Skip to content
Part 36 of 41 in the Series Rumfar Kara by Rufaida Umar

Da wani irin farin ciki ta wayi gari, na farko, za ta je garin Kano. Garin da bata taɓa zuwansa ba, za ta ga Yaya Adam. Na biyu kuwa, za’a hukunta wanda ya kashe mahaifinta za ta ga danginsa kuma. Wannan ta sanya tun asuba zumuɗi ya hanata komawa bacci. Ta ɗakawa Amira da Jamila duka akan su tashi.

Fa’iza diyar Alhaji Mujahid, wacce ta kasance sa’arsu ta ja tsaki gami da cillamata filo a fuska.

“Kedai Allah Ya sauwake maki, ƴar kauye kawai. Wai ke baki iya komai a hankali ba?”

Humaira ta kai mata duka ta kuwa kauce da sauri tana ƴar dariya haɗi da miƙar gajiya.

“Ban iyaba! Wallahi Fa’iza ki fita idona. Dallah malamai ku kuma ku tashi ku yi sallah ku shirya, kun manta Umma ta ce da wuri za’a tafi?”

Amira ta ja tsaki.

“Bani da sallah fa.”

“Amman ai kya tashi ki yi wanka.”

Fadin Humaira.

“Wai ke zumudin me kike yi? Ko su Mama dai nasan yanzu suke sallah, kuma ko zasu yi wanka su shirya ba yanzu ba.”

Fadin Jamila dake mutsistsika idanu tana mai miƙewa zaune.

“Kema kya faɗa, wayasani ko ɗan balarabennan take don zuwa gani. Yayannan naku mai aiki a Kano. Mene ma sunansa kuka ce?”

Cewar Fa’iza  sadda ta murɗa kofar banɗaki za ta shiga.

“Au, wai Yaya Adam? Ke Humaira, soyayya ku ke?” Fadin Amira wacce tuni ta ji baccin ya kauracemata.

Harara Humaira ta watsamata, kunya duk ta kamata.

“Allah Ya sauwake, kema dai kin san Yayana ne, babu soyayya a raina. Duka-duka yaushe na cika sha hudu?”

“Ga jikinki kuwa kamar ƴar sha takwas.”

Suka sanyamata dariya wanda ya yi daidai da murɗa kofar dakin da akai, da sauri Fa’iza ga shige banɗaki. Maryam ce, tambaya ta yi musu kan hayaniyar me suke da asuba. Karshe ta umarci kowannensu da shiryawa idan sun yi sallah.

*****

Washegari da misalin karfe uku da mintoci na ranar Alhamis, Barrister Abeed ya damƙawa Salma takardun, bayan sun kammala saka hannu ya miƙa wanda ya cancanta ga Halima. Daga nan ya yi musu sallama ya fice.

Halima na fita daga gidan ta yi wani murmushi, wayarta ta hau ƙara. Ta duba, Gwaska ne, ta sanya a silent ta tashi motarta. Tana yin gaba wayar ta kara daukar sauti, Hajiya Murja kenan. Ta kashe wayar gaba daya.

“Zan nunamaku wace Halima.” Ta furta a fili gami da sakin murmushin mugunta.

*****

Tun shigowarsu garin Kano take ƙarewa garin kallo baki a hangame. Ba ta kara tsinkewa ba sai da ta ji su a saman wani titi shi ba a sama na shi ba’a ƙasa ba, daga iya har Jamila suka kama santinsa bayan an sauka, faɗi suke inama ba’a sauka ba. Unguwar Gandun Albasa nan suka yada zango a katafaren gidan da Prof ya gina sai ya zamana Baba Mujahid kadai kan sauka a gidan wasu lokutan idan ya zo Kano da iyalinsa. Gini ne na bene, ya ƙawatu iyakar ƙawatuwa.

Hannunta ta ja suka shige wani ɗakin, ta dubeta dakyau cike da damuwa.

“Wai ƴar uwata meke faruwa haka don Allah? Ina lura da ke tamkar ba’a hayyacinki kike ba. Meyafaru?”

Maryam ke maganar cike da rauni tana duban Bilkisu da idanunta gana daya sun yi zuru-zuru. Maganarta ya sanya Umman murmushin yaƙe.

“Ba komai Maryam, kaina ke sarawa kadan, amman banda wannan lafiyata kalau. Karki damu, na gode.”

Ta juya za ta fita.

“Dama akwai ƴar haka tsakaninmu? Na dauka yanzun dukkanku kuna yimin kallon ƴar uwa kuma ƴa.”

Jin wannan yasa Umman juyowa ta fasa fita.

“Kiyi hakuri, ni kallonki nake kamar Kanwata ma.”

Maryam ta nace da son jin matsalar Umma, a dole Umman ta aminta da faɗa mata amman da hujjar sai sun yi sallah tukunna. Suna idarwa Umma ta yi zaman labartamata komai tun daga farkon zaman ƙasƙancin da ta yi a gidan Hayat har sadda ya haɗu da masoyiyarsa kuma tsohuwar abokiyar karatunsa Salma.

Tunda ta ambaci Salma, ta kara da Fu’ad, Maryam ta shiga dogon nazari ga wani fargaba. Ta matsu ta ji ƙarashen labarin don za ta fi fahimta sosai.

Ba karamin girgiza ta yi da jin badakalar da ake ba, Fu’ad ɗan Bilkisu?

“Fu’ad ɗanki ne?! Wallahi su ne! Su ne wallahi!”

Abinda Maryam ke faɗi kenan gaba daya ta ruɗe idanunta kuwa tamkar an watsa ruwan borkono, sun kaɗa ga ruwan hawaye da ke faman kwararomata.

“Su ne me? Me kike nufi?”

Maryam dai ba amsa sai faman girgiza kai take tana kuka. Can Umma wani tunani ya faɗomata a rai. Da wani irin gigita ta dubi Maryam.

“Alhaji Haisam mijinki ya taɓa zuwa gidana kafin rasuwarsa.”

Jin wata sabuwa Maryam ta ɗago, shakka babu hatta da zuwan da ya yi ya rubuta a kundin sirrinsa. Umma ta bata labarin yanda suka yi. Maryam kuka, Umma kuka. Sun fahimci Hayat shi ne bakin munafiki. Fahimtar Umma daban da na Maryam.

Umma abu daya ta karanta, Hayat da Salma sun ci amanar Alhaji Haisam, sun kwace dukiyar da ba rabonsu ba sun zalunci marainiya Humaira. Zuwa yanzu ta kara gaskata cewar babu wani abu a duniya da Hayat ba zai aikatawa ba. Da alama kirjinsa babu zuciya.

A bangaren Maryam kuwa, tunaninta ya tafi akan kashe mijinta, wai ɗan uwanta, kuma jinin mahaifiyarta. Ƙani uba ɗaya har da sa hannunsa? Me yafi wannan baƙin ciki. Ashe Fu’ad din da ta rayu da shi, shima ba shi da laifi? Bai ji ba, bai gani ba aka yi mishi wannan yankar kaunar? Aka rabashi da mahaifiyarsa kawai don a zalunci bawan Allah?

“Ya zama lallai muyi shari’a da  mutanen nan! Naji ciwon kasancewar Hayat cikin wannan zuri’a mafi karamci da zumunci.” Maryam ta furta cike da tsantsar damuwa.

Sai da Humaira ta shigo domin kiran Umma bisa umarnin Uncle Hashim, suka daina koke-koken ganin hatta ita Humairar ta ruɗe tana kukan su faɗamata abinda ya faru. A dole suka rarrasheta. Maryam ta dubi Umma dake shirin fita.

“Idan asibitin za’a je, zan bi ku.”

Umma ta gyada kai jikinta ba kwari ta fita. Nan kuwa ta tarar hakan ne, aikawa Maryam sako ta yi akan ta fito. A bakin motar suka yi kiciɓus da Malam Kabiru. Nan Umma ke sanarmishi cewar za ta yi musu rakiya, ta san komai. Ya jinjina kai. Kallo daya ta yi mishi suka gaisa, sai ba ta ji dadin damuwar da ke kwance saman fuskarsa ba, sai dai a yanzun dole ce, dama aski idan ya zo gaban goshi hausawa suka ce ya fi zafi. Kaɗan ma suka ji akan katon sirrin da ta sani.

*****

Tun a harabar asibitin Uncle Hashim ya yi kiran Adam, hakan ya sa suna shiga suka yi kiciɓus da shi, yana ganin Uncle ya rungumeshi idanunsa suka kawo ruwa sai dai ya dake. Ya karasa ga Umma dake kukan tun ganin da ta yiwa Adam, tunaninta ya tafi akan shi kadai ne babban ɗanta namiji, ashe ba ta da masaniyar abinda gobe za ta haifar.

Rungumeta ya yi kafin ya ɗago ya sharemata fuska. Nan kuma aka gaisa sannan ya yi musu jagora zuwa ɗakin Fu’ad.

Yana jingine jikin gado, Haidar ne zaune gefensa yana kuka domin kuwa kasa jurewa ya yi sai da ya yi kiran Adam ya na rokon ya faɗa masa inda Fu’ad yake. Ganin yanayinsa ba karamin tashin hankali ya ji ba. Shigowarsu ce ta sanya Haidar din ficewa daga dakin bayan ya gaishesu.

Fu’ad yana hada ido da Umma ya soma kuka hannunsa dage da saitin zuciyarsa wanda yake jin kamar zai fashe. Cikin sauri Adam ya rikeshi.

“Ya isa please, idan ka ci gaba da kukan zan sanya ta koma. Ka yi shiru.”

Ya gyaɗa kai kamar wani ƙaramin yaro. Tausayinsa ya cika zuƙatansu. Fu’ad ya yi wani baƙi ya sauya kamar ba shi ba. Umma ta ƙarasa ya riƙe hannunsa, nan da nan wata tsantsar kauna ta shiga ratsa zuƙatansu. Tana son rungumeshi sai dai ba ta san ta yaya ba gudun kada ta fama mishi ciwonsa. Tuni ya rungumeta duk da azabar da ya ji har tsakar kansa, ba wai na raunin dake a cikinsa ba, sai na zuciyarsa da ke mishi raɗaɗi.

“Umma, kece mahaifiyata. Ke ce.”

Ya furta don ya ma rasa me zai ce. Ta ɗago kansa tana ƙara damƙe hannunsa cikin nata. Idan a baya aka ce tana kama da yaron sai ta ƙaryata mutum. Takan dai yi mamakin kamanninsa da Adam, takan manta cewar Adam kama yake da ita a fanni da dama. Bambancin Fu’ad da Adam ƙalilan ne. Hancin Fu’ad irin na mahaifinsa ne a maimakon ita. Sosai take kuka wata kaunarsa  na ratsa dukkan sassan jikinta.

“Ni ce Fu’ad, ni ce.” Ya rike hannunta gam yana murmushi mai bayyana haƙora ga hawaye caɓe-caɓe saman fuskarsa.

“Ki yafemin don Allah.” Ta yi saurin girgiza masa kai gami da rufe bakin.

“Ba ka taɓa yimin komai da saninka ba, idan ma ka yi ni Bilki na yafemaka Allah Ya baka lafiya, Ya yi maka albarka.”

Ya ji wani sanyi, ya kwantar da kai a kafaɗarta gami da sauke nannauyan ajiyar zuciya yana ji kamar an mishi bushara da gidan aljanna.

“Alhamdulillah, ko yau na faɗi na mutu, naji dadi Ummana.”

Su Malam suka ƙaraso, suka yi mishi ya jiki, duk ya bi ya nemi gafararsu gami da riƙe hannuwansu.

“Fu’ad ya jikin?”

Ya maida duba ga mai maganar, ya ganeta, mahaifiyar Humaira ce. Ya tuna abinda su Hayat suke shirin aikatawa ga ɗiyarta sai da gabansa ya fadi.

“Ka amsa mana.”

Fadin Umma a hankali, ya dubi Umma kamar wanda ya farka daga bacci sannan ya amsa.

“Ba ka ganeni ba ko?”

Malam na shirin magana, Maryam ta ɗora zancen bayan ta matsa kusa da Fu’ad yanda zai ji dakyau.

“Ka tuna Maryam matar Alhaji Haisam? Abokiyar zaman Salma?”

Ya zaro idanu yana dubanta, cikin sauri ya sa hannu ya dafe kirjinsa.

“Kunga Allah Yana sona da rahma ko? Yana haɗani da mutanen da na taɓa yiwa kure a rayuwa, Yana bani damar neman gafararsu.”

Sai ya fashe da kuka wanda idan yana yi shi kadai ya san azabar da zuciyarsa ke mishi. Adam ya riƙe shi a karo na biyu, ya dubesu idanunsa a kaɗe.

“Please.” Shi ne abinda ya iya furtawa don ya rasa ta ya zai ce su fita su bar kaninnasa ya huta. Uncle Hashim ya dubesu.

“Ku yi hakuri mu je daga waje.”

Girgiza kai Fu’ad ya yi.

“A’a, kar ku fita don Allah. Ummana ki tsaya kar ki ƙara barin ɗanki.”

Ta ji wasu hawayen sun zubomata. Yana rike da hannun Adam ya dubi Maryam karo na biyu.

“Na ganeki yanzu, ban taɓa yi miki kallon kurillah ba, koda nayi ba lallai na gane ba saboda a baya da kuruciya tattare da ni. Ashe ba ki mutu ba? Aka ce mana kin mutu? Kenan Humaira diyar Daddy ce?”

Murmushi Maryam ta yi tana mai gyada mishi kai lokaci guda tana sharar kwalla.

Ya rike Adam gam jin da ya yi kamar kirjinsa zai tsage. Bangaren Malam Kabiru da Uncle Hashim, sai suka shiga ruɗani. Suka tuno labarin Maryam, hankalinsu ya tashi, idan Fu’ad shi ne ɗan da ake zaton na Haisam ne, ta tabbata dagaske Salma ce matar da ta yi zaman kishi da Maryam?

‘Innalillahi wa inna ilaihir raajiun!’Malam ya shiga nanatawa a zuciya. Ya dubi Hashim.

“Ɗan fito muyi magana.”

Ya furta ƙasa-ƙasa. Hashim wanda shi kansa karin bayani yake nema, dole ta sanya ya fita jin abinda Malam zai ce.

“Na shiga ruɗu Hashimu, kada dai Hayatunmu ne ya auri Salmar da Maryama ta faɗi a labarinta?”

“Haka nake tunani Baba, idan ya tabbata ita ce. Kenan da haɗin bakin Hayat a cin amanar marigayi Haisam. Ta tabbata kenan komai da aka yi kuma ya faru, har da sa hannunsa.”

Girgiza kai Malam Kabiru ya shiga yi.

“Allah wadaran naka ya lalace, wato duniyarnan ba komai a cikinta illa darussan rayuwa. Yanzu Hayat ba zai ji kunyar ace duk inda ya je ya buga cuta, da jininsa yake yi ba? Da zuri’armu? Tsatso ɗaya? Ko hawu ce ta kama Hayatu, iyakar abinda zai yi kenan.”

“Baba anya ba asiri aka yi mishi ba? Wannan masifun da ya ɗorawa rayuwarsa sun yawaita.”

“Kul! Kada ka ƙara irin wannan zancen. Ka sani haramtacciyar soyayya ya yi, kuma ta dulmiyar da rayuwarsa cikin hatsarirrika masu yawa da girma. Ina jiyemishi tsoron makomarsa muddin bai gaggauta tuba ba. Ina son ganin Hayatu kafin na bar garinnan.”

“Baba ganinsa ya zama dole ai, domin dole ne mu shigar da ƙararsa kotu. Idan yana ganin ya ci bulus a abinda ya aikata ga Bilkisu, to wallahi karyarsa. Ai dama RUMFAR KARA ba abin dogaro bane, domin komai daren daɗewa gaskiya za ta yi halinta. Yanzu sai ya girbi abinda ya shuka.”

“Allah Ya kyauta, Ya shirya mana.” Shi ne kaɗai abinda Malam ya ce.

*****

Asibiti sai ya koma wurin zuwan Umma, nan take wuni. Tun tana ɓoyewa sauran jama’a, har Malam da kansa ya haɗa meeting da sh Prof da dukkan jama’ar gidan ya zayyanemusu komai. Masu salati nayi masu kuka nayi. A karshe aka yi fatan alheri ga Fu’ad. Humaira sosai abin ya taɓa ranta, ta tuna yanda yake mutum mai barkwanci idan ya so, yana da nutsuwa da kamun kai na rashin son raini. Amira kam sai da ta yi sunan zaune a karshe ta kara godiya ga da bai ɗora mata soyayyarsa ba. Suka dubi juna da Humaira suka yi murmushin tuna hirarsu ta Yobe akan Fu’ad da Shuraim.

Bayan Kwana Biyu

Motocin suka faka a daidai wani ginin bene mai kalar ruwan toka da fari.

Motar Hashim ce a gaba sannan ta Prof da iyalinsa sai ta Baba Mujahid da ta Abba. Kusan lokaci guda suka firfito. Baba Mujahid ne ya soma yin gaba suka yi musabaha da maigadi kafin ya ce a sanar da Hajiyar zuwansa da iyayensa.

Tsohon dattijon Maigadin ya mike don ba yau ya san Mujahid din ba, yakan leƙo lokaci-lokaci tare da Abba, bisa umarnin Prof, su gaisa Hajiya Karime. Har suke zuwa a karon kansu jefi-jefi.

Ya dawo ya isar da saƙonta akan su shigo don har Nura ta turo. Nura sam bai gane Maryam ba ita kuwa kallonsa take, ba ta yi mamaki ba don a sannan yana yaro, da ace Sadik ne shi yake da tabbacin zai ganeta a kallo ɗaya.

Hajiya Karime na zaune a falo ta sha lulluɓi, Sadik wanda bai jima da zuwa gidan tare da matarsa Juwairiyya ba, yana zaune suna hira. Sallamarsu ce ta katse tunaninsu. Basu tsammaci suna da yawa har haka ba. Sai da duk suka shiga kafin sallamar Maryam ta dauki hankalinsu. Hajiya Karime ta mike  tana mai jin kamar ta saki fitsari a wando, Sadik ma miƙewar ya yi yana ambaton sunanta gami da salati. Hankalinsu ya koma ga Juwairiyya da ke salati tana ambaton sunan Hajiya. Ashe suma ta yi.  Da sauri suka yi kanta aka yayyafa ruwa, tana farfaɗo wa ta ƙara yin arba da Maryam cikin wadanda suka riƙe ta, ita kuwa Maryam kamannin Hajiya Karime da Haisam ne ya ƙara tayarmata da tsohon fami.

“Maryam nake gani? La’ilaha illal lahu Muhammadur Rasulullah (s.a.w), ni Karime jikar mutum hudu  Allah Ka yafemin, Kada ka dauki raina ban sanya jikana Fu’ad a ido ba.”

Abin ya so basu dariya, Humaira ta kunshe baki don kakarta ta ta bata dariya, duk wai don ta ga Maryam ne.

“Hajiya ba mafarki bane, ni ce dai Maryam din da kika sanj, ban mutu ba.”

Sadik ya hakikance yanzun dagaske ne, don haka ya lallaɓa Hajiyarsa suka hada hannu sosai da Maryam, nan kuma sai Hajiya Karime ta fashe da kuka.

“Maryam ina kika shiga? Ina kika tafi kika bar mu? An ce mana kin rasu, har mun ci gumbarki, ashe karya ne? Meyafaru haka? Ina cikinki? Allah Sarki Haisam, Allah Ya yi maka Rahma.”

Gaba daya kuma sai ta basu tausayi. Aka koma kowa ya zauna hannun Hajiya Karime cikin na Maryam.

“Bakya son ganin jikartaki da alama. Tunda kukan ya ƙi tsayawa.” Fadin Abba cikin zolaya. Sadik wanda ya zubawa Humaira idanu tun shigowarsu,daga ya dauke sai ya maida. Shi ya yi saurin yin magana.

“Wannan ce ɗiyar Maryam ko?” Duk suka dubi wacce ya nuna, Humaira ce. Duk da hawaye take sai da ta yi murmushin da ya bayyanar da dimple dinta, hakan ya sanya Hajiya Karime daukar salati.

“Wallahi wannan jinin Haisam dina ce. Ko ba’a faɗa ba, fuska ta nuna. Matso nan na ganki da kyau.”

Humaira ta karasa, ta rungumeta tana kuka da roƙarwa ɗanta aljanna. Ta dubesu.

Ba komai ne ya sanya nake matsawa sai naje na ga jikana ba illa yawan mafarkin Haisam da nake, yana yawan cemin naje na ga abinda ya haifa. Ashe ba Fu’ad kadai yake min inkiya ba, har da ke. Mene sunanta?”

“Humaira ko?” Sadik ya tari zancen da sauri ya a dariya. Nan Maryam ta tuna a gabansa ma Haisam ya taɓa cewa sunan ɗiyarsa ta farko a duniya A’isha Humaira. Ta gyaɗamasa kai tana dariya.

Wuri sai ya hautsine da hira, Umma ba ta jima wani sosai ba ta wuce asibiti wurin ɗanta. Adam da kansa ya zo daukarta sai dai kwata-kwata bai shiga gidan ba. Zuwa yanzu ciwon Fu’ad ya fi komai tashin hankalinsa duk kuwa da ya so ganin Humaira. Yanzun ma waya Dr Ibrahim ya mishi akan ya taho da Umman, wannan ta sanya shi zuwa bayan an mishi kwatance.

*****

Tsaye ya yi yana duban kofar gidajen iyayennasu, burinsa ya ga giftawar wani na gidan domin ya yi tambayar da zai yi. Babu hanyar sanin komai dake faruwa idan ba zuwan ya yi ba. Allah Ya taimakeshi ya hangi Baharu zai shige gida. Ya yi saurin kiransa. Baharu bai gane motar ba hakanan bai hangi na ciki ba sakamakon duhun gilashin motar. Hayat ya sauke gilas, ganinsa ya sanya Baharu nufi wurin da ƴar fara’a. Bayan sun gaisa ya ce.

“Mutan gidan suna nan?”

Tambayar ta bashi mamaki. Ganin haka Hayat ya sauya zancen.

“Ina nufin basu fita ba.”

“Eh amman su Baba Malam basu dawo ba.”

Ya gyara zama jin an zo inda yake son ji.

“Daga ina kenan?”

“Ai da suka je Maiduguri wurin iyayen Anti Maryam sai suka wuce Kano. Naji ance wurin dangin baban Humaira suka je.”

Bai san sadda tusa ta suɓuce ta fito ba har sai da Baharu ya mishi kallon kasan me ka yi kuwa? Yana muzurai ya share gumi.

“Shikenan, nima yanzu na shigo garin, zan je masauki idan na huta zan shigo. Ka kama bakinka kada ka faɗa wa su Baba na zo, zai yi faɗa akan dalilina na ƙin shiga.”

Dama Baharun ba mai maganar bane, ya amsa da toh, Hayat ya yi saurin zuge gilashin motar ya fice jikinsa har rawa yake. Ta faru ta ƙare! Ruwa ya ƙarewa ɗan kada! Ya san kuma shikenan komai zai fito a yanzun.

Waya ya dauka ya kira Salma.

“Duk inda kike ki koma gida ki shirya kaya. Ki sanya Salihu ya yankar mana ticket na jirgin zuwa Abuja gobe, jirgin safe. Akwai babbar matsala.”

Salma ta yi turus, wannan kalma ta matsala ta soma jagula lissafinta.

“Meyafaru?” Ta yi maganar a sanyaye don yanzu ta soma gajiya. Tsoron da fargabar sun mamayeta fiye da zatonta.

Ya bata labarin abinda ke faruwa. Tana zaune sai da ta mike tsaye.

“Shikenan! Bari na kirashi!” Ta fadi cikin daga murya na wacce ta tsorata. Kai tsaye ta kira ya tabbatar zai samar, ta kashe ta tura masa kudin ta account. Salihu ya jima yana kular musu da harkar tafiye-tafiyensu kasancewarsa ma’aikaci a filin jirgin Malam.

A daren Hayat ya dawo Kano, shima harhaɗa kaya ya shiga yi. Daga bisani ya yi kiran Alex a waya ya mishi bayani kan ya kula da asibitin na wasu lokutan tafiyar gaggawa ta kamashi.

*****

“Ina jinki.”

Sadik ya furta yana duban Maryam.

“Gidan Barrister Munir nake son ka kaini. Ina dauke da magana mai muhimmanci.”

Ya yi shiru yana dubanta sai kuma ya girgiza kai.

“Haba Maryam, ko ba ki samu Barrister da kanki akan dukiyar Humaira ba, zamu yi maganar mu da kanmu. Ki sani, dole sai an hado  dukkan kadarorin da aka damƙawa Fu’ad tunda yanzu ta tabbata ba shi ne kaɗai ɗan Yaya ba. Ki…”

“Wallahi ka fahimceni baibai Sadik, tun can za ka yimin shaidar abin hannun yayanka ba shi ne gabana ba. Mun yi aure ne bisa turbar so da kauna da kuma yarda da juna. Wannan wata magana ce ta daban ko kuma ince amana da Haisam ya damƙamin kafin rasuwarsa. Ya zama dole kuma a cika wasiyyar mamaci.”

Ya ɗan yi shiru jikinsa sai ya ɗan yi sanyi.

“Shikenan. Allah Ya sa alheri ne.”

Ta amsa, ya fiddomata da lambar a wayarsa, ta yi amfani da wayar da Hashim ya damƙamata don amsa kira ta dauki lambar sannan ta mishi godiya suka rabu.

*****

Waya ya shiga amsawa.

“Inspector Kabir Rano.”

“The great Doctor, fatan an wuni lafiya?”

Adam ya yi murmushi gami da gyara zaman wayar yana kallon hoton Fu’ad dake cikin frame saman teburin ofishinsa.

“Alhamdulillah Inspector. Wani taimako nake da bukata.”

“Feel free to say it, ba yau da muke tare ba Doctor.”

Ya ji dadin furucinsa duk kuwa da cewar yasan da yawa cikin abokan karatunsu sun mance da shi, to akai-akai suna gaisawa da Inspector. Hakanan ko a WhatsApp ya ganshi online, zai kulashi.

“Wata mata nake son a kama.”

Nan ya ba shi labarin Halima da abinda ta yiwa Fu’ad, Inspector ya jinjina abin. Ya bukaci akan Adam ya zo ofishinsa don ya shigar da ƙarar. Daga nan suka yi sallama.

A ranar Adam ya ziyarci Inspector, suka yanke maganar. Fu’ad da kansa ya ba Adam adireshinta. Suka rabu da Inspector yana mai godiya da karamci ganin har ya tura a taho da ita.

*****

Sauri-sauri take ta bar gidan zuwa Airport sakamakon tsoron abinda zai biyo baya tsakaninta da Gwaska da Hajiya Murja. Ta tabbatar ba zasu kyaleta ba sai sun zo inda take. Ba yanda ba ta yi da Hanan akan ta zo su tafi tare ba sai dai ta ce babu inda za ta je har sai Fu’ad ya warke sun yi aure. A dole ta rabu da ita bayan ta gargaɗeta kan ta ɓoye sirrin inda ta je kada ta bari kowa ya ji.

Ta janyo akwatinta ta shiga kiciniyar rufe gidan gami da jefa mukullayen a jaka. Tana bude mota da zummar shiga, sallamar ƴan sandan ta ratsa dodon kunnenta. Hanjin cikinta suka kaɗa, baki na rawa take dubansu.

“La..la..lafiya?”

Ƙatuwar matar wacce ta matse tumbinta da belt ga dubeta sa’ilin da take bugun hannu da sandarsu.

“Madam sannu, mun zo arresting naki ne.”

Cikin alamun rashin gaskiya ta zaro ido.

“Akan wane dalili? Me nayi muku?”

Wani murmushi Matar ta yi.

“Akan kokarin kisan kai da ki ka so yi ga Fu’ad. Sai kuma wasu tambayoyi da ake son ki amsa.”

‘Na shiga uku!’ Halima ta furta a zuciya.

Duk yanda ta so ta turje ba ta samu wannan damar ba, har roƙonsu ta yi akan za ta basu ko nawa suke so, fadin hakan ya sanya matar kifamata mari har sau biyu a kuncinta. Ta sanya Sajen ya ja ta zuwa motarsu. Halima da karfi ta cewa Maigadi.

“Kar ka bar uban kowa ya shiga gidana, ka rufe ko’ina.”

Fadi yake Toh.

*****

Wani farin gida ne mai kyau da tsari, daidai nan suka faka. Hashim ya dubeta.

“Nan ne gidan bisa kwatance da kuma lambar gida da ya ba ki.”. Maryam ta gyada kai.

“Nan ne.”

Suka fito a tare, an rubuta Barrister Munir’s residence a jikin wani ɗan katako. Waya ta yi mishi, ba jimawa sai Maigadi ya budemusu gidan. Suka shiga da motarsu, bayan Hashim ya faka, dama Maryam na tsaye a harabar tana jiransa.

Ya fito ya tako har inda take tsaye, fa kauda kai.

“Mu shiga?”

Ya tambaya idanunsa a kanta. Ta amsa da toh. Suka shiga bisa jagorancin Maigadin. A falon saukar baƙi suka iske Barrister Munir zaune. Dattijo mai tarin ilimin boko da arabi, kansa duk furfura ya sanya tabarau a idanunsa. Kar yake kallonsu. Tun shigowar Maryam din yake ƙaremata kallo yana jinjina hukuncin Ubangiji.

“Allah Hakeem! Mrs Haisam Zakariyya, kece dai nake gani din ba karya ba.”

Maryam da Hashim suka yi dariya.

“Ni ce Barrister. Fatan na sameku lafiya.”

“Lafiya kalau Maryam, to ya akai aka haihu a rataya?”

Sai kuma ta ji idanunta sun yi rauni.

“Kukan ya isa fa, haba.” Ta tsinci muryar Hashim ta ɗan dubeshi sai ta yi murmushi.

<< Rumfar Kara 35Rumfar Kara 37 >>

1 thought on “Rumfar Kara 36”

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×