta haɗa ta fito zuwa tsohon gidansa, anan suka kwana.

*****

Tun asuba da suka farka basu koma ba, nan kuma aka shiga shirin tafiya, Humaira nan da nan take sanyi da zarar ta tuna Adam ba zai samu zuwa ba. Har suka kammala shiri sannan Gwaggo ta aiketa ta dubo ɓangaren Engineer ko sun shirya. Ta ɗora farin mayafi a saman atamfarta mai launin fari da ja. Takalminta marasa tudu ne, ta yi kyau duk kuwa da cewar hoda kadai ta shafawa fuskar sai man leɓe. Kiciɓus suka yi da Nuriyyah, da sauri ta karasa ta rungumeta suna murna.

“To fa, a sakarmin mata kar a raunatamin Baby.”

Fadin Huzaifa dake shigowa gidan. Suka yi dariya. Ta gaida Huzaifa ya amsa.

“Anti Nuriyyah, da ke zamu tafi?”

Murmushi Nuriyyah ta yi.

“A’a Humaira, amman wataran zan je. Na tayaki murna kwarai. Ina Mama?”

Da dariya Humaira ta amsa.

“Tana ciki.”

Daga nan suka nufi ciki ita kuwa ta ƙarasa gidan Engineer. Sai da ta soma shiga ɓangarensa ta gaidashi ya amsa kamar ya haɗiyeta tsabar kauna. Ya ɗan ja ta da zolaya tana murmushi.

“To ita kakar taki ta Cinnaku ta iso?”

Girgiza kai Humaira ta yi da mamaki.

“A’a. Za ta zo ne?”

“Me zai hana Indo? Ai duk wani masoyin Maryama idan har ba dalili kwakkwara ba, in Sha Allah zai je.”

“Har ni a cikin masu zuwan?”

Suka tsinci daddaɗar muryarsa daga waje. Kusan lokaci guda suka juya suna kallonsa. Ya haɗe cikin wani farin yadi mai shara-shara har ana hango farin vest dinsa ta ciki. Hatta da hular kansa Damanga fari ne ƙal. Kwantaccen sajensa da kwanta miliyan dinsa, ya ƙara fiddo ainahin kyawun halliitar da Allah Ya yi mishi. Kamshin turaransa ya cika kofofin hancinta. Ba ta san ta shagaltu a kallonsa ba har sai da ta ga ya ɗauke nashi idanun yana murmushi gami da takowa ciki. Ta yi azamar sauke kanta tana jin kirjinta na bugu kamar zai faɗo, ba ta taɓa zaton jin irin yanayin akan kowane rai ba. Ba za ta iya fasalta ma’anar hakan ba.

“Likita bokon turai, ka samu zuwa kenan?”

Yana kallon Humaira yana mai ci gaba da tsotsar alawar TomTom dake a bakinsa ya amsa.

“Na samu zuwa, ai dolena ma naje. Wayasani ko na sama maku ƴar Maiduguri. Kaga kuwa sai aure kawai.”

Dariya Engineer ya yi ita kuwa Humaira satar kallonsa ta yi, ya ɗagamata gira yana murmushi, ta mike har kafafunta na rawa, ta ji ranta ya ɓaci, dakyar ta gaidashi ya amsa sannan ta bar ɗakin har tana tuntuɓe. Adam ya sauke ajiyar zuciya, idan zai tsaya fasalta yanda yake jin Humaira a ransa, to zai zama kamar ya ɓata lokaci ne don ba za ta fasaltu ba. Ita ce farkon wacce ya soma so, ba kuma ya jin akwai wacce zai so bayanta.

*****

Zuwan Inno da Jamila ba karamin murna ya sanya Humaira ba. Ta rukunkume Jamila suna ihun murna har da kukansu. A karshe kuma suka shiga labari, nan take jin har an kai kudin auren Jamila. Koda aka tashi tafiya su uku suka hadu, Amira, Jamila da Humaira. Motoci hudu ne, da na Adam, sai na Uncle Hashim, sai na Huzaifa sai kuwa Sienna ta gidan Baba Engineer. Suna niyyar shiga motar Uncle Hashim, Adam ya yafito Amira da hannu. Nuni ya yi mata da motarsa, ta kuwa ja hannun Humaira da fadin.

“Ku zo muje motar Yaya Adam.”

Sai sannan Humaira ta kara kallonshi, ya ci bakin gilashi ya haɗe fuska, kai ka rantse hankalinsa ba’a kanta yake ba, koda ta tuno furucinsa a dakin Baba Engineer, itama sai ta haɗe nata ran. Amira za ta shiga gaba ya girgiza mata kai gami da mata nuni da Humaira da hannu.

Hannunta kawai ta ja ta mata nuni da mazaunin gaba.

“Kinga kin fi mu jiki, gwara ki zauna a gaba kada mu matse tunda har Baba Yaha ma nan za ta shigo.”

Kafin Humaira ta yi yunkurin cewa ba za ta shiga gaba ba, tuni Amira ta shige ya zamana sai wurin Baba Yaha Ta saci kallonshi, ya ɗora hannu saman motar yana danna waya sai dai murmushi sosai yake yi bai ko kallonta. Turo baki ta yi gami da shiga gaban ta zauna.

A gidan Uncle Hashim, Umma ce kadai za ta je sai kuwa Amira da Shuraim. Sai manyan iyayensu, sannan Huzaifa, Adam sai Baba Yaha.

Zama ya yi da Bismillah, tana ji ya karanta addu’ar matafiyi.

“Allaahu ‘Akbar, Allaahu ‘Akbar, Allaahu ‘Akbar, Subhaanal-ladhee sakhkhara lanaa haadhaa wa maa kunnaa lahu muqrineen. Wa ‘innaa ‘ilaa Rabbinaa lamunqaliboon. Allaahumma ‘innaa nas’aluka fee safarinaa haathal-birrawattaqwaa, waminal-‘amalimaa tardhaa, Allaahumma hawwin ‘alaynaa safaranaa haadhaa watwi ‘annaa bu’dahu, Allaahumma ‘Antas-saahibu fis-safari, walkhaleefatu fil-‘ahli, Allaahumma ‘innee ‘a’oodhu bika min wa’thaa’is-safari, wa ka’aabatil-mandhari, wa soo’il-munqalabi fil-maaliwal’ahli.”

Motar ta yi tsit har ya kammala su ma suka yi a zuci. Yanda ya karanto larabcin sai ka rantse wani Balaraben ne. Ta ji ya kara burgeta. Motar Huzaifa ce ta soma yin gaba sannan ta su Engineer sai kuwa ta su Maryam, kusan su ne karshen tashi.

A hankali ya zuge gilasan motar, ya kunna Ac. Ya kara kai hannu ya dauki wani CD ya sanya, wakokin yabon Annabi s.a.w ne na mutan Sudan, Sahwa.

Motar ta yi shiru sai muryar Amira da ke ƙusƙus tare da Jamila. Baba Yaha kuwa ta dukufa karanta hisnul-muslim, da alama addu’o’i take karantawa.

Ya saci kallonta, ta wani haɗe rai kamar ba ita ba, ya juya kai ya ɗan kalli window yana murmushi kafin ya fidda gilashin da ya ƙwama. Rage murya ya yi.

“Baba Yaha.”

Ya yi daidai da sadda ta shafa addu’a ta amsa mishi.

“Na’am Adamu.”

“Idan fa muka je Maiduguri zan samo maki suruka.”

Ta washe baki.

“Kai masha Allahu, hakan ya yi wallahi. Ai gwara ka yi auren tun muna raye musha biki. Ƴar Maiduguri ce?”

Ya yi murmushi ya na duban Humaira wacce ta ƙara haɗe girar sama da ta ƙasa, har wani ruwan ƙwalla ne suka cika mata idanu. Dauke kai ya yi gami da cije lebbansa na ƙasa da haƙora ya ƙara taka totir motar ta ƙara gudu.

“A’a, addu’a za ki yimin na samu tsakiyar shuwa Arab.”

“Lah Yaya, ina wannan kawar tawa? Ummita Sulaiman? Itama dagaske Shuwa ce. Ai na taɓa nunamaki hotonta ko Humaira?” Fadin Amira tana taɓa kafaɗar Humaira.

Humaira ta yi bakam kamar ba ta ji ba, ko juyowa ba ta yi ba. Adam ya na tuƙin cike da nishaɗi, ko ba komai tana jin abinda yake ji koda shekarunta basu kai ta tsinkayi hakan ba.

“Wai wai wai! Anya Shuwa? Nifa tsoron mutanen nan nake. Ina raba ka da su.” Yaha ta yi zancen iyakar gaskiyarta.

“Suna da wani aibun ne?” Ya nemi ba’asi.

“Eh kam, aurensu kam akwai sanya aljihu kuka. Sai ka shirya.”

“A shirye nake ai, kowa ya ɗebo da zafi bakinsa. Ku tayani da addu’a. Wai ma, ba ki ji wani mawaki na cewa komai na mata bane? Idan an samu a ringa basu ba?”

Yaha ta tuntsire da dariya su Amira na tayata ciki-ciki. Humaira ta kasa daurewa ta kalleshi, shima ita yake kallo sadda ya ɗan rage gudun. Ta kasa jure yanayin kallon wanda ke kara dulmiyar da zuciyarta cikin kogin so da kaunarsa. A hankali ta dauke kanta.

“Humaira ba kya magana yau, lafiya?”

Ya fadi tamkar bai san dalilin ba, ya bude ɗan kwabar da ke gefen hannunsa ya dubi Amira.

“Lil, daukarmuku TomTom.”

Da saurinta ta dauka tana godiya. Ya mikawa Humaira wurin guda biyar.

“Ɗan taimaka ki buɗemin ɗaya.”

Ta karɓa ba musu ta buɗemishi. Ya sanya a baki sannan ya kara sautin muryar rediyonsa.

Tafiyar da bata wuce awanni arba’in da biyar ba sai da ta kaisu awa biyu sakamakon checkpoint da suka ringa tararwa a hanya.

Suna shiga garin Maiduguri, sai ya zamana sun koma bin bayan motar Uncle Hashim wand a ciki Maryam take, sunan unguwar bata ɓace mata ba sai dai gidan. Suna zuwa unguwar suka shiga tambaya, mahaifinta tsohon Farfesa ne kuma wanda ya yi suna, hakan yasa basu sha wuyar sanin kwatancen gidan ba.

Har kofar gidan aka kaisu. Maryam ta zubawa kofar gidan kallo, mamaki take na yanda aka ƙara ƙawatashi, ya kasance part ne har uku sai dai ba ginin bene ba. Tsayuwar motocin ya dauki hankalin wani dan saurayi dake zaune tare da Maigadin gidan sai wani yaro a saman keken yara yana dan zagaye. Yaron fari tamkar buzu.

Gaba daya suka shiga fitowa daga motocin. Maryam cikin faduwar gaba da rawar jiki ta yi gaba tana mai gaida Maigadin wanda ba ta sanshi ba. Tun tahowarta saurayin ya dubanta idanu, ba don komai ba sai don kamar da ta yi da Abbansa.

“Wurin Professor Adam Zannah muka zo. Mahaifin Abba da Mujahid.”

Jin sunan duk babu bare a wurinsu ya sanya Maigadin miƙewa.

“Nan ne gidan, kuma yana nan. Bello, ko za ka sanar da Alhaji?”

Wanda aka kira da Bello ya mike tsaye, duk suka zubamishi idanu suna kallo, dattijan suna daga mota a zaune suna jiran a yi iso sannan su fito. Maryam kuwa jikinta har tsuma yake, don ganin iyayenta kawai take. Hawaye take fitarwa, Maigadin na lura da yanayinta yana mai mamaki. Jim kadan Bello ya fito.

“Yauwa, yace kuna iya shigowa.” Maryam da sauri ta faɗa kafin sauran suma su shiga. Mazan Bello ya budemusu masaukin baƙi yayinda matan ya musu umarnin shiga daga ciki.

Kirjinta banda bugu ba abinda yake yi. Bisa jagorancin Bello suka karasa ciki har babban falon Hajiya Rasheedat. Tana zaune da surukarta Zainab suna hira. Jin tashin muryoyi cikin sallama ya dau hankalinsu. Wani irin miƙewa Hajiya Rasheedat ta yi.

“La’ilaha illallahu Muhammadur Rasulillahi s.a.w. Dama nace bata mutu ba! Wallahi Maryam ɗina ce.”

Sai kuka. Maryam a guje ta karasa ta faɗa jikin mahaifiyarta, sosai Hajiya Rasheedat ta rungumeta tana kuka har da sheshsheƙa. Ba wanda ba su sanya zubar hawaye ba. Ganin haka Bello ya yi saurin fita ya sanar da Farfesa Adam abinda ke faruwa. Shima cikin rawar jiki ya taho yana tokara sandarsa, Bello rike da hannunsa suka ƙaraso falon.

Mutuwar tsaye ya yi ganin ɗiyarsa wacce suka yi zaman makokinta shekaru goma sha  da suka gabata.

“Allahu Akbar, Maryamar ce dagaske?”

Ta saki Hajiya Rasheedat ta karasa ga mahaifinta shima ta faɗa jikinsa. Zainab matar Mujahid tuni ta dau waya ta danna mishi kira tana kuka ta sanar mishi da abinda ke wakana. Take ya ce gashinan zuwa.

*****

Firgigit ya mike tsaye, meyasa ma bai kawo tunanin hakan ba? Ta yaya zai mance ba gida ɗaya garesu ba? Akwai gidan Hayat? Shakka babu tunda har Maigadi ya sanar mishi cewa da jaka ta fita, to yana da tabbacin can ta nufa.

Da sauri ya yi wanka ya sauya kaya. Wandonsa three quarter sai t-shirt fara marar hannu. Tun kafin ya shiga motar ya shiga kwalawa Maigadinsu Joshua kira. Umarni ya ba shi akan ya bude Gate da sauri. Shi kuwa tuni ya shiga mota ya tayar. Ya ɗan dakata ta dauki zafi kadan sai dai jikinsa har mazari yake. Burinsa ya je ya yi gaba da gaba da Salma.

Ta cikin gilashin ya hangi wata dattijuwa da wasu samari su biyu Joshua na musu umarnin su fice. Fitowa ya yi daga motar ya ƙaraso garesu. Sam bai shaidasu ba. Su kuwa kallonsa suke sosai. Hannu ya ɗagawa Joshua dake shirin koro jawabi.

“Sannu Mama, ina kwana.”

Wani shauki da kauna ke ratsata, ba wanda ta tuna sai ɗanta Haisam.

“Fu’ad? Ashe da rabon na sanyaka a idanuna? Salma tana min ɓoyonka saboda abin duniya ko?”

Cikin rashin fahimta ya yi shiru yana kallonta. Jin sunan da ta ambata ya sanyashi tuna ainihin wanda take nufi. Da wani irin murna ya karasa zai rungumeta sai kuma ya tuno kalaman Hanan ya ja baya. Ta rike hannunsa tana hawaye.

“Ka dinga ziyartana jikana, kai kadai nake da shi a bangaren Haisam da zan kalla na yi farin ciki. Wannan ƙaninsa ne Nura, wannan kuma jikana ne ɗan ɗan uwansa kuma yayansa Idris, Shu’aibu. Adalilin Salma duk baka sansu ba ko? Ka daure ka dawo garemu. Muna sonka. Kada ka zama azzalumi mai son abin duniya fiye da ƴan uwanka kamar Salma.”

Idanunsa suka kaɗa, ta ƙara tayarmishi da wani miƙi. Ya miƙawa Shu’aibu da bai fi sa’ansa ba hannu suka gaisa, hakanan Nura. Ya maida duba ga Dattijuwar yana rike kafaɗarta.

“Kiyi hakuri, zan zo Hajiya. Zan zo har gida. Yanzu akwai wurin da zan je. Na miki alkawarin zan zo har inda kike na sameki a kwanan nan. Shu’aibu sanyamin lambarka sai na kira ka yimin kwatance.”

Da sauri-sauri ya koma motarsa ya ciro wayarsa ya dawo ya mikawa Shu’aibu bayan ya cire password. Yana sanyamishi, suka yi sallama ya rakasu har mota, duk da halin da yake ciki sai da ya ja Hajiya da wasa da dariya har sai da ya basu dariya gaba daya. Kafin nan suka yi sallama ya dawo ya shiga mota ya fita a miliyan.

*****

Hajiya Salma na zaune, Hayat a gefenta, Gwaska bai jima da barin gidan ba inda suka gama kashe magana akan sace Humaira.

A wannan yanayin ya shigo gidan, koda Maigadin ya hanashi shiga jan ido kawai ya mishi a dole ya bude mishi kofar ya shiga yana mai barin motar a waje.

Da sassarfa yake tafiya, har zai murɗa murfin kofar ya ji suna maganar da ya fi kaunar ya ji. Don haka sai ya tsaya cak a karshe ma ya karasa ta wurin window yana mai kasa kunne cikin faɗuwar gaba.

<< Rumfar Kara 31Rumfar Kara 33 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×