Skip to content
Part 4 of 41 in the Series Rumfar Kara by Rufaida Umar

Ta sauke ajiyar zuciya gami da kasa tankawa. Ta kara tsintar muryar ɗanta na faɗin.

“Na yarda Umma, Rumfar Kara ne mu, bamu da amana. Bamu santa ba, bamu da adalci, muga…”

Ta yi saurin rufe bakinsa ta hau girgiza kai.

“Kar ka ƙara, zunubi ne babba. Domin ka tuna su waye mazan, nima a baya da na yi furucin zafi da ɓacin rai ne ya sanyani.”

Ta dauke hannunta, ganin kamar ranta ya 6aci sai ya mike tsaye yana ƴar dariya.

“Duk yanda kika ce hakan za’ayi. Ba zan ƙara faɗi ba da yardar Allah. Ayi hakuri ranki ya daɗe.”

Ya ƙarashe yana dan rankwafawa, ta kuwa kai mishi rankwashi a ka, suka yi dariya daga nan ya yi mata sallama ya dauki kayan aikinsa ya fice. Da kallo ta bi bayansa tana nazarin maganarsa, shiyasa fa magana gaban yara ba shi da wata fa’ida. Kai sai ma ka manta da ka faɗi amman su abin sai ya zauna a ƙoƙon ransu. Bata mance sadda ta yi furucin ba, a ranar kuka take tana furta kalmomi na ɓacin rai ga mijinta Hayat. Wannan ce rana ta farko kuma ta karshe kamar yanda ta ke fata da ta ta6a maida mishi martani ba wannan biyayyar ba tausasa murya.

A ranar ga tsohon cikin ƴan biyu, ya zazzageta tas har yana neman ta6a musu iyaye wanda hakan ya fusata zuciyarta ta gasa mishi maganganu cikin zubar hawaye. Adam na tsaye yana kallo yana nashi kukan, wannan ranar ta bar mishi tabon da ya kasa mantawa. Tana da yaƙinin yana daga cikin ranakun da suka kara assasa tsanar uban a zuciyar ɗansa.

Sosai Umma ta shirya gidanta, ta gyara sashin Maigidan tsaf don dama ba ta barin kowa ya gyara. Sai karfe takwas da mintuna na dare ya shigo gidan. Sadda ya shigo Umma na zaune tare da yan biyunta, sun maida hankali wurin yin assignment dinsu na makaranta, suna yi suna cacar baki kamar yanda suka saba. Ita kuwa tana amsa wayar yayanta da suke ciki daya, Hashim.  Jin hayaniyarsu ta soma damunta ya sanya ta katse wayar, tana shirin yi musu magana suka tsinci sallamarsa. Kamar an yi ruwa an dauke, haka Amir da Amira suka yi tsit. Amir gabansa har faɗuwa yake tsabar tsoro ganin yau ma kamar koyaushe fuskarsa a murtuke.

“Abba sannu da zuwa.”

Ƴan biyun suka faɗa kusan a tare, ko kallon inda suke bai yi ba sai dai ya ɗan gyaɗa kai. A duniya ba wanda yake jin haushi da tsanarsu kamar su biyun domin a cewarsa cikinsu ya zo mishi ba tare da ya shirya hakan ba. Duk iya kokarinsa a matsayinsa na kwararren likita bai ci nasara wajen ganin bayansa ba sakamakon girman da ya riga da ya yi. Hakan yasa ya ke musu kallon Kaddara.

Har ya shige bai dubi inda uwartasu take ba ballantana ya amsa tayin kar6ar jakarsa da ta yi mishi. Ta bi bayansa da kallo sannan ta juyo ga yaranta cikin son bagarar da abinda ya afku  ta hanyar ƙaƙalo murmushin dole a saman fuskarta ta ce.

“Amira idan kun gama ku je ku kwanta, ban yarda ku kunna kallo ba.”

“Umma meyasa Abba ba ya sonmu?” Amir ya furta cike da damuwa, Amira wacce ta ji kwalla na shirin zubomata sai kawai ta sunkuyar da kai ta hau tattara litattafansu. Umma ta tamke fuska.

“Amir ban hanaku irin wannan maganar ba?”

Ganin ta ɓata rai ya tuna gargadin Yaya Adam garesu. Sai ya hau bata hakuri. Ta bishi da murmushi kafin ta karasa ta ja hannunsa su zauna. Ita dai Amira na binsu da kallo ba uffan sai hawaye.

“A duniya ka ta6a jin mutum ba ya son abinda ya haifa?”

Amir bai ce komai ba. Har abada ba zai iya ƙaryata Ummansa ba, ya gwammace ya yi shiru. Itama fahimtar da ta yi maganar basu shige shi ba ya sanya ta basarwa.

“Ku yi ta addu’a, komai nada lokaci hakazalika komai idan ya yi farko zai yi karshe, kar ku kara damuwa akan hakan. Kun ji yan albarka ƴaƴan Umma.”

Suka yi dariya domin samun nutsuwarta, itama ta saki fuska kafin ta fice sashin Abbansu.

Ta iskeshi zaune ya rage kayan jikinsa yana videocall da tauraruwar zuciyarsa Salma. Hausa yake yi sai dai shigowarta sai ya juya harshen zuwa turanci. Ba yau farau ba, tun hakan na damunta har ta bagarar ta bar sanyawa a ranta.

Ba ta bi ta kansa ba ta shige banɗaki ta haɗa mishi ruwan wanka yanda yake bukata sannan ta fito. Har ta wuce bai ko kalleta ba, yana wayar yana kyakyata dariya gami da girgiza ƙafa. A karshe ya koma harshen Hausa.

“Toh shikenan mu jima da yawa, na ƙagu da dawowarku.”

“Haba dai, sai ka ce Bilkisu ba ta gidan.”

Sai a sannan ya dubi inda Bilkisun take. Tana tsaye gaban sif tana ciro mishi kayan da zai sanya. Kauda kai ya yi ya maida duba ga Salma ta wayar.

“Kema kinsan dawan garin ai ba sai na ce komai ba.”

Tana jin sadda Salma ta kyalkyale da dariya kafin su yi sallama. Murmushi kawai ta yi, zuwa yanzu ba ta neman soyayya, ba ta sonta. Ba ita ce a gabanta ba, amanar da Allah Ya bata na yara uku ta isheta nauyi. Ga jarrabawar da Ya yi mata na bautarSa da yin biyayya ga mijin da bai ta6a kallonta a wata abar darajawa ba. Za ta ci gaba da juriya har zuwa sadda Ubangijinta zai yaye dukkan damuwarta.

Sai da ta kammala sannan ta fice, tuni ya shige banɗaki. Falon ta koma ta haɗa kayan abinci ta jera tsaf yanda yake da bukatar gani. Ba jimawa ya fito ya zauna, serving dinsa ta shiga yi. Tun tana zubawa ta lura da yanda yake yamutse fuska.

“Mene wannan?”

Ta dubeshi kafin ta maida duba ga abincin, tuwan semo ne sai miyar danyen kubewa da ta sha kifi da nama. A ɗaya filas din kuwa romon kaza ce, sai zo6o mai sanyi da ta dafa da ɓawon abarba, ya sha kayan haɗi har da su cucumber.

“Tuwo ne.”

Ya ture da hannu.

“Sanin kanki ne bana cin abu mai nauyi a wannan awannin.”

Ta gyada kai.

“Hakane, wai gani nayi ka jima ba ka ƙasar za ka yi marmarinsa.”

Ya kara murtuke fuska.

“To na koshi.”

Ta yi murmushi gami da gyaɗa. Shi dai har mamakinta yake wani sa’in, kamar wacce ba ta da zuciya? Akwai sadda har hannu ya kai saitin kirjinta don kawai ya ji akwai zuciyar a ciki. Akwai kuma sadda ya kai ta wurin likitan ƙwaƙwalwa nan ma don a auna lafiyarta. A sadda zasu bar wurin yana cewa A dalilin rashin zuciyarta da kuma rashin fushi ya sanya yake tantamar kamar tana da matsala.

Ta bishi da kallo sa’ilin da ya tattara tarkacensa ya shige ɗaki. Ta kasa rike hawayenta, zuciya ba ta da ƙashi balle a tankwarata. Tun tana yarinya ta ke jin maganar zuciya mai son mai kyautata mata, akan Hayat takan ji kamar kamar ba akan kowane DAN ADAM bane hakan ke afkuwa. Tasa zuciyar ƴar ƙauye ce, bata da wayewar da za ta san wannan hadisi ingantacce. Ba ta san wayewar da za ta bambance aya da tsakuwa ba.

Ajiyar zuciya ta saki, kirjinta wani zafi yake, tana iyakar kokarinta ganin ba ta sa damuwa a ranta ba sai dai hakan yakan shallake tunaninta. Ta daure ta mike, tana tattara kwanukan zafin kirjinta na ƙaruwa. Dakyar ta iya mikewa ta fice.

Kicin ta shige ta maida komai inda ya kamata sannan ta fito, dakyar ta isa ɗakinta.

Misalin karfe bakwai na safe Amira ta shiga dakin Umma ta sameta kwance tana juyi hannunta rike da kirjinta. Cikin kidima ta karasa saman gadon tana jijjigata.

“Umma! Umma!!”

Inaa! Ba ta san ma tana yi ba sai idanuwanta da suka soma kakkafewa. Ƙara ta saki wanda ya ja hankulan Amir da Yaha har ma da Adam da shigowarsa falon kenan da shirin zuwa asibiti.

Wannan ihun da Amira ta yi ya sanya suka bazama cikin dakin gaba dayansu.  Adam da wani irin zafin nama ya ƙarasa gareta. Jikinsa ya saki sakamakon yanda lokaci guda bakaken kwayoyin idanunta suka yi sama sai fararen kake iya gani.

“Wayyo Umma ta mutu!”

Amira ta furta ba’a hayyaci ba.

*****

Saɗaf-saɗaf take tafiya, burinta ta fice daga gidan ba tare da kowa ya ganta ba. Jin motsin fitowar Inno daga banɗaki ya sanya ta yi wuf ta ɓuya bayan bukkar Malam. Ganin ta shige ne ya sanya ta fitowa ta fice a guje.

Ba inda ta nufa sai hanyar makaranta, jikinta busu-busu kamar wacce aka tono daga rami. Tana tafe tana waige. Zani ne daure a ƙugunta sai ƴar t-shirt da ta sanya. Kan kuwa ba ko dankwali, dama ba sabon Humaira bane.

Yau ma kamar kullum Iro ya barta ta shige. Hankalinta kwance take tafiya kasancewar makarantar karkara ba’a fiye basu tsauri da kulawar da ƴan Birni ke samu ba. Wannan ta sanya ba wanda ya damu da tambayar inda ta nufa. Wasu cikin malaman basu zo ba, wasunsu kuwa su na ciki suna koyarwa. Ajin su Bilal ta kaɗa kamar koyaushe. Daidaita tsayuwarta ta yi jikin tagar tana kallon Malamin wanda ya dage yana rubutu saman allo. Ƙuri ta yiwa allon tana karantowa harafi ɗaya-ɗaya.

“W..r…i..t…t..”

“Kee!” Ta tsinci muryar Bilal cikin raɗa amman da karfi. Ta juyo tana dubansa, ya zaro ido yana mata alamun ta bar wurin. Ta harareshi kamar idanun zasu faɗo kafin ta turo baki ta maida hankali ga allon. Ya yi daidai da juyowar Malamin, idanunsa caraf a kanta sai dai ba ta lura ba don hankalinta ya tafi a kan karasa karatun da ta dauko.

Ta dayan kofar ta fice, sai lokacin ta lura da fitarsa, wannan ya bata damar sakin jiki da gyara tsayuwa, ba ta ta6a zaton wurinta ya nufo ba sai kawai ji ta yi an riƙe hannunta. A tsorace ta dubeshi. Ya tamke fuska.

“Me kike yi anan?”

Ta daburce, karshe ta daga yatsa ta nuna Bilal. Bilal ya zaro ido yana dubanta, ba ta Malamin yake ba, wannan mai sauki ne. Malam yake tsoro. Bai da masaniyar abinda zai biyo baya.

<< Rumfar Kara 3Rumfar Kara 5 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.