Ya dubi sashin da Anti Khalisat take. Ya gaisheta sa’ilin da ya sa hannu zai kar6i Jidda. Ta kuwa noƙe akai dariya.
“Lallai yau naga ɗan gidan Abbun Kyautar, ashe zanƙalelan saurayi ne har haka, Masha Allah.” Adam ya yi dariya sosai yana shafa karamin gashin da ke haɓansa.
“My brother.” Saurayin nan ya furta yana duban Adam da murmushi, har kasan ransa ya ji kaunarsa sosai. Ba shi da wani dan uwa da zai kira da nashi na jini. Hakan yasa sunan ya kwanta masa. Ya miƙa hannu suka gaisa.
“Shuraim, am I right?”
Saurayin ya gyada kai yana dariya.
“Na’am.” Ya amsa da harshen larabci. Adam ya ja shi suka dan rungume juna cike da farin ciki sannan suka rabu.
“Akhee, nifa?”
Ya dubi yar yarinyar, ganin yanda take noƙe kafaɗa gani da tura baki ya sanya shi dariya gami da ɗagata cak.
“Ta ya zan manta da wannan beautiful angel din? Jira nake na gama da wannan yayannaki.”
Ta kara washe bakinta, a karshe suka dunguma gaba daya suka nufi wurin mota inda anan Yaha da su Amira ke tsaye. Amira ta ci ado cikin riga da wando ta ɗora afterdress a samansa. Kirjin ya soma tasawa kaɗan, alamun ƙirar budurci ta soma bayyanarmata. Amir kuwa koriyar riga da bakin wando na jeans ne a jikinsa.
Suna isa Yaha ta shiga washe haƙora tana kallon dan uwanta. Koda ta gaisheshi bai ganeta ba sai dai ya mata ƙuri yana bibiyarta da kallon sani. Ya nuna ta da yatsa.
“Kamar na san fuskarnan.”
“Ka sanni Yaya Hashim, Yahanasu ce diyar Baba Hannatu.” Sai kuma aka shiga sabuwar gaisuwa. Shuraim ya kurawa Amira ido, tun tana mishi murmushi har sai da ta ji haushi, ta watsa mishi harara ya kuwa tuntsire da dariya. Suka dubeshi, shafar lallausan gashin kansa ya yi irin na Khalisat ya ɗan ɗaga ƙafaɗa. Amira bata kara kallon inda yake ba. Bayan haka gaishe-gaishe suka dunguma gaba daya cikin mota wanda tuni an ɗura kayayyinsu a Boot, sai gidan Dr Hayat.
*****
Sai safa da marwa take yi, zuciyarta na cike da zumuɗin son ganin ɗan uwanta wanda suka haura sama da shekaru rabonsu da juna. Bini-bini sai ta karasa jikin window ta ɗan ɗaga labule ta duba, da ta gaji ta nemi wuri ta yi zamanta saman kujera. Ba jimawa ta ji ƙarar tsayuwar mota, ta mike kuwa, Adam ne ya faka a kofar gidan. Hijab kawai ta zura ta fito tana wani irin fara’a wanda rabonta da irinta tun ranar da burinta ita da Adam ya cika na zamtowarsa kwararren likitan gynea.
Maigadin ya taso da sauri ganinta ta fito.
“Ranki ya daɗe.”
“Budemin gate.” Ba musu ya ɗan bude kofar sannan ya dawo jiki a sanyaye.
“Kiyi hakuri Ranki ya daɗe, Dakta ya hana na budewa Adamu kofa.” Jinjina kai kawai ta yi tana mai jin tsanar Hayat, ta sa kai ta fita daga gidan. Hashim wanda ke tsaye yana duban Adam da ba shi da niyyar shiga gidan hankalinsa ya dauke da ya ji muryar yar uwarsa na ambaton sunan da ta saba kiransa da shi
“Hamma.”
Ya juyo suka dubi juna, da saurinta ta zo ta rungumeshi sai kuka mai karya zuciya, kukan da ya ta6a zuciyarsa ya kuma ta6a na ma’abota gidan wadanda sun san komai dangane da kalar rayuwar da take fuskanta.
Ganin kukan zai yi yawa Hashim ya dago fuskarta, idanunsa sun kaɗa, kukanta ya saka zuciyarsa cikin tunani, yana bukatar amsoshi da yawa dangane da hakan sai dai ya shanye zuwa lokacin da zuciyar za ta nutsu.
“So kike dai mu juya mu koma inda muka fito da alama Kanwata. To ke kin ji, kanwartamu ba ta maraba da mu.” Ya ƙarashe da dariya yana duban Anti Khalisat. Aka dan dara sannan ta share fuskarta tana ƴar dariyar. Adam da ya koma sashin boot ya wayance da fiddo kayansu yana miƙa wa Maigadi da Yaha ya yi murmushi kawai, a karshe ya sa hannu a aljihu ya ciro bakin gilashinsa ya kwama a idon. Sai da ya kammala cire kayan kaf, a lokacin su Khalisat da yara duka an shige ciki, daga Umman sai Hashim da shi, ya zagayo ya dubi Umma yana murmushi.
“Bari naje asibiti ana nemana.”
Harara ta banka mishi wanda ta kusan ba shi dariya don bai yi kyau da mai sanyin hali irinta ba. Kafin ma ta kai ga magana Hashim ya rigata yana girgiza yatsa.
“A’a, wannan tatsuniya ce fa, ai yau sai fatan Allah Ya ba patient lafiya, sauran likitocin su yi nasu iyawar. Yau hira zan yi da ɗana don haka muje.”
Zai yi gardama Umma dakatar da shi sanin da ta yi rufa-rufa kawai yake.
“Kaga wuce mu shiga ciki, ina da labarin komai daga Babanku, kada ka damu.”
Ba don ita din ba ce da ya yi rantsuwar ba zai sake taka gidan wannan mutumin ba, sai dai ba gwanin tsallake umarninta ne ba shi, ya danna lock ya rufe motar suka dunguma gaba daya zuwa ciki. Umma na shiga tana tuno yanda suka yi da Hayat, tana kuma kara sanin matsayin da take a yanzun, ta tashi daga matar aure zuwa bazawara. A hankali ta ji wannan kunar zuciyar na taso mata, ta daure ta kara rike hannun dan uwanta. Suka dubi juna su ka murmusa alokaci guda suka maida kai ga kofa. Hashim ya gama tabbatar da zarginsa, akwai tarin damuwa a rayuwar Bilkisu, ba zai takura mata ba yanzun, a hankali yasan za ta warware mishi zare da abawa.
Bayan sun huta sun ci abinci sannan aka kai su masauki. Sai a sannan Hashim da Bilkisu suka yi zaman hira, a lokacin Adam ya wuce. Sun rabu akan ya shigo da wuri don su samu su tafi Yobe da wuri. Umma hakanan ta hakura da maganar da ta so su yi ganin idanun Yaya Hashim a kanta.
“Bilkisu mai gadon zinari, bani labari toh? Ina Mijin naki?”
Ta daure ta ƙaƙalo murmushi.
“Ba ya nan.” Ta amsa kai tsaye domin dagasken ma ba ta san inda yake ba tun bayan da suka yi wannan ƴar hayaniyar ya fice daga gidan ma gaba daya.
“Meke damunki? Kin rame kin sauya kamar ba wannan Bilkisun da na sani ba a baya. Menene har haka ya chanjaki lokaci guda? Ko wani cikin gareki?”
Tambayar karshe sai ta bata dariya, don haka ta sunkuyar da kai tana murmushi, shiru ya biyo baya. Bai yi aune ba ya ga hawayenta na ɗiga saman hannunta.
“Na sani, tun zubar hawayenki na farko nasan Kanwata na cikin wata damuwa. Abin tsoron shi ne tun yaushe ki ke ciki?”
Ta dago da mamaki ta dubeshi. Ya yi murmushi mai ciwo gami da gyaɗa kai.
“Na’am, kinsan ko Nuhu da Zahra’u baza su faɗamin wacece Bilkisu ba. Kukanki, murmushinki, dariyarki, damuwarki. Ba wanda zai rufu a wurina da iznin Allah.”
Kawai sai ta fashe da kukan, yi take ba ƙaƙƙautawa. Ya yi shiru, bai hanata ba, bai kuma katse ta ba, sai da ta yi son ranta ta soma sakin ajiyar zuciya san nan ya zura hannu cikin dogon wandonsa ya zaro hankicif ya miƙamata. Ta kar6a ta share hawayen. Tiryan-tiryan ta shiga karanto mishi irin rayuwa da ta fuskanta a zamantakewarta da Hayat. Tun yana ji daga zaune yana umm, umm, har ya mike tsaye yana sinturi da gyaɗa kai. Idanunsa sun ji jazur har da ɗigar kwallah yayinda jijiyoyin kansa suka tashi.
“Innalillahi wa inna ilaihir raajiun!” Ya maimaita sau uku kafin ya zauna yana kallonta.
“Bilkisu ki kai irin wannan rayuwar amman ko sau ɗaya ba ki faɗamin ba? Ba ki tuna da ni Hashim ba koda ace ba za ki iya furtawa ga iyayenmu ba? Kina kuwa da hankali?”
Ya ƙarashe a tsawance. Sai kuma ya shiga faɗa, faɗa sosai da dukkan muryarsa. Hankalinta ya tashi ganin wani abin bai ma san me ya faɗi ba. Ba ta kara tsinkewa ba sai da ta ji ya kunduma ashar ta tabbatar ya dauki zafi. A rikice ta mike ta durkushe a gabanshi gami da rike kafafunsa.
“Ka yiwa Allah ka rufan asiri ka yi shiru. Hamma kar mu tashi hankulan mutan gidannan.” Ta fadi da a raunane. Sai kuma ya yi shiru ya koma ya zauna yana kwafa.
“Kin min laifi Bilkisu, kin cutar da rayuwarki kin cutar da mu yan uwanki. Wallahil azim koda Hayat bai kai ga sakinki ba ina mai rantsuwa da Allah sai ya sake ki koda bai shirya ba. Koda ace karshenta kotu zamu shiga sai dai a shiga. Yanzun ma ba zan bar shi ba domin kuwa maganarnan sai ta kai ga iyaye. Sai an daukarmaki fansar wannan zalunci da tauye hakkin. Shakka babu kin yi hakuri, kin yi inada Bilki, domin inada yaƙinin kaf danginmu babu wanda zai iya wannan hakurin. Kin nuna ke mace ce mai tarbiyya, kin nuna son yaranki akan kanki. To mu muna sonki, ba zamu bar rayuwarki ta ci gaba da gudana haka ba tunda yanzu mun san halin da kike ciki. Zamu share maki hawayenki In Sha Allah. Bilkisu kin cancanci dukkan farin ciki, wallahi kina daga cikin mata yan aljanna.”
Hashim kusan raba dare suka yi magana guda, a karshe dakyar ta roƙe shi ya tafi makwanci sannan itama ta shiga daki. Sai da ta yi nafila ta mika godiyarta ga Allah tana mai jin kamar an ɗaukemata wani gungumeman dutse mai nauyi a zuciyarta.
Safiyar washegari gaba dayansu su na zaune su na karyawa, duk motsinta Hashim zai tambaya me take bukata. Amira kuwa tana a saitin Shuraim, duk ɗagowar da za ta yi idanunsa a kanta, ta daure fuska tana kara jin kanta kamar cikakkiyar budurwa ta sauke kanta ba ta ƙara ɗagowa ba.
“Sis, wannan ya fiye kallo.” Amir ya faɗi saitin kunnenta. Ta taɓe baki gami da amsawa ƙasa-ƙasa.
“Eh wallahi, duk ya takuramin.” Amir ya ƙunshe baki yana dariya.
“Abi, twins ɗinka sun haɗe kai su na gulmata.” Shuraim ya furta idanunsa akan su. Lokaci guda suka dubeshi gami da zato ido, karshe suka maida idanunsu ga Hashim. Sai suka ba mutan gurin dariya. A haka Adam ya shigo falon ya iske su. Bayan sun gaisa shima ya ja kujera ya zauna. Ya miƙa wa Shuraim hannu suka yi musabaha.
“Ni fa?” Khairat ta ƙara faɗi. Adam na dariya ya amsa.
“Da alama wannan ƴar adawarka ce, kamar komai akai maka za ta nemi nata ko?” Shuraim ya ɗan ja kunnenta ta yi ƙara kaɗan.
“Ai wannan yarinyar haka take, wuyarta a ce Shuraim zo, Shuraim Bismillah. Kamar wani abokin kishinta.”
Ta turo baki gami da kokarin miƙewa, da sauri Adam ya rike hannunta ya maida ya zaunar yana ƴar dariya.
“Afuwan Kanwata, shareshi kinji? Bari kiga tsarabar da na kawomaki.” Ya zura hannu aljihu ya fiddo kwalin cingam din Orbit ya miƙamata. Ta kar6a ta hau dariya.
“Shukran Ya Akhee.” Ta furta tana langaɓar da kai, ta basu dariya gaba ɗaya.
Bayan gaba ɗaya an kammala aka hau shirin tafiya. Kasancewar a kimtse suke, kayan kawai suka shiga fitarwa. Adam na mamakin yanda Umma ta loda kaya, ga nata ga na yara. Ya dubi kayan sannan ya dubeta, ta yi murmushi wanda bai gane manufarsa ba. Yasan dai ba burinsa ne ya cika ba don haka ya kauda tunanin yana taya direban motar da zai kaisu jera kayan a Boot, Shuraim ma ya shiga tayasu.
Bai yi aune ba ya ji an dafa kafaɗarsa an bubbuga, Hashim ne.
“Kamin laifi, kasan da hakan ko?” Ya yi shiru don bai gane ba, shima bai ƙara komai ba ya yi gaba ya kyaleshi.
A daidai kofar gidan Malam Kabir Abdallah motarsu ta yi parking. Fitowar Bilkisu ce ta ankarar da yaran wurin ko su wanene don tun jiya ta yi waya. Fuskarta kuma ba ɓoyayya ba ce ga samarin dake kofar gidan. Jin sunan da manyan suka ambata sai yaran suka ɗunguma a guje zuwa cikin gidan su na shelar zuwan Anti Bilki da Kawu Hashim.
Tun a kofar gidan wasu a cikin matan suka soma fitowa tarbarsu, haka har aka shiga tsakar gidan inda sauran jama’ar gidan kenan. Nan aka hau ina ka saka ina ka ajiye da su. Gwaggo Kubra (matar da Malam ya aura bayan rasuwar mahaifiyar su Bilkisu), sai ka rantse ita ta haifesu domin ba ta nuna bambanci tsakaninsu da wadanda ta haifa su biyu.
Zafi yake ji, gaba daya jinsa yake a takura hakan yasa ya nemi zuwa masauki. Ba musu Gwaggo ta sa Ashiru yaron wurinta kuma auta ya mishi rakiya. Wurin tsaf da shi, ya na karewa dakin kallo yana mai jinjina ga Uncle Hashim sanin da ya yi duk aikinsa ne gyaran gidan. Kayan jikinsa ya rage ya faɗa banɗaki, bayan ya fito ya zauna bakin katifa yana duban wayarsa dake faman ƙara. Ba shi da niyyar ɗagawa sanin ko wacece mai kiran. Dr Zainab ce, ya na da tabbacin ba wani muhimmin abu da ya shafi aiki za ta faɗa masa ba hakan ya sanya ko kallon wayar bai ƙara ba. Karshe da ta ke neman takura rayuwarsa ya sa hannu ya kashe wayar baki ɗaya.
A hankali ya lumshe idanu yana shafar sumarsa. Burin Umma ya yi aure, sai dai bai gama tantance matar da yake so ba, asalima bai iya soyayyar ba saboda har yanzun babu matar da ya ke ganin zai iya aura har ya zauna da ita.
Aminu Kano International Airport.
2pm
Babbar mace ƴar gayu wacce ta iya ado da kwalliya. Tana sanye da doguwar riga ta abaya kalar maroon, ta yane kanta da ɗankwalin abayar, fuskarta ta sha make-up. Ta saƙala jaka mai maroon da baƙi hakanan kalar takalminta ma. Banda ƙamshi babu abinda ke tashi a jikinta. Sai baza ido take tana duban ta inda za ta hangoshi sai dai babu ko alamunsa. Ta ja guntun tsaki ta dubi mijinta.
“Wai ina yaron nan ya shige? Na fa gaji da tsayuwarnan.”
Mijin ya dubi agogon da ke ɗaure a fatar hannunsa, umarni ya yiwa direba akan ya rufe Boot ganin ya tsaya sauraronsu.
Kafin ta kara cewa komai, ta hangoshi tafe. Ajiyar zuciya ta saki ta dubi Mijinnata.
“Ka ganshi can, na ɗauka ai ɓata ya yi daga zuwa.”
Ya yi dariya sosai yana kallonsa. Sai ka rantse wani Balaraben ne ka takowa ba shi ba, dogo ne kuma kakkaura, yana sanye da baƙar riga shara-shara wacce ba ta ɓoye halittar kirjinsa ba, sai baƙin wando mai tsaga-tsaga. Idan ba ka san gayun ba kana mai iya rantsuwa akan ketawa aka yi bisa kuskure. Gashinsa kuwa an mishi wani ɗan iskan aski, inda aka aske gefe da gefe aka bar ɗan tsinin gashi a tsakiya. Ya sanya baƙin gilashi a idonsa ta yanda ba a iya hangen fararen kwayoyin idanunsa. Hannunsa ɗaya rike da karan sigari yana zuƙa yana fesarwa yayinda ɗaya ke riƙe da wata ƙatuwar Tab. Fuskarsa sai ka rantse bai ta6a dariya ba, koda ya iso inda suke bai kallesu ba ya bude gidan gaba ya shige.
“FU’AD kenan.” SALMA ta furta kafin ta girgiza kai tana murmushi. A dole Hayat ya ƙaƙalo murmushin shima ya jefamata sai dai ya gama kaiwa bango da wannan rashin mutunci na yaron. Suka shige gidan baya suka zauna sannan direba ya ja. Hannu ya sa ya ƙara ƙarfin Ac, wani irin zafi yake ji saboda sam bai saba da yanayin weather ta ƙasar ba. Asalima ji yake ya tsani ƙasar gaba ɗaya, ganinsu yake wasu ƙazamai na ƙin ƙarawa shiyasa bai kallon dukkan wani ɗan ƙasar da mutunci. Hatta da saitin da direban yake bai ko kallo don a tunaninsa yana kalla amai ne zai taso mishi. Yana jin muryar Maminsa da mijinta su na zuba hira, karshe da suka dameshi ya ja guntun tsaki gami da toshe kunnuwansa da Earpiece ya ware kiɗa. Gami da sauke gilashi ya yi jifa da karan sigarin da ya riga ya zuqe.
Kallon gidan ya shiga yi daga waje, ba laifi ya yi kyau. Sabon gini ne na daban wanda Salma da kanta ta gina kayanta. Tsari ne wanda ta san Fu’ad zai so shi. Ta rantse ba za ta zauna gida ɗaya da Bilkisu da yaranta ba, hakan ta sanya dole Hayat ya hakura ya amince mata.
Fitowa ya yi daga motar sa’ilin da direban ya faka, karewa gidan kallo yake. Maigadi ya ƙaraso da saurinsa.
“Sannu da zuwa yalla…”
“Oh shit! Ba ka da hankali ne?!” Ya furta da iyakar karfinsa yana ja baya har yana sakin Tab din a kokarinsa na toshe hanci. Gaba daya Maigadin ya rikice, jikinsa har rawa ya soma don bai ga abinda ya yi ba. Shi kuwa Fu’ad banda warin baki babu abinda ya ji ga wani miyagu da yake tofeshi da shi.
Hayat da Salma suka dubeshi. Salma wacce ta san dawan garin sai ta dubi Maigadi, ganin duk ya ruɗe ta mishi alama akan ya bar wurin.
“To ranki ya daɗe, tuba nake.”
Daga nan ya fice, Fu’ad ya ja tsaki ya shige gidan ransa a ɓace.
“Akwai matsala My Hayat, sai an sauya ma’aikata, Fu’ad ba ya son ƙazanta. Ka fi kowa sani.”
“Yanda kika ce tawan. Ai ni bani da ja.”
Ta yi mishi wani farr da ido tana murmushi san nan ta yi ciki, ya bita da kallon kauna har ta shige ciki. Shi dai bai ma san irin son da yake yiwa Salma ba.
*****
Shiru kake ji sai ƙara tauna. Su biyu ne kaɗai a ɗakin, su Inno na can babban falo su na cin abinci da su Hajiya Hafsatu.
Humaira ta ɗaya katon cinyar kazar da ke hannunta tana kallo sannan ta dubi Jamila.
“Jamila, su kuwa a inji ake ƙyanƙyashe kwan kasarsu?”
Dariya sosai Jamila ta sanya.
“Wallahi santi kike.” Humaira ta yi saurin saita kanta. Cikin murya ƙasa-ƙasa ta ce.
“Ke mantawa nayi ai, bari na nutsu kada wata ta shigo ta ganni. Sai a rainani ma.”
Dariyar dai Jamila ta ƙara yi. Abinci ne lafiyayye irin wanda Mama ta saba girkamusu duk radda aka samu cefane mai kyau a gidan Malam. Sai dai wannan har ya so ya zarta na Maman a daɗi. A cewar Humaira.
Bayan sun kammala suka fita da kwanukan zuwa kicin. Da tambaya suka shiga, nan ma galala su ka yi su na kallon haɗuwa. Humaira ta kurawa gas cooker ido, ganin yanda yake ci ana ta suyan nama. Ganin mai suyar ta juyo sai ta kauda kai tana mazewa.
“Ajiye a kan nan. Kar ki ajiye a ƙasa.” Ta dubi matar mai magana sannan ta dubi inda aka umarceta da ajiyewa. Wani irin tiles ne mai kyalkyali har da gilashi a samansa, kenan anan za ta ajiye? Ta ɗan yi turus sai kuma ta amsa da to sannan ta nufi wurin da tunanin za’a dakatar da ita ace ba nan ba. Sai dai shiru, sai ma tambayar sunayensu da matar ta shiga yi. Jamila ta sanarmata, Humaira a wayance sai da ta ɗan ta6a wurin tana mai mamaki. Ashe ba gilashi bane, tsabar kyalkyali da kyau ne yasa ta ga kamar gilashi ne a farko.
Bayan fitowarsu ta ja hannun Jamila.
“Ke zo mu dan zagaya gidan, me zamu zauna muyi a ɗaki bayan su Mama na falo? Zo mu zagaya wallahi.” Ba musu suka tafi, wata hanya suka bi yar karama, suka saki baki galala ganin wata kofa baka mai gilas a tsakiya-tsakiya, ga furanni zagaye da ita, ta ciki suka leka. Shukoki ne kala-kala a wurin.
“Allahu AlRazzaaku. Wurin nan akwai kyau. Zo mu shiga.”
Jamila ta fisge hannunta.
“Kut, wallahi ba da ni ba. So kike mu yi ɓarna Mama ta dakemu?”
Humaira ba don ta so ba suka juya, za ta so su shiga wurin. A hanya suka yi kiciɓus da budurwar da aka ce ita ce Amaryar, ta sanya dogon hijabi. Su hudu ne da wasu yanmata da alama fita ne zasu yi. Tun a jiyan take sakarmusu fuska sosai don har cewa Inno take ita fa Humaira bar mata ita za’a yi. Ana dariya. Wannan ta sa koda suka hadu yanzun, Humaira ta karasa ta gaisheta fuska a sake. Itama ta amsa, ta dubesu.
“Ƴan matan Inno daga ina haka?”
Suka yi shiru, ta dubi Humaira.
“Kuna so ku ga garinmu?” Ta fadi tana dariya, da gaggawa suka hau gyaɗa kai suna washe haƙora.
“Oya, ku faɗawa Inno zamu fita sai ku same mu wurin mota.”
“Haba Nuriyyah, kinsan irin yawon da zamu yi na rabon kati. Meyasa za ki jawo mana yara?”
Humaira ta waigo ta dubi mai maganar, wata siririyar kawar Nuriyyah ce da bata fi a hure ba.
“Kema dai kina ɓata bakinki Ameena, kin san Nuriyyah da yara, ballantana yar wajen Inno, ba ruwanki da shirginsu. Ya fi dai a bar su a mota wani sa’in, ai hakan ma sun ga gari.”
Fadin wata cikinsu, sauran suka amsa da hakane. Nuriyyah ko ta kansu ma ba ta bi ba don bata da niyyar tankawa.
“To nikam wallahi ba zan je ba. Aikin banza kawai, ku haɗa tafiyarmu da wasu kauyawa can da ko dressing ba su iyaba.”
“Sannu gwanar tsafta, ai kam zaman gidan ya sameki domin idan babu ke ba fasa yin komai zamu yi ba. Dama na lura da take-takenki tun jiya a wurin saloon. To idan dubu ne a kanki ni miliyan nake yawo da su. Mtsww.”
Daga nan ta yi gaba, kiciɓus suka yi da su Humaira na shirin fitowa. Ta ja hannunsu suka fice sauran ukun suka mara musu baya, Ameena ta juya ta koma ciki tana kunkuni. Dama bakin ciki biyu ne suka tarar mata, da na irin mijin kece rainin da Nuriyyah ta samu, da kuma na irin kudin da aka sakarwa Nuriyyah wanda a gidansu ita mahaifinsu shegen maƙo babu wani abu da ake sakarmusu kusan a komai ma Nuriyyah ta mata zarra. Wannan takaicin ta huce a kan yan kauyen da basu ji ba, ba su gani ba.
Zagi kwando-kwando ta sha wurin Humaira. Ta ji ta tsaneta ma. Gidaje har hudu suka je, wasu dattawa suka kaiwa kati daga nan suka shiga kasuwa. Murna sosai Jamila da Humaira ke yi, ko ba komai sun ga gari. A karshe suka yanke shiga wani katafaren mall na Fa’iz Store wanda sai wane da wance ke shiga. Sun fito daga motar Nuriyyah ta dubi su Humaira.
“Oya, ku muje.” Suka dan yi turus su na kallon yara sa’anninsu da ma manyan dake shawagi a wurin, yan gayu sosai. Humaira ta kalli Jamila. Ta sha kwalliyarta har da kwalli an yi hawayen masoyi da shi. (An ja shi dogo) jan janbaki ne a lebbansu wanda aka bi baƙi a samansa. Sai ɗige-ɗige da suka yi. Kayansu kuwa a koɗe. Ƴanmatan sun fahimci kunyar kansu suke ji, hakan yasa suka dara. Karshe Nuriyyah ta budemusu kofa suka fito ta ja hannunsu gefe ta zaunar saman wasu kujeru da ke kusa da motar.
“Kar ku damu, ku zauna a nan ku ga gari, yanzu zamu fito.”
Wannan ya fi musu dadi kasancewar wurin bishiya ce lulluɓe asalima ba a hangensu sosai su ne zasu more kallon gayu.
Shigowarsa harabar wurin kenan, ya nemi daidai karkashin bishiya ya yi parking, tinted glass ne a motar yanda ba ka ta6a hangen na ciki. Ya sha takaici duk sadda ya ɗauki motar dan uwansa Nasir idan ya zo garinnan, ya rasa dalilinsa na zama mayen gilasan mota irin wannan. Ya sha ce mishi da alama ba shi da gaskiya, sai dai ya yi dariya a wuce wajen. Yau dinma kar6owa ya yi adalilin fitar da ta zame mishi dole. Ya mance turarukansa a saman gado dab da zai bar gida. Ya daukosu da zummar sanyawa a jaka sai dai Allah bai nufa ba. Shi kam ba ya jin zai iya zama babu turare. Yana shirin fitowa ya ji tashin muryarta tana kallon motar.
“Kan uban can! Kiga wata mota, alkur’an ko me za’a ban ba zan shige ta ba. Hum um! Wannan fa tsaf sai a yanka mutum a ciki a je a yar.”
Humaira ke wannan furucin tana kara kwalalo idanu tana duban motar. Jamila ta cafe.
“Kee, irin ta na ta6a gani a wani Film a gidan Daso Amarya! A ciki wasu yan fashi suka sace wata suka je suka ƙulleta.” Hanjin cikin Humaira suka kaɗai, ta zaro ido tana duban motar sannan ta dubi Jamila.
“Dagaske?” Jamila ta gyada kai.
“Wai tsoro kike?” Shiru Humaira ba magana sai kallon mota, hankalinta ya rabu gida biyu, ta kalli mota ta kalli mutanen wurin.
Ya yi tsai yana karemusu kallo, ko ba’a fada ba irin masu tallarnan ne dake zuwa daga kauye. Sai dai ya tausaya musu ganin su yara kananu kuma gasunan ba laifi kyawawa ne musamman wacce ta soma maganar.
Hannu yasa ya bude motar ya fito, ai kamar wadanda aka tsikara da allura, a guje suka mike suka runtuma sai cikin mota. Adam abin ya so ba shi dariya, ya dubesu da mamaki, direban da bacci ya soma daukarsu ya mike firgigit.
“Lafiya?” Ya nemi ba’asi. Suka mishi nuni da Adam wanda tuni ya juya baya ya soma tafiya sai dai murmushin nan mai ƙara mishi kyau bai guje ba daga fuskarsa. Ya fahimci dai baƙi ne amman yan ƙauye wadanda a farko ya yi musu kallon ƴan tallah, hirarsu kawai yake tunanowa ya ba shi dariya.
“Me wancan din ya yi muku?”
Suna haki suka amsa.
“Daga wannan bakar motar ya fito, kuma su ne masu sace mutane su gudu.”
Ya kalli bakar motar kafin ya dubesu ya sa dariya.
“Yaro ma dai yaro ne, ko ince ɗan kauye.”
Jin haka Humaira ta haɗe rai.
“Ai kowa asalinsa kauyen ne. Kuma kaima daga can ka ke.”
Ta ba shi mamaki sai ya yi dif bai ƙara magana ba, Jamila na zungurinta ta ja tsaki ta ja gefe, har yanzu kirjinta bai bar bugu ba. Ita kallon Aljani ma ta mishi.
“Adam Ibrahim?”
Ya ji an kira sunansa, ya juya, da mamaki yake dubanta sai kuma suka yi ƴar dariya lokaci guda.
“Nuriyyah Labaran, Wow! Kwana da yawa? Kin kara girma.
Ta yi dariya, kawayenta sun shagala a kallon wannan halitta.
“Wallahi sai hamdala, ai ina jin rabonmu da juna tun ranar convocation dinku da su Yaya Najib.
Ya yi murmushi yana mai jinjina kai.
“Hakane, shi mukan dan gaisa ta Chat.”
“Bai faɗamaka aurena ya zo ba?” Ta ƙarashe kanta na kasa, ya ɗan taɓe baki gami da ɗaga kafaɗa.
“No, ba mu yi maganar ba. Yaushe ne?”
Hannu ta miƙa wa ta gefenta.
“Bani card biyu.”
Tana kar6a ta miƙa mishi, sunan da ya gani ya ba shi mamaki har ya dan dara.
“Ikon Allah, to Ni kuma ai ɗan uwana za ki aura. Huzaifah Nuhu Kabir Yola. Kinga kenan mu ne masu gayyata ba dai a gayyacemu ba ko? Amman hakan ma na gode. Sai mun hadu next time, Allah Ya sanya alheri.” Ya fadi yana murmushi. Ya yi musu sallama bayan ya miƙa musu katin.
“Kai Nuriyyah, I’m in love wallahi.” Fadin Khadija Yunus.
“Ba ke kadai ba Khady, nima na tafi da yawa.” Hidaya ta fadi tana bin bayan Adam da kallo. Namiji har namiji, ya hada kusan abinda kowace mace ke buri a siffar halittar mijin aurenta.
“Lallai, kuna fa da aiki, idan har Adam Ibrahim ne. Shi ne namijin da na soma so a rayuwata, tun ma bansan ma’anar soyayyar ba. Albarkacin Yaya Najib mu kai mutunci kadan da shi. Ku cire rai, yan matan jami’a ma sun yi sun hakura.”
Daganan ta yi gaba ta a jan babban 2basket din da ta cika da kaya zuwa wurin cashier, basu da za6i sai na su maramata baya,nan kuma suka soma hasashen irin gayun da zasu dauka wurin dinnerparty domin suna ji a jikinsu tabbas zai je.
Kananun kaya kala-kala har uku, Nuriyyah ta siyamusu sai ice cream da biscuits kala kala masu dan karen dadi. Kamar su yi tsalle a motarnan haka suke ji. Godiya da addu’a kam ta sha. To haka ma a gida, Inno da Maryam sun ji dadi kwarai suka bi ta da godiya. Hajiya Hafsatu ta bada gaba dayansu a yi musu ankon biki. Humaira da Jamila har da na yara da za’ayi na Dinner ta sa akai musu. Wannan ma karamci ne da ba zasu mance ba.