“Yayana na biyo.”
Ya bi wurin da ta nuna da hannu, Bilal ya mike tsaye. Malamin ya yafito shi da hannu.
“Zo nan.”
Hanjin cikinsa ya kaɗa, ya fito yana satar kallon Humaira yana harararta.
“Ya kuke da ita?” Malamin ya watso mishi tambaya.
“Kanwata ce, tana son zuwa makaranta amma Malam ya hana mata zuwa, ita ce ba ta jin magana.”
Ya yi shiru yana dan nazari. Can ya bada amsa.
“Meyasa ba ya son mace da karatu? Alhalin ilimin mace mai amfanar duniyar ce ma gaba ɗayanta.”
Sai lokacin Humaira ta soma magana cikin kuka.
“Ina son boko amma Malam ya ce ba zamu yi ba. Ina so na koyi Ingilishi.”
Da murmushi Malamin ya bata amsa.
“English ake cewa, kar ki damu In sha Allah ni zan je na samu Babannaku, ya bari ku yi karatu saboda amfanin al’ummarmu ce baki ɗaya. Za ki yi karatu kinji ko?”
Ta hau gyaɗa kai tana wangale baki. Bilal ya zaro ido.
“A’a Malam, wallahi dukanmu za’a yi a gida. Malam ba zai ta6a yarda ba. Ba ya so ya tsani karatun boko ga ɗiya mace.”
Humaira jin haka ta turo baki tana harararsa.
“Ai dai zai iya gwadawa a gani ko? Watakila Malam ya yarda idan ya ganshi ƙatoto.”
Bilal ya tabbatar kora take son jawo mishi daga makaranta, abin mamaki sai ya ga Malam Nuhu ya yi dariya karshe ya dubeta.
“Hakane Kanwata, yanzu dai ki koma gida idan an tashi zan zo da Bilal ya nunamin inda zan samu Babannaku. Za ki yi karatu da yardar Allah kinji ko?”
Ta hau dariya tana gyada kai, kafin ma ya fice ya barta da Bilal, har ta yi gaba ta fice daga makarantar.
Wunin ranar haka ta shanye faɗan Inno da Maryam akan fitar da ta yi da sassafe. Babu inda ta kara komawa hakan yasa suka ji kamar dagaske gargaɗin ya ratsa ta.
Karfe hudu da mintuna na yammacin ranar, aka zo sallama da Malam. Malam na tare da almajiransa a lokacin. Ya kurawa baƙonnasa idanu ganin yanda ya haɗe cikin coat har ya faka mashin dinsa ya ƙaraso. Bilal tun daga nesa da ya nunamasa gidan ya arce zuwa gidansu don yasan yau ba sauki.
Bayan sun gaisa da Malam, ya jefamasa tambaya.
“Gashi kuma ban dauki fuska ba.”
Ya yi murmushi.
“Hakane, gaskiya ba ka ta6a ganina ba, sunana Malam Kamal, malami ne na boko a makarantar Cinnaku Primary and Secondary School.”
Malam ya gyaɗa kai.
“Na gane, Allah dai Yasa ba wani laifin jikokin nawa sukai ba?”
Ƴar dariya Malam Kamal ya yi.
“Ko ɗaya, sai dai wata magana da ta kawo ni mai matukar muhimmanci.”
Jin haka sai Malam ya dubi almajiransa. Hannu yasa ya yafito wani ya ce ya dau tabarma ya shimfida musu daga ƙasar bishiya gefe guda.
Bayan ya sha ruwan da Malam ya sa aka kawomishi ya hau magana.
“Allah ya gafarta Malam, magana ta kawo ni akan diyarka Humaira.”
“Allah Yasa ba wani laifin ta aikata ba?” Malam ya faɗi fuska cike da damuwa.
“Ko ɗaya, sai dai yarinya ce mai hazaƙa da saurin daukar karatu. Yarinya ce mai matukar son ta yi karatu. A takaice dai na zo neman alfarmar ka bar yarinyarnan ta nemi ilimin zamani kamar yanda..”
“Dakata, dakata don Allah.”
Ya furta ransa a ɓace.
“Tun sadda ka cemin kai Malami ne kuma na makaranta, naji ina kallonka da wata ƙima da daraja. Kar ka yi sanadiyyar da wannan girma zai zube, wala’allah su yaran basu faɗamaka ba, Haruna ba shi da ra’ayin karatun zamani ga ƴaƴa mata, wannan ta sanya duka yarana mata ke zaune ba karatun sai na sanin hukunce-hukuncen addini. Babban abinda yasa na yarjewa yara maza su yi, bai wuce duba da cewa nan gaba zai iya zamtowa na kwaresu ba saboda su maza su ne idon duniya. Su ne masu yawo cikinta, mace kuwa…”
“Ka gafarceni, ba wai na katse ka ba, sai dai mace kamar namiji, akwai bukatar ta yi ilimi domin ita uwa ce, ita ke renon ’ya’ya, kuma halaye da dabi’unta abubuwan kwaikwayo ne ga ’ya’yanta. Yanzu idan bata je boko ba, nan gaba za ta iya aure, kaga ba ta a karkashin ikonka. Wala’alla wanda ta aura mai ra’ayin boko ne…
Haka Malam Kamal ya yi ta dogon jawabi sai dai uffan Malam bai ƙara faɗi ba sai sauraronsa. Bayan ya kai aya Malam ya dubeshi.
“Na gode da wannan bayanin, sai dai zan yi tunani akai. Kana iya tafiya.”
Jiki a sanyaye Malam Kamal ya miƙa hannu sukai sallama sannan ya tashi ya tafi ba tare da ya iya fassara ainahin abinda ke saman fuskar Malam Haruna ba.
A cikin gidan kuwa, Humaira na zaune tana daka gyaɗa ta miya, tana yi tana jefawa a baki. Inno ba ta gida ta je duba Maikudi ba lafiya. Karshe da ta ga idon Mamarta a kanta sai ta bari. Maryam da ke zaune tana yankan alayyahu na miya ta dubeta da kyau.
“Ke.” Ta juyo tana mai amsawa fuskarnan sai ka rantse ko yatsa ka sanya ba zata ciza ba.
“Yau kin yi wanka?”
Maryam ta jefamata tambaya. Ta hau mutsistsika idanu gami da girgiza kai.
Maryam ta girgiza kai gami da jan guntun tsaki.
“Allah Ya shiryamana ke Humaira. Ajiye dakan nan maza ki shiga wanka tun ban ɓallaki ba.”
Ba musu ta ajiye turmin ta mike ta bar wurin. Bin bayanta da kallo ta yi, a duk sadda ta kalli fuskarta, fuskoki da yawa kan fadomata a rai amma cikin ikon Allah sai ta ji kamar an yi toshemata kwakwalwar, ta nemi komai ta rasa.
Tana kallon diyar har ta shige wanka, a bangaren Humaira itama dai mamakin kallon da Mamar ke yawan bin ta da shi lokaci zuwa lokaci take yi, bata kawo komai ba sai na nason dauɗar da take yi. Shigarta ba jimawa Malam ya shigo da sallama. Maryam ta amsa gami da miƙewa ta kar6i ledar hannunsa tana mishi sannu da zuwa. Ya amsa kafin ya karasa saman tabarma ya zauna. Sai da ta kawo mishi ruwa ya sha, sannan ta juya da nufin komawa bakin aikinta ya dakatar da ita.
“Amm Maryama, zo ina son magana da ke.”
“Toh.” Ta amsa kafin ta zo ta zauna tana mai gyara zaman hijabinta, domin abu ne mai matukar wuya ka risketa ba hijab a jikinta.
“Malamin makarantar yarannan ne, su Bilal. Ya sameni da batun sanya yara mata a boko. Ya yimin gamsassun jawabai wadanda bayan na musu kyakkyawan nazari na gane ya fi ni gaskiya duk da cewar ni dinma abinda na hanga a farko abu ne mai muhimmancin da za’a duba.”
Tiryan-tiryan ya yi mata bayanin yanda sukai a gajarce, ba ta ce komai ba sai dai tana murmushi a kasan ranta. Ba ta iya ja da umarnin bayin Allahn nan, saboda tana musu kallon mutane mafi daraja a wajenta. Sun dauketa sun bata kulawar da ba za ta iya biyansu da komai ba. Hakan ya sa ta danne kaunarta da son Humaira ta yi karatun boko kawai don ta faranta zuƙatansu. Sai dai ba ta gama fahimtar dalilin Malam na yi mata maganar ba alhalin yana da karfin ikon yin duk abinda ya ga dama, kamar kuwa yasan tunaninta sai ya katse ta.
“Nasan za ki so sanin dalilin yi miki wannan maganar, ba komai bane face neman shawara. Ya ki ke gani?”
Girgiza kai ta yi.
“Baba duk abinda ku ka yanke daidai ne a wurina. Wallahi bani da ja.”
Murmushi ya yi yana lura da yanda lokaci guda farin cikinta ya kasa ɓuya, a can karkashin zuciyarsa yana mai tausayamata na gushewar tunaninta wanda ya janyo har yanzu ba ta iya tuna komai nata. Addu’a kam ba’a fasa ba, su na fatan tabbatarsa.
“Allah Ya yi miki albarka Maryama. Allah Ya warware dukkan kullin da bamu san da shi ba.”
Ta amsa a raunana kafin ya bata umarnin tafiya bayan ya mata nuni da ledar da ya kawo.
“Wannan a ba jikalle.”
Ya ƙarashe da ƴar dariya, da murmushin ta yi godiya sannan ya fice. Humaira ta fito daga wanka tana duban Mamarta, ganin yanda take murmushi ya sanya ta ƙarasawa gareta ta zauna kusa da ita.
“Mama menene?”
Maryam ta dubeta da murmushin.
“Akwai labari, tafi ki sa kayanki ki dawo.”
Jin haka ta washe baki aikuwa ta ruga ciki a guje. A gaggauce ta zira wata doguwar rigarta da ta samu tsaraba daga Sarkin Dawa lokacin da ya je aikin Hajji. Ta dawo ɗankwalinta a hannu ta yiwa Mamar tsaye sa’ilin da ta ke wanke ganyen Alayyahu. Dubanta Maryam ta yi kafin ta yi ƴar dariya ta kauda kai.
“Tafi ki ci gaba da yimin daka, idan kin kammala ga tsarabarki can daga Malam.”
Ba wannan ta so ji ba, hakan ya sanya ta rike hannun Mamar, a shagwaɓance ta ce.
“Mama don Allah ki ban labarin.”
Dariya ta ba ta.
“To shikenan, kammala aikin tukunna.”
Ba musu ta fice tana kukan shagwaɓa. A gaggauce ta karasa ga ledar, yalo ne kaya guda sai karas. Yalo ta dauka ta wanko, ta karasa wajen turmin, tana daka tana cin abinta idonta akan Mamar tana lura da yanda take farin ciki.
Ba ita ta ji labarin ba sai da ta kammala komai tsaf sannan Maryam ke faɗamata batun makarantar da Malam ya ce zasu yi. Murna da tsalle ba’a magana, kasa zama ta yi ta ruga gidan su Jamila a guje tana kwalamata kira. Mamar Jamila, Karima na zaune da kishiyarta ta faɗo gidan ar sai da ta basu tsoro. Can kuma Yalwa ta ja tsaki ta kauda kai. A duniya ba yarinyar da ta tsana sama da Humaira, acewarta yarinyar da ba’a san asalinta ba ta zo ta fi jikokin gida gata da mutunci a idon iyayen da kakannin.
“Ke kam Humaira sai dai addu’a.” Karima ta furta.
Humaira ta yi dariya.
“Inna ina Jamila?”
“Bata nan na aiketa kai niƙan..” Sallamar Jamila ta katse hanzarinta. A guje Humaira ta nufeta ba ta ko bi ta kan garin da ke bisa kanta ba. Karima na dakatar da ita sai dai ina! Ji kake bam! Gari ya watse a kansu. Humaira duk da haka labari ta ke ba Jamila.
“Ke! Malam ya ce zamu je boko! Yanzu Mama ke faɗamin.”
Jamila ta kasa motsi don tasan sun yiwa Karima laifi. A can kasan ranta wani mugun farin ciki ke ratsa ta don dama dannewa take amma tana son bokon. Tsoro ne ya ja ba ta bin Humaira.
Rankwashin da Humaira ta ji a tsakar kanta ya ja mata nutsuwar dole, kafin ta ankara ta ji an riƙe kunnenta gam! Yalwa ce cikin faɗa take magana.
“Yar iskar yarinya da ba’a isa a hanata ba! Yau kya faɗamin shegiyar da ta turo ki ki ɓararmana da garin tuwo.” Yalwa na maganar tana kara matse kunnen, banda ihu ba abinda Humaira ke yi. Karima na magana sai dai ko ta kanta Yalwa ba ta bi ba, ta hau jibgar Humaira kamar an aikota. Shigowar Yaron Malam ne ya sanya ta sakinta gami da ja baya tana haki. Humaira farin ciki ya koma akasinsa, banda kukanta ba abinda ka ke ji. Fuska a daure Yaron Malam ya dubi Yalwa da ke cika da batsewa.
“Meke faruwa haka? Wane irin rashin hankali ne?”
Yalwa ba ta ce uffan ba ta kauda kai.
“Karima lafiya? Ke tashi daga ƙasa.”
Ya ƙarashe yana duban Humaira. Karima ce ta zayyane mishi abinda ya faru. Ya dubi Yalwa.
“Ko me ta yi bai kyautu ki mata irin wannan dukan ba Yalwa, kar ki manta har yanzu Humaira yarinya ce don ba ta fi sa’ar Jamila ba.”
Ta yamutse fuska.
“Toh, ai kuma yanzu zan ji ba dadi tunda na ta6a ƴar gwal. Aikin banza kai harara a duhu, Allah na tuba idan kun yi wa ku ka yiwa? Yarinyar da ba’a san asalin uwarta…”
Tsawar da Yaron Malam ya dakamata ne ya sa ta kame bakinta ala dole.
“Ku shiga daki ku sauya kaya.” Yaron Malam ya faɗi yana duban Karima, ta karasa tana kakka6ewa Humaira jikinta ta ja su sukai ɗaki.
“Ina miki gargaɗi da babbar murya, ki kiyayeni Yalwa! Ki kiyayeni akan cin mutuncin dan adam. Koda wasa kar ki kuskura ki ƙara aibata Maryam ko Humaira idan ba haka ba ina miki rantsuwa da Allah zan sa6amaki.”
Daga nan ya yi gaba ta bishi da fadin “To ai kuma yanzu sai ka kara auno mana garin tuwon tunda ƴar gwal ta ɓarar.” Bai ko juyo ba balle ya dubeta, ta bi bayan da harara zuciyarta na kara cika da tsantsar kiyayyar Humaira.
Koda ta koma gida sanye da kayan Jamila, Inno ke neman ba’asi. Ba ta ɓoye komai ba ta faɗamata. Ta kara da jefa tambaya.
“Inno wai dagaske ba’a san asalin Mamana ba?”
Maganar ta yi musu girma a tsakar kai, Maryam ta ji ta kamar saukar aradu sai dai ta kauda kai ba ta ce uffan ba, kwalla suka tarar mata. Inno cikin fada ta ce.
“Duka Yalwar ce ta faɗamaki?”
Ta gyada kai tana sheshsheka, Humaira ba ta kaunar abinda za ta6a lafiyarta don har yanzu ba ta bar jin ciwon jiki ba ga kunnenta ya yi ja.
Gani sukai Inno ta kwalawa Umar kira, umarni ta ba shi da ya cewa Yaron Malam ya zo tana nemansa. Sai a lokacin Maryam ta magantu.
“Inno kiyi hakuri tunda ya tsawatar in Sha Allah ba zai kara faruwa ba. A yi mata uzuri don Allah.”
Kwafa Inno ta yi, sai sannan Umar ke jin dukkan abinda akai daga bakin Humaira. Ya ja tsaki gami da girgiza kai.
“Ai matarnan za ta yi abinda ya fi haka wallahi. Da gaskiyar Yayata, a kyaleshi tunda ya tsawatar.”
Dakyar suka shawo kan Inno ta hakura da batun kiran Yaron Malam, karshe aka bar maganar zuwa na batun tafiyar da Inno zasu yi zuwa Yobe ta ke mata albishir za ta da ita har Maryam. Wannan ya fi komai faranta ran Humaira suka koma kan batun makarantar da Humaira zasu soma. Umar ke fadamusu Malam ya mishi maganar akan ya turo mishi yayyunsa su tattauna game da makarantar su Humaira. Hirar da ta fi so aka shiga yi don kawai farin cikinta, nan da nan ta ware ta watsar da tambayar da ke cin zuciyarta gami da sakin fuska sosai aka hau hirar makaranta tana gwadamusu yanda za ta dinga tafiya cikin uniform Umar na gyaramata.
*****
A gaggauce Adam ya ƙarasa ga Umma bayan ya janye Amira daga jikinta, hannunsa ya kai bakin hancinta. Jin tana numfashi ya fahimci suma tayi, nan da nan ya dau ruwa ya yayyafamata, wata nannauyar ajiyar zuciya ta sauke kafin ta hau ambaton Allah tana buɗe idanun da sukai mata nauyi. Da zafin nama ya ɗagata cak ya yi hanyar fita da ita. A farfajiyar gidan ya umarci Amira da ta bude mishi motarsa. Ta hau tambayar mukulli, nuni ya yi mata da aljihunsa, ta zira hannu ta dauka. A gaggauce ta bude gidan baya ya sanya Umma, Yaha ya ba umarnin shiga. Su kuwa ya ce su zauna gida su jira. Tayar da motar ya yi suka fice, wannan ƴar hayaniyar ce ta fito da Abba. Ya sauko ƙasa ya riski Amir da Amira na kuka.
“Ku mene hakan? Meke faruwa?”
Suka yi shiru, sai da ya dakamusu tsawa kafin Amira ta soma magana baki na rawa.
“Um..ummaa ce, sun tafi asibiti da Yaya Adam bata da lafiya.”
Ya yi shiru, haka kawai sai jikinsa ya yi sanyi. Kada fa ya kashe Bilki, yana da tabbacin iyayensu ba kyaleshi zasu yi ba muddin suka ji shi ne sanadi. Ganin yanda yaran ke kallonsa ya zaro musu ido.
“To mayu! Cinye ni zaku yi kun kuremin ido?”
Tun ma kafin ya kai karshe sun sauke idanun, Amir jiki har rawa yake. Tsaki ya ɗan ja.
“Shi kuma Adamu da yake ya gama raina ni ina gidan bai zo ya gaisheni ba jiya, yau kuma ya ɗaukar min mata ya fita da ita ba neman izini. Wane asibiti suka tafi?”
Ya ƙarashe yana duban yaran. Ransu na ƙuna, Amira ta kara daurewa ta yi magana.
“Watakila asibitin su Yaya Adam.”
Ya hau faɗa don me ba’a kai ta nasa asibitin ba, yara dai ba baka sai kunne. Ya gama bambamin sannan ya ja tsaki ya koma sama. Amir na kuka yake fadin.
“Na tsaneshi nima wallahi, na tsaneshi, ba zai ta6a mutunci a idona ba.”
Ganin haka Amira ta koma rarrashi karshe ya ruga ɗakinsa ya bar ta ita ɗaya. Jim kadan uban ya fice cikin shirin da ya saba zuwa asibiti sai dai basu da tabbacin inda ya nufa. Ganin haka gidan ya yi musu faɗi, Amira ta yi kiran Amir suka fice gidan Maman Hanifa makwabciyarsu. Ba ta jima da dawowa daga kai su Hanifa makaranta ba, ganin su ba karamin mamaki ta yi ba. Baban Hanifa shima kuramusu idanu ya yi gami da ajiye jaridar dake hannunsa yana karatu.
“Amira, Amir lafiya? Ba ku je makaranta ba?”
Duk Maman Hanifa ke jero musu tambayoyin a lokaci guda. Amira ta labarta musu dukkan abinda ya faru game da rashin lafiyar Umman. Salati suka shiga yi, Baban Hanifa ya dau waya.
“Bari na ji wane asibiti suka je.”
Suka yi jugum-jugum sa’ilin da Baban Hanifa ke sarrafa waya, Maman Hanifa kuwa har ta soma matsar kwallah. Duk yadda Bilkisu ke son ɓoyemata bakin cikin da take shaƙa tsawon shekarunnan da suka rayu tare su na masu makwaftaka da juna hakan ya faskara don wani abun kusan da gayya ake mata a gaban baƙi. Ta lura wannan ne ya sa kafin ta yi yunkurin zuwa wurinta, Bilkisu ta shigo saboda gujewa dukkan cin zarafi. Yanzun ma bata raba ɗayan biyu takaicin Hayat ne ya ke nukurkusarta har ya yi mata illa.
*****
Cikin gaggawa aka shigar da Umma ɗaki don ceto rayuwarta. Adam a gaggauce ya sanya farar rigarsa ta aiki, farin mutum ya koma jazur tsabar tashin hankali. Jijiyoyin goshinsa sun fito raɗau yayinda jikinsa har kaɗawa yake. Hannunsa ya ji an riko sa’ilin da yake kokarin cusa kai ɗakin. Rai a zafafe ya kai duba ga mai shi. Amininsa kuma abokin aikinsa ne, Ibrahim.
“Kar ka shiga, ka bari zamu dubata.”
“I know, zan shiga ne kawai.”
Ibrahim ya gyaɗa masa kai gami da ba shi hanya ya shige. Sosai suka dukufa kanta, yana tsaye yana Safa da marwa yana dubansu. Yakan ce su yi wancan su yi wannan har aka samu aka shawo kanta numfashin ya daidaita. Ko ba’a mishi bayani ba ya san matsalarta. Idan kuwa bai yi dagaske ba ciwon zuciya na dab da kama mahaifiyarsa banda hawan jinin da take fama da shi yanzun.
“It’s alright, Allah Ya bata lafiya.” Fadin Dr Ibrahim yana dubansa. Jinjina kai kawai ya yi ba tare da ya ce uffan ba. Dr Samuel da Dr Nabila sukai mishi barka da fatan samun saukin Umma gaba daya tare da jaddada masa sai an kula, shi likita ne da ba sai an mishi karin bayani ba. Godiya ya musu har suka fice daga dakin. Ya karasa ga Umman ya rike hannunta yana duba, shigowar Yaha ce da sallama ya tunasar da shi tare suke.
“Sannu Adamu, ya jikin nata?”
“Da sauki, ta samu bacci nan da kamar 4hrs za ta tashi.”
Ya fadi yana duban Umman. Yaha ta jinjina kai tana share kwallarta. Kwankwasawa akai kafin a shigo. Dr Samuel ne, ya dubeshi.
“Sir, your dad is here.”
Ji ya yi kamar an watsamishi wuta a kirji.
“Don’t let him enter.”
“Saboda kai ka haife ni ko? Ko kai ka ke aurar min ita?!”
Suka tsinci muryarsa a kausashe. A tunzure ya yi nufin miƙewa da zummar kai mishi shaƙa, Yaha ta yi saurin riƙoshi.
“Ina haɗaka da girman Allah kar ka yi haka Adamu. Ka duba darajar mahaifiyarka, da ace idonta biyu ba za ta ji dadin abinda ka ke niyyar aikatawa ba.”
Ganin abin ya koma family issue ya sanya Dr Samuel ficewa ya turo kofar. Da yatsa Adam yake nuna Dr Hayat.
“Bai ta6a farantawa Umma ba! Bai ta6a yin abinda zai sa ta ji ita mace ce mai daraja a wajensa ba. Mene amfanin yin shiru? Lokaci ya yi da ya kamata ace mun farka mun wartsake daga baccin da muke mafi muni! Time has changed! Lokaci ya wuce da za’a tsaya ana hakuri da rufa asiri wadanda basu san mene ma’anar kawaici da kyautatawa ba. I’m fed up! Yarannan bai ta6a dubansu da mutunci da ƙima ba, tun tasowarsu har zuwa yanzu Umma da Ni ke fafutuka akan komai da ya dangance su. Kwandalarsa ba ta ta6a shiga hannun Umma da sunan wai ta siyawa Amir da Amira riga ba. So yake ya kashe mana ita?! Ya shigo nan don ya karasa mana ita? To bai isa ba! Bai isa ba nace! Ina rantsuwa da Allah ya ƙaraso nan (ya yi nuni da gadon da Umma ke kwance) sai na kashe shi!”
Ya karashe murya a ɗage, Dr Hayat wanda ya yi mutuwar tsaye yana duban Adam, gaba daya sai ya sha jinin jikinsa. Wani irin tsoro ya shige shi. Dagaske zai aikata duba da yanda tsigar jikinsa ke tashi yana wani mazari. Idanunsa kurr akansa babu ko russunawa. Ganin haka sai ya hau borin kunya.
“Kai ni kake faɗawa haka? Dakyau! Eh ai ga irin tarbiyyar da ka samu daga Bilkisu. Darajar mahaifina da ya yi rantsuwar tsinuwa gareni duk radda na saketa ta ci ba don haka ba wallahi daga ku har ita da tuni na watsar. Aikin banza da wofi! Ka haifi yaro ya ce zai ci mutuncinka. To wallahi kar na kara ganinka a gidana, idan ka shiga ban yafe ba! Shashashan banza da wofi!”
Daga nan ya sa kai ya fice gami da bugo kofar da karfi. Yaha ta durkushe tana kuka da fadin.
“Ka gani ko Adamu? Ka ga abinda nake gudu? Meyasa ba ka tausasa kalamanka ba? Ka manta hakuri yana daga cikin kyawawan ɗabi’u mafi daukaka?”
Adam don takaici bai ce uffan ba, ya fice daga dakin zuwa ofishinsa. Kulle kansa ya yi ya zauna saman kujera ya shiga tunanin mafita. Zuciyarsa na ingizashi akan ya sanar a gida sai dai gargaɗin Ummansa da ta ke yawan yi mishi yana hanashi. Ya kwantar da kai saman kujerar sai dai ba sauki, karshe ya mike ya faɗa banɗaki ya dauro alwala ya tada sallar walha. Bayan ya kammala ya jima anan yana kai kukansa ga Allah. Bayan ya shafa ne ya sa hannu a aljihu ya zaro wayarsa dake faman ringing. Sunan Barrister Haladu (Baban Hanifa) da ya gani ne ya tunasar da shi batun ƙannensa. Da sauri ya dauka. Bayan sun gaisa ya tambayeshi ko a asibitinsu Umma take.
“Eh tana nan, yanzu dai an shawo kanta bacci take sai nan da kamar awa hudu zuwa biyar za ta farfaɗo.”
“Toh Alhamdulillah. In Sha Allah zuwa anjiman zamu zo.” Barrister Haladu ya faɗi.
“Yauwa, don Allah ko za’a yimin alfarma a dauko su Amira su..”
“Ai gasunan ma tare da mu, an samu sun yi shiru. Muna tafe anjima tare da su In sha Allah.”
Ya ji sanyi sannan ya mishi godiya daga nan sukai sallama. Missed calls ya gani barkatai, ba wanda ya ja hankalinsa sai na Uncle Hashim. Kiransa ya yi. Bayan sun gaisa ya ce.
“Wai kuwa lafiya ina ta kiran Bilkisu ba ta dauka?”
Ya ɗan yi shiru kafin ya bada uzuri.
“Ah lafiya kalau Uncle, ba ta ji dadi ba shi ne na kawota asibiti amma yanzu da sauki ta samu bacci.”
“SubhanAllah, jiya-jiyannan fa mukai waya lafiya kalau. Allah Hakeem, meke damunta haka?”
Ba ya so a san ainahin larurarta hakan ya sa ya ɗan rufe.
“Ciwon kai da zazzaɓi, amma yanzu da sauki.”
“To Allah Ya bata lafiya, nima gobe zamu taso daga nan zuwa Kanon, cewa zan yi ta jira zai fi mu wuce Yoben tare. Shima Hayat din na kira domin na faɗamasa bai ɗaga ba.”
Sunan ma ba ya so, ga shi dai babansa ne amman ko a makaranta sai da ya sauya suna daga Adam Hayat Bello zuwa Adam Bello kadai.
“Toh zan fadamata In sha Allah Uncle. Allah Ya kawoku lafiya.”
Hashim ya amsa sukai sallama. Hashim mazaunin Cairo ne, can ya yi karatunsa na harshen larabci, nan Yobe ya yi aure ya dauki matarsa zuwa Cairo. Shekaru kusan ashirin kenan yana zaune can, zuwansa gida bai fi sau goma ba. Tsakaninsa da yar uwarsa sai waya. Sau dubu zai tambayeta ko akwai wata matsala, sau dubun dai za ta amsa da babu ta rufawa mijinta kuma ɗan uwansu asiri.
*****
Misalin karfe biyu da mintuna Umma ta dawo hayyacinta, sunan Allah a saman le66anta. Yaha da sauri ta karasa gareta.
“Kin farka? Sannu Bilkisu.”
Umma ta waigo tana dubanta, kanta ke sarawa hakan ne ya sa ta gyaɗa kanta kawai ba tare da ta iya cewa uffan ba.
“Ko na ɗan ɗaya ki?”
Nan ma kai ta gyada sai abin ya ba Yaha tsoro.
“To Bilkisu ya ba kya magana? Meke damunki?”
Ta nuna kanta da dan murmushi mai tafe da ruwan kwalla.
Yaha na shirin magana Adam ya turo kai da sallama. Cikin sauri ya ƙarasa ga Umman ya riko hannunta. Bai ce komai ba ya dafa kanta, zafi ya ji. Ya dubeta.
“Ciwon kai ko?” Ta gyada kan. Idanun Adam suka kara kaɗawa, da taimakon Yaha suka samu ta ci abinci, daga nan suka lalla6ata ta sha magungunan.
“Bari nayi sallah.” Yaha ta taimaka mata suka shiga banɗaki ta kama ruwa, da hijabin Yaha ta yi sallah. Suna nan zaune aka ƙwanƙwasa kofar. Maman Hanifa ce ta shigo da sallama, a bayanta Amira ce sai Hanifah da ba ta fi sa’ar ta ba. Sai Amir. Da gudu suka yi kan Ummansu, zasu faɗa jikinta Adam ya daka musu tsawa. Hakan yasa suka nutsu suka fahimci manufarsa, hannunta duk suka rike, Amira mai arhar hawaye sai kuka, to Amir dinma ka sa daurewa ya yi ya soma hawaye.
“Ji wannan shirmen, maimakon ku yi mata ya jikin?”
Fadin Yaha kenan, ƴar dariya Maman Hanifa ta yi ta ce.
“Barsu dai, duk kukan da suka sha bai ishe su ba sai sun ƙara anan. To ya isa haka ko yanzu na juya da ku.” Wannan ta sanya suka yi shiru.
Sai a sannan Adam ya samu ya gaisa da Maman Hanifa, ta amsa sadda take ajiye kwandon hannunta a gefen gado. Ta gaishe da Yaha kafin ta juya ga Umma.
“Maman twins sannu, ya jikin?”
Kai Umma ta gyada tana dan murmushi.
“Alhamdulillah, da sauki sosai.”
Sai sannan yaran suka gaisheta baki daya ta amsa daya bayan daya.
“Barrister na waje, tare muke.” Fadin Mama Hanifa.
Jin haka Adam ya mike ya fita suka shigo tare, bayan sun gaisa da Umman ya yi mata ya jiki daga nan ya fita. Sosai ya kara yiwa Adam nasiha akan hakuri da lamuran rayuwa. Duk da cewar ba wani mutunci suke sosai da mahaifin Adam din ba sai dai yakan tsinci abubuwa da dama daga yanayin Adam da kuma bakin jama’ar unguwa. Tun ba ya dauka har ya soma gani a zahiri. Daga lokacin yake jin Adam tamkar shi ya haife shi duk da cewar a shekaru bai kai sa’an mahaifinsa ba, zai iya kiransa da kaninsa kasancewarshi sa’an ƙanin nasa.
Sosai nasihar ta ratsa Adam, godiya ya yi mishi. A dalilin dawowar Hashim ya sanya washegari Umma ta dage akan sai dai su sallameta ko ta tattara ta bar asibitin, wannan ta sanya dole Dr Samuel ya rubuta mata takardar sallama sannan suka tafi a motar Adam.
Daidai kofar gidan ya faka motarsa. Umma ta dubeshi.
“Maigadin ba ya nan ne?” Adam bai ce uffan ba, Yaha da tasan dawan garin sai kawai ta bude kofar motar.
“Zai iya yiwuwa, muje ko?”
Ba musu Umma ta bude kofar ta fita. Ya fita ya dubi Umman da idanunsa rinannu, ya yi kokarin ɓoye damuwar ta hanyar jifanta da murmushi.
“Ku shiga, za a turo kayan.”
“Kai me yasa ba za ka shigo ba?”
Ya ɗan kauda kai.
“Akwai aikin da ke jirana.”
Gyada kai kawai ta yi ba don ta yarda ba, karya ba ta kyau a muhallin da ba’a saba da ita ba. Ba’a maisheta abar ado da tinkaho ba. Shigewa ta yi ciki ta barsu tare da Yaha.
“Adamu ka sami Yaya ka ba shi hakuri. Ba za’a tafi a haka ba, ko don lafiyar mahaifiyarka. A yanzu ne ta fi bukatarka a kusa.”
Maganar ya ji ta sosai a ƙoƙon rai, akan mahaifiyarsa ba abinda ba zai iyaba. Shi kansa yana tuna makomarta idan ya kara nisanta daga gareta kamar yanda ya ta6a zamanin da yake rayuwar jami’a. Ya tattare ya koma hostel rankatakaf saboda bakin cikin mahaifinsa.
“Zan san abinda zan yi.” Amsar da ya ba ta kenan, ya taimaka ta fidda duka kayan a mota sannan ya ja abarsa ya yi gaba. Gudu kawai ya ke yi, hon da danna ashar ba irin wanda bai sha ba. A karshe ya nemi gefen titi ya faka. Dukan sitayari ya yi, watakila ajalinsa ne yake kusantoshi, mai yiwuwa mutuwar za ta fi akan irin azabtuwar da ruhinsa ke yi a kullum. Hawaye suka soma kwaranya a saman fuskarsa.
*****
Bilkisu Kabiru Abdallah
Haifaffiyar garin Damaturu ce, Yobe. Mahaifinta Kabir, babban limamin masallacin juma’a ne a garin.
Kabiru shi ne ɗa na tara a wajen Abdallah. Gaba daya yara ne ga Zulaihat wacce ta kasance mace ɗaya tilo a wajensa. Duka suna raye idan ka cire Hassan da Hussaini wadanda suka rasu suna da shekaru bakwai a duniya. Babbar diyarta mace ce, sunanta Hadiza sai Hannatu, Bello, Lawwali, sai Rakiya da auta Kabiru.
Sun taso kansu a hade, asalinsu Fulani ne ba sirki ko kadan. Auratayya ne ya sanya suka samu yare iri-iri a zuri’ar Malam Abdallah. Sana’ar iyalan gidan kasuwancin man shanu da nonon shanu da sauran kayan saƙa sai kuwa noma.
Duk cikinsu ba irin Kabiru a wurin neman ilimin addini da fafutuka. Hakan ya sa ya zama haziki kuma babban Malamin da ake ji da shi. Bello kuwa babu inda ya fi mayar da hankali irin neman ilimin zamani gami da na boko. Yana kokari a kowane fanni sai dai bai kai Kabiru a na addini ba. Wannan ta sanya kai tsaye suke kiran Kabiru da Malam.
Sanadin ilimin boko ya sanya gwamnati daukar nauyin karatun Bello da wasu cikin hazikan dalibai zuwa kasar Ingila karatu. Mahaifinsu Abdallah sam bai hana shi ba. Ƴan uwan abin ya yi musu dadi sosai ba kamar Bello wanda ke ji kamar ya yi tsuntsuwa ya ta6a sararin samaniya.
Suna da shekaru goma sha shida a duniya, Bello ya tafi London karatu iyayensu na mishi fatan alkhairi da samun nasara.
Lawwali ya bada ƙaimi wajen neman ilimi shima na boko da Arabi, karatun zamani ba ya daga cikin burin Kabiru, hakan yasa ko an tura shi boko ba ya zuwa sai dai ya zagaya ya wuce sauraron tafsir. Hakan ya fi komai faranta ransa.
Alokacin yan uwansu mata duk an aurar da su idan ka cire Rakiya wacce itama tana cika shekaru goma sha uku Mahaifinsu ya aurar da ita.
Bayan shekaru masu dan dama, alokacin Abdallah ya rasu, har lokacin Bello bai waiwayi gida ba. Tun su na zuba ido da sa rai har suka fidda. A sanadiyyar kukan rashin sanyashi a ido, mahaifiyarsu ta kamu da ciwon ido. Lokacin daga Lawwali har Kabiru sun ajiye iyali. Yaransu sun tasa sun zama matasa.
Kabiru yana auran diyar abokin mahaifinsu Fatima, ta haifa masa yara uku a lokacin tana dauke da tsohon cikin na hudu.
Lawwali ma yaransa biyar cif a duniya. Ba zato ba tsammani watarana da hantsi suka ji sallamar Bello. Abin da ya basu mamaki ba shi kadai bane yana tare da wata mace da yaro karami. Farko fada sosai ya sha wajen mahaifiyarsa karshe ma ta ce ya tashi ya fita ba ta kaunar ganinsa. Da ban hakuri da roƙo da kuka ya samu dakyar ya shawo kanta. Anan yake jin rasuwar mahaifinsa, ranar ya sha kuka kamar ba gobe.
Bayan gama koke-koke sai kuma aka shiga labarin bayan rabuwa, ya nemi su gafartamasa a irin rayuwar banzar da ya gudanar a baya amma ya tabbatar musu daga baya Allah Ya shiryeshi har ya nufeshi da yin aure. Suka kar6i tubansa, matarsa Halisa da kuma dansa HAYAT. Suna wannan zaman aka isar da sakon haihuwar Fatima ga Kabiru. Ba karamin farin ciki aka shiga ba, Bello nan take ya dubi dan aiken.
“Me aka samu?”
“Ɗiya mace.”
Da dariya ya dubi dansa kafin ya dubi mahaifiyarsa da yan uwansa.
“Ai shikenan, wannan yarinya ta zo mana da alkhairi, In sha Allah ni zan mata huɗuba. Ba ta kuma da miji sai Hayat muddin ina raye in Sha Allah.”
Hatta da Halisa sai da ta dara, ba wanda bai ji dadin wannan furucin na Engineer Bello ba. Albarka mahaifiyarsa ta shiga sanyamasa da fatan Allah Ya tabbatar da alkhairi.
Haka ya yiwa yarinya huduba da suna BILKISU.
*****
Bayan shekaru sun ja sosai, Bilkisu ta zama balagaggiyar mace, alokacin Hayat na Kano yana karatu. Ita kuwa Bilkisu ba ta da karatun da ya wuce na addininta. Mahaifinta ba shi da ra’ayin dora yara mata a turbar ilimin boko.
Ta taso yarinya mai hakuri, da wuya ka ji an yi fada da Bilkisu. Yarinya ce mai sanyi hakanan marar hayaniya. Ba za ka ta6a jin an kai ƙarar Bilkisu ba sai dai a cuceta ƴan uwanta su faɗa. Tsakanin Hashim, Nuhu da Zahra, babu wanda tasu ta fi zuwa daya da Bilkisu irin Hashim. Sun shaku sosai, yakan dau mataki ga duk wanda ya zalunceta. Sanyi da hakurinta ne da kuma biyayya ta sanya duk cikin yaran Kabiru ya fi kaunarta.
Lokacin da ta kai munzalin aure ne ya zuba ido don jin ta inda Bello zai 6ullo da batun aurenta da Hayatu wanda ke dab da kammala karatunsa na likitanci. A wannan lokacin Allah Ya dau ran Zulaihat mahaifiyar su Kabiru.
Kamar da wasa kuwa bayan sati biyu ya riskeshi har gida da batun. Ba karamin farin ciki ya ji ba, ya kuwa yi na’am. Nan take suka sanya ranar aure da zarar Hayat ya kammala karatu don lokacin bai fi mishi watanni ba.
Koda maganar ta je kunnen Bilkisu ba ta da wani ja, ta jima tana jin batun aurenta da ɗan uwanta Hayat. Ta kuma lura ko zuwa ya yi garin da sunan hutu ba ya ko kallon inda take tun sadda ya ji wai ita ake son aura masa. Haka zuciyarsa ta ginu da tsantsar tsanarta.
Bayan kammala karatun Hayat ya dawo gida kowa na mishi murna da fatan alheri. Abinda ya mishi saura bai wuce bautar ƙasa ba. Bayan kammala hutunsa na kwanaki biyu ne, Bello ya tareshi da maganar aurensa da Bilkisu. Nan da nan ya bugi kasa ya ce shi sam bai san da maganar ba. Yana da wacce yake so. Bello ya ce bai isa ba aurensa da Bilkisu kamar anyi an gama.
Babu irin borin da Hayat bai yi ba akan lamarin aurensa da Bilkisu a karshe babu yanda ya iya haka ya hakura bisa furucin mahaifinsa na tsinuwa gareshi muddin bai aureta ba. Da wannan akai auren Bilkisu da Hayat auren gata tun ma kafin Hayat ya kammala bautar ƙasa.
A Kano suka tare inda yake bautar ƙasa, gida mai kyau kuma karami Bello ya gina musu. Zagi da aibatawa ba irin wanda Bilkisu ba ta sha a wurinsa. Ya zageta ya zagi iyayenta, a cewarsa kwadayin dukiyar mahaifinsa ce ta sanya suka dage sai sun ga ya aureta suka ƙi aurar da ita akai zaman jiransa.
Sau da yawa yakan kira abokansa mata da maza, ita zai sa ta yi ta hidimar yi musu girki, ya maidata tamkar baiwa. Haka take hakuri da juriya wajen hidimta masa. Nasihar mahaifinta koyaushe ke sanyawa ta ke jure dukkan cin kashin Hayat. Ya mata gargadi akan kawo ƙarar miji, ya kwadaitar da ita game da hakuri da kuma aljannar da Allah ke sanya ma’abotanta. Ya nuna hakan kadai shi ne sakamakon biyayyar da take musu, ta ninka hakan akan mijinta don anan aljannarnan nata yake. Wannan ya sa ta bar ganin Hayat a kowane matsayi face miji abin yiwa hidima. Burinta koyaushe bai wuce ta samu aljannarnan ba.
A wannan hali sai Allah Ya jarabceshi da sha’awarta har abinda Allah Ya nufa ya tabbata. Ba tausayi ballantana rangwame, haka ya yi mata kaca-kaca ya bar ta anan. Wannan ranar ita ce sadda ta soma jin ya ambaci Salma a bakinsa. Tun lokacin ya maida sunan kamar abin goranta mata. Duk abinda ta yi na kyautatawa zai gwatsaleta ya ce ai da Salma ce da za ta yi wancan ba za ta ta6a yin wannan ba. Tun abin na sosa ranta har ta danne ta hakura. Cikin ikon Allah ta samu ciki. Sai da cikin ya yi watanni biyar sannan Bello ya ziyarcesu tare da Halisa. Koda suka ga yanayinta, suka yanke shawarar turo mata abokiyar zama. A gabansu sai ka rantse Hayat na masifar kaunarta duba da yanda zai nunamata.
Yahanasu diya ce ga Hannatu, bazawara ce da mijinta ya rasu tun tana da kuruciya sai dai har girmana cimmata ba ta samu yin aure ba. Hakanan bata da ɗa ko ɗaya. Duk wanda ya zo da nufin auren sai ya tafi wannan ta sanya ta tattara ta hakura da auren. A wannan lokacin a zuri’ar aka yanke tura ta gidan Bilkisu.
Da farko farkon zuwanta, ta ga kamar dagaske Hayat na kula da Bilkisu yana kyautata mata, sai daga baya ta fahimci ba haka ba. A hankali a hankali kuma ya watsar da dukkan kame-kamen ƙaryar da yake a gaban Yaha ya dawo Hayat dinsa sak. Bayan kammala bautar kasar sa ya samu aiki a babban asibitin koyarwa na Malam.
Cikin Bilkisu da wata tara ta haifi Adam. An sha suna, mutan Yobe sun zo. Har suka yi kwanaki uku suka watse babu wani abu da Hayat ya nuna ga Bilkisu a gabansu. Ita dinma takan biyemishi da yanda ya so gudun kada a kaiwa iyayenta labari marar dadi akan zamantakewarsu. Yaha abu na cin ranta sai dai babu damar cewa uffan.
Bayyana irin rayuwar da Bilkisu ke shaka a zamantakewarta da Hayat abu ne mai matukar tsawo😭. Bayan shekaru uku ta kara haihuwa sai dai abinda ta haifa bai zo da rai ba. Wannan ya sa Hayat fusata, a cewarsa bai ma san ya akai ta samu wani cikin ba don haka ya yi mata tsarin iyali.
Tasowar Adam babu irin cin zarafin da bai ji mahaifinsa na yi ga Umma ba. Kusan kullum sia ya duramata bakin ciki. Wannan ta sa ya tashi da tsanarsa sosai a kasan rai. Ya sha yunkurin sanarwa kakanninsu, alokacin Fatima mahaifiyar Bilki ta rasu, shi kuwa Hashim yana Cairo da zama tare da iyalinsa. Yayinda sauran yan uwan Bilki ke Yobe. Babu damar fadawa kowa bisa kyakkyawan gargaɗin da Umman ta yi mishi. Bayan wasu shekaru kuwa da ta samu cikin yan biyu kasa fadamasa ta yi saboda tsoron abinda zai biyo baya. Shi kansa hankalinsa a sannan ba ya wurinta sakamakon auren da ya gingimo na Salma mai ɗa guda ɗaya, Fu’ad. Ba wanda ya hanashi aure a dangi musamman da suka ji Bilkisu bata da matsala da hakan. Nan ma ya kara shaƙa jin cewa duk wanda ya fadawa batun aure a iyaye to magana ta farko da za’a tambaya Bilkisu ta sani kuma ta amince?
Sai bayan an yi auren a lokacin arzikinsa ya kara ninkuwa ya gyara ginin gidansa ya yi shi babba mai ɓangare-ɓangare, ya lura da cikin dake tattare da Bilkisu. Ranar ta sha mari a karshe ya ce zubarwa zai yi don ya yi rantsuwa da Allah akan bai shirya haihuwa ba. Koda ya ji watannin cikin sai ya ji kamar an watsa mishi garwashi a kahon zuci. Hakan yasa ya fita lamarinta gaba daya. Tun da aka haifi yan biyu bai ta6a kashe koda kwandala saboda su ba. Umma ce ke kokarin basu kulawa da taimakon Adam.
Adam shi ya zama karfin yaran, sai ya ƙi siyan komai a makaranta don kawai ya tara kudin ya siyo koda Pampers ne a sanyamusu. Itama Bilki da taimakon Hashim dake mata aiken kudi akai-akai adalilinsa na kada ta cika tambayar miji kudi zai tsaneta, da su take amfani wurin rufawa yaranta asiri ganin uban ba ya ta6a sanyasu a lamuransa. Hakan ya sa Adam daina tambayar sisin uban, nan kuwa Bilkisu ta ce bai isa ba, wannan yasa ko bai tambaya ba ita ke kar6ar mishi abin bukatu na makaranta koda hakan zai zamo ɓacin rai.
Haka Bilkisu ke rayuwa a gidan, gori akan boko da ma wayewar rayuwa ba irin wadda ba ta gani. Ta jure iyakar juriya, ta shanye abubuwa a shekaru sama da ashirin. Abubuwan da a zamanin da ake ciki yanzu ba wacce za ta iya jura. Tsakaninta da Salma kuwa ko kallon arziki ba ta isheta ba. Takan kirata da Bora a lokuta da dama, hakanan take shanyewa. Yan biyu na da watanni takwas a duniya, Salma da Fu’ad suka tafi London, har yau da yan biyu keda shekaru goma sha uku basu leƙo Nijeriya ba.
Wannan kenan!
A gode Allah yakara