Zarah aro jarumta tayi duk da cewar bata da ƙarfin zuciya faɗa dashi ammah ba zata yarda ya raɓu da jikinta shi yasa tayi shahadar ture shi in yaso komi zai faru ya faru, tagaji da wannan abun nashi nacewa dole kullum sai ya rugumeta sai kace wata ‘yar sa, gashi ba mutum ba zuciyarta a matuƙar tsorace take jinta take kamar a kan ƙaya take tarasa yadda xatayi ne yasa dole tayi ƙarfin halin tureshe.
Tsawa ya da kamata yana cewa “guduna kike kin haukace ne nine fa mijinki.” “Mijina fa kace. Tir tir tir, Allah ya tsareni da auren ka yo mahukaciya ta haifini da zan auri jinsin da banawa ba Allah kiyaye nama sara wanda zan aura saikai har abadah kasa wannan a ranka.”
Zaro ido waje fatima tayi cike da mamaki tace Lalle zarah yaushe kikayi baki? Safwan ranshi ya sosu “Ke” Nikike faɗawa haka zaki matso gurina ko sai nazo na illah taki, gurin ta ya tafi gadan gadan! da sauri ta matsa jikin banko tana cewa karka taɓani! Hannuka bashi da tsarki
Cikin zafin nama ya janyo ƙafarta ya sake kaita ƙirjinsa ya rungeta yana sakin uban nishi kamar tsohon zaƙin da yasheka baici komiba. shafa jikinta yaje yana yimata kiss kamar wata matar sa Zarah jitake kamar tayi amai saboda warin da bakin shi yake yi,ba shiri Zarah ta fashe da matsanancin kuka, bil haƙƙi da gaske take kukan tana cewa please karabu dani ka ƙyaleni minayimaka, miyasa zaka Azaftar dani kana tilas tawa zuciya ta abun bataso kuma bata yi niya ba Kai wani irin fasiƙi ne? Safwan tsaya yayi cak! da shafata da yake yi Fuskar sa” ta canja kala ya ɓata rai sosai sakin ta yayi ya tashi ya fuce daga ɗakin a fusace Domin ta ɓatamai rai Shi datakira shi fasiƙi dole sai ya hukun tata Ammah bazai iya saboda yana santa sosai Fatima ko uffan batace ba dan ta itama a kauta zarah fitar safwan ke da wuya.
Fatima ta ƙyalƙayale da dariya wanda harsaida ɗakin ya amsah ɗan tsagaitawa tayi da dariyar takama gashin zarah tace “bazamu rabu dakeba har saina auri abun sona wato ahmed shiɗin nawane banaki nabane kidainama tunanin komawa ko ina domin nan gidanki ne. Domin safwan na matuƙar ƙaunarki saita ɗan juya ta kalli safwan, wannan tsohon daya koma santalelen saurayi to sunansa safwan ɗan sarkin aljannu hatsabibi wanda yake matuƙar san zarah tunda yaɗota idonshi akanta shikenan aka shiga ukku.
Tunda ya ganta ya ƙwallafawa ranshi santa duk da kuwa takasance ita mutum ce ammah hakan baisa ya rabu da itaba duk cewar ansamai rana dashi da fatima yarinyar da suke kulla makirci su tare da ita wanda ita ahmed takeso ba safwan ba shima safwan ɗin zarah yakeso shiyasa suke kullamakirci yadda sukeso, Yana san zarah yasoyi mata gata Ammah da yazo gurinta sai kuka taƙi bari ya raɓeta, Ammah baya bari fatima ta cutar da ita da tuni takashe ta saboda bata da imani so yake Zarah ta amince mai A ɗaura auran ammah abu yagagara saboda zarah taƙiyadda tashi.
Maganar ta kullum dan Allah surabu daita ta koma ga masoyinta Ahmed hakan yana matuƙar fusata safwan gata da ƙokarin guduwa to sukuma basa so ta fito waje domin kar ‘ƴan gidan su ganta shiyasa suka ɗaureta Sun zaɓi sukawota nan ne domin safwan yace bai yarda da zaman ta a wani guri daban ba sai dai ta zauna a babban gidan saura wanda gidan ne gabaɗaya a babban gida ne bangare bangare ne a gidan sunzaɓi inda wasu basa zuwa gidan Ammah suna bata abinci da ruwa sannan basu bugonta wannan kenan
Fatima bin bayan Safwan tayi
waje kwala mai ƙira tayi tare da dakatar dashi da tafiyar dayake yi inason magana dakai ne kallonta yayi yace inajin ba Annuri a fuskarshi kallonshi tayi tace miyasa ɗazu kamare ni?”ga mamakinta sai yayi ɗan murmushi A karan farko saboda tuna yadda tayi a lokacin.
“Ai duk cikin shiri ne”
kar kidamu! sai tace to dama munyi dakai zaka mareni? shuru yayi tare dacewa to kinyi haƙuri bazan sakeba,to” kawai tace tafiya suke suna fira kamar masoyan gaskiya duk wanda ya gansu sai yace sai ya tsokane su dacewa masoya a cikin ajinsu su suna cikin firar ne safwan ya jefowa da fatima tambaya nikuwa fatima a ganin ki mizai hana nayi yadda nake so da Zarah nasake ta kema kiyi yadda kike da Ahmed ma’ana kikasance da shi na tsawo sati kina morar sa nima haka sai mu rabu dashi muma muje muyi auren mu saboda a halin mu bazasu bari mu auri jinsin bil Adamaba kituna fa yadda mai martaba baya da sauƙi, tasan abinda ya faɗa gaskiya ne ammah tsabar mugun halinta yasa tace bata yarda ba sai Ahmed ya zama nata har abadah.jin wannan furuci nata yasa jikinshi yin sanyi Ammah baice komi ba.domin shi duk hatsabiban cinsa yabasa abunda za’ayi ta magana akai ana ciccira zance yasan kuwa muddin wani yasani a fada to dole su fuskanci hukunci domin sarki aljannu musulmi ne wanda baya da zalumci saidai ɗansa bai biyo halin sa ammah yana shakkar sa.
Shi safwan yana san fatima saidai san da yakewa zarah yafinata shiyasa yayarda suyi wannan yarjejeniyar ya yinda iyayensu basusan wainar dasuke toyawa ba,kuma basusan maganar su zarah ba domin ba zasu barsu su auri bil adamaba shiyasa basu yadda suka sani ba.
Sun nemi a ɗaga aure su domin sucika mummunan ƙudurun su akan su zarah sannan sai su auri junan su
Zarah da Ahmed masoyan da babu ruwan suna soyayyar su hankali kwance sannan ansamusu rana auren su bazai wuce 2week ba waɗannan aljannu suka shiga rayuwar su a lokacin dabasu tsammaniba zarah tasan hakan Ammah Ahmed baisaniba domin kuwa shi basu saceshima Ammah suna da ƙudurin haka.
Sa’adatu da sadiq sun isa gona lafiya lau sannan susaki dabbobi domin suyi kiyo sun sami guri sun zauna suna kallon dabbobin
Jejin saraswati cikin wata ƙona ƙatuwar gaske wani saurayine da matashiyar buduwar suna zaune kayan fulani ne ajikin su tana riƙe da ƙwarya tana shan fura yayinda yake da sanda a hannushi yana wasa da ita gefensu kuma shanayene da tumaki da dabbobi suna kiyo da’alama kiyo yakawosu gurin Sa’adatu da sadiq kenan wanda suka taho ƙiwo ɗazu da safe Ajje kwaryar furar tayi takalleshi cike damuwa tace hamma sadiq wlh ina kewar adda zarah, har ƴanzu ba’asan idan takeba “Sadiq” shima cike damuwa wacce takasa ɓoyuwa, yace “nima ina matuƙar kewar add zarah” To Ammah yaza’ayi sa’adatu mudai tayin Addu’a akan Allah yabayyana ta cikin Aminci.
Har cikin ranshi bayajin daɗin rashin addarsa Zarah wacce takasance yayace gare shi da kuma ƙanwarsa SA’ADATU, yashaƙu da ita sama da kowa a gidan su, sannan Zarah tana jiyamai daɗi masa da yadda take kulawa da SA’ADATU Duk da takasance itace Auta a gidan Ammah tafiji da Sadiq Shiyasa daka nemeta akarasa ya fikowa shiga damuwa dan har ciwo yakwanta Ammah Da Sa’adatu tafara girma sai kamamminta sak da na ‘ƴar’uwata Zarah,
Shiyasa yaɗau san Duniya yaɗorawa Sa’adatu………kamar yadda suke fita da Zarah ko ina” idan an aikesu to haka ya koma fita da Sa’adatu danji yake kamar Zarah ce, Allah Sarki Rayuwa Bazaitaɓa manta da yadda akayi zarah ta ɓace ba, sunzo gona kamar ko yaushe suna tsaka da kiwon shanun su gwanin birgewa suna fira a tsakanin su “kwatsam!
ya juya bayansa yaga bata nan bazauce ga abinda ya faru ba AMMAH BAIMANTA BA.
Ya tsuduma cikin duniyar Tunani wata guguwa ƙatowa tataso mai ƙarfin gaske dabbobi sukafara kuka suna zagaye cike da tashin hankali su Sa’adatu suka tashi suka nufi gurin dabbomin domin haɗa kansu” kwatsam! sai gawasu mutane su wajen mutum takwas da amalanke biyu a hannu su A malanke ɗaya dabbobi ne a ciki duk sun ɗauresu sai kuka suke daret gurin dabbomin su Sa’adatu suka nufa, “domin kwashe su,” Dama ɓarayi ne sadiq hankalin shi suna kan dabbomi sai ƙokarin haɗasu yake yayinda da sa’adatu take gefenshi a tsaye ta kallo ikon Allah A daidai lokacin ne
Mutane nan konace su ɓarayin nan suka isa ga inda sa’adatu take daga bayanta bisa rashin sani kwatsam sukayi ciki da ita duka Amalanke tafaɗi duka dambobin suka zube yayinda ciyawa suka lulluɓe su a ciki kuwa har da sa’adatu ciyawa ta rufeta, mutum huɗu daga cikin wannan ɓarayin suka tsaya a gurin amalanke suka fara kwashe dambobin suna sakawa yayinda ciyaye sun rufe dabbobin da ciwar suka ringa ɗaukarsu suna sakawa a ciki a malanken, “sa’adatu” tana kwance ta suma saboda a malanken ba ƙaramin bugo yayi mataba wanda har saida Amalanke tafaɗi ƙas! gashi sa’adatu kayan jikinta farare ne itama kuma ciwar tarufeta ɗaya daga cikin waɗanda suke saka dabbobin a cikin a amalanken ya juya yana magana ya sungumi sa’adatu ya sakata aciki ba tare da yasani ba,ya cigaba da ɗauko wasu dabbobin yansaka su a ciki ya yinda ba wanda yasan da sa’adatun a cikin su
Saida suka gama sakawa suka nufi gurin sauran suna tambayarsu “ya? sun gama ɗiba “Ae” sukace masu bacin sun gama cikika dabbobi mutane a cikin amalen kenan dama a gonar ba dabbobin su sa’adatu bane kawai akwai nawasu dasuka saki a gonar jan amalanke sukayo suka taho suka baro dajin fitar su daga gonar keda wuya wannan guguwar ta lafa sadiq ya haɗa kan dabbobin su duk baiga wasu daga ciki ba ammah yasa sauran a hanya gidan, juyowa yayi domin ya kama sa’adatu sutafi gida ammah baiganta ba waige -waige ya fara yana kiran sunanta ammah babu ita babu dalilinta tashin hankali da ba’asamai date ! gudu gudu yafara yana ta duba sa’adatu ammah baiganta ba gari naƙara duhu hadari naƙara haɗuwa Sadiq babu inda baiduba Ammah baiga sa’adatu ba saikace wacce taɓace lokaci ɗaya “bazato ba tsammani “ruwa ya fara zuba sadiq ya rasa yadda zaiyi wata zuciyar tacemai ƙilanfa sa’adatu tatafi gida tunda dagan babu nisa zuwa gida.
Dam kwanakin baya yataɓa zuwa da ita ta koma gida cike da yaƙinin abinda zuciyarsa tafaɗa yanufi hanyar gidan ,
ruwa yakece kamar da bakin kwarya zuba kawai yake ba ƙakkautawa gudu ya fara ya isa inda dabbobin suke yaja su suka ƙarasa gida dama sunkusa gida.
Shigarsu gida keda wuya yaga ummon sa tana tsagaye a barandar gidan sai zuwa take tana dawowa gurinta taga su sadiq sun dawo Domin gabanta sai faɗuwa yakeyi to ina suka tsaya bacin suna ganin hadari har anfara ruwa kuma su tsaya.
“Kwatsam! saitaji sallamar sadiq cike da jindaɗi ta taresa tare dacewa sadiq ina kuka tsaya har akafara ruwa kalli yadda kajiƙe ina sa’adatu take ita taya zaka barta a baya sadiq bacin kasan sa’adatu yarinyace gaban sane yayi mugun faɗawa ɗagowa yayi yakalli ummin cike da alamar tambaya? da tsoro sa’adatu kuma ummo batazo gidaba gaban ummo yagaɗi ras! tace bataxo gidaba kuma kamar ya ya sadiq bangane mikeke nufiba nantake gabansa yaƙara faɗuwa cike da ɗar-ɗar yace ummo nifa naduba ta ko ina ammah wlh ko alamarta banganiba naɗauka tataho gida.
Tofa tashin hankali daba’asamasa date ! Sadiq kasan mikake faɗa anya kana da hankali kuwa gashi sai kwarara ruwa ake suna tsaka da wannan tattaunawar saida Baffan su sadiq ya shigo gidan shima duk ya jiƙe da ruwa.