Zaman Kotu
Dakin sauraron shari’ar a yau ta fi koyaushe haɗa jama’a akan zama na farko da akai akan shari’ar Alhaji Haisam. Kowa da ke gurin burinsa ya ji hukuncin da kotu za ta yankewa wannan bayin Allahn. Jim kadan da zuwan Alkali, wuri ya dauki shiru. Aka gabatar da Gwaska da Halima. Ba tare da wani ɓata lokacin kotu ba suma suka amsa laifinsu. A karshe kotu ta yankewa Hayat hukuncin daurin rai da rai, hakanan Salma da Gwaska. Ita kuwa Halima kotu ta yankemata hukuncin zaman shekaru ashirin da biyar a gidan yari.
Hayat kukan ma ya ƙi fitowa sai na zuci. Salma kuwa zaman yan bori ta yi tana rusa uban kuka tana roƙon Innarta ta ceceta. Inna banda kuka ba abinda take, ta san lalacewar Salma har da sa hannunta, ita ta fara buɗewa diyarta ta idanu da nunamata cewar kuɗi su ne komai na jin dadin rayuwa.
Da ido yake bin Maryam da kallo har ta ɓacewa ganinsa. Kowa ya watse a kotun cike da jimami.
*****
Gidan take bi da kallo, tabbas nan Garbati ya kwatanta mata matsayin gidan iyayen Sidi Oscar. Gida danƙarere wanda aka bata kyakkyawan labari game da mahaifin Sidi wanda ya kasance babban malami da ake ji da shi kuma limamin masallacin juma’a na unguwar. Tasan za ta rikita mutan gidan ta kaɗamusu ƴaƴan hanji.
Fitowa ta yi cikin shigar abaya da mayafi, duk wanda ya ganta zai rantse mutuniyar kirki ce, koda dai rayuwa ta koyar da ita darasi yanzun. Akwai nadama da dana sani a ƙasan ranta.
“Baiwar Allah wa kike nema?” Maganar Maigadi ya katse tunaninta.
“Ina don ganin Malam ne. Don Allah ka yimin alfarma ka sanar da shi yana da baƙuwa.”
“Sai dai ko hakuri, Malam ba irin Malam din da ki ka sani bane, yana amsa tambayoyin mata amman ta hanyar gidajen rediyo idan ya je gabatar da shirin tambayoyi da amsarsu.”
Hanan ta jinjina kai, wato dai mahaifin Sidi, Malamin nema gasken gaske.
“Ka taimakeni ka isar da saƙona, wannan magana ce ta kawoni game da ɗansa Sidi.”
Sai da ta yi ta faman magiya kafin ya amince ya ce ta jira yana zuwa. Nan ta tsaya jira, jim kadan ya dawo. Budemata ƙofa ya yi gami da mata jagora zuwa ciki.
Kwarjinin dattijon ya mamayeta, ta ji wani shakka-shakkarsa. Malam Iliyasu Rano ya dubeta dakyau sadda ya ke amsa gaisuwarta.
“Ina sauraronki yarinya, meke tafe da ke akan Sidi?”
Ta ji idanunta sun kawo ruwa, ba ta ɓoyemishi ko ita wace ce ba da kuma alaƙarsu da Sidi, ta gangaro har kan cikin da ya ɗuramata. Ya kuma rantse ba zai karɓa ba.
Salati Malam Iliyasu ya shiga maimaitawa, akan kawomishi ƙarar ɗan nasa sai dai bai tsammaci ɓarnar ta kai girman hakan ba sai yanzu. Ya dau waya ya yi kiransa. Yana gidan, wannan ta sa bai yi wani jinkiri ba ya shigo. Ganin Hanan ya ji hantar cikinsa ta kaɗa. Daga irin duban da ya yi mata da kuma tsoron da ya bayyana saman fuskarsa, Malam Iliyasu ya samu amsar tambayoyinsa.
“Ka santa?”
Bai iya musawa ba, ya amsa cewar ya santa. Malam ya ji ciwon abinda ɗansa ya aikata.
“Kenan ka san abinda ke tafe da ita? Kasan cewar tana dauke da cikinka?”
Ya kasa magana sai bada hakuri, girgiza kai Malam ya yi ransa a matukar ɓace.
“Ya isa, bari na fadamaka. Hanan za ta haifi abinda ke cikinta koda kuwa ɗan zina ne. Za kuma ka aureta idan ta yi istibira’i. Wannan shi ne hukuncin da na yanke, batun auren Hanifah kuwa, ka ajiyeshi gefe, an fasa wannan auren.”
A gigice Sidi ya kalli mahaifinsa. Nan ya shiga roƙo, wata tsawa da ya dakamishi dole ya kama bakinsa. Ya yi musu wa’azi mai ratsa jiki, ya kuma jaddada musu kan su ji tsoron Allah. Karshe ya yi kiran mahaifiyar Sidi, Hajiya Saude, ya yi mata bayanin komai, har kukan bakin ciki ta yi. Malam ya umarci da a shigar da Hanan ciki a samarmata wurin zama inda ido ba zai kai kanta ba har sai ta haihu kuma ya rantse Sidi sai ya aureta. Wannan hukuncin ya yiwa Hajiya Saude daidai don a cewarta ko mene laifin ɗan nata ne. Sidi kamar ya yi hauka saboda ba karamin so yake yiwa Hanifah ba, akan me zai auri wacce ke bin maza ga kamalilla a gida? Wannan ne tunaninsa wanda ya mantar da shi, mazinaci ba ya aure sai da mazinaciya.
Bayan Wata Daya
“Dagaske Baba ya rasu?” Hayat ya kara tambaya yana kallon Malam Kabir da Kawu Lawwali cikin tashin hankali. Su kansu cike da jimami suka gyada kai.
“Ya rasu, sati uku kenan da rasuwarsa. Sai hakuri. Lokaci ya yi.” Fadin Malam a sanyaye. Banda kuka ba abinda Hayat yake, su kuwa kallon yanda duk ya sauya suke. Kai kace sa’an su ne duba da yanda ya rame ya ajiye ƙasumba fari ƙal.
“Nayi nadamar abinda nayi Malam, inama ina da damar gyarawa. Yanzu wa gari ya waya? Akan soyayya da kudi na biyewa mace mun aikata abinda ba shi ba. Kaicona ni Hayat.”
Ya ƙarashe yana kuka cikin sarƙewar murya. Duk ya basu tausayi.
“Haka Allah Ya ƙaddara. Ba don an yi hakan ba ai da mahaifinka bai haɗu da ƴar uwarka ba. Yanzu gashinan sanadin hakan, Allah Ya cikamasa burinsa kafin ya rasu, kawa dai sai dai ka yi ta tuba kana kaiwa Allah kukanka.”
Kawu Lawwali ya furta. Shi kuwa Hayat nan da nan ya shiga duhu.
“Kawu wa kenan? Wace yar uwata?”
Kawu Lawwali da Malam suka dubi juna, sun yi mamaki da har zuwa lokacin bai da labarin komai.
“Maryama mana. Mahaifiyarta Hajiya Rasheedat ai yayarka ce. Mahaifinku daya.”
A gajarce Malam ya labartamasa, ya dafe kirjinsa yana salati gami da girgiza kai.
“Yanzu dama duk abinnan, yar uwata na cutar? Yar uwata?” Ya ƙarashe cikin sarƙewar murya kafin ya zube sumamme. Ganin haka masu tsaro suka yo kansa aka yayyafa mishi ruwa aka samu ya farfaɗo. Suka sallami su Malam kan su wuce, haka suka bar shi rayukansu ba dadi. Shakka babu iyakar nadama Hayat ya yi sai dai ba yanda suka iya mishi. Haka Allah Ya ƙaddara mishi.
Yobe
Rasuwar Engineer, ita ta kawo Hajiya Rasheedat Yobe. Tun bayan sadaka kuma sai ta zauna cikin yan uwanta don a ƙara sanin juna.
Su Humaira sun koma makaranta. Hashim da kansa ya kaita ya kuma bada hakurin rashin zuwanta da dalilai. Wannan ta sa mai makarantar ta ce sai an kara yi mata jarrabawa don a ga ko tana fahimta. Bayan jarrabawa ta basu mamaki don ba karamin kokari ta yi ba, hakan yasa Malamar sauyamata aji zuwa aji na biyu a sakandire. Ta ci gaba da karatunta hankali kwance. Damuwarta bai wuce na sauyawar da Adam ya yi mata ba, ko ta gaidashi zai amsa kamar ba ya so. Tsakaninta da Amira kuwa, komai ya wuce sun koma kamar baya.
Yau ma tana dawowa makaranta, ta yi kiciɓus da shi zaune a kofar gida tare da Fu’ad wanda ya tankwashe ƙafafu yana shan fura ana hira.
Kallo daya ya yi mata ya kauda kai, ta ji ba dadi. Ta karasa gami da gaishesu.
“Lafiya Gorgeous, ya karatu? Zo ga fura.”
Ta dubi Fu’ad, tunda ya farfaɗo yake ambatonta da sunan da ya santa da shi a wurin Adam. Da murmushi ta girgiza kai.
“Na ƙoshi.”
“Kinsan Allah sai fa kin sha. Wannan ba irin furar da kika sani ba ce don wannan har da kwakwa. Zo ki dauka ki tafi da shi. Dama ya isheni.”
Ta amsa sannan ta karasa ta ɗauka, satar kallonsa ta yi, ya haɗe fuska yana danna waya. Idanunta suka cicciko ta mike ta bar wurin a sanyaye.
“Wai me yarinyar nan ta maka? Naga ba ka da kamarta a baya amman yanzun gaisuwarta dakyar kake amsawa.”
Ya ji maganar Fu’ad tamkar daga sama. Bai taɓa kawowa ana gane takunsu ba. Ya yamutse fuska.
“Kai ka ga hakan. Ni yanzu da ka bayar da furar na ce maka na ƙoshi da abina?”
Dariya Fu’ad ya yi kafin ya ɗan ja hanci kamar mai jan majina.
“Hum, Allah Ya ba ka hakuri. Yaushe za ka koma Kano? Don ni ba inda zan je, na ga wurin zama.”
Kallonsa ya yi kawai ya dauke kai.
“Kana namijin ka ce kaga wurin zama, sai dai ko noma za ka yi mana a nan? Kuma wa zai ci gaba da kula da kamfanin kanwartaka? Ko ka manta yanda ku ka yi da Mama?”
Fu’ad ya yi shiru, bai mance ba, sadda aka tattara komai na gado aka ƙara kasawa, Humaira ta samu har kamfani wanda a gaban jama’a Mama ta ce ta ba shi amanar ya ci gaba kula da kula da shi.
“Abin ya min nauyi ne Bros.”
Ya furta a sanyaye. Adam ya dubeshi.
Hakanan za ka riƙe, I trust you. Nasan za ka iya.”
Murmushi Fu’ad ya yi.
“Thank you Bros.”
Suka murmusa tare.
*****
“Ai fa, kya wani shigo kina kumbura baki, sai ki zo ki masgeni. Aikin ɓurr.”
Humaira ta girgiza kai, bata da lokacin fadan Gwaggo. Damuwarta Adam ne. Sauyin da ya yi gareta ya mata tsauri sosai. Wanka ta yi ta sauya kaya, furar ta yi zaman sha. Duk dadinta ba ya mata dadin sakamakon tunanin Adam. Wayar da Uncle Hashim ya siyamata ita da Amira ta jawo, wurin hotuna ta shiga. Kan hoton Adam ta je wanda ta tura daga wayar Amira ba tare da ta sani ba. Kallo ta tsaya yi tana murmushi. Gyaran muryar da ta ji ne ya sa ta azamar ajiye wayar. Ya sa hannu ya dauka ya bude.
Murmushi saman fuskarsa ya ɗagamata gira. Yaya Fu’ad ne.
“Uhum, kuna son juna kuna kaiwa kasuwa ko? Why?”
Duk sai ta bi ta diririce ta rasa abin yi. Ta mike da sauri za ta fice ya dakatar da ita ta hanyar sa hannu ya ture ƙofar. Ta dubeshi idanunta cike da kwallah.
“Ba haka bane wal..”
“Shii! Kar fa ki rantse Malama don za ki yi kaffara.”
Ta yi shiru ta haɗiyi miyau har dimple dinta ya fito.
“Yanzu kar ki damu, zan shiryaku. Zan sameshi na ba shi hakuri. Komai zai yi daidai kinji ko?”
Ta zaro ido.
“Zai ce na kawo ƙararsa. Don Allah ka yi hakuri ka kyaleshi.”
Harararta ya yi.
“Ba zan kyale ba. Ke na san Bros fa daidai gwargwado. Na fi ki kaunar wannan abun, na matsu ya yi aure wallahi ko nima za’a waiwayeni. Yanzu kowa maganar aurensa ta rufemishi ido, ko ta ni ba’a yi.”
Sai ya bata dariya.
“Kai Yaya Fu’ad, bayan ko budurwa ba ka da shi?”
Ya yi murmushi.
“Wa ya fadamaki? Inada wacce nake so. Yarinyar dai tana min yanga amman hakan ba zai sa na janye ba.”
“Don Allah wacece?”
Ta nemi sani cikin zaƙuwa. Ya ɗan dubi hanya sannan ya dubeta.
“Kar fa ki faɗawa kowa. Salima ce.”
Humaira ta ji kamar ta daka tsalle.
“Wayyo Yaya..” Ya yi azamar toshemata bakin da hannu ganin za ta tona asiri. Ya yi daidai da shigowar Adam, sai da ya ji gabansa ya fadi, Fu’ad ya yi saurin kauda hannunsa itama ta nutsu ta sunkuyar da kai. Bai ce komai ba ya sauke labulen ya yi gaba.
“Kin gani ko? Yanzu fa Bros kishi yake? Ki rikemin sirrina, Allah kuwa kika sake wani ya ji sai na tona asirinku da Bros a gaban su Mama. Idan ya so ko bakwa so sai an yi aurenku.”
Daga nan ya fita, ta bishi da kallo tana dariya. Kaso tamanin na damuwarta ya tafi a sanadin Fu’ad. Mutum da ba ruwansa ga barkwanci. Yakan bata tausayi don har lokacin bai karasa maida jikinsa ba, yana kuma kan magani.
*****
A bangaren Adam kuwa ji yake kamar ya yi me? Zuciyar ba dadi, ya kasa gasƙata wai kishin Fu’ad yake. Ya daure suka gaisa da Gwaggo sai dai duk surutan da take ba ya tsintar komai. Karshe ma sallama ya yi mata da zummar gobe sammako zai yi zuwa Kano. Bayan fitarsa kai tsaye gidan Engineer ga shiga. Nan ya yi sallama da su Mama da Hajiya Rasheedat daga haka ya wuce ya shiga motarsa.
“Bros.” Muryar Fu’ad ya tsinta, dubansa ya yi, ya riƙe murfin motar.
“Please Bros ka ne wannan abu ya wuce mana. Na fa san me Humaira ta aikata gareka. Ta yi nadama, yarinyar tana sonka da yawa. Ka yafemata mana.”
Kalmar so ta ɗan kashe jikinsa, sai kuma ya harareshi.
“Naji, sakarmin murfi zan wuce.”
Ganin ya dage tasa dole Fu’ad sakin murfin, sai dai ya zagaya ya shige mazaunin gefe.
“Ina za ka bini?”
“Wurin Umma.”
Girgiza kai Adam ya yi, ya gaji da rigimar Fu’ad, akan dole ya ja motar suka tafi. A hanya don ma kar ya mishi zancen, sai ya ware rediyo inda ake waƙa da harshen Fulani.
Sun iske Umma a falo tana kallo yayinda su Amira ke gefe suna duba litattafansu. Ta amsa sallamar yarannata da murmushi saman fuskarta.
Amira da Amir suka gaishesu kafin Amira ta shiga dauko ruwa. Umma ta dubi Adam ganin yanda yake daure fuska, ta maida dubanta ga Fu’ad fuskarta dauke da alamar tambaya. Fu’ad ya taɓe baki ya ɗan saci kallonsa.
“Uncle yana gida?”
Umma ta amsa da eh, ya mike ya ƙyalesu. Fu’ad ya dawo gefen Umma ya zauna.
“Kinsan me? Shi da budurwarsa ce suka samu saɓani shikenan ya hana kansa walwala. Kuma laifinsa ne.”
Jin haka Umma ta kara karkatowa tana duban Fu’ad ranta fari sol. Amira ma washe haƙora ta yi.
“Yaya don Allah wacece?”
Harararta ya yi.
“Ji gulma, kamar ba ki sani ba?”
Umma ta dubi Amira sannan ta dubeshi.
“Fadamin wacece? Dama yana da budurwa?”
Shafar suma ya yi.
“Wallahi Umma za ki so yarinyar ma. Humaira ce fa. Sonta yake kamar son Majnun ga Laila.”
Umma ta rasa bakin magana, ta shiga jero hamdala ga Ubangijinta. Haɗa zuri’a da mace irin Maryam abin alfahari ne ballantana kuma Humaira wacce take kauna.
“Sai dai Umma kar ki mishi maganar, da da hali ma ki faɗa wa Uncle kawai a sanya rana.”
Umma ta yi murmushi.
“Dama ai ya sani, Yaya kwanaki ya ba shi akan ya fiddo matar aure ko su zaɓamasa, na tabbatar yau ma zai nanata mishi zancen. Kar ka damu, muddin bai magana ba ni da kaina zan yiwa Yaya maganar.”
Dadi kamar ya kashe Amira, Fu’ad dinma hango nesa yake ta matso kusa gareshi ballantana itama Amira wacce ba ta da burin da ya wuce na aure Shuraim wanda zuwa lokacin sun dinke su na soyayya kamar wadanda suka shekara tare.
*****
Rai a ɓace ta fito daga dakin, ya biyo bayanta har zuwa ɗakinta. Zama ta yi gefen gado ta fashe da kuka. Hashim ya ƙaraso ya zauna gefen gadon gami da kai hannu ya dafe cinyarta, ta ture hannun.
“Hashim ka ƙyaleni! Ka rabu da ni! Ni dai Khalisat na hakura da kai, ka je ka auri Maryam ku rayu har karshen abada. Dama tun shigowar Maryam zuri’arku na gane take-takenka da irin kallon da kake mata tun farkon ganinta. Yau har ka iya buɗe baki ka cemin wai aurenta kake son yi? Kuna yan uwa ni kuma ina bare a cikinku? Salon na wulakanta? Toh ba zan iyaba.”
Hashim duk iyakar bayanin da ya yi ta ƙi fahimta. Dole ranar suka kwana kowannensu a dakinsa. Washegari da wuri ta shirya ta dauki yaranta mata suka bar gidan da zummar za ta koma can wurin yan uwanta ta rabu da shi. Dakyar Umma ta rarrasheta, suka sanyata gaba da Hashim suka taushi zuciyarta gami da nunamata ta wuce matsayin yaji a yanzu.
*****
“Toh Alhaji Dikko dai da na sani mahaifin abokin Fu’ad? Ai bana mance shi ba. Ka ce ya shigo.” Baharu ya mike cike da ladabi ya fita don sanarwa Alhaji Dikko tare da Alhaji AbdulKarim saƙon Malam.
Malam ya gyara shimfida suka shigo, bayan gaisuwa a mutunce. Alhaji Dikko ya gyara zama
“Sai kuma ka ganmu har Yobe.”
Yar dariya Malam ya yi.
“Gaskiya kam.”
“Ai Haidar ne ya bamu kwatance. Ya kuma ƙarin hakurin rasuwar da akai?”
Jin an mishi famin rashin dan uwa, fuskarsa ta ɗan nuna damuwa.
“Mun gode Allah.”
Suka yi addu’ar Rahma ga Engineer. Can Baharu ya dawo dauke da ruwa da lemuka ya ajiye ya fita. Bayan sun jiƙa maƙoshi. Alhaji Dikko ya gabatar da Alhaji AbdulKarim matsayin amininsa kuma mai neman auren Bilkisu. Malam Kabiru ya ji abin kamar daga sama, yana yiwa Bilkisu fatan alheri da fatan samun miji nagari, bai kawo ko da wasa wani ne daga jahar Kano ba kuma babban mutum irin wannan.
Malam ya ce musu su yi hakuri su nemi yardarta. Ya musu iznin hakan. Shi ya sanya Baharu yi musu rakiya har gidan Hashim.
Aka yi sa’a yana gida don yana nan suna case akan aurensa da Maryam don Khalisat sam ta ƙi yarda. Jin saƙon Malam a bakin Baharu cewar baƙi ne daga Kano, mahaifin Haisam da amininsa, ya sanya ya umarci Shuraim ya bude dakin saukar baƙi. Bayan sun zauna an gaisa, ya ji abinda ke tafe da su, har kwalla ce ta cikawa Hashim ido tsabar murnar abin alherin da ya doso Bilkisu. Ba shi da burin da ya wuce ya ga ta samu mijin aure mai sonta. Jin yanda suka yi da Malam ya goyi baya ɗari bisa ɗari. Ya kuma ce shiga gidan ya ce ta je tana da baƙo.
Umma ta dubeshi cikin rashin fahimta gabanta na faɗuwa.
“Kar fa ki damu, su Alhaji Dikko ne daga Kano.”
Jin haka ta ɗan saki ajiyar zuciya da murmushi. Har ranta ba ta kawo komai ba ta zura hijabi ta fita.
Alhaji AbdulKarim ya kasa sukuni ganin abar kaunarsa. Bayan sun gaisa, Alhaji Dikko ya yi bayanin abinda ya kawosu, Umma ta ji abin kamar daga sama. Ta tuno ire-iren rayuwar da ta gudanar da Hayat, hawaye suka zubomata. Alhaji Dikko ya basu wuri ya fita waje.
“Bilkisu.”
Ba ta amsa ba sai dai ta ɗan kalleshi ta kauda kai.
“Bilkisu ni da ke ba yara bane, idan ba magana ta aure ba, babu abinda zai kawoni wurinki a shekaruna. Ki sani, tun ganin da nayi maki a asibiti na rasa nutsuwar zuciya da ƙwaƙwalwa. Tunaninki ya kasa barina. Ina ji a jikina kina daga cikin mata salihai wadanda Annabin Allah s.a.w ya yi mana nasiha da mu aura. Ki yi nazari Bilkisu, duk abinda kika yanke a kaina, zan karɓa. Ki yimin adalci, wallahi ina kaunarki domin Allah. Fatan za ki karɓi tayina mu raya sunnar Ma’aiki s.a.w. Ba zan miki alƙawarin zan jiyar da ke dadin da za ki mance dukkan bakin cikinka ba, domin nima AbdulKarim, ɗan adam ne, tara nake ban cika goma ba. Sai dai in sha Allah bakin gwargwado zan kare martabarki zan kuma ƙimantaki na nunamaki kauna matsayinki na matata abar kaunata. In sha Allah zan zauna da ke na rayu dake a kowane yanayi. Ki yi tunani, duk abinda kika yanke ki nemeni ta waya ki sanarmin. Na gode sosai.”
Ya mike gami da ajiye mata katinsa mai dauke da lambar wayarsa jiki ya kara yi mata sallama haɗi da faɗin ta gaidamasa ƴan biyunsa sannan ya fita. Ta bi bayansa da kallo tana nazari, Hashim na musu rakiya ya dawo gareta.
“Mene ra’ayinki?”
Umma ta dubeshi.
“Yaya mene shawararka game da lamarin?”
Murmushi ya dan yi, hakan ya nunamishi mutumin ya dan kwanta a zuciyar kanwartasa.
“Kar ki gaggawar yanke hukunci, ki adduar neman za6in Allah. Shi kaďai zai miki za6i. Na yarda da lamarinsa. Da gani mutum ne wanda ya san abinda yake yi. Ina fatan Allah Ya za6amaki abinda ya fi alheri.”
Daga haka ya shiga falonsa ya barta cikin tunani. Ta share hawayenta ta mike gwuiwa ba kwari ta shiga ciki.
*****
Hashim kuwa ganin abinsa da Khalisat ya ki wucewa, ya yi kiran Malam gidan ya mishi bayani.
“Allah Mai iko.” Shi ne abinda Malam ya furta. Ya hadasu ya yi musu nasiha, karshe ya roki Khalisat ta kwantar da hankalinta, idan har Allah Ya riga ya kaddara auren zai tabbatu, to fa ba za ta iya hanawa ba.
An dau kusan sati biyu ana abu daya, a karshe ta aminta ta hakura bisa shawarar Yayarta mahaifiyar Salima.
“Khalisat, gwara wacce kika sani aka kuma san halinta. Wallahi Maryam kaf zuri’ar Alhaji idan suka budi baki, yabonta kawai suke yi. Kiyi hakuri da dukkan abinda Allah Ya kaddara. Yanzu bari kiji, tunda har Hashim ya so aurennan, ko ba ita ba, to ki tabbatar zai yi aure. A zamaninnan kuwa, yanmatan yanzu ba kunya garesu ba. Sai su yi abinda zai ba ki kunya ke da yara su kuwa ko a jikinsu. Maryam nada hankali, inada yakinin ba za ki sameta da irin matsalolin kishiyoyin da ake gudu ba. Kiyi hakuri ki rungumi kaddararki. In sha Allah alheri ce gareki. Kedai kawai ki san kanki. Ki kara zage damtse wurin biyayya ga mijinki. Kin ma ji dadi da ya tsaya lallabaki, da wani namijin ne sai dai ki yi abinda za ki yi. To wannan fa yana sonki ne.”
Da wannan shawarar Khalisat ta sauko ta amince da aurensa da Maryam.
*****
Sakin baki Humaira ta yi tana duban mahaifiyarta. Harara Maryam ta watsamata. Yaha ta buge bakin hakan ya wartsakar da ita.
“Wai Uncle Hashim?”
“Zan ci kaniyarki fa Humaira, ni sa’arki ce?” Maryam ta fadi tana zaro ido karshe ta wayance da mikewa ta bar wurin. Suka yi dariya, Amira ta mikawa Humaira hannu suka cafke gami da sakin guďa. Duka Yaha ta kara kai musu suka mike da gudu-gudu suka yi daki.
“Ke wallahi iyayenmu duk aure zasu yi fa. Umma ma har zance ta yi sau biyu.”
Dadi kamar ya kashe Humaira.
“Wallahi dadi nake ji, Allah Yasa a kularmana da su, a rikemana su amana.”
Amira ta amsa da amin.
“Ana yin nasu, zaa waiwayemu ni da Sweet Shuraim dina.”
Yamutse fuska Humaira tayi.
“Yanzu ko kunya kike maganar aure? Duka-duka shekararki nawa? Ai da kunya. Nidai sai na kai shekara ashirin cif ma zan yi in sha Allahu.”
“Wa? Yaya Adam din ne zai bari ki yi ashirin? Ashe dai a tsoho za ki aureshi.”
Zaro ido Humaira ta yi.
“Kai Amira, wa ya fadamaki soyayya nake da Yaya Adam?”
Harararta ta yi da wasa.
“Dalla yimin shiru, wai ki ta boyemin magana alhalin kallonku kawai ake, an gane kuna soyayya.”
Ta zaro ido gami da dafe kirji.
“Dagaske don Allah? Wallahi bai taba cewa yana sona ba. Bamu taba maganar soyayya ba. Ba yamin magana ma yanzu.”
“Meyasa?” Ta labartamata. Amira ta ja guntun tsaki.
“Ai ke kika ja Humaira, nima don dai ban iya fushin bane. Sai dai Yaya Adam ba shi da fushi, bansan me ya zafafa abin har haka ba. Kinsan me? Ki dinga aikamasa sakon friday greetings mana. Yana balain sonsu. Ya taba fada a gabana.”
Humaira ta yi shiru tana dubanta, Amira ta ci gaba da zugata tana hawa har ta amince da hakan.
Bayan Sati Uku
An daura auren Bilkisu Kabir Abdullah ta zama matar Alhaji AbdulKarim, hakanan Maryam Adamu da Hashim Kabir Abdullah.
Babu wani taro da akai sai wunin jamaar gidan kawai. Sai kuwa Hajiya Hafsatu mahaifiyar Nuriyyah da ta zo adalilin zuwan Inno garin. Tare ta zo da Umar danta mazaunin garin Madina a kasar Saudiya. Idan ka ganshi sai ka kara kallo tsabar sauyawar da ya yi. Tunda ya kyalla idanu kan Humaira ya ji yana sonta, ta lura da kallon da yake mata tun da ta shigo falon don gaishesu.
“Wallahi Inno mamakin girman yarannan nake, ita da Jamila kamar wadanda ake jansu.”
Aka yi dariya, Hajiya Hafsatu ta amsa.
“Banda abinka Umar, kaima ai ka sauya. Haka ka tafi ka bar Innontaka? Ka dawo ka zama wani jibgege, ba don ma naga shaidar kammala karatunka ba ai sai nace hutu kawai ka je.”
Ya yi dariya gami da yin larabci wanda ke mishi kyau sosai.
“Kai Hajja.”
Humaira dai ta mike ta bar su, tama shiga daki ta ja tsaki. Amira da Jamila suka dubeta.
“Tsaka, yau me akai maki?”
Hararar Jamila ta yi.”Ke wai shi Baba Umar kallo ya koyo a Saudiyar? Ya dameni da kallo wallahi.”
Suka yi dariya.
“Wayasani ko sonki yake.”
Fadin Jamila, Amira da Humaira suka dubi juna.
“Ai kuwa yana da aiki, don wannan dai mun mata miji.” Fadin Amira, daga yanayin furucin kasan taya dan uwanta kishi take. Murmushi kawai Humaira ta yi, mutumin da ko sako ta mishi ba ya mayarwa shi ne za ta tsaya batawa kanta lokaci da shi? Ta girgiza kai kawai, dakyar ta janye wannan hirar aka shiga hirar bikin Jamila da ya matso sosai.
*****
Karfe bakwai na dare, suna zaune a tsakar gida gaba daya ana hira, hasken lantarki ya haske ko’ina. Humaira na gefen Nuriyyah wacce duk ciki ya sauyawa halitta, ta kara kiba da kumatu. Shuraim ya shigo, ya gaishesu yana cillawa Amira kallon soyayya, ta yi murmushi ta lumshe idanu.
“Af kar ma manta, Humaira je ki waje kina da bako.” Ta ji faduwar gaba. Tasan an ce Yaya Adam ya zo, sai dai sam ba ta sanyashi a idanu ba.
“Surukinnamu ne kenan? Kai na gode Allah. Tashi maza ki je kinji Indo.” Gwaggo ke maganar da zumudi. Ta turo baki, ganin sun matsa ta mike ta fita bayan ta yafa gyale.
“Amm..Amira, zo ki ji mana.” Cewar Shuraim yana shafar keya. Amira ta yi wuri-wuri da ido. Jamila ta kashemata ido, ta kasa tashi.
“Tashi kije kafin ya fasa auren.” Maganar Gwaggo ta basu kunya, Amira ta mike a guje ta fita zaure. Shuraim ya bi baya a kunyace, aka kuwa kwashe da dariya.
Tana kaiwa zaure ta tsaya gami da harararsa a wasance.
“Kana sanyani kunya wallahi.”
Ya yi dariya gami da dagamata gira.
“Nima kunyar naji. Kinsan kinmin laifi, nayi ta kira ba ki daga ba. Bani da nutsuwa fa idan ban ji ko na ganki ba.”
Murmushi ta yi saboda jin dadin kalamansa, nan suka shiga tsinken fure abinsu.
*****
Ita kuwa Humaira waje ta tsaya tana rarraba idanu. So take ta ga mai kirannata.
“Assalamu Alaikum.” Ta dan runtse ido ta bude don tasan Baba Umar ne, ta dubeshi da dan murmushin yake ta amsa.
“Ni ke kiranki. Zo muje daga can mana.”
Ya yi mata nuni da karkashin bishiyar darbejiyar gaban gidan. Ta dan dubi wurin majalisar su Baharu, hira suke abinsu. Ta karasa gabanta na dukan tara-tara. Tasan maganar gizo bai wuce na koki. Tasan abinda take gudun ji ne za ta ji. Ya soma da yan zantuka kafin ya furtamata yana sonta.
*****
Tuki yake cikin nutsuwa, Fuad a gefensa yana bin wakar da ke tashi a motar, shi kuwa da zarar ya tuno text din Humaira a kwanakinnan, ransa fari yake. Komai ya riga da ya wuce a ransa, burinsa tozali da ita kawai. Yana faka motar idanunsa ya mishi wani mugun gani. Fu’ad ya kara kura idanu gami da murzasu yana duban inda Humajra ke tsaye da wani mutum kamar buzu.
“Humaira ce can wai? Wancan balarabe ne ko buzu?”
Ya furta da son Adam ya tayashi tantancewa, bai ji budewar kofar Adam ba sai ganinsa ya yi ya nufi inda suke tsaye. Ya yi saurin duban mazaunin Adam din, sai kuma ya biyo bayansa.
Humaira wacce ta rasa amsar da za ta ba Umar da ya nace ta amsa mishi. Tun tsayuwar motar da irin yanda ta haske fuskokinsu, ta ji kamar ta saki fitsari.
“Wannan fa?” Baba Umar ya furta yana karewa Adam kallo sadda ya matso wurinsu. Kamar mai rada ta ce.
“Yayan Amira ne.”
Kasancewar yasan Amirar, ya gane. Hakan tasa ya mikawa Adam hannu sadda ya iso. Adam ya yi fuska ya kauda kai gami da maida idanunsa ga Humaira. Ba tare da ya amsa gaisuwarta ba ya ce.
“Ke me kike anan? Da iznin wa kika fito?”
Za ta yi magana ya dakamata tsawa wanda ya gigita ta. A guje ta shiga ciki ya bi bayanta. Fu’ad ya karaso yana karewa Umar kallo. Bayan sun gaisa ya ce.
“Sai fa hakuri, shi ne wanda za ta aura. An sanyamata rana.”
Umar ya ji abin banbarakwai. Ya yi murmushin yake.
“Inno bata fadamin haka ba, ban kuma ji ba, da ba zan nemi soyayyarta ba. Ku yi hakuri.”
Fu’ad ya jinjina kai, sai dai ya sha jinin jikinsa, ya akai ya san Inno? Ko danta ne? Ya karasa ya gyara parking na motar ya fito ya karasa ga Baharu. Anan yake jin ko wanene, sai ya ji kunyar karyar da ya mishi. Amman dai kusan hakan ne.
Amira masu zance ganin Humaira a guje suka tsaya tunanin lafiya, shigowar Adam zauren ne yasa Amira arcewa cikin gidan itama. A tsakar gidan Adam ya yi ta masifar don me zaa bar Humaira fita zance? Shi ba ya son ta kula kowa yanzun.
“To wai Adamu ko kai za ka aureta ne?” Fadin Gwaggo da ta cika ta yi fam.
“Gaskiya da alama yar gida ce zaa yi.” Fadin Inno tana dariya. Sai a sannan Adam ya lura da jama’ar gurin, har da Nuriyyah surukarsa. Kunya ta sa ya fice da sauri-sauri bayan ya gaisar da su Inno. Dariya sosai ake mishi. Shigowar Fuad yake basu labarin abinda ya faru.
“Umar ne ai dan wurin Fatima.”
Cewar Hajiya Hafsatu. Inno dai ta yi shiru, za ta so hada zuri’a da Maryam sai dai ya zama dole ta dakatar da Umar kada ya kawo rudani. Ya hakura tunda shi ya zo daga baya.
Humaira dai na daki tana leke ta window, tsoron Adam ta ji, dafa kafadarta da Amira ta yi ya tsoratata. Suka dubi juna sai kuma suka tuntsire da dariya. Kowacce na yiwa yar uwarta dariyar mugunta.
*****
A ranar Hashim da kansa ya zo ya tafi da matarsa bayan Malam ya musu nasiha. Washegari kuwa aka kai Bilkisu Kano gidan Alhaji AbdulKarim. Nan suka ga duniya, abin har rudasu ya yi don basu zaci kudin Alhaji AbdulKarim ya kai hakan ba. Kowa ya yi mata fatan alheri da fatan ya kasance mijinta har mutuwa.
Da wannan dattawan suka juyo zuwa Yobe.
Bayan Watanni Shida
Mika ta yi gami da saukowa saman gadon, wayarta wacce tun a cikin bacci take jin kararta ta jawo. Da murmushi ta yi kokarin dagawa saidai kafin ta kai ga hakan ya katse. Yaya Adam ne, dan biyutiful. Hankalknta ya kai ga sakon text da ya turo. Kalamai ne masu dadi game da birthday dinta. Shaf ta manta a yau take cika shekara goma sha shida a duniya. Murmushin ta kara wanda ya bayyana dimple dinta.
“Wai nikam Humaira ba za ki fito ba sai na zo? Shikenan mutum idan ba shi da sallah sai ya kwanta ya yi ta bacci?”
Ta ji muryar Mama sadda take nufo hanyar dakin. Da sauri ta mike ta ajiye wayar ta shiga wanka, bayan ta fito ta shirya cikin riga doguwa yar kanti kalar coffee wanda ya dace da kalar fatarta ya yi mata kyau. Ta fito falon mahaifiyarta tana kallonta. Mama ta harareta ta yi murmushi ta karasa ta gaidata. Fada ta yi mata kan yawan bacci marar amfani.
“Adam ma ya kira nemanki a wayata nace bacci kike. Sai ki kira ki ji.”
Kunya ta dan kamata. Maryam tuni ta fahimci alakarsu don har Hashim ma ya sani. Murmushi kawai Maryam ta yi gami da mata umarnin zuwa cin abinci. Ta mike da sauri ta bar wurin ta yi hanyar kicin. Tana shiga ta danna wayarta dake faman kara tun tana gaban Mama.
“Haba Gorgeous, me nayi ne?”
Yanda ya yi zancen a shagwabe kamar yaro ya bata dariya.
“Kamar dariya kike ko?”
Ta toshe baki gami da girgiza kai kamar yana ganinta.
“Um um.”
“Ai shikenan. Na gaji fa wallahi. Zan zo kawai na fadawa Uncle a dauramana aure. Ba zan iyaba Gorgeous, shekarata nawa ba aure? Yanzu kuma auren nake so.”
Murmushi take tana wasa da jelar igiyar gaban rigarta.
“Na baka dama dan beautiful.”
“Are you serious?”
Ta yi yar dariya.
“Yes.”
Ya yi hamdala, nan kuma aka bude fagen kalaman soyayya masu dadi.
Sati biyu bayan haka, ba zato ba tsammani, tana sashin Anti Khalisat tana yiwa Jidda tsifar kai suna kallon wani film din India mai suna Lakshmi, hawaye sosai Humaira ke yi tana sharewa don yarinyar ba karamin tausayi ta bata ba. Sallamarsa ma ba ta ji ba, sai gani ta yi Jidda ta mike a guje ta yi wurinsa. Ta yi saurin kallonsa, dariya yake da mamakin hawayenta. Ya kara kallon tv, ya dubeta.
“Kar ki cemin film ne ya sanyaki kuka Gorgeous?”
Ta turo baki gami da share fuskarta. Ya yi daidai da fitowar Anti Khalisat daga daki.
“Aa, Dr saukar yaushe?” Ya karaso ya zauna gefen Humaira ya gaidata yana dariya.
“Ban jima ba Anti. Wannan yarinyar kuka fa take yiwa film.”
Dariya Anti Khalisat ta yi.
“Kadan ma kenan indai aikin Humaira ne. Kuma abin haushin ta kalli film dinnan ya fi a kirga, duk kallon da za ta yi sai ta zubar da hawaye kamar ibada.”
Suka yi dariya. Humaira ta cika ta yi suntum. Ta mike za ta bar wurin ya kuwa rike gefen rigarta.
“Dawo ki zauna. Anti aure fa zan yi.”
“Dagaske Adam?”
Ya na kallon Humaira na zara ido gami da kokarin guduwa. Ya kuwa kara damke rigar dole ta dawo baya ta zauna.
“In Sha Allah, ga matar tawa nan.”
Ya nuna Humaira da ido. Farin ciki fal a zuciyar Anti Khalisat. Ta yi musu fatan alheri. Bayan shigarta daki, ya dubi Humaira duban soyayya.
“Fushi? Ban burgeki ba da na tona asirinmu? Aure fa za su yi mana.”
Ta yi mishi hararar wasa, ya daga gira da murmushi.
“Kallon manufa.”
Ta dubeshi sai ta yi murmushi, ita kadai tasan me yake nufi.
Tare suka fice sashin Mama. Kasancewar ita ce da aiki, tana wurin Uncle. Ya dubi Humaira.
“Zo ki rakani, kinsan fa na zo fadamusu alakarmu ne.”
Ta noke kafada tana murmushi.Ya lumshe ido da murmuahi kafin ya bude ya nufi bangaren Uncle Hashim.
Mama da Uncle Hashim ba su ji wani mamaki sosai ba. Suka sanyawa abin albarka har Uncle Hashim na fadin ba zaa dau dogon lokaci ba. Wannan ya fi komai yiwa Adam dadi.
Kamar wasa magana ta je gurin su Malam, ba bata lokaci aka ajiye maganar nan da wata daya. Fuad ma ya zo da tasa matar da yake son aura, Salima. Sai kuwa Shuraim da Amira da ta je Kano gurin Mahaifiyarta. Abin ya yiwa iyayen dadi. Aka yanke hada maganar aurensu lokaci guda bayan an samu dangin mahaifin Humaira da zancen. Su kansu abin ya musu dadi.
Nan kuma aka hau shirin biki sosai, Hashim da kansa ya yiwa Adam lefen aure aka kai Kano hannun Hajiya Karime. Wannan girmamasun da akai ba karamin dadi ya musu ba. Takanas Humaira ta koma gidan Nura wurin matarsa Kausar. Ita ce ta tsaya tsayin daka wurin gyaramata jiki da shiryata yanda ya kamata. Amira ma nan ta zo tare da Salima. Ta hadasu gaba daya ba nuna bambancin komai ta shiga gyara don dama sana’arta ce.
Kafin sati hudu sai ga Amare fatarsu ta sauya sun yi wani kyau na ban mamaki. Tsakaninsu da mazajensu sai ta waya, nan ma har korafi suke akan don me zaa hanasu zuwa garesu.
A kwana a tashi ba wuya wurin Allah, biki ya gangaro. Jamila bata samu damar zuwa ba don a sannan itama Amarya ce a gidanta. Su Faiza su ne yan uwa kuma kawayen Amare.
Kamu da yini gaba daya aka hada a kawataccen event centre mallakin Rufaida Umar.
Amare sun ci adon kayan fulani kalar blue black. Idan ka gansu sai ka kara kalla tsabar kyau. Kawayensu kuwa suka yi shigar fararen kayan fulani. Iyakar kyau sun yi abinsu tsaf.
An yi taro lafiya aka watse, washegari da safe aka daura aure. A gidan Umma Bilkisu aka yi taron. Idan kaga Umma sai ka rantse wata matar gwamnar ce tsabar mulmulewa da ta yi ta yi kyau. Ta ci uban shadda fara kal, ta yi adon zinare. Yan uwanta banda hamdala da sambarka ba abinda suke. Hatta Yaha wacce ta dawo wurinta da zama itama ta yi kyau tsaf. Kowa ya ganta yasan tana cikin kwanciyar hankali.
Da dare aka shirya tafiya dinnerparty.
Farida beauty aka dauko har gidan Umma Bilkisu, nan Amaren suka kwana, ta fente musu fuskokinsu da kwalliya. Suka yi shigar lemon green da silver. Sun yi kyau ba kadan ba. Yan matan duk sun yi gaba ya rage sai Amaren. Suka fito falo don tafiya bayan zuwan Angwaye. Umma wacce ta ci adon leshi dan ubansu, ta yi wata kiba da murjewa kamar ba ita ba. Kai kace tunda take bata san wata aba wai wahalar rayuwar aure ba. Murmushi kawai ta ke ganin kyan da suka yi. Mahaifiyar Salima ma murmushin take yi. Nan wata zabiya ta shiga guďa. Suka karaso suka yiwa iyayen sallama don tafiya. Inno ta kara fesamusu turare sannan suka wuce.
Motoci uku, Dr Ibrahim ya budewa Humaira murfi ta shiga, Amira ta shiga ta Fuad wanda Haidar ke tuki. Sai Salima a cikin ta Shuraim.
Hada idon da suka yi sai suka kasa janye kwayoyin idanunsu.
“Amarsu ina gaisuwa.”
Muryar Dr Ibrahim ta katsesu. Ta yi hanzarin kauda nata idanun ta gaida Dr Ibrahim. Hannunsa ta ji a kugunta ya rike gami da murzawa kadan. Ta dubeshi a tsorace, kallo mai kashe jiki yake mata. Kayansa farare kal, kyau kam ya mata shi ba kadan ba. Duk kokarinta ya ki sakinta, karshe ta hakura, haka ya yi ta shafa karshe ya saketa. Ya rike tafin hannunta na dama yana murzawa. Shi kadai yasan me yake isarwa, itama tana jin sakonnin na zagaye dukkan sassan jikinta.
Anyi dinner lafiya an watse. Koda suka koma gida, sai da Dr Ibrahim ya fita a motar ya basu wuri. Kamar jira yake kuwa ya matso gami da jawo habarta ta kalleshi.
“Sorry, yau an gajiyarmin da ke da yawa.”
Ta runtse ido jin yanda kirjinta ke bugu da sauri-sauri. Ya sa hannu a aljihu ya fiddo cingam ya dubeta
“Kin tuna wannan?”
Ta bude idanun ta sauke kan abinda yake nunamata. Bata san sadda ta yi murmushi ba. Cingam na tunamishi farkon ganinsa da ita da yanda ta ba shi. Ya fadamata ya fi sau nawa. Gyada kai ta yi sadda ya sakarmata ha6a. Murmushi ya yi ya 6are daga ledar, a bakinsa ya sanya a tauna kafin ya rungumota gaba dayanta ya sanyamata a baki ya tsotsi bakin son ransa. Wani irin shock take ji, abin ya fi karfin tunaninsu gaba daya. Ratsa dukkan sassan jikinsu yake suna kara jin son kasancewa a wannan yanayin har abada. Jikinsu har rawa yake kasancewar dukkansu farin shiga ne. Kwankwasa gilashin motar da Dr Ibrahim ya yi shi ya katse dukkan hanzarin Adam dake kokarin wuce gona da iri.
“Man, dare fa nayi.” Gilasan motar masu duhu ne baa hangen na ciki, daga waje Dr ke maganar.
“Ok.” Ya furta a ciki-ciki don ba shi da tabbacin ko Dr ya ji. Ya gyaramata zaman mayafinta yana murmushi.
“I love you.”
Ta kasheshi da kallonta mai hargitsa dukkan tunaninsa. Ya lumshe idanu yana matse hannunta cikin nasa.
Da dabara ta zare gami da bude murfin motar.
“Sai da safe.”
“Zan kira.” Ya ce ba tare da ya amsa sallamarta ba. Ta gyada kai ta fita da sauri-sauri.
Ya haura ya koma gefen Dr Ibrahim ya zauna gami da sakarmishi hon, Dr Ibrahim ya bude gaban motar ya shiga gami da harararsa. Suka yi dariya.
“Daga kai har kaninnaka bansan irinku ba fa. Yanzu Haidar ya kirani wai shi wallahi ka kira ka tsawatarwa Fuad don ya dage gidansu zai kaisu da matarsa.” Jin haka Adam ya mike zaune sosai.
“Are you serious?”
Bai jira ma amsarsa ba ya dauki wayarsa ya kunna. Kiran Fuad ya yi ya tsawatar mishi. Hakuri ya ba shi gami da tabbatarmasa ma sun taho gidan. Daga nan ya kashe wayar. Abin kuma sai ya basu dariya, suka dara da shiriritar Fu’ad. Koda dai shi kansa Adam ji yake inama zai iya tafiya gidansa direct da Gorgeous dinsa.
Washegari da safe aka mika Humaira gidan iyayen Haisam, nasiha mai ratsa jiki su ka yi mata. Daga nan aka dauketa zuwa wurin Prof da Hajiya Rasheedat. Nan ma nasihar ce wacce ta sanyata kuka ganin har misali ake mata da irin hakurin mahaifiyarta.
A bangaren Amira ma, Umma ta sanyata a daki ta nunamata cewar aure dan hakuri ne.
“Da ace ban yi hakuri da rayuwar da na fuskanta a baya ba, ba zan kai wannan matsayin ba. Ki sani bautar Ubangiji za ki je ki yi. Kar ki zama mai wasa da sakaci da dukkan abinda aka ce ibada ne. Kiyi hakuri da dukkanin kalar rayuwar da za ki fuskanta a gidan aurenki. Bar ganin Shuraim matsayin dan uwa wanda a rayuwar gida ki kan raina ko ki batamishi rai, yanzu ya wuce haka Amira. Ina miki fatan dukkan alkhairi a zaman aurenki da ke da yan uwanki. Allah Ya yi miki albarka.” Kuka sosai Amira ke yi daga nan ta wuce sashin Alhaji AbdulKarim. Mutum wanda ba ya bambanta su da dansa. Kamar yanda Umma ta rike amanar dansa da zuciya daya, ya zama kamar ita ta haifeshi. Ya kuma zama aminin Amir. Basu rabo da juna.
Adam da Fuad, tare Umma ta yi musu nasiha bayan an tafi kai Amare. Ta nunamusu misalai da dama na rayuwarta wanda ya fama musu miki da ba zai ta6a goguwa a ransu ba. Karshe ta roki alfarma kan su yafewa mahaifinsu, idan kuma an kwana biyu, su je su ziyarceshi. Basu ja da maganar ba suka amince don faranta ranta. Alhaji AbdulKarim ya yi musu tasa nasihar irim ta uba ga dansa sadda ya yi aure. Suka kara jin kaunar mutumin. A komai nasu yakan nasu shawara wannan ya kara tabbatar musu cewar mahaifiyarsu ta yi sa’a a rayuwa.
*****
Ya karasa dakin da sallama. Murmushi ya yi ganin yanda ta rakube a karshen gado tana kuka har da sheshsheka. Karasawa ya yi gami da ajiye ledar hannunsa sannan ya fita ya rufe kofofin gidan ya dawo. Mayafin ya daga gami cusa kansa ciki. Sharemata hawayen ya yi, ya tallafo keyarta goshinsu ya hadu wuri guda. Shiru ya yi yana sauke numfashi tana tayashi.
“Kiyi hakuri Humaira, in sha Allah zan rike amanarki a zamantakewa. In sha Allah Adam zai miki adalci daidai gwargwado. Ba kuma zan zamemaki Rumfar Kara ba.”
Ya yaye mayafin, suka dubi juna sosai, jawota ya yi ya kwantar saman kafadarsa. Ta yi lamo gami da lumshe idanu. Nasiha ya yi mata akan su zauna lafiya da kare hakkin juna. Karshe ya taimakamata zuwa bandaki ta dora alwala shima ya yi nashi. Bayan sun yi sallah ya ciyar da ita kaza da yoghurt mai sanyi sai ruwa. Daga nan kuma labari ya sauya. Adam ya san wacece Humaira, suka kafa tarihi mai dadi wanda mantawa zai musu matukar wuya. Ji suke kamar su hadiye junansu tsabar so da kauna. Ya sanyata dariya ya kuma sanyata kuka ya rarrashi abarsa. Banda hamdala ba abinda yake ga UbangijinSa.
*****
Jerowa suka yi su uku har cikin gidan yari. Zama suka yi suna jiran a kawoshi. Jim kadan ya iso wurin, kallonsa suke, wannan karon an gyara mishi sumarsa an rageta. Idonsa daya ba ya gani sosai, dayan kuwa garas yake kallonsu. Ko daga bacci ya tashi ba zai mance fuskar yarannasa ba. Ya zauna ya mika hannu sai kuka, Adam da Fuad lokaci guda suka damke hannunsa suna nasu hawayen.
Komai ya wuce a wajensu. Ya ci gaba da rokon gafara suka nuna ba komai. Amir kuwa kallonsa yake cike da tausayi. Ya nemi gafararsu don tun suna yara har girma, bai ta6a damuwa da su ba. Suka nuna sun yafe. Can kuma suka shiga hira, suka sanya ya sake da su ya bar dari-dari. Da zasu tafi sai ya ji kamar ya bisu, ya aika sakon gaisuwa gurin Bilkisu. Haka suka rabu da shi kamar kada su tafi. Tausayi sosai yake basu. Sun yarda idan dai mutum ya haifeka, to akwai boyayyar kauna ko yaya ne.
Bayan Shekaru Uku
Abubuwa da dama sun faru ciki kuwa har da rasuwar Salma a gidan yari, Halima kuwa ciwo ta kwanta sosai a karshe aka tabbatar ta kamu da kanjamau. Wannan tasa Hanan ta kara tsorata da lamarin Ubangiji. Ta rike aurenta gam! Don a yanzu Sidi dole ya sauko yana nunamata kulawa da kauna ganin ya rasa Hanifa har abada. Ba ta kuma cire a ranta cewar zai fasa aure nan gaba ba. Ta dai gode Allah da Ya cireta daga layin mata mazinata. Abinda ta haifa dama bai rayu ba. Bayan aurensu ta kara haihuwar danta namiji ya ci sunan Malam Iliyasu.
A bangaren Hajiya Murja kuwa, tun abinda ya faru da su Halima sai ya zamemata ishara. Ta watsar da makamanta na zuwa wurin boka ta rike mijinta da zuciya daya sai dai tana fuskantar kalubale iri iri.
Tun mutuwar Salma, Inna ta kwanta rashin lafiya, wata uku tsakani itama ta rasu. Wannan kadai ya kara tsoratar da mutanen gidan su Salma, sun tabbatar duk abinda ya yi farko to zai yi karshe. Ya zamemusu darasi babba ganin yanda duk takamar Inna a gidan da nuna isarta ita da diyarta Salma, yau gashinan babu su a duniyar gaba daya.
Hayat ya tuba ba kadan ba, wannan ta sa yaransa kula da shi sosai da kuma ziyartarsa akai-akai duk don su nunamishi dagaske komai din ya wuce. Rayuwar kenan dama.
*****
Yarinyar ke gudu tana bin yaron tana kuka. Iyayen dake gefe suna aikin shan ruwa kasancewar lokacin azumi ne. Humaira ce ta soma ankara ta kwala kira.
“Na’eem!” Yaron kyakkyawa da shi ya juyo a dan firgice sannan ya yi jifa da yar tsanar. Humaira ta yunkura don ta je ta jibgeshi. Adam ya taka gefen rigarta ta koma ta zauna ba shiri. Su Amira na dariya.
“Ba ki isa ba, idan na barki wataran sai kin nakastamin ďa. Ba ya girmeta ba? Gudu yake koyamata.”
Fuad ya saki baki.
“Haba Bros, mai sunan Umma ce fa. Kana son kai da yawa. Wato dai naka naka ne.”
Adam ya harareshi.
“Ka fita idona Fu’ad. A zamaninnan kowa nasa ya sani. Zo nan my son.” Ya karashe da mikawa Na’eem hannu, yaron ya yunkura zai taho suna hada ido da Humaira ya kasa sakamakon hararar da ta zabga mishi. Adam ya yi dariya ya kwalamata cokali a kai.
“Allah kuwa ki fita idona kema. Na lura kina matsawa yaronnan. Idan bakya son shi zan nemomishi sabuwar Anti.”
Kishi ya motsawa Humaira. Amira da Salima suka gimtse dariyar dake cinsu sanin halinta.
“Ka nemo mishi kaka ma ba Anti ba. Ai yanzu ka tsufa ba budurwar da za fa aureka.”
Suka tuntsire da dariya banda ita da ta cika ta yi fum.
“Kike gani? Ko zaa gwada toh?”
Ta yi kwafa, idan wannan wasan ne ya sabarmata da shi, burinsa ta yi ta kumburi tana maida martani yana sheka dariya. A karshe dakyar ya rabu da ita suka ci gaba da ciye ciye. Bayan tafiyar su Fuad, ya ja matarsa jiki ya kasheta da soyayya kala-kala gami da bata hakuri.
Komai na rayuwa ya sauya musu. Azumi yana da kwana goma sha biyar suka ziyarci dakin Allah. Anan Humaira ta kara samun ciki. Adam ji yayi kamar ya lasheta. Ta zama mishi haske a rayuwarsa ta ko’ina.
Daren ya nunamata soyayya ba kadan ba. Ya lalubi kunnenta gami da mata rada.
“Gorgeous kin zamemin haske cikin duhu. Koyaushe kara sonki nake. Madallah da mace ta gari. Allah Ya barmu tare har abada. Ya rabamu da cin amanar junanmu har mutuwa.”
Ta yi murmushi gami da juyawa ta dubeshi, lokaci guda ta hade bakunansu wuri guda wanda ya kara susutashi ya rukunkumeta.
ALHAMDULILLAH.
KARSHE
Godiya ta musamman ga dukkan wadanda suka bani aron lokaci suka bibiyi labarina har karshe. Allah Ya barmu tare.
Har abada ina tare da ku ina kaunarku.:
Ummu Abdool (Allah kaɗai zai biyaki bisa kokarin da kika min na ganin na kammala littafin nan)
Barrister Firdausi Kabir (Ba zan taba mance gudunmuwarki ga labaraina ba. Kina daga mutanen da ba zan manta ba wurin bani shawara duk sadda na kuskuro. Allah Yabar kauna)
Batool Mamman (Kina biye da ni har karshen labarina. Allah Ya bar zumunci, Ya raya su Abeed.)
Fatima Ummu Hanan. (Har abada ana tare. Na gode sosai da jimirin bibiyar labarin Rumfar Kara.)
Na gode duka. Sai mun hadu a Next Novel ɗina in Sha Allah
RUMBILHAK muna godiya gareku gaba daya. Allah Ya bar zumunci. Ameeen.
Alhamdulillah littafi yayi dadi Allah qara basira
Masha Allah
Alhamdulillah dai dai yadda na so haka littafin nan ta bada ma’ana. Mun gode sosai
Littafi yayi wlh
One more tnxx