Skip to content
Part 23 of 73 in the Series Sakacin Waye? by Sumayyah Abdulkadir (Takori)

A gefen ma’adanar motocin sa ya ga farar kankanuwar motar ta G-Wagon a fake, wannan ya tabbatar masa ‘yar nacin tana cikin motar tana jiran sa all this while har karfe tara na dare. A kusa da ita yayi parking tasa motar, ta dago ido daga kan wayar ta da take dannawa suka hada ido. Har da sassanyar ajiyar zuciya ta saki. 

Wani irin hade giran sama dana kasa yayi cikin alamu na ta shiga rayuwar sa. Baya bukatar ganin kowa a daren nan hutawa yake son yi. Kafin ya fito daga motar gaba gadi cikin irin gait dinsa (takun sa) na sassarfa da aji na musamman, ya doshi kofar shiga falon sa. 

Suhaila Barkindo ta bude motar ta  mai kofa daya da budadden sama wato G-WAGON ta fito ta doshe shi kai tsaye tana kokarin yi masa barka da zuwa, tareda gaya masa tsayin lokacin da ta dauka tana jiran sa, tun kafin ta gama ya dakatar da ita.

“Bani da lafiya Young Lady, please leave me alone to enable me carry my own problems”. Amma hakan bai sa ta tafi ta rabu da shi din kamar yadda yake so ba illa bin bayan sa da tayi zuwa ciki kamar matar sa. Ya san dama bazata tafin ba sai ta yi niyya. Naci na Suhaila ba yau ya san shi ba. 

Tare suka shiga cikin gidan. Ko zama bai yi ba ta zarga hannayen ta a wuyan sa ta soma rage masa nauyin Suit din jikin sa kamar wata matar sa, duk da ya ce ta bashi waje baya jin dadi baya son ganin kowa amma ko a jikin ta kamar bata ji shi ba. Sai shige masa take kara yi kamar mage. Shi kuma kara rokon ta yake kan ta tafi don Allah yana bukatar kadaici. Suhaila ta dago cikin sarewa da al’amarin sa na rashin darajja dimbin soyayyar da take masa. 

“Zan tafi only in kayi alkawarin amsa gayyatar liyafar cin abincin dare dana shirya maka tare da ‘yan gidan mu a gobe, don Allah Hamzah kada ka ce min a’ah, na riga na gaya musu cewa tare da fiance dina zamu yi dinner  a goben. Na shirya komai. Kuma Baba na ya yi maka shirin tarba na musamman.”

“Fiancè?” 

Hamzah ya fada da sigar tambaya mai nuna mamaki, “am i really your fiance Suhaila B.? Yaushe na kai wannan matsayin?” Ya sake fada idanun sa kai tsaye cikin nata, cikin sakawa maganar ta katotuwar ayar tambaya, sabida a sanin sa dai bai san yaushe ya amsa mata maganar aure ba da har ta kira shi wanda zata aura gaba gadi a gidan su. 

“Ina mamaki Suhaila. Idan na tuna cewa ke Musulma ce. As far as i know Moslem women are not like that,  koyarwar addinin su tasaka basa tallata kan su ga mazan da ba addinin su daya ba da kowacce irin alfasha ko da neman aure. Ta ina zan aure ki alhalin addinin mu da abinda muka yarda da shi ba daya bane? Am not sure ma idan ina son ki, am not sure ma idan addini na da naki sun amince da hakan (aure tsakanin su).”

A cire maganar addini da al’ada, wadanda kin jima da ajiye su a gefe, kin ara na nasara kin daura na kasar da ba taki ba, kawai don neman abinci ya kawo iyayen ki. Har gobe ba’a haifi matar da ni Hamzah Almustapha  Mawonmase zan so ba tukunnah. Sai wadda zuciyata ta amince she’s pure (tsarkakakka ce) ciki da waje. Not even within my ethnic group and my religion (koda cikin kabila ta da nawa addinin). 

Daga hakan na fahimci cewa; ba’a haife ta ba tukunna because pure ladies are rare. Ni kuma ba kowacce mace zan iya aure ba yadda na kiyaye kaina ina son wadda zata rike amana ta itama ta kaunace ni da zuciya daya. I’m very choosy akan diya macen da zan aura, i’m sorry Suhaila ban fada don na bata ran ki ba sai don kada na yaudare ki, na jima ina gaya miki wannan amma kin ki fahimta ta da gangan.

Let me confess it again and again; ni Christian ne (mai bin addinin Christianity).  A cikin Christianity din ma i’m Catholic (wadanda sun fi kowa rikon addini). I’m not in the same religion as you just because of my appearance (Ba addinin mu daya ba don kawai ina da kamanni irin naku). A shawarce ki nemi miji mai son ki mai nagarta dan naki addinin ki aura, ina ganin zai fi daidai a kan wannan Hamzan da babu komai a gaban sa sai ayyukan sa.”

Da gama fadin haka ya haye saman benen sa da sassarfa. Ya bar Suhailah Barkindo kamar an kafe ta a wurin, tana fadi a fili, “ka yi karya Hamzah ka kwana da yunwa! Idan har kudi na sayen komai, idan mukami da mulki suna bada komai…… Baba na zai sayo min soyayyar ka……”.

Ba damuwar ta kin auren ta da yake confessing a fili da hujjar cewa ba addinin su daya ba kuma bata da kamun kai irin wanda yake so, damuwar ta yadda ta mallaka masa zuciyar ta ta zubar da ajin ta da pride din ta na diya mace wadda bata rasa komai a rayuwa ba, da gatan ta da ilmin ta amma duk tasa kafa ta take ta kwantar  da kai ta nemi ya aure ta, tunda a tunanin ta, matsayi da kudin mahaifin ta a kasar ta Amurka zasu saka ya aure ta, kamar yadda ta san maza irin sa sun fi yin auren jari. 

Ita ba ruwan ta da wani addinin sa shi ya shafa, Hamzan kawai take so ba addinin da Hamzan ke bi ba, duk da Abban ta yace babu aure tsakanin namijin Christian da musulmar mace. To su kam addinin musluncin nasu ma ai a baki ne ita da family din nata duka. Sallah kawai suke yi a lokacin da suka ga dama suka samu faraga daga sabgogin su na neman duniya, Azumi wannan ba kowa ke iya jure shi a gidan su ba, bayan wannan bata ga marabar ta da Hamzah Mawonmase ba.

Tunda ya ji alamar ta bar gidan ta hanyar jin fitar motar ta cikin fushi, ya sakko ya kulle ko’ina yana mamakin  matan Najeriya a kasar Amurka. Allah ya kawo mu wani zamani da ‘ya’yan musulmi ke sarayar da mutuncin su a inda bai dace ba, a ce mace mai daraja musulma ke bin namijin da ba addinin su daya ba har gidan sa take neman sa da yaka haram yaka halal, shi kam a al’adar da ya fito wannan ba karamin abun kunya bane let alone  banbancin addini. 

A inda duk kawar zuciyar su ta raya musu sai su kai kan su babu duba ga abinda ya dace, don samun momentary pleasure na zuciya da gangar jiki na dan takaitaccen lokaci. 

Ya samu contentment na cewa shi kadai ne a gidan sa yanzu. Sai ya kashe duka fitulun gidan ya bar dim light. A lokacin ya samu ya kwanta rub da ciki (kwanciya ce ta wadanda ba musulmi ba) cikin doguwar kujerar kayataccen falon sa, ya dauki wayar sa ‘Thuraya’ ya kira Kakar sa da yake kira GrandMa.

“The only Parent i have, my  one and only relative, my great  efficient Grandma!”

Bayan sun gama gaisawa yadda suka saba ta ke gaya masa cikin harshen Birom. “Mawonmase zaka zo gida a satin farko na watan Afrilu, akwai bikin al’ada wato ‘Nzem Birom Festival’. Kuma kwanan watan yayi daidai da sauran manyan bukukuwan Birom wato “Mandyeng, Wusal Berom, Badu da Nshok”. 

Ta kara da cewa “wannan shekarar bana so ka yi missing kowanne biki kamar yadda ka yi missing na waccan shekarar. Kana SAKACI da al’ada.”

Hamzah ya kwantar da murya cikin ladabi yace da Kakar sa “kiyi hakuri Grandma, zan tafi Russia tare da Team din ofis dina a daidai wannan lokacin da kika ambata, domin dauko muhimmin rahoto ga VOA, i’m very sorry Grandma bazan samu halartar ‘Nzem Birom Festival’ ba again a wannan shekarar, sai ko shekara ta gaba in muna raye.”

“Mawonmase kana wasa da al’adun ka sabida aiki ko? Mawonmase aikin ka yafi ‘Nzem Birom Festival’ albarka ne? Mawonmase akwai albarka mai yawa a tare da festival dinnan da sauran festivties da zasu biyo bayan shi, kayi kokarin da zai yiwu ka halarta, ba zan karbi uzurin ka ba ko daya”.

“Grandma ba haka bane, komai da lokacin dana ke ware masa….kinsan…..” tayi maza ta katse shi cikin fushi. 

“Yaushe rabon ka da zuwa Church ka yi addu’a ga iyayen ka da ke Heaven suna jiran mu? Sabida aiki ko Mawonmase? You dedicated all your precious time for this career bayan ba da shi kadai ka dogara ba.

Yaushe rabon ka da zuwa church don yin addu’a a kan Allah ya baka mata uwar iyali tagari tamkar mahaifiyar ka?”

Shiru yayi kamar ruwa ya ci shi, shi kan sa ba zai iya tuna rabon sa da zuwa Church ba, sabida yadda kullum yake busy da ayyukan ofis din sa. Gashi baya karya a tsarin rayuwar sa balle ya kare kan sa da karya. Kaka tayi fadan tayi fadan kamar ta ari baki. A karshe tace bata yi masa uzurin kin zuwa Festival na wannan shekarar ba, ko da kuwa bai samu halartar sauran bukukuwan ba to kuwa lallai ya zo ‘Nzem Birom Festival’ ko na kwana uku ne. Domin tana son ya ga diyar Sarkin Birom da zata zo daga Sweden ta kammala karatu watau “Tina Gyang” da take son ya nemi auren ta.

“Saura wannan karon ma ka kara bani kunya”. Da haka ta kashe wayar ta.

Koda ya gama waya da rigimammiyar Kakar sa sai ya fada a tunani, Grandma is somehow right wato ta wani fannin tayi gaskiya, lokaci yayi da ya kamata yayi aure haka, ‘he is so much in need of a pure young lady by his side’ ko domin ta dauke masa damuwar da ya kan kasance ta kadaici da kewa a lokuta irin wadannan da yake shi kadai idan ya dawo gida, ta raba shi da karakainar da matan titi ke yi a gidan sa kamar shikadai ne namiji a fadin Washington, ta taya shi da sauke bukatar shi na dan adam mai lafiya kamar kowanne namiji at his thirties a stage din da babu abinda yafi bukata a yanzu sai diya macen. Amma yayi rantsuwa ba zai yi Zina ba, he will reserve himself har sai ya samu matar da ta dace da ra’ayin sa da burin sa. Bai taba zina ba, don haka ba zai yarda ya auri mazinaciya ba.

All these girls coming here are nothing more than international prostitutes masu biyar gida da ofishin maza  kyamar su yake yi, yana ganin kazantar su a fili, don ya san yadda suke bibiyar sa, haka suke bibiyar sauran mazan da suka yi musu a kan titi. Yana ganin lokaci yayi da zai yi aure da macen data dace ya ajiye iyali tare da ita.

Domin a zahiri yana gab da fita shekarun kuruciya, idan har lissafin da yakeyi daidai ne shekarun sa talatin da takwas. To amma wa zai aura?

Suhaila?

She’s really NOT a prostitute, laifin ta daya gare shi ita take bin sa ya aure ta, kuma tana ganin matsayi da kudin ubanta ne zasu sayo mata soyayyar sa ta karfi. 

Da sauri ya kawar da tunanin ta da ya tuna cewa musulma ce, mawuyaci ne iyayenta su yarda su bashi auren ta. Amma don kyau Suhaila kyakkayawa ce ta bugawa a jarida shikuma naturally yana son mace mai kyau. Bayan wannan sai ya kasance bai da feeling ko yaya na aure a tare da ita bai san meyasa ba. A kasar America bakidaya ita ce macen da alaqar su ta yi tsayi amma da ya gane tana amfani da mulki, matsayi da kudin mahaifin ta wajen neman soyayyarsa ta karfi sai ya janye mata.

Abinda bata sani ba career din sa is quite okay for him, baya bukatar komai a rayuwa because VOA pays him enough, bashi da wani nauyi a kan sa bayan na tilon Kakar sa. Kuma kamar kowanne (BIROM Man) shi babban manomi ne a kasar Najeriya. Ba da aikin sa kadai ya dogara ba.

Kwadayin shan Barasa ya zo masa, ya kan sha ta lokaci – lokaci idan kadaici irin wannan yayi masa yawa. Tunani ya addabeshi yana neman abinda zai dauke masa hankali daga tunanin aure. Ya bude firjin gefen gadon sa suna nan a jere reras, brand daban daban, masu tsada irin wadanda basa bugarwa sosai, ya dauko kwalbar Trophy ya bincire murfin ya kafa a kai yana kwankwada with so much feelings of loneliness and desperation na son kadaicewa da diya mace…. sakamakon kusantar sa da Suhaila ta yi dazun. Har yanzu akwai scent dinta na ‘Azzaro Visit’ a jikin sa.

Sai kawai innocent muslim fuskar nan dake ta kallon sa dazu cikin familiarity (sanayya), matsanancin fushi da jin haushi ta zo ta gilma ta cikin idanun sa. Tamkar an bude wani shafi na cikin littafin hotuna wato album.

“Who is that Beautiful Damsel???” 

(Wacecce wannan kyakkyawar ZINARIYA?)

Hamzah ya tambayi kan sa a fili bayan ya sauke kwalbar barasar a kasa, hoping zai samu wata murya ta zo daga can sama ta amsa masa tambayar sa, ta bashi cikakken bayani akan yarinyar, domin ya kasa manta bafullatanar fuskar ta dake dauke da kallon sanayya, as well as look of anger and hatred  din dake cikin idanun ta.

Ya ajiye kwalbar a kasa yana ganin duniya na juya masa…..tana zagayawa da shi akan gajimare, one thing with Trophy tana zagayawa da shi a duniyar gajimare ta mantar da shi damuwoyin sa, yana fadin….

“Gara min na sha Barasa da dai in yi Zina”

Wani bangare na zuciyar sa ya kalubalance shi da cewa a’ah, Jesus yayi musu hani da kowannen su (shan giya da yin zina as well). Amma a rashin uwa akan yi uwar daki a ganin Hamzah, gara wani zunubin da wani zunubin,  “ina fatan idan na yi aure da matar dana ke so na fara haifar yara suka tasa in daina shan barasa, ko don sabida ganin idanun su da lafiyar shekarun manyantaka.”

Da wannan ya lumshe idanunsa ya kwanta rub da ciki a wurin yana barci mai nauyi. Kwanciya ce da yafi so wato ya kwanta akan cikin sa bayan ya sha Barasa iyaka shan sa.

Bai rasa komai a rayuwar duniya ba domin ya mallaki gidan zama cikin ‘Cielò Apartments’ a kwaryar tsakiyar birnin Washigton D.C da garin su Jos din Nigeria, yana da motocin hawa guda biyu nasa na kan sa, ya mallaki manyan gonaki da ake yi masa noman Dankali da Cocoa a Barikin Ladi da Riyom kananan hukumomin da ke Southern Jos. 

Ya dade yana aikin broadcasting da International Media domin a kalla ya shekara goma yana aiki da rediyoyi da talbijin din manyan kasashen duniya kuma ya samu alkhairi sosai a tare dasu kasancewar duk inda yaje dan gaban goshi yake komawa sabida tarin baiwarwakin hikimar iya sarrafa zance da Allah yayi masa. 

Amma somehow, duk da tarin wadannan nasarorin bai san meyasa a irin wannan lokacin yake jin babu wanda ya kaishi maraici a duniya ba. Wanda ke nuna gatan Da namiji mafi rinjaye shine matar aure tagari. Musamman ga wanda ya tsare kan sa daga aikata laifuka. Ya zabi permanent pleasure akan temporary.

Duk da cewa shi din maraya ne dama, amma akwai wani maraicin bayan na iyaye dake sakadar sa, wanda ya tabbata bana komai bane na rashin matar aure ne a shekarun sa talatin har da takwas. Shi kuma har gobe ji yake ba’a haifi matar da zai so a duniya ba. Musamman da yake matan ne ke kulafucin ya aure su tun kafin yayi nazari ya ce yana son su.

<< Sakacin Waye? 22Sakacin Waye? 24 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.