Tun a daren na hada komai nawa tsaf, da taimakon Aunty Nasara. Ummati sai cewa take “Allah raka taki gona”. Ko don rashin mutuncin da ummati ke mini naji ina son tafiyar, idan da hali kada in sake dawo mata gida.
Amma kuma bazan iya barin Najeriya ba tareda na je na nemi gafarar Abban mu ba koda kuwa zai koro ni ne da sanda.
Aunty Nasara na zuge trolley dina taga ina sharar hawaye, tace “Dotty, ki kwantar da hankalin ki kin ji, na miki alkawarin zama makwafin Wasila insha Allahu. Sannan zan tsaya tsayin daka wajen ganin rayuwar ki ta tafi daidai kamar ta kowacce mace ‘yar musulmai jikar musulmai, da yardar Allah kuma zaki samu auren duk wanda kike so Young Abba ba zai taba bari a tauye ki ba.”
Nace “ba damuwata ba kenan Aunty Nasara, ina tunanin yadda zan cigaba da rayuwa alhalin Abba na ya koreni, yana cikin fushi dani, son samu mu fara biyawa ku tayani in bashi hakuri, ko bai bar ni na zauna ba ya yafe mini, ya yarda cewa tafiyar Ya Omar haka Allah ya tsara don babu kaddarar aure a tsakanin mu.”
Nasara tace “zan yi ma Adam magana mu fara tsayawa a Abuja.”
Muka kama hanya a washegari muka bar Gembu. Tafiya dasu Young Abba tafiya ce mai dadi kwarai, kana tare dasu kana daukar ilmin zamantakewar aure nagari, akwai kyakkyawar fahimta tsakanin sa da maidakinsa, ana tafe suna ta raha suna tsokanar juna cikin soyayya, wannan abu ya kara dasa min son aure na soyayya ya kuma sa nayi ta raya abubuwa da dama a raina inda ace nice tare da “Mr Radio” kamar yadda Ya Umar ya kira shi. A haka muka isa Kano muka kwana washegari muka karasa FCT.
Abuja
Daga Abba har Anty Wasila suna gida yau, kasancewar karshen mako ne, Maryam Jamila ce ta fara ganin fitowata daga mota ta kuwa kwaso da gudu tana ihun murna ta rungume ni. A haka muka karasa cikin main parlour kamar zata cinye ni don murna.
Abba da Anty suka amsa sallamar Young Abba nidai sai rabewa nake a jikin bango.
Anti ta taso ta bude min hannuwa ina hawaye na shige cikin jikin ta. Ina kallon Abba na satar kallon mu da harara amma ya maida hankalin sa kan dan uwan sa Adamu da ya kwana biyu bai gani ba yana “lale da mutan Legas”. Nasara ta gaishe shi nima na zamo daga jikin Anti Wasila na durkusa a gabansa ina hawaye na ce.
“Abba na ina wuni!” Sai kuka.
8 Kuka nake mai motsa zuciyar duk mai sauraro balle zuciyar Uba mahaifi. Ina kallon yadda fuskar Abba ke takunewa cikin yanayi na rashin jin dadi ga kunyar kanin sa da maidakin sa don baya so maganar ta hada mu a gaban su, bai san cewa Ummati ta riga ta gaya musu komai ba.
Young Abba yace “Dr. Siyama tayi kuskure kuma ta karbi kuskuren ta ba zata sake ba, ka yafe mata”. Abba yace “Adamu ka fita a maganar Siyama, bata da kirki bata da lissafi, tunda har Omar ya bar ni a dalilin ta itama bazata zauna min a gida ba, ta tafi Mambilan tayi ta zama idan zaman kauye dadi ne.
Gatan dana nuna mata shi ya bata kwarin guiwar bijiremin da bijirewa umarni na, to na janye gatan ta je tayi rayuwar ta yadda take so.”
Young Abba yace “ni zan dauki Siyama ta zauna a hannu na ta cigaba da karatu, idan ta samu miji zan mata aure, auren dole bashi da ma’ana Yaya, na san kana son Omar kana kuma yi musu hange mai kyau ne amma dukkannin su suna da ‘yancin su rayu ba ta hanyar auren juna ba, suna da damar su zabi abokin rayuwa wanda zuciyar su tafi kwantawa da shi.”
Abba ya ce “saidai ta bi ka din kuwa, ban haifi dan da saidai ni in bi shi ba, ba dai shi ya bi ni ba. Kullum na ganta a gaba na bacin rai zata dasa min na kore min Omar.”
Na gurfana gaban Abba na kama kafar sa nace “Abba na yi alkawarin nemo maka Omar, ko bajima ko ba dade, nayi alkawarin dawo dashi gida, ni dai fata na ka yafe min Abba, ka daina fushin nan da ni don Allah…”. Na kama shi na kankame kamar bazan sake shi ba sai ya furta ya yafe min din.
Abba ya ce afuwata daya ce gare ki Siyama in ga Umar ya dawo gida, na janye kalamai na kamar yadda yake so.”
Abba ya soma matsar kwallah wanda hakan ya kara gigita ni na rushe da kuka mai tsanani.
Nace “alkawari ne zan dawo maka da dan ka, amma ban yi alkawarin zan aure shi ba.” Cikin mamakin taurin kaina Anti Wasila ta daka min tsawa tace “Boddo ke da kike neman afuwa kuma kike tada bara bana, Abba yana jin ciwo in kika ce bazaki auri Umar bane gara ki bar ra’ayin ki a ran ki tunda ya ce ya janye kudurin sa.”
Kowa ya hau yimin fada har Young Abba, yace tunda na karbi maganar kuma nace ban amince da auren dole ga kowannen ku ba, kada ki kara maimaita wannan maganar. Afuwar sa muke nema ba tada tsohon zance ba.”
Abba yace “In dai bazata zauna min a gida ba taje ko ina zata je bani da matsala da wannan.”
“…..wanda ke nufin Abba baka yafe min ba? Na tuba Abba na bi Allah na bi ka. Ka furta yafiya a gare ni don in ga albarka a rayuwa ta. “Abba yace “zan yafe miki only ranar dana ga da na Omar a cikin gidannan, na aura msa matar data fi ki” aka kada aka raya Abba ya ki canza maganar sa.
Amma ya amince in bi su Young Abba duk ma inda zasu je ba matsalar sa bace.
A hakan cikin rashin kwarin jiki kowa ya kwana a gidan. Don hukuncin Abba bai yi mana dadi ba, bai yi wa kowa dadi ba, bana so ina tafiya a duniya babu afuwar sa a jiki na, don haka na dauki aniyar nemo Ya Omar ko ta halin kaka.
Washegari jirgin Azman muka bi zuwa jihar Ikko. Cikin sati biyu Young Abba ya gama yi min duk wani shiri na tafiya tare da su a cikin alfarmar iyalin sa. Ranar wata Litinin babbar rana muka sauka a birnin Washigton D.C din Amurka, inda acan ne headkwatar US Diplomatic Mission yake. Gidan Young Abba bashi da nisa da ofishin su.
Tun saukar mu a kasar Amurka na samu nutsuwar data yi min karanci, Aunty Nasara kuma ta maida hankalinta kacokam kan zaryar asibiti akan matsalar haihuwar ta don ita ke da matsalar ba shi ba. Ta kan ce a kullum in yi mata addu’a Allah ya bata haihuwa ko guda daya ne, idan Young Abba yayi mata kishiya mutuwa zata yi sabida kishin sa.
Kalaman ta na bani dariya a yawancin lokuta, sai kuma in ga in nice nima hakan ce zata faru dani, muddin wanda nake so na aura kamar ta.
Sau tari ni kadai nake wuni a gidan, ba da jimawa ba Young Abba ya mallakamin wayar hannu, yace sabida su dinga jin halin dana ke ciki idan basa gida.
Wato kadaici da kwanciyar hankalin dana samu sai ya dawo da bara bana. Na koma mafarkaina da shi, abin har yayi ta’azzarar da ya zarce na baya. Na kuma fi jin closeness dina da shi cikin zuciyata a garin Washington fiye da gida Najeriya.
Saina koma nemawa kaina hanyoyin debe kewa da zasu rage min feelings din dana ke ji a kan sa, na abokantaki Talbijin a halin yanzu. Na zama mai bibiyar VOA TV: AMURKA. Kullum ranar Allah sai na kalli labaran VOA TV har Aunty ta canza min suna zuwa Siyama-VOA, don tace ta ga alama ina yin su sosai.
Na sha kona mana girki akan kallon TV Programmes na VOA. Har ta kai ta kawo Aunty Nasara ta daina bar min girki yanzu, ban san abinda ke fizgata ga son sauraron su da kallon su ba. Face wani abu tamkar magnet dake jan zuciyata yake fizgata akan gidan talbijin da radio na VOA tunda na tabbata bana raba dayan biyun a can ne na fara jin real sautin sa a radion Abba na.
Silent Encounter
Kimanin watanni takwas kenan da dawowar mu birnin Washington. Na gyagije na zama goyon ‘yar gayu Aunty Nasara na yi tsaf da ni kwanciyar hankali ya wadace ni. Weather din birnin Washigton ya ratsa fatar jiki na. A yau shirin da VOA suka sako a safiyar yau is a Live TV Programme.
Kwance nake a cikin sofa-bed ina cin gugguru, ina kuma kallo, a gefe ga hot coffee na hada sai turiri yake. Na mike zaune ina kurba ina cin gugguru kafin kuma na maida hankali na ga makekiyar talbijin din dake manne jikin bangon daki na na gidan Young Abba. Kimanin watannin mu takwas da zuwa Washington kenan. And there was where it all happened. Today I saw HIM!
Bayan sallama ga masu saurare, tare da gabatar da kan sa a matsayin sa na Broadcastern VOA mai amsa sunan “Hamzah Almustapha Mawonmase”. Sai ya fara gabatar da shirin sa LIVE na vedio tare da mara lafiya “Adam Toobin” mai fama da lalurar Celebral Palsy…… cikin harshen turanci daga sashen turanci na VOA.
Hamzah ya cigaba da kwararo bayani kan lalurar Toobin…
“……. OVERCOMING OBSTACLES…..”. Taken shirin sa kenan.
-“LIVING WITH CELEBRAL PALSY…..!!!”.
Shine shirin da Hamzah yake gabatarwa kai tsaye (live) tare -da mara lafiya Adam G. Toobin wanda ke kwance cikin wheelchair mutumin kasar Amurka ta kudu, wanda ke rayuwa shekaru talatin cikin cutar ‘Celebral Palsy’ ba tare da motsi ba. Baya motsi (movement) kamar kowanne dan adam bai kuma taba sanin menene lafiya ba, amma yana magana daga cikin kujerar sa, yana kuma gayawa duniya yadda yake rayuwa cikin wannan larura, yake kuma tafiyar da al’amuran kamfanin sa a haka, tare da koyar da ma’aikatan kamfanin yadda zasu tafiyar da al’amuran kamfanin, yana gaya musu hanyoyin magance matsalolin da suka taso wa kamfanin in oral form. Hamzah na tattaunawa da shi yana bada feedback yana kuma daukar sa a hoto da vedio din sa.
(Shi ba fari bane, baki ne cikakken dan Najeriya, dogo haka siriri mai zankadeden dogon karan hanci, wanda ya tafi ya dan rankwafa kadan a saman bakin sa sabida tsayin sa).
Mutumin nan ne mai tarin gargasa a fuska da saman giran idon sa, mai murya irin ta Asians mai sassarfar magana, maimakon Hausar dana san shi da ita yau turanci yake yi zallah.
Bashi da kauri kuma babu annuri a fuskar, a lokacin da yake gabatar da shirin “……. OVERCOMING OBSTACLES…., LIVING WITH CELEBRAL PALSY…. !”. Tamkar yana taya client din sa Toobin alhini da juyayin halin lalurar rashin lafiya na har abada da yake ciki.
Yana sanye da farin siririn gilashi na kara karfin gani. Wanda na tabbata yawan duban camera ne ya yi mujazar lalaurar idanun nan.
Sanye a jikin sa ‘Black – Grey Japanese Suit’ ne, ya matse wuyan sa daga ciki da tsukakken neck-tie fari sol.
Exactly yadda nake ganin sa cikin MAFARKI na, exactly yadda nake ganin sa a IDO BIYU na, wato inimaginations… haka exactly yadda nake picturing din kasancewar sa! Sannan muryar bata canza daga yadda na santa na kuma haddace ta ba.
Wannan shine HAMZAH ALMUSTAPHA …….. da na dade ina baku labari, wanda na rayu shekaru rututu cikin mafarkan sa, wanda na taba tsinkayar muryar sa a kunnuwa na daga gidan rediyon VOA watanni masu yawa a baya.
Yau dai ga Hamzah na gani cikin idanu na, Hamzah a kan screen din talbijin din daki na, a kan allon talbijin dina…. In reality ba’a mafarki ba, ba kuma a sautin murya ba. Yau na ganshi ne ganin idanu na. Ina kallon sa ina kuma jin sa.
Kwarai sunan da ya ambaci kan sa da shi a wancan lokacin ma da na kasa tunawa kenan “HAMZAH ALMUSTAPHA MAWONMASE!!!” Amma a wancan lokacin kidima da ikon Allah basu bani ikon rikewa ko tunawa ba!!!
Wani abu tamkar zubar kankara ya bi ilahirin jikina ya sankarar da ni a inda nake kwance. Zuciya ta tamkar ta fito ta baki na. Yawun baki na ya kafe rayas. Nayi kokarin hadiyar miyau don jika makoshi na da ya bushe kamas, amma na gagara yin hakan saboda kidima. Sakamakon haka na jin numfashi na na shirin barin gangar jiki na. Ko wanene wannan shine ‘dream man’ dina, da ya hana rayuwata sukuni, ya rabo ni da gidan mu da iyaye na, ya raba ni da Ya Umar, ya jefa rayuwata cikin kaka-nikayi, shine mutumin da ke zuwa min kullum cikin MAFARKI KO A IDO BIYU! Shine wanda Ubangiji ke nufin al’amura da dama a tsakani na da shi tun ban san kai na ba, wadanda ban san farkon su balle karshen su ba.
Iya abinda na iya tunawa kenan sai na shide cikin emotion, kowacce gaba ta sassan jikina na maimaita kiran sunan “Hamzah Mawonmase!” Don kada in kara mantawa ko ya kara bace min in sake shiga halin ha’u’la’i.
To amma sanin da na yiwa Hamzah a yau bashi da wani amfani tunda dai ba zan dauki kafa a matsayi na na diya mace bafullatana mai daraja in tafi ofishin VOA neman sa ba, in ganshi in ce masa me? Ai sai kima da daraja ta na diya mace su fadi. In nayi haka na siyar da mata, na siyar da fulanin Mambilah wadanda ko a cikin fulani daban suke.
A hakan dai zan cigaba da kwankwadar azabar soyayyata ni kadai, har zuwa ranar da numfashi na zai kare da sunan Hamzah Almustapha a cikin sa.
Ko babu komai yanzu zuciyata ta samu sa’idah, na cewa Hamzah mutum ne bil adama, yana rayuwa ne a gidan radiyo da talbijin na VOA. Kuma muna cikin kasa daya. Kuma Allah ya nufa na gan shi in a silent way. Zuciya ta ta yarda shine mutumin mafarki na dana rayu da shi tsayin shekaru kusan goma a zuciya da kwakwalwata.
Koda wannan kadai na tsira ya ishe ni kwanciyar hankali har karshen rayuwa ta; HAMZAH ALMUSTAPHA is a human, living in America.