Skip to content
Part 6 of 41 in the Series Rumfar Kara by Rufaida Umar

Magana da ba ta da wuyar ji a karamin gari musamman idan akwai masu taimakon yaɗawa irin su Humaira, nan da nan gari ya dauka yaran Malam mata zasu soma karatu. Wadanda a baya basu yi ba saboda Malam bai yi ba suka soma shirin kai masu yaran ciki kuwa har da gidan Sarkin Dawa wanda kememe ya hana yaransa mata karatu saboda kawai Malam bai saka na gidansa ba. Maikudi ce ta so kawo mishi cikas ta ce sam yara ba zasu yi karatun yahudanci ba. Dakatar ya shawo kanta ta amince.

Da misalin uku da mintoci na yammacin ranar Alhamis, kasancewar ba islamiyya, Humaira ta yada zango a gidan Sarkin Dawa. Da sallamarta ta shiga hannunta leda ce kunshe da garin lalle wanda za’a yi mata na tafiya biki Yobe.

Matan Sarkin Dawa hudu su na zaune a tsakar gidan da yara, daga can gefe Maikudi ce kwance a kofar ɗakinta saman tabarma tana taunar goro. Suka amsa sallamar Humaira.

“Lale da jikalle, maza taho nan mu gaisa.” Cewar Maikudi tana dubanta. Taɓe baki  ta yi.

“Ni yau ba wurinki na zo ba, ai naji furucinki akan bokon da zamu soma. To dai kin ci zamaninki kar ki ɓatamana tamu. Daga ni har jikokin naki boko kamar mun je mun gama da yardar Allah. Atoh!”

Kame baki Maikudi ta yi bayan ta kokarta ta mike zaune.

“Asheee! Ni kike gayawa magana Indo? To don uwarki idan na ga dama da kaina sai na samu shi Malam din da ya dauremuku gaba na hanashi. Aikin wofi me ake da yahudawa? Duk wani ɓatanci da turba marar kyau su ne jagororinta. Shegu matsiyata.”

 Dariya Humaira ta sa, sauran surukan ba damar yi sai ƙasa-ƙasa. Yanzu gigin tsufa ya kara kama Maikudi ta yanda abu kadan zasu yi ta hau fada da zaginsu, karshe ta ce sai ta sa an sake su. Wannan ta sanya suke takatsantsan bisa gargaɗin mijinsu.

“Oho dai, karatu mun yi mun gama. Ni bar ni haka, kunshi na zo a dauramin zamu je Yobe.”

 Sai a sannan Amarya ta yi magana.

“Ke Humaira, yanzu har bikin da Malama ke magana ya zo?”

Humaira ta washe haƙora.

“Eh Amarya, kuma zamu yi sati a can fa. Haka Inno ta cemin.”

“Ah dole ki kunshi, bari na gama tsigar kan nan, da kaina zan sanya miki.” Fadin Amina kenan, matar Sarkin Dawa ta uku wacce a baya sunanta Ta Goma. Murna sosai ya kama Humaira.

Aikuwa tana kammalawa ta soma saka mata lalle. Abinda da farar fata, bayan ta cire kafarta ta yi jazur ta kama. Duban hannunta tayi yanda shima ya kama sosai ta hau dariya.

“Kai Anti Amina kin fiddo ni wallahi. Ni nasan Amaryar ma sai na fi ta kyau.” Dariya suka sanya.

“A’a ɗiyata, wannan irin yabon kai? To shi kuma kitson yaushe za’a yi?”

Tana dariya ta amsawa Hajara uwargidan Sarkin Dawa wacce a baya ake kira da Fanteka.

“Ai Anti Karima ce za ta yimin. Ta wanke min gashin, kin gani.” Ta zame ɗankwalinta, bakin gashinta wuluk ya fito. A cike yake taf sai dai babu relaxer ko kadan. Ba shi da laushi sai tsawo da cika.

“Eh lallai kam Karima za ta fiddo ki.” Sukai murmushi.

Ba ta wani jima ba ta yi musu sallama kasancewar gidan ba sa’anninta sosai, daga wanda ta girmewa sai wadanda suka girmeta da kadan. Sa’anta namiji ne, wannan ya sa ba ta fiye shigowa gidan ba sai jifa-jifa ta zo ta ja Maikudi ta fice abinta.

Tun daga nesa ta hango majalisar su Yakubu. Wani tsaki ta ja, ba don sun riga sun hangota ba abinda zai hanata sauya hanya ba. A duniya ba wanda ta tsana irin Yakubu saboda mutum ne da tarbiyyarsa sai a hankali. Ga shi ya takura mata, shi a lallai nan duniya bai ga abar so da kauna sama da ita ba. Dauke kai ta yi ta ci gaba da tafiya. Ta wuce majalisarsu da kadan ta ji an sha gabanta. Ko ba’a fada ba ta san shi ne mai wannan aikin, sai zatonta ya zama gaske sa’ilin da suka haɗa idanu. Harara ta banka masa, shi kuwa sai ya bita da murmushinsa mai kama da mai nishin kashi.

“Malama Aisha Humaira, abin har ya kai a ganni a kauda kai? Kauna ba ta ce haka ba.”

Ta ja karamin tsaki da ɗan karamin bakinta.

“An dauke kan, ni kallo ba ka ishe ni ba ballantana na tsaya magana da kai. Banda lokacinka sai anjima.”

Ta gota shi za ta wuce ya kara shan gabanta. Ta kulu iyakar ƙuluwa.

“Ka fita hanyata Yakubu, Ni ba sa’ar ka ba ce don na fi karfinka wallahi. Kana 6ata lokacinka ne kawai.”

Ya yi dariya, hakoransa masu kalar masara suka bayyana a fili. Ta ji amai na shirin tasomata hakan yasa ta tofar da yawu a gefe.

“Ki bar ganin ina lalla6aki, wallahi ba karamin aikina bane na yi miki hukuncin da ba za ki ta6a mantawa ba. Don ma kin ci sa’a kamar ni ɗan Salihu Attajiri ina sonki shi ne kike wani taƙama kike tunanin kin fi karfina? Da dai ace ba’a san asalin balbale ba ne.”

Ba ta fahimci komai a karin maganar da ya yi ba, wannan ta sanya ta kara gifta shi  ta wuce ba ta ce uffan ba. Ba ta yi aune bata ji ya rike gyalenta.

“Kut!” Ta furta sannan ta durkusa ta ɗebi ƙasa ta watsa mishi a fuska. Ganin ya tsaya mirza idanu abokansa suka taso suka nufota. Da gudu ta bar wurin, tana yi tana waige har ta isa gida. Ganin yanda ta faɗo gidan ne ya tabbatarwa mutan gidan ta yi abinda ta saba, wato neman tsokana.

Tana haki ta ke dubansu sai kuma ta nutsu.

“Wa kika jibga kuma yau?” Inno ta jefamata tambayar, shigowar Malam ta sanya suka maida hankali kansa suna amsa sallama. Kai tsaye ya nufo inda take.

“Ina zaune na ga shigowar ta a guje shiyasa na zo naji meke faruwa. Ke, wa ya biyoki haka?”

Malam ya ƙarashe yana dauke idanunsa daga kan Inno zuwa na Humaira.

“Haba Malam, Humaira da ba ta rabo da tsokana kuma ka tambayi wa ya biyota? Ai idan dai wannan yarinyar ce, to idan ka bincika ita ce ba ta da gaskiyar.”

Humaira ta ɗan turo baki a shagwaɓance ta ce.

“Wallahi Inno ba ruwana, Yakubu ne fa dan gidan Attajiri ya kama min gyale ni kuma sai na watsa mishi ƙasa a ido shi ne abokansa suka biyo ni zasu kamani na gudu.”

“Shi Yakubun?” Malam ya fadi a fusace.

Ta gyaɗa kai.

“Eh, dama haka yake min idan ya ganni wai yana sona, ni kuma karatu zan yi.”

Girgiza kai Maryam ta yi kawai ba ta ko kallesu ba. Malam ya yi ta fada a karshe ya ce da kansa zai je ya sami Alhaji Salihu ya ce ya gargadi ɗansa akan Humaira. Da wannan aka bar batun.

A ranar aka yi mata kitso kananu masu kyau, Jamila ma ta sha kunshi da kitso abinta ta yi shar. Tafiyarsu ta zo daidai da zuwan Umar Maiduguri domin soma shirye-shiryen tafiya. 

Umar da sassafe ya yi sammako zuwa cikin birnin Maiduguri yayinda su kuwa sai wurin karfe hudu na yammacin ranar suka tafi. Biyar da mintoci suna cikin garin Damaturu, Yobe. Bakin Humaira ya ƙi rufuwa. Kowannensu fuska fal da fara’a.

Unguwar Shagari, nan suka yada zango a gidan Alhaji Labaran. Mijin babbar aminiyar Inno kuma diyar makwafci ga Malam Zubair wanda akai zaman mutunci tare a baya, Hajiya Hafsatu.  Auren autarta a mata, Nuriyyah ne silar zuwansu garin.

Gida ne ginin zamani har da bene, bai zama sabon abu a wurin su Humaira ba ganin ginin bene don ko a Kauyen Cinnaku akwai gidan Alhaji Salihu Attajiri. Sai dai duk kyawun gidan Alhaji Salihu, bai kama kafar wannan ba. Ya burgesu sosai, Humaira ta dubi Jamila ta ga yanda ta saki baki. Da hannu ta kai mata dunguri. Cikin raɗa-raɗa ta ce.

“Kefa ba ki da wayo, so kike a yi mana kallon kauyawa? Idan an zo irin nan mazewa ake a tafi da zamani.”

Jin haka Jamila ta kama kanta bayan ta dubi Humaira ta ga yanda ta haɗe fuska ta na tafiyar taƙama.

Da sallama suka shiga, ganin Inno nan yaran gidan suka soma oyoyo. Abin sai ya burge Maryam, ta tuna sadda Inno ke yawan cewa za ta je garin, ba ta ta6a marmarin biyota ba, takan dai ji Inno na bayanin karamcinsu da irin kaunar da Hajiya Hafsatu ke mata. Ita shaida ce akan wannan domin ta ta6a zuwa kauyen har sai uku kawai don ta ga Inno, ba kuma ta zuwa hannu rabbana sai da abin arziki. Kullum fatanta Allah Ya bayyanawa Inno iyayenta da har yau babu labarinsu.

“Kin gani ko? Ba su fi mu ma da komai ba. Mu ma akwai hancin da farin.” Humaira ta kara yin raɗa a  kunnen Jamila, wannan karon harara Jamilar ta watsamata. Sai a sannan Humaira ta karewa hancin Jamilar kallo ta tuntsire da dariya. Dariyarta ce ta sanya jama’ar wurin kallonsu sai dai fitowar Amaryar a guje ta fada jikin Inno shi ne ya yi sanadin da aka maida hankalin kanta. Kyakkyawar budurwa mai shekaru ashirin a duniya. Kallo daya za ka yi mata ka fahimci dagaske Amarya take sakamakon gogewar da fatarta ta yi, ga wani kamshi na musamman da ke tashi a jikinta.

“Na yi fushi fa Inno.” Da dariya Inno ta amsa.

“Haba diyar albarka, autar Inno da Hajiya, a yimin uzuri Amarsu, ai ba don ma na ji ƙamshi ba da ba zan gane ki ba tsabar kyau.” Sai kuma ta saketa ta ruga ciki a guje, aka sa dariya. Humaira ta rike baki.

“Oh ni, wata ta6arar sai a birni, wannan goɗoɗuwar budurwa nono fal kirji take gudu kamar barewa?”

Ba zato ta ji an kai mata bugu a baki, ganin Mamarta ce sai ta nutsu, sam ba ta yi zaton ta ji ba. Ciki suka ƙarasa, anan ma falon wasu mata ne kusan goma. Iyaye da yan mata, zamansu ba wuya ana gaisawa. Wata hamshakiyar mace ta fito daga wani dan corridor.

“Lale lale da aminiyar kwarai, yar uwa rabin jiki” Tuni Inno ta mike su na dariya suka rungume juna. Mutanen wajen na dariya.  Wata cikin manyan iyayen ta mike zaune daga kishingiɗar da ta yi.

“Wai kar ku cemin Fatimar Malam Zubairu ce wannan ?”

“Ita ce, ba ku gane juna ba?” Hajiya Hafsatu ta furta da dariya. Inno ta yi tsai tana duban matar sai kuma ta hau salati ta karasa ta mike mata hannu su na dariya.

“Kamar Hamida dai ta gidan Malam Bala? Innalillahi wa inna ilaihir raajiun! Ta ina zan ganeki kin kara hawa kamar wacce ake hurawa?”

Suka yi dariya, Humaira dai ta lura babu wani shan ƙamshi anan, hakan yasa ta saki jiki gami da sakin fuska.

Hajiya Hafsatu ta zauna suna gaisawa da Maryam, tasan kaɗan daga labarinta a wurin Inno. Daga nan aka gaggaisa kuma aka shiga hira. Sai a sannan Humaira da Jamila suka gaishesu. Hankalin Hajiya Hafsatu ya koma kansu. Da murmushi ta amsa tana duban Inno.

“Fatima wacece Humaira anan?”

Inno dake hirar yaushe rabo da Hajiya Hamidah, ta juyo tana dariya.

“Ashe ba ki manta ɗiyartaki ba, to canki idan ba ki canka daidai ba sai ki bani gari.”

Jin haka Humaira da Jamila suka murmusa, ido ya koma kansu. Maryam dai kanta a kasa tana murmushi.

Da yatsa Hajiya Hafsatu ta nuna Humaira.

“Kamar dai ƴar fararnan ce, mai kama da Fulani.”

Suka yi dariya.

“Lallai kin canka daidai, to ita ce. Wannan kuma Jamila diyar ɗanki ce.”

“Shakka babu girma ya ƙara kama mu fa, Allah Ya rayamana su mu sha biki wataran.” Aka amsa da ameen. Daga nan ta sa aka kai su zuwa masauki. Humaira aka kara dakewa gudun kada ayi kauyanci.

Inno na can suna hira su kuwa aka kai su lafiyayyan daki, an shimfida katifu a saman carpet din dake malale a tsakar wurin. Ko’ina tsaf, hakanan banɗakin dake wurin. Bikin alokacin saura kwanaki uku cif a soma. Wannan ta sanya ba mutane sosai.

*****

Ta duba agogo ya fi a kirga, ta gaji ta fito falon inda su Amira ke zaune tare da Yaha.

“Wai Adam bai dawo bane? Na kira wayoyinsu a kashe, lafiya kuwa?”

Ta bata tausayi, ta kasa magana. Umma ta lura kamar akwai abinda Yaha ke 6oyemata.

“Ki fadamin Yaha, ko hatsari ya yi ne?”

Sai sannan ta girgiza kai da ƴar dariya.

“Ko kusa, Adamu ya yi hatsari kin ganni zaune haka? Kin manta ne idan zai shiga operation kashe wayoyinsa yake?”

Ta numfasa.

“Amma duk sadda Adam zai shiga tiyata, sai ya sanar da Ni koda ta text ne domin na yi mishi addu’a da fatan nasara.”

“Mai yiwuwa dai wannan karon ta gaggawa ce. Ni kuwa me su Yaya Hashim sun taho?”

Ta furta don ta dauke hankalin Umma daga tambayar inda Adam ya shiga.

“Eh sun ta so, zuwa karfe tara in Sha Allah su na Kano. Zamu je tarbarsu. Maganar da nake nema na yiwa yaronnan kenan.”

“In dai Adam ne yana sane, wuyarta ya shigo gidan.”

Umma ta jinjina kai. A ranar Yaha ita ce karfin aikin, Amira da basu je makaranta ba ita ke taimaka mata ganin Umma ba ta gama warware wa ba.

Girki har kala biyu sukai sai abin sha. Bayan sun kammala Yaha ta miƙa Amira makwafta gidan kitso, a wannan lokacin Umma ta kara gwada kiran Adam cikin sa’a ya shiga. Haka ya yi ta ringing ba amsa har sau wajen biyar.

Lokacin yana gidansa na cikin asibiti kwance saman gado. Lamarin mahaifiyarsa ke damunsa ba shi da walwala ko kaɗan. Yana sane ya kashe wayoyinsa adalilin ba shi da abinda zai fadamata, ba ya kaunar tada mata hankali a banza. Tunawa da ya yi da batun dawowar su Uncle Hashim ne ya sanyashi kunna wayar. Tun ma kafin ya kammala abinda zai yi, kira daga ofis ya soma shigowa akan ana bukatarsa. Nan da nan ya mike ya shiga wanka. Ko bayan kammala shiri ya tadda missedcalls na Umma. Yasan za’a rina, daurewa ya yi ya danna kira. Ba ta wani jima tana ringing ba aka amsa.

“Haba Adam, lafiya kuwa? Ina kira a kashe, na kuma kira ya shiga ba amsa?” Umman ta furta cike da damuwa.

 Ya ƙaƙalo murmushi yana mai shafa kwantacciyar sumarsa.

“Ki yi hakuri Umma, na dan shiga busy amma in Sha Allah zan shigo anjima muje Airport.”

Ta sauke ajiyar zuciya cikin kwanciyar hankali.

“To amma Adam ba haka ka sanar mini ba, duk sadda kake cikin aiki, ka kan kirani ka faɗamin. Me ya dauke hankalinka har haka?”

Shiru ya yi, ba zai iya ce mata ga dalili ba. Ya daure ya amsa.

“Ki yi hakuri.”

Ita dinma ba ta kara cewa uffan ba sakamakon Hayat da ya shigo ya yi mata kerere. Dakyar ta daure ta ce.

“Shikenan, sai ka zo din.”

Tana kashe wayar ya dubeta.

“Ina fatan ba wannan yaron kike shirin gayyato min ba?”

Yasan ba zai damu da ya ji ingancin lafiyarta ba, hakan yasa maganar da ya faɗi ta daure mata kai.

“Bangane ba, da Adam nake waya.”

Ya harɗe fuska sosai.

“Ai nasan da wanda kike wayar shiyasa nake gargadinki akan gayyatomin shi muhallina don kuwa har abada ba ni ba shi, kar ki tsammaci zan bari ya ƙara takomin gida! Daga yau idan ni ne ubansa to na rabashi da gidana har abada! Tunda ba shi da mutunci bai san kunya ba saboda ba ita ya gani ya koya ba!”

Ya ƙarashe yana mai daga murya da hayayyako mata kamar zai cinyeta ɗanye.

“Kai a wa?! Hayatu nace kai a wa? A wace isar?!!”

Shiru kamar anyi ruwa an dauke. Ya tsaya galala yana kallonta, ji yake kamar mafarki yake da sai an farkar da shi zai mike. Idan ba kunnuwansa ne suka yi mishi karya ba, kamar Bilkisu ce ke kokarin maida mishi martani a yau?

Mamakinsa ya ƙaru alokacin da ta ci gaba da magana cikin ɗaya murya, jikinta har wani rawa yake tamkar mazari yayinda idanunta suka kankance.

“Baka isa ba! Wallahil Azim ka yi kaɗan Hayatu! Ka yiwa Amir da Amira na jure, amma ba ka isa ka hanamin ɗa taka gidan ubansa ba! An fadamaka don kai nake zaune? Toh bude kunnenka dakyau ka ji! Zama nake a gidannan domin ƴaƴana, da kuma biyayyar iyaye. Idan babu wadannan ba abinda zai kara zaunar da Bilkisu a gidanka! Don haka wallahi Allah ka dage akan cewa Adam ba zai dawo ba to ka kwana da sanin ni Bilkisu na bar gidanka har karshen abada. Ina da zuciya! Nasan abinda nake.”

Ya tsorata ba kaɗan ba, sai dai anan yana bukatar amfani da kwanjinsa a matsayinsa na ɗa namiji don haka sai ya yi ta maza ya soma ɓaɓatu.

“Aikin banza da wofi! Idan an ce wajenki yara suke koyon rashin kunya sai ki hau ladabin karya da munafunci. An fadamaki bansan meke riƙe dake a gidana ba? To na jima da sani shiyasa ba wani abu da za ki yi ki burgeni a rayuwa. Na jima da sanin dukiyata kike yiwa, yau kuma da ya kasance na kori magajin daga gidana sai hankalinki ya tashi. To ahir dinki daga ke har yarannaki. Na faɗa na kuma ƙara, Adamu ba zai kara tako kofar gidana ba balle harabar. Ki yi duk abinda za ki yi amma ki sani, yaron nan ya sa ƙafa ya shigo gidannan to Bilkisu A BAKIN AURENKI!

Daga haka ya fice yana mai ji a ransa ba yau ne na farko yana korarta ba, wannan karon ma za’ayi abinda aka saba, ƙin tafiyarta.

Umma ta bishi da kallo, yau hawayen babu koda ɗigo face wani zafi da take ji kamar ana hura wuta a kahon zuciyarta. Ta kudurce a ranta muddin ta sa ƙafa ta fita daga gidan Hayat ta fita kenan, ta sa a ranta ko duka duniya za ta haɗemata kai, ba su isa tsayar da ita daga ƙudurinta ba. Tsuma kawai take tana jiran dawowar Adam gidan. Tana ji a zuciyarta ba wanda ta tsana sama da shi. Dakyar ta daure ta dawo da walwalarta. Ta yi niyyar kiran Adam ta mishi maganar sai dai ta share akan sai sun haɗu. Bayan sallar isha’i ya kirata a waya ya sanarmata ya iso acewarsa gudun kar su ɓata lokaci ba zai shigo gidan ba. Su Amira ta tura da Yaha ta ce ita kam za ta yi jiransu. Da ta kara tambayar Hayat iznin zuwa wani wurin ta gwammace ta zauna kar ta je ko’ina. Adam ya dauka wani laifin ya kara da bai ga Umma ba, sai da ya kirata waya ta sake sosai ta tabbatar mishi babu komai sannan ya samun nutsuwar tafiya.

Baƙin mutum kuma giant, ga tsawo ga jiki mai kyau. Yana sanye da doguwar jallabiya mai kyau da tsada. Matarsa Khalisat, farar mace mai madaidaicin tsawo ta yi kyau cikin bakar abayarta. Tana rike da karamar diyarta a hannu, Jidda. A gefenta wani saurayi ne wanda koda Adam ya girmeshi ba zai fi da shekaru biyu ba. Yana sanye da kananan kaya, ya rufe kwayoyin idanunsa da farin gilashi. Hannunsa rike da na wata ƴar yarinya mai shekaru bakwai cif a duniya. An mata ado cikin doguwar riga gown yar kanta wanda da kadan ta wuce gwuiwarta sai dogon leggings fari ƙal da ta sanya. Kanta kuwa duk da cewa rufe yake da hula bai hana mutum hango siraran kitsonta ta gefen fuska ba. Sai washe baki take tana ɗane hannun ɗan uwanta tana washe baki.

Yana daga wurin tarbar baƙi yana ƙare musu kallo, iyakar burgewa sun burgeshi. A kallo ɗaya ya fahimci tarin so da kaunar dake tsakanin zuri’ar. Ganin sun soma waige-waige har Uncle Hashim ya ciro waya sai ya nufesu shima fuska a sake.

Uncle Hashim ya tsaya yana karemishi kallo, photocopy din Bilkisu kanwarsa yake gani, bambancinsu wannan ƙirar ta maza2 ce hakazalika namijin ne. Kyawun da yanayin murmushi har ma da hasken fatar duka nata ne. Tun ma kafin ya ƙaraso, Uncle Hashim ya ƙarasa suka rungume juna suna dariyar farin ciki. Ya sake shi ya riƙe hannun gam kamar wanda ake shirin rabasu.

“My beloved Son, Dr Adam Hayat Ibrahim!”

Kasancewar yana cikin farin cikin ganin Kawunsa, wannan ta sanya koda wasa bai ji rashin dadin hada sunansa da na Hayat da akai a wuri guda ba.

<< Rumfar Kara 5Rumfar Kara 7 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.