Skip to content
Part 26 of 73 in the Series Sakacin Waye? by Sumayyah Abdulkadir (Takori)

Subahin ranar, karar waya ta ce ta tashe ni. Koda na duba bakuwar lamba ce. Na mika hannu ina mamakin wanda zai kira ni a irin wannan lokacin amma hakan bai hana ni amsa wayar ba.

“Just to wake you up for Subhi prayer. Kin tashi lafiya Siyaam?”

Tuni na wartsake daga barci na, jin muryar Hamzah, Hamzahn da na kwana mafarki wai gashi yana rera karatun Al’qur’ani, ko Abdurrahman Al-Sudaith a iya karatun da fidda Tajweed albarka.

Da sauri na canzawa wayar position zuwa kunnen dama, na kuma kara rike ta da kyau, tamkar hannayensa ne na kama na damke nake son jan shi zuwa addinin Allah.”

“Ka taimaka da ka tashe ni don har na makara sallah. Bana gaida kowa sai na fara gaida Ubangiji na.”

“Fine, na kira ne dama in tashe ki ai, i know it’s your prayer time, in kuma gode miki for yestardy. You really brightened my day! Ina fatan kasancewa ta ba dan addinin ki ba, ba zai sa ki kyamace ni ba Siyaam, I have picked interest in you. I must confess I really admire you!”

Numfashi na naji yana neman sarkewa. Yaya mafarkan suke warware kan su, suke son zama reality kuma? Bayan na riga na bar su a zuwan mafarkai marassa tudu bare abin dafawa. I have found a great interest in you. I admire!”

Me hakan ke nufi?

Sai kawai na katse wayar a hankali. Na cusa kaina a karkashin filo na, ina jin wani irin contentment a cikin rai na. Zan yi amfani da wannan admiration din a kan ka Hamzah, in janyo ka ta karfi ka shigo cikin hasken shiriya!!!

Na ki zuwa VOA a washegari, duk da ina da muhimmin report da zan yi a yau din, ba don komai ba sai don ina so in ga da gaske Hamzah ya damu da ni din kamar yadda ya ce ya samu great interest a kaina?

Wajejen karfe hudu na yamma sai ga sakon sa ya shigo cikin waya ta. “SIYAAM, gani a kofar Condo din ku, zan iya ganin ki?”

A fili na yi hamdalah ga Allah, na kuma soma neman mayafin da zan rufe kai na. Na fita na tadda shi a tsaye a jikin motar sa.

Sabanin jiya da yake cikin nutsuwa fes-fes, kal-kal, yau bakidaya a birkice na gan shi, gashin kan sa mai laushi ya cukurkude alamun bai ga tazar musamman da extra kulawar da yake samu duk safiya ba, idanun sa sun dan tasa.

Alamu ne na rashin samun wadataccen barci ko kuwa rashin lafiya ga dan adam. Ina fitowa yana takowa majestically zuwa gare ni hannayen sa biyu zube cikin aljihu, sanye da shadda Getzner ruwan makuba an yi masa dinkin Boda. Wallahi babu marabar sa da Bakanon Bahaushen da ya shekara talatin cif a cikin musulunci. Zaka iya zabge masa shekaru takwas dake kan nasa, ka bar shi da shekaru talatin cif.

“Why are you not in the office today? Are you not an intern at political department?”

Shine abinda ya fara tambayata da dukkan concern din duniya cikin muryar sa da idanun sa. Hannun sa dake cikin aljihun wandon dake jikin sa ya fiddo ya miko min a zuwan muyi hannu, na girgiza masa kai cikin murmushin karfin hali, sabida gabadaya na shiga damuwa da ganin yanayin sa na rashin lafiya, kafin nace.

“We, (muslims), bama handshake da mazan da ba muharraman mu ba, kai ko da yayyen mu maza ne al’adar mu bata yarda ba.” Da sauri ya maida hannun sa cikin aljihun shi yana apologizing. Na fahimci ba da hakuri a inda ya san yayi kuskure na daya daga cikin kyawawan halayen sa, koda kuwa ga wanda ke kasa da shi ne. 

Yace “na so in san hakan kuma fa. I’m just desperate da son sanin abinda ya hanaki halartar karatun ki yau. Bayan yau bani da aiki amma naje station don kawai in gan ki.  Na je har department din da aka kai ku da kaina na yi bincike na gane you are an intern.”

“Ba na jin dadi ne Mr. Hamzah, shi yasa ban je ba” cikin rausayar da kai ya ce “nima haka Siyaam, tunda muka rabu nake wani irin zazzabi-zazzabi masassara-masassara, ban iya tabuka komai ba dana koma gida, yau kuma dana je office ban iya yin komai ba saboda tunanin abinda ya hana ki zuwa. Are you feeling the same? Kalle ni da kyau Siyaam, ba haka nake ba jiya kafin haduwar mu, gabadaya kin hargitsani kin hanani sukunin zuciya Siyaam, why?”.

Lumshe idanuna nayi ina fadi a zuciya ta “gara Allah ya rama mini, ni yau shekaru goma kenan baka bar ni na yi barci mai nutsuwa ba, baka bar zuciyata ta huta ba, da ka san wacece Siyaam a kan Hamzah, da baka yi korafin na hana ka barci dare daya ba. Ina jin sanadin zuwa na kasar nan ma kai ne, da Abba bai kore ni a kan ka ba da ban zo ba.

Kawai sai hawaye suka balle a idanu na, hawayen kewar Abba na da nadamar abinda na yi masa. Yau ga Hamzan ya bayyana gare ni amma bai tashi bayyana ba sai a matsayin mushriki wanda aure tsakanina da shi haramtacce ne. Kuka nake don sanin cewa duka wannan emotions din nawa na banza ne, garin banza ne a farau-farau din banza zasu kare,  tunda bani da damar auren sa don cimma burin wannan soyayya. Har ila yau, kuka nake na farin cikin ganin cewa Hamzah ya damu dani shima yau, yayi tattaki da kafafun sa ya zo har kofar gidan mu a domi na. 

Amma duka in vain a haka zamu kare, a kalaman fatar baki, a alaqar kofar gida da bakin hanya, don kuwa ba zan yi Ridda in bar addini na na gaskiya a kan sa ba, kamar yadda naji an ce mata da yawa marassa imani na yi a kan sa…….

Kwantar da kai nayi jikin motar Hamzah Mawonmase na yi kuka na yi kuka, kukan da zai ishe ni samun sanyin zuciya don na hanga na duba bani da riba a soyayyar dana ke yi wa Hamzah, don kuwa ba zan yi Riddah a kan soyayya ba, sannnan Abba na da Ummati ba zasu taba amanna da shi ba koda zargi na a kan shima ya fara jin abinda nake ji a kan sa ya zama gaskiya.

“Oh my God! Siyaam, what happened?” Ya fada muryar sa na rawa, kamar yadda zaciyar sa da jikin sa bakidaya ke raurawa da wannnan kuka na Siyaam da bai san dalilin sa ba. Shi ba abun ya rungume ta ba domin ya lallashe ta, tunda yanzu ta gama gaya masa handshake haramun ne to balle kuma runguma. Shi kuma ba abinda yake so yayi mata a lokacin banda tight hug din ko taji irin yadda zuciyar sa ke harbawa a kan ta. Ko ta ji yadda kukan ta ya tada tsigogin jikin sa. Ya dugunzuma kowacce nutsuwa da ya mallaka. 

“Oh! Siyam, ki yi wa Allah ki taimakeni ki daina kukan nan. Na fadi wani abu ne wanda ya bata miki rai? A shirye nake da in durkusa akan guiwoyi na in baki hakuri in dai hakan zai sa ki daina kukan nan, ki kuma gaya min damuwar ki.”

Na soma share fuska ta da bayan hannu na bayan na samu sassauci ta hanyar kukan da nayi. In banyi kuskuren fahimta ba jikin Hamzah Mawonmase yana rawa ne yana kuma kokawa da hannayen sa a iska da ke matukar son su kai min runguma. Da sauri na ja da baya ina rufe fuska da gefen gyale na, ina fadin ka yi hakuri “baka yi min laifin komai ba, na tuna Abba na ne, wanda yau shekaru hudu rabon da in saka shi a ido na.”

Hamzah yace “Abba kuma yana raye?” 

Nace “alive and healthy, na yi masa laifi ne.”

“Tell me little about you Siyaam?”

“Me kake son ji? Labari na is unbelievable ga duk wani mai sahihin hankali. Domin labari ne dake tafiya tsakanin MAFARKI da IDO BIYU. 

Babu kuma wanda zai gasgata cewa mafarkaina daga Allah ne. A yanzu na gama samun tabbatuwar mafarkai na, bani da sauran buri a kasar nan, zan gayawa marikana cewa zan koma gida Mambillah in nemi gafarar Abba na ya yi min aure da dan uwa na da na tozarta shi a kan….”. Na yi maza na toshe baki na cikin jin kukan ya dawo min gabadaya. Da nadamar subutar bakin dana ke yi.

Cikin tashin hankali Hamzah ya nutsa hannayen sa cikin lallausar gashin kan sa. Ya runtse idanun sa ya ce “in kika yi hakan baki yi mun adalci ba. Don me zaki shigo cikin rayuwa ta dare daya ki hargitsa ni sannan kice min wai zaki gudu ki auri dan uwan ki? 

Ban gane maganganun da kike yi ba as if kin dade da sani na. Na roke ki ki gaya min komai a kanki including mafarkan ki din nan. Ki fidda ni duhun da kalaman ki ke sanya ni. Ban yarda wai jiya kika sanni ba Siyam, tunda har kin batawa Abban ki a kai na”.

Kukan da nake rikewa na cigaba da yi, ba abinda nake so a lokacin sai ganin Ya Omar in nemi gafarar sa, in gaya masa ban ci ribar komai a soyayyar dana yi wa Hamzah ba, domin da ya tashi bayyana sai ya bayyana a matsayin wani mutum da aure tsakanina da shi haramtacce ne. A matsayi na na ISLAMIC SCHOLAR wadda ta nazarci Islamic Mysticsm and Jurisprudence (Tasawwuf and Fiqh) bana bukatar sai wani ya fahimtar da ni cewa aure tsakani na da shi haramtaccen abu ne. Soyayyar dana shekara goma ina yi masa ta tashi a banza!

Bansan abinda nake fada ba domin daga karkashin zuciyata maganar take fitowa. Ina so ne kawai in amayar masa da ko kadan cikin wahalar dana sha a kan sa. Don in na bar abin a raina ni zai kashe. A kalla ko bai yi min abinda nake so ba wato ya dawo musulmi, to ya dandana  suspense din dana kasance a ciki na jiran zuwan sa. Amma bai tashi bayyana ba sai a matsayin wani mutum da bazan taba iya aure ba.

“Yaya zaka ji a ran ka idan ka kwashe shekaru goma kana mafarkin wani mutum da baka sani ba, da burin kasancewar sa mijin auren ka (uban ‘ya’yan ka), ka bata da iyayen ka da suka gama yi maka kowanne irin gata na duniya a kan sa, ka bijirewa auren dan uwan da ya wahalta maka tun haihuwar ka har girman ka a kan sa? 

Amma sai kawai ya bayyana gare ka a matsayin wanda bai yi imani da Allah da Manzon sa ba?

Na bar ka da wannan Mr. Hamzah, ina yi maka fatan alkhairi.”

Ina gama fadin hakan na juya da sauri zan shige gida don bana so ya ga hawayen karshe da suka tsirgo min tun daga tsakiyar jijiyoyin ido na. 

Sai ji nayi wuf! Hamzah ya rike hannu na daga baya da karfin da ban isa in kwace ba. Ya ce “kada ki haukatani Habeebty. Ki fidda ni duhun da kalaman ki suke dada jefani. I’m intrigued!

Na kasa fuskantar inda zantukan ki ke dosa. Na rantse ban fahimci komai a cikin zancen ki ba. Abu daya na fahimta na yi miki laifin da ya karya miki zuciya.

Kasancewa na Christian ne ko?”

Da sauri na juyo na dube shi da jajayen idanuna da ke jike da hawaye. Ban so ya fahimce ni haka da wuri ba, na so ne in bar shi cikin suspense din da zai yi ta caccakar zuciyar sa. Kamar yadda ya shekara goma yana caccakar tawa zuciyar. Da alama mai dimbin basira ne wajen maida theory ta koma practice da kuma saurin fahimtar magana. 

Wani lallausar murmushi ya sakar min, ba tare da ya cire idanun sa daga cikin nawa ba. Ba tare da ya yarda ya saki hannu na ba. Sosai ya kara damke shi cikin nasa har sai da kashin hannu na ya amsa. Ya ce a tausashe. 

“Zan iya wiping tears din nan da hannaye na?” 

Da sauri na girgiza masa kai alamar a’ah. Sai ya zaro hankici da dayan hannun sa dayan kuwa na rike dani tamau bai sake ni ba, yayi amfani da shi wajen tsane hawayen idona ba tare da fatar hannun shi ta shafi fatar fuska ta ba. Sannan ya hada hankacin da hannaye na ya dunkule su cikin nasa.

“Ina so ki sa a ran ki cewa kasancewar ki MUSULMA ba yin kan ki bane ba. To haka nima Hamzah dana kasance CHRISTIAN ba yin kaina bane. Amma idan har zaki iya aure na a addinin dana ke, nayi miki alkawarin wanzar da soyayyah da kauna da farin cikin rayuwar aure mara yankewa till eternity har ranar karewar numfashin mu. 

Ban taba haduwa da macen dana ji ina so in aura ta zama uwar ‘ya’ya na ba sai ke Siyaam. Tun daga gani na da ke na farko naji a jiki na ke din mata ta ce.

Ban ce ki bar addinin musulunci ba nima bazan bar addini na ba. Aboki na Muhyideen ya taba gayamin akwai aure tsakanin mu da ku…… Addinin ki na gare ki nima addini na yana gare ni. 

What matters most is the pure LOVE that binds us together. Cikin girgiza kai nake kici-kicin kwace hannu na daga nasa. 

“Sakar min hannu, wannan haramun ne a addini na. Baka isa ka sa na yi RIDDAH ba, irin wadda aka ce mata na yi a kan ka. 

Son da zuciya ta take maka bai yi isar da zai fidda ni a addini na ba. 

Ko waye ya gaya maka wannan fatawar katoton jahili ne. Babu aure tsakanin Musulma da Kirista..”

Na yi nasarar kwace hannaye na nayi cikin gida da gudun gaske. Na bar Hamzah tsaye standstill yana so yayi repenting kuskuren sa na rike hannu na da yayi. amma ban bashi wannan damar ba.

Da a ce Passport dina a hannu na yake, kuma inada kudin jirgi, babu tantama a yau ba sai gobe ba zan koma Mambillah.

Tun daga ranar ban kara zuwa VOA ba na watsar da karatun, musamman da ya kasance iyayen riko na basa gari so basu san cewa bana zuwa karatu na ba. Har zuwa ranar asabar da Anty ta dawo daga Atlanta. 

Anty ta ganni kozai kozai da ni babu kimtsi da jemammun idanu, domin kuwa yadda nake ganin rana haka nake ganin dare bana iya barci da tunaninnika daban daban, na Hamzah ne, na halin da yake ciki ne, ko kuwa na yadda zanyi na nemo Umar ne? Ko kuwa yadda zanyi in koma gida Najeriya ne in nemi gafarar Abbah?

In gaya masa cewa na gane babu wata riba a cikin kin bin maganar iyaye. Duk wanda yayi SAKACI da biyayyar su zai ga abinda ba daidai ba. Hamzan dana saba masa a kan sa, ban same shi musulmi ba sai katon kafiri.

Aunty Nasara ta dimauta da ganin halin dana ke ciki. Ta yi tambayar duniyar nan nace mata babu komai gida kawai nake so in koma. Da budadden baki take kallo na tace “karatun ki kuma fa? In kin yi hakuri kin karasa zaki koma ne ai. Ni ko dai bayan tafiya ta wani abu ya faru a gidan nan ne?”

“Ba abunda ya faru Anty. Kawai na san ban kyautawa Abba ba. Zan koma ne in nemi gafarar sa in kuma nemo Ya Omar, in gyara kuskure na.”

Aunty ta dube ni ba don ta yarda ba abinda ya farun ba, a sanin ta Siyamar ta bata boye mata komai da ya shafe ta amma yau ta tabbata akwai abinda nake boye mata.

Amsa ga zargin ta sai ga pop-in messege na shigowar sako a wayar Siyama, wadda take aje a kusa da cinyar ta. Idanun ta ya kai ga sakon da ya shigo ganin cewa an rubuta ‘Mr. Radio’.

Wuf tayi ta dauki wayar kafin na kai hannu na, ta bude sakon. Alhalin tana mitar..        “Ni na san tabbas akwai wanda ke da alhakin birkita min ke Siyama. In kuma har ban yi kuskure ba, bana raba dayan biyun HAMZAH MAWONMASE NE!”

SIYAAM,

“IDAN NI NA KARBI NAKI ADDININ ZAKI FASA KOMAWA NIGERIA?”

                                                                                  -HAMZAH                                                     

<< Sakacin Waye 25Sakacin Waye? 27 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×