Skip to content
Part 39 of 41 in the Series Rumfar Kara by Rufaida Umar

“Fu’ad lafiya? Ina Umma?”

Fu’ad ya kwantar da kai saman cinyar Adam sai kuka, kuka sosai yake kamar yaron goye ya kasa cewa uffan.

Adam duk dauriyarsa sai da ya ji hawaye na gangarawa saman kuncinsa. Ya kunna karatun ya ci gaba da saurara ba tare da ya ce mishi uffan ba, bai kuma hanashi ba. Tunawa ya yi da  Amira wadanda suma dakyar ya rarrasheta har sai da Malam ya haɗa da nasiha kafin a shawo kanta ta nutsu. Suna da labarin komai a yanzun dangane da mahaifin da tun haihuwarsu ya tsanesu don kawai sun mishi zuwan bazata duniyar tamkar shi ya Haliccesu.  Amir kam ko a jikinsa don dama shi bai daukeshi a matsayin Uba ba tun tashinsa. Ya fi girmama Adam ma a kansa. Ya tabbatar da Adam abin ya shafa zai yi abinda ake kira kusan hauka.

“Ka yi hakuri, kuka ba zai mana maganin komai ba. Ta faru ta ƙare sai addu’a kawai.”

Adam ya furta a karshe, Fu’ad ya ɗago don zuciyarsa ta mishi dadi fiye da a farko sakamakon karatun Alkur’ani da Adam din ya kunna.

“Na yi bakin cikin kasancewarsa mahaifinmu. Inama ana sauya uba?”

Murmushi mai ciwo Adam ya yi ganin ire-iren kalaman da ya saba furtawa ga Umma ne tun yana karami tana kwaɓar bakinsa. Turo kofar da akai a firgice ya sa suka kalla. Umma ce, ganin Fu’ad tare da Adam sai ta sauke ajiyar zuciya ta rufe kofar ta shigo sosai.

“Haba Fu’ad, ka faɗarmin da gaba nayi zaton ko saceka aka yi. Kada ka ƙara yimin irin wannan.”

Cike da so da kauna irin ta ɗa ga mahaifiyarsa yake dubanta. Hakuri ya bata daidai sadda Adam ya kashe karatun. Ta  zauna tana dubansu a nutse.

“Ku yi hakuri, kada ku kasa cinye jarrabawar Ubangiji a kanku. Ku sani cewa kowane bawa dake a doron ƙasa akwai irin tasa kaddarar. Babu yanda za’a yi haka Allah Ya so. Wa ya taɓa tsammanin fitowar bara girbi har irin Hayatu daga zuriyar Malam Abdallah? Mutum mai yawan ibada da tsoron Allah? Sai dai ku sa a ranku, da ace ban aureshi ba, ba zan sami yara masu albarka irinku ba. Fatana ku haɗa kai ku zama tsintsiya maɗauri guda. Ina alfahari da ku hakan kan ragemin bakin cikin da na ƙunsa a hannunsa.”

Kalamanta sun sanyaya zukatansu sosai. Ƙwanƙwasa kofar da aka yi ne ya dauki hankalinsu, Nos ke sanar da Adam ana bukatarsa a emergency, hakan yasa suka mike suka koma daki shi kuwa ya fita.

*****

Ranar litinin cikin watan Maris da misalin karfe tara na safe. Kotun ta cika maƙil da jama’a da wadanda abin ya shafa har ma da wadanda bai shafesu ba. Can a gefe guda, Umma ce tare da Maryam sai su Hajiya Karime da Alhaji Idris, sai kuwa Hashim da su Khalisat wadanda suka zo ranar Lahadi. Humaira ba ta yi gigin zuwa ba don tasan zuciyarta ba zata iya dauka ba. Adam na zaune ya zuba ido ya ga ta inda za’a fara. Haidar suka bari a wurin Fu’ad.

Jim kadan Alkali ya shigo aka mike har bayan zamansa sannan kowa ya koma mazauninsa.  Bayan kotu ta nutsu, Alƙali ya gama ƴan rubuce-rubucensa kafin ya nemi jin shari’a ta farko a ranar. Registrat ya mike ya karanto shari’ar kisan Alhaji Haisam wanda ake zargin Hayat da Salma. Daga nan aka fito da Hayat da Salma zuwa wurin tsayuwar mai laifi a kotu (Dock). Idanun kowa akan Salma da Hayat sa’ilin da aka tutso ƙeyarsu cikin kotun. Yan uwansa suka kalleshi, gaba daya ya muzanta ya koma tamkar ba shi ba. Adam ya kauda kai saboda ɓacin ran da kallonnasa ke jawomishi a rai. 

Bayan zamansa Barrister Ridwan ya miƙe ya soma gabatar da kansa.

“Sunana Ridwan Munir, daga (Kano State Ministry Of Justice). Mai fafutukar kare hakkin wanda aka kashe, Alhaji Haisam. Ina neman kotu ta bani damar yin tambayoyi ga wadanda ake zargin da aikata laifin.”

“Kotu ta ba ka dama.” Fadin Alƙali, ya yi godiya sannan ya karasa ga Salma.

“Hajiya Salma ko?”

Ta gyada kai tana sharar hawaye hango Innarta da ta yi tsamo-tsamo a cikin ƴan kallo tana zubar da nata hawayen. Dama banda Innar bata da ran ganin wasu daga gidansu don ba ta daukesu mutane ba.

“Shekara nawa da aurenki da tsohon mijinki marigayi Alhaji Haisam?”

“Mun kai shekaru goma sha biyu tare kan ya rasu.”

Barrister Ridwan ya jinjina kai.

“Kuna tare ya rasu?”

“A’a.”

“Abinda kowa ya sani ne, Alhaji Haisam ya rasu ta sanadiyyar hatsarin mota wanda kuma a karshe aka gane cewar kashe shi ne aka yi bisa la’akari da bayanan da ya bari a  kundin sirrinsa.”

Ya miƙa kundin sirrin ga  Registra shi kuwa ya miƙa ga Alƙali.

Salma ta bi kundin sirrin da kallo tana mai mamaki, ashe sirrinsu ya jima a ɓoye, bayyanuwarsa ne sai yanzun?

“A cikin wannan kundin sirri wanda ya zamo mallakin Marigayi Alhaji Haisam. Ya yi bayanin yanda tsohuwar matarsa Hajiya Salma da tsohon saurayinta Dr Hayat, suka ci amanarsa ta hanyar da ita Hajiya Salma ta kai mishi ɗan da ba jininsa ba a matsayin nasa don wata manufa nata. A karshe bayan asirinta ya tonu sai suka ci ɗamarar ganin bayansa ita da tsohon saurayinta Dr Hayat. Marigayi Alhaji Haisam ya rubuta tun daga sadda ya ji wayar da ta yi da shi Dr Hayat akan fitowar da za ta yi ta aureshi har zuwa sadda suka soma barazanar kashe shi.”

Barrister yana kaiwa nan, jama’ar kotun suka soma ƴar ƙusƙus har sai da Alƙali ya tsawatar. Hayat kansa a ƙasa hawaye kawai yake don jikinsa ya gama sanyi yayinda ita kuwa Salma ke rarraba idanu ta rasa inda za ta saka ranta ta ji dadi. Barrister Ridwan ya dawo gareta.

“Hajiya Salma da kanki kin shaidawa ofishin yan sanda cewar kina da hannu a kisan Alhaji Haisam, hakane?”

Ta gyada kai.

“Hakane.”

“Ko za ki iya bayyanawa kotu ta yanda akai ku ka kashe shi?”

Salma ta ɗago ta dubi bangaren da Maryam ke zaune da yan uwan Haisam, ta sauke kanta murya da jikinta su na rawa ta soma magana.

“Tun aurena da Haisam nake da burin na haifarmasa ɗa don kawai ya zama magajin dukiyarsa. Sai dai shekarunmu hudu ko ɓatan wata ban taɓa ba. Wannan abu ya tashi hankalina ganin har a dangi an soma zugashi kan ya yi aure. A wannan lokaci ne kuma sai na samu ciki. Kulawa da kyautatawa ba irin wanda Haisam da yan uwansa basu nunamin sai kuwa Hajiyarsa da muke samun rashin jituwa kadan sakamakon tun farko ba ta kaunaci aurena da shi ba. Wannan bai dameni ba saboda irin yanda Haisam ke sona. Ranar farko da na soma zuwa awo a asibiti muka hadu da Hayat. Ya yi mamakin ganina hakanan ni kaina ban yi zaton zan sake ganinsa ba sanin da nayi ɗan Yobe ne, karatu ya kawoshi Kano. Ganin da Hayat ke min a asibiti ya yi sanadiyyar tasowar tsohuwar soyayyar da ya yimin a baya. A hankali kuma sai ya kasance duk zuwan da zan yi asibiti zamu hadu da shi mu sha hira, tun bana biyemasa har ta kai nakan wuni a ofishinsa. Babu labarin da ba ya ban akan matarsa Bilkisu da irin kiyayyar da yake gwadamata duk domin ni. Nakan  ji dadi ko ba komai Hayat na yimin mahaukacin so fiye da wanda Haisam ke yimin.  Cikina nada watanni huɗu, aka yimin scanning aka gano cewar mace ce. Tun a lokacin na tashi hankalina, na nuna sam ba haka na so ba don na fi kaunar ɗa namiji fiye da mace. Hayat ya yi ta lallaɓani akan nayi hakuri za’a san abin yi, lokacin yake bani labarin matarsa Bilkisu tana dauke da juna biyu kuma watanninmu ɗaya hakanan scanning ya nuna cewar namiji ne a cikinta. Muddin hakan ta faru shi mai iya daukar abinda ta haifa ne ya bani su zama yara biyu. Na yiwa Hayat kallon mahaukaci a lokacin don har fada mukai ganin rainan hankali kawai zai yi. Da wannan na tattara na wuce gidanmu na yiwa Innata bayani, ita ce ta kara karfafa min gwuiwa game da shawarar Hayat ta kuma tabbatarmin zai yi tunda ta ga irin soyayyar da ya nunamin kafin aurena da Haisam.

Halima ta kasance mazauniyar daya daga cikin gidajen karuwan da a shekarun baya aka ƙona aka kuma tashe su. Ni na taimaka Halima ganin ba ta fi sa’ata ba kuma ko ba komai lokacin inada bukatar wacce za ta taimaka mana kamar yanda Hayat ya sani nemowa, na kai ta nan gidan Haisam matsayin yar aiki da Inna ta samomin daga kauye. Ban ga alamun ya yarda da hakan ba sai dai ya kyaleni ya kuma ce tana iya zama.

Duk wata kulla-kulla da Halima mukai, ban ɓoyemata komai ba da kuma abinda muke so ta yi ta tabbatarmin ko mene za ta yimin tunda har na taimakamata lokacin da asirinta ke shirin tonuwa, lokacin da cikina ya cika watanni tara, ina jin alamun naƙuda na ja Halima muka tafi asibiti ba tare da sanin Maigidan ba. Sai dai kuma ikon Allah ina cikin wannan yanayi, ita Bilkisu babu ma alamar naƙudar. Hankalinmu ya tashi, muka rasa abin yi. Ga lokacin Haisam ya ji labarin bani da lafiya ya zo asibitin.

Sai da nayi kwana biyu a wannan yanayi sannan na haihu kuma namiji na haifa maimakon Macen da aka ce a scanning.

Cikin ikon Allah kuma a ranar aka kawo Bilkisu na naƙuda, Hayat ya kai ta ɗaki kusa da nawa, bayan ta sauka ya yi saurin ba Nos dake dakin umarnin fita, sanin da ta yi matarsa ce ya sanya ta fice daga dakin. Alokacin Halima ta shigo dakin sanye da kayan aiki suka yi kiciɓus, shi ya fice da jaririn ita kuwa ta yi ciki da jaririn da na haifa babu rai. Ta samu Bilkisu ta mikamata gami da bata hakuri cewa abinda ta haifa bayan wasu sakanni ya rasu. Bilkisu ba ta kawo komai ba ta yi hawayen rashin ɗanta daga nan aka gyaramana jiki ta koma gida bisa umarnin Hayat da ya ce zai kula da ita a gida.

Ni kuwa sai ya kasance na rungumi jaririn da Bilkisu ta haifa matsayin nawa, ni na shayar da Fu’ad na raineshi na mishi komai. Kafin barin asibitin Hayat ya tabbatarmin muddin ban cika alƙawari ba nan gaba kaɗan, zai tona asiri. Muka rabu akan hakan ma ba zata faru ba.”

Salma na kaiwa nan ta yi shiru tana kallon fuskokin jama’a, Umma hawayen ma ta kasa ta dai yi shiru ta zubawa Salma ido tana kallon abin kamar almara. Wato dai niyyar Hayat ya bata diyar da ba jininta ba ta raina. Kenan da ace jaririyar Salma na raye, zai kasance ita ce ta shayar da ita a madadin Salma.

‘Wannan wane irin son duniya ne?’. Fadin Umma a zuciyarta.

“Game da kisan Haisam kuwa, shawarar Hayat na bi..”

Muryarta ta kakare sai kuka, jama’ar kotun suna kaico da Allah wadai. Dakyar wurin ya tsagaita bisa tsawatarwar Alƙali kafin kuma Barrister Ridwan ya ɗora bayan ya maida hankali ga Dr Hayat wanda ba ya ko kwakkwarar motsi.

“Dr Hayat Bello. Kana tare da mu a kotu, me za ka ce game da bayanin da Hajiya Salma ta yi?”

Hayat ya kalleshi, matashin yaron da bai fi sa’an Adam ba, yau shi ke titseshi akan mummunan laifi wanda da sa hannunsa a ciki. Me ya fi wannan ciwo? Ashe dai RUMFAR KARA ba abin dogaro bane. Yau ga ranar ƙin dillacin.

“Dukkan bayanan da Salma ta bayar gaskiyane.”

“Ko za ka yi karin bayani akan yanda ku ka kashe Marigayin?”

Hayat ya gyada kai yana sharar fuska.

“Bayan fitowar Salma daga gidan aurenta, na samu damar aurenta na kai ta gidana.  Muka ci gaba da bibiyar Haisam akan ya yi abinda muke so ko mu kashe shi, zuwan da muka yi ofishin Haisam tare da Salma na karshe, na yanke shawarar kashe shi kafin asirinmu ya tonu saboda mu samu gadon Fu’ad. Tun Salma na gudun kada ayi kisa har na samu a karshe na shawo kanta ta amince da hakan bayan na nunamata wannan kadai ne hanyar da asirinmu zai rufu. Wannan tasa tare da taimakon Gwaska. Gwaska wani dan fashi da makami ne, na sanshi sanadin Halima kasancewarsa daya daga cikin abokan ashararancinta. Muka nemi da ya ɓullo da hanyar da za’a kashe Marigayin ba tare da jama’a sun lura da mu ba. Sai muka yanke shawarar kunce tayoyi gaban motarsa ta yanda zai yi tangal-tangal a titi har ya yi mummunan hatsarin da zai haddasa mishi mutuwa.”

Kotun kowa ya shiga fadin albarkacin bakinsa, Umma ta dubi sashin Adam, babu shi ba dalilinsa da alama ya jima da ficewa ma a kotun. Maryam kuma take sosai tuna tsohon mijinta kamar yanda su Nura ke share hawayen tuno da yayansu mutum mai son zumunci da yawan fara’a ga kuma hakuri.

“Ta yaya ku ka yi nasarar kwance tayoyin motarsa?”

Hayat ya dora.

“Gwaska, shi muka sanya. Sanin da muka yi Alhaji Haisam mutum ne mai taimako, yasa muka yi amfani da wannan damar. Hurdo Street hanya ce da babu yawaitar ababen hawa hakazalika sai ayi awanni biyu babu ko giftawar wata halitta. Da wannan muka yi amfani muka sa Halima ta ɓadda kama zuwa mabaraciya mai tsananin bukata. Daidai sadda Alhaji Haisam zai wuce da motarsa bayan fitowarsa daga gida, Halima ta tsaya gaban titin da sanda alamar makauniya ce. Ya faka motar ya nufi wurinta, da niyyar taimako. Kuka ta sanya ta ba shi labarin yanda ta kwana ta wuni ba ta ci ta sha ba. Tsayuwar da Alhaji Haisam ya yi don taimaka mata, Gwaska ya yi anfani da damar wurin kunce notunan tayar gaba ta bangaren direba.  Halima na aikin daukar hankalinsa har sai da Gwaska ya bar wurin. Bamu tsaya anan ba, na bi sahun motar har zuwa inda hatsarin ya gudana domin kuwa motar ce ta yi ta juyawa saman titi har ta ci karo da ƙatuwar bishiyar darbejiya. Tare da Salma muka fito daga tamu motar bayan mun ɓadda kama, ganin bai karasa cikawa ba, na yi amfani da dankwalin Salma na shaƙe wuyansa a yayinda yake ta ambaton Allah. Salma ta ankarar da ni tahowar mutane wannan ya sanya ni saurin sakinsa bayan mun tabbatar ya ƙarasa muka shige mota muka bar wurin ba tare mun tsaya ba.”

Kotu ta kara daukar hayaniya, yan uwan Hayat kamar su nutse tsabar kunyar abinda ya aikata. Malam Kabiru ne kawai ya iya zuwa sai Kawu Lawwali. Barrister Ridwan ya kara jefawa Hayat tambaya.

“Bayan kashe Marigayin, kun nemi kashe Matarsa Maryam a sadda ta gano abinda ke faruwa, ko za ka ba kotu bayanin yanda komai ya faru?”

“Tabbas mun yi niyyar kashe Maryam sai dai Allah Ya kwaceta daga hannunmu.”

Ya bada labarin yanda duk abin ya kasance da yanda suka sanya Gwaska nemanta.

Bayan gama tattara jawabai Alƙali ya yi rubuce-rubucensa kafin a karshe ya ɗaga shari’ar zuwa wani makon. Ya kuma bada umarnin gurfanar da Gwaska da Halima a gaban kotu a zama na gaba.

<< Rumfar Kara 38Rumfar Kara 40 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×