A Brave Man From Berom Kingdom
Tafe yake a kan titin da zai kai shi gidan sa, bayan rabuwar sa da Nasara bai koma office ba kai tsaye gida ya nufo. Yana tukin amma hankalin sa baya jikin sa. He cannot afford to lose this pure soul and beautiful damsel, and he cannot quit his religion da sauki GrandMa bata tsine masa albarka ba.
Ba Grandma ce damuwar sa ba a baya Siyaman ce, ko zata so shi alhalin yana Christian tana Moslem? Wannan ita ce damuwar data sabbaba masa zazzabi da masassara bayan rabuwar su. Sai kuma yau ya ji wani labari mai ban al’ajabi which was unbelievable ga duk wani mai hankali. Siyaman da yake shayin samun soyayyar ta tun daga ganin farko da yayi mata ta riga shi fara son sa. Ita nata son ma bai taba jin mai irin sa ba. Ya samu kan sa a cikin wata irin soyayya cikin dan kankanin lokaci wadda bai taba tsintar kansa a ciki ba. Ya ji yana burin mallakar wannan sahihiyar soyayya dake dankare a ruhin Siyama a gidan aure. It will be a great achievement su zama miji da mata. Labarin da yaji daga daga bakin Nasara ya ninnika soyayyar da yake mata sau dubu saba’in da ta baya.
A wannan lokacin Hamzah gumi yake yana yarfewa yana kuma cigaba da tuki zuwa gidan sa, duk da na’urar sanyaya mota da sanyin birnin Washington D. C, duk da ya san cewa he’s BRAVE a kan duk abinda ya sanya kansa amma yau sai ya ji yana shakkar haduwa da Kakar sa, idan ya tuna yadda fuskar GrandMa zata kasance yana idan yana labarta mata ya samu matar da kullum take masa addu’a, amma musulma ce.
Ya sani sarai Kaka will throw a tantrum like a thunder, she will extremely mad and she will disown him (kaka zata yi bala’i kamar kwarankwatsa, zata haukace da bacin rai kuma zata daga masa nono) bayan ita kadai ya mallaka a duniya da zai kira uwar sa ta jini kuma uban sa sannan dangin sa. Yana girmama ta yana karrama ta kamar shi ta haifa ba mahaifin sa ba.
Wannnan ya samo asali ne sabida ta raine shi tun yana shekara biyu. Kaka ta yi sana’ar sayar da Cocoa da Dankalin turawa wanda take nomawa da kanta a Barkin Ladi. Don dai kawai yayi karatun zamani bayan da ta gane amfanin sa. Ko a cikin addinin Kirista Kaka Pastor ce wato malamar addinin kirista. Tana matukar bakin cikin yanayin rayuwar sa ta rashin maida kai a addini da abokantaka da ‘ya’yan musulmi. Kullum cikin fargabar kada yace zai musulunta take.
Bai samu shiga firamare da wuri ba sabida a lokacin Kaka bata yarda da karatun boko ba, wanda turawan missionaries suka kawo Jos. Sannan bata da komai da zata iya yi masa hidimar karatu sai filin gona da bata fara shuka komai ba.
Babban abokin sa shine Hamzah Mustapha wani yaro wanda musulmi ne gidan su na makwabtaka dana juna, Hamzah yana zuwa makarantar firarmare sabida iyayen sa na iya biya masa, sai su tafi tare shi ya zauna a waje yana leken su yana karanta abinda ake koyar dasu. Sabida shi Kakar sa bata saka shi a boko ba. Sunyi wata irin shakuwa da Hamzah Mustapha domin tare suka taso ko barci baya raba su a gidan su Hamzah yake kwana a yawancin lokuta.
Kaka na matukar kin musulmai amma bata kin yaron nan Hamzah domin ta ga kamar Mawonmase ba zai iya rayuwa ba tare da shi ba. Sannan kuma tana lura da duk wani takun su, Hamzah baya koyawa Mawonmase addinin sa, abokantakar su is purely friendship daga Ubangiji.
Rana daya Hamzah ya soma rashin lafiya bayan ya kammala Firamare, amai da gudawa na annoba ya tafi da yaro Hamzah Almustapa. Ba karamin gigita Mawonmase ya shiga ba saida iyayen Hamzah suka tausaya masa domin kwanciya yayi shima yayi ta rashin lafiya. Da kyar aka samu kansa ya warke ya koma rayuwa shikadai cikin takura da damuwa. Baban Hamzah ya zo ya samu Kaka ya lallashe ta akan ta bar Mawonmase ya shiga makarantar Sakandire da kwalin Hamzah tunda Allah yayi shi ba zai mori ilmin ba, ya nuna mata alfanun yin ilmin zamani ga ‘ya’ya musamman maza, ya kuma ce in dawainiyar karatun ce bazata iya ba shi zai dau nauyin karatun Mawonmase. Kaka tace “musulmi na da kirki da son mai son nasa, ta yarda albarkacin marigayi Hamzah jikan ta Mawonmase ya shiga sakandire da sunan sa”.
A lokacin noman cocoa da dankali data fara ya fara albarka. Ta dauki nauyin karatun Mawonmase da kanta. Ta kuma je makarantar ta ce lallai a kara da “Mawonmase” a cikin sunan sa don shine sunan sa na yare kuma na al’ada mai nufin ‘I PRAYED AND RECEIVED’.
A haka rayuwa ta mika musu shi da Kaka wadda sunan ta na ainahi Veronica. Tana noma duk shekara, tana nome dankali mai yawa da Cocoa shi da ita su sayar a kasuwa. Ya iya aikin noman dankali wanda da shi ya budi ido, tun yana karami yake da buri akan noma sabida abinda ya budi ido da shi kenan.
Tun yana sakandire Allah yayi masa baiwa ta iya magana a gaban mutane (Public Speaking) da iya sarrafa harshe. Ya iya darasin Hausa ya iya na turanci kamar me. Kaka bata san cewa Linguistics ya cike da zai shiga jami’a ba inda ya zabi Hausa da Turanci zallah yayi Degree a kan su. Bayan kammala digirinsa na farko ya samu aiki da wani gidan talbijin mai zaman kan sa a cikin garin Jos ya fara aiki yana taimakawa Kaka, sabida a lokacin ta fara tsufa.
Aiki da ya samu bai sa ya bar noma ba, suna noman Dankali shi da Kaka har zuwa lokacin kuma duk Lahadi da shi take zuwa Chochi bata bari yayi sake da addini don shigar sa jami’a ya sa mu’amalar sa da Hausawa da musulmai ta karu. Abin kamar a jinin sa yake na cewa abokansa musulmai ne, musamman Muhyidden Tokumbo Adesola, Bayerbe amma musulmi.
Kamar da wasa a wata shekara ya gwada applying masters da CHEVENING Scholarship. Cikin ikon Allah yayi nasara ya samu tafiya karantar Kimiyyar Yada Labarai a Jami’ar Sussex din Birtaniya. Tsahon shekara daya kacal ya kammala ya samu aiki da BBC London inda yayi internship, yayi aiki na shekaru uku kafin DEUTSCHE WELLE radiyon Jamus su gane shi, su kwace shi ya koma Germany yayi aiki na lokaci mai tsaho tare dasu.
Wadannan damarmakin ne suka sa sunan sa yayi fice ya shahara a duniyar international media, yafi karbar sashen Hausa kuma a nan yafi kwarewa. Da daukakar sa ta yi daukaka a iya broadcasting sai VOA suka gayyace shi suka kuma ninnika masa abinda Deutsche Welle ke biyan sa, suka sake wuf dashi daga Germany. A yanzu haka yana cikin masu ruwa da tsaki kuma ‘yan gaban goshin “Voice of America”, yana jagorantar Department guda (Media and Publicity) wanda ke gabatar da programs na duka Turanci dana Hausa, sannan akwai masu gabatarwa da sauran yarukan duniya 48 da VOA ke amfani da su wajen yada shirye shiryen su.
Ana zargin sa da yaudarar mata iri-iri saboda farin jinin sa. Ba zai manta da Sarina Miqdad ba, ‘yar asalin garin Katsina data bar musulunci don ya aure ta. Ita kadai ce kuma sau daya ne hakan ta faru amma kasancewar sa a fuska da kunnuwan duniya anyi exaggrating abin fiye da kima cewa yana hurewa mata kunne su bar addinin su, kuma ba auren su zai yi ba sai dai ya raba su da mutuncin su. Zai iya rantsuwa da littafin sa bai taba zina da ‘yar kowa ba, kuma bai taba neman soyayya daga kowacce mace ba, domin ya raina su, sabida yadda basa daraja kan su suke masa tayin kan su kamar akan faranti. Mafari kenan da har kullum yake ganin cewa ba’a haifi matar da zai iya aura ba.
Daga ranar 30/12 na shekarar da ake ciki, wanda yayi daidai da cikar VOA shekaru 80 da kafuwa yayi wannan gamon da katar din. Ya ganta tsaye jikin motar abokiyar aikin sa Mrs. Alkali. Ba komai ya ja hankalin sa kanta ba sai tsananin kyawunta na fulanin usuli da kuma kallon tsanar sa da jin haushin sa da ke cikin idanun ta.
A matsayin sa na dan jarida mai jiran kiris, a take ya saka mata capital ayar tambaya na meye business din ta da shi har haka da take masa wannan kallon tsana da sanayyar?
A ranar da glimse din fuskarta ya kwana, ko yaya ya rufe ido sai ya ga wulgawar fuskar ta, which is very unlike him yayi ta son sake ganin mace don ya ganta sau daya amma ita wannan ya kwana ne da begen sake ganin ta koda sau daya ne a rayuwar sa.
Rannan kamar cikin sa’a ya hango ta tare da Mrs Alkali again suna fita daga federal builing tana gaban motar su tana saita daurin kallabin atamfar ta. Gashin kanta ya kwanta lambam a dokin wuyanta baki sidik da shi mai sulbi da sheki. Ya kura mata ido yana fadin “Jesus Christ!” Daga ranar kuma kamar kiftawar ido tunda suka bace masa bai kara ganin ta ba.
Ya sha tunain ya je ya samu Nasara Alkali har ofishin ta ya yi mata tambaya a kan ta. Sai kuma yayi tunanin bai dace ba. A wane dalilin zai yi hakan tana Musulma yana Christian?
Untill that fateful day da yayi arangama da ita a cikin lifter. “Oh Dear Jesus!” Abinda ya fada a ran sa kenan. Ya kuma ji cewa ba zai iya barin wannan damar ta wuce shi ba, ba tareda ya yi amfani da ita ya ji dalilin kallon haushi da sanayyar data ke masa ba.
Abinda ya biyo bayan haduwar mai girma da nauyi ne da ya shallake tunanin sa…., ya shallake tsammanin sa akan diya mace. Ya yarda akwai mata masu aji ba duka ke ruduwa a kan maza su tallata kan su ba. Musamman in suka samu ‘yar dama komai kankantar ta na cewa namiji mai aji da mukami ya kula su.
Daga wannan ranar shi ya san bai kara barci ba, sai na tunanin yadda zai yi ya mallake ta, ya kuma haifi ‘ya’ya tare da ita masu kama da ita.
Banbancin dake a tsakanin su mai girman gaske ne, da bai san yaya zai yi da shi ba. Islam and Christianity are never in comparison. Balle ace magana ce ta aure da soyayya. Dan hope din da ya samu a lokacin shine Muhyiddeen ya ce akwai aure tsakanin musulmi da kirista.
Bai bashi bayanin a bude ba, sai ranar da ya taka ya je gidan su Siyama. Ta fada masa hakan da kakkausar murya cewa ba mai yuwuwa bane. Kuma bazata bar addinin ta sabida soyayya ba. Duk da bata bashi komai a bude ba, a ranar ya gane ta dade tana masa wani irin so na hakika. Kawaici da sanin darajar kai ne irin na ‘ya’yan musulmi yasa ko a fuska bazaka gane hakan ba.
Yau kuwa Nasara ta bashi komai a bude. Labarin da ya jefashi cikin wani yanayi na karin soyayyar Siyama, ya kuma jefa shi cikin wani hali na kaka-nikayi. Zuciyar sa ta yi mata katuwar shimfida mai fadi da laushi da girma da wani irin respect da yafi karfin harshe ya bayyana shi. Respect ne mai tuna cewa; soyayyar da ta dade cikin wahalarta bata ma san shi a zahiri ba, is just in imaginations and fantasies na rayuwar mutum, sannan duk karfin soyayyar bazata bari ta raba ta da addinin ta ba.
Maimakon hakan, ta zabi ta koma kasar ta ta bar masa kasar, ta auri dan uwan ta, domin ta gyara kuskuren ta, akan dai ta sake ganin sa, daga lokacin da taji daga bakin sa cewa shi ba musulmi bane.
Ajiyar zuciya mai nauyi Hamzah yayi da tunanin sa ya zo nan. Daidai lokacin da ya iso gidan sa, yayi parking a inda ya tanada don ajiye motocin sa, ya kifa kai a kan sityari ya kasa fita daga motar ya kuma kasa kashe ta.
Zai so ya auri wannan kamilalliyar yarinya da ke masa so daga Allah, ba don wani abu da ya mallaka ba, ba dan ta san shi ko ta san waye shi ba. Ya amince there will be something special a tare da ita daga Ubangiji da ya tanadar masa, kuma watakila itace haske ga rayuwar sa.
Ya dade yana challenging addinin sa, ya dade da sanin cewa addinin musulunci shine addinin gaskiya, ya dade da sanin cewa Allah is ONE. Who created the universe and mankind ba tare da ya aure su ko ya haife su ba.
Ya dade da sanin wannan a karan kansa.
He’s a christian because he was born into christianity. Bai taba tunanin canza addini ba, bai taba tunanin cewa wai sanin hakikanin gaskiyar da yayi zai sa ya canza addinin da ya tashi a ciki ba. Yafi gane a je a hakan don a zauna lafiya. Musamman da ya san cewa ba zai iya jure sallah da suke yi da alwallah sau biyar a rana ba, da sauran obligations masu wuya na addinin.
Amma yau?
Hamzah ya kama kansa ya nutsa hannun sa cikin tarin lallausar sumar kansa yana damkewa.
Sequel to labarin da ya ji a kan yarinyar daga bakin marikiyar ta, bayan nashi feeling din na karan-kansa da ya yi developing cikin dan kankanin lokaci a kanta, labarin da yaji din have raised a deeper amount of love than ever. Bai san mai future ta tanadar masa ba, bai san me kaddara ta ajiye masa ba, amma zai gwada karbar addinin musulunci in dai shi zai bashi damar samun AISHA-SIYAMA. The pure soul that he can never resist for the sake of religion.
He will give it a try.
Nasara ta masa alkawarin sanya Siyama daukan wayar sa. Ya kintata ya ga cewa zuwa yanzu ta dade da isa gida. Jikin sa rawa yake yi zazzabi na shigar sa. Yatsun sa ya samu da daukar wayar sa a gefe suka hau dialling no. din Siyama wadda cikin dan lokaci ya haddace nambobin a cikin kan sa.
Har tayi kukan ta ta gama ba’a dauka ba. Shi kuma bai hakura ba ya sake kira a karo na biyu. Har sai da ta kusa katsewa kafin ya ji alamun Siyama ta daga. Amma bata ce komai ba, bayan dagawar da ta yi, shi ba musulmi ba balle ta nema masa aminci daga Ubangiji ta ce masa “Assalamu Alaykum”. Sannan ita ba gwanar fara waya da “Hello” bace. Sai kawai tayi shiru tana numfarfashi, domin yanzu Aunty Nasara ta gama gaya mata Mawonmase yau a ofishin ta, ya durkusa da guiwowin sa ya roke ta alfarmar ta bar shi ya yi magana da ita.
Tace “na duba cewa Oga na ne duk da wannan ba office affair bane amma ya cancanci in masa alfarmar da ya roka albarkacin zaman tare, ban san ranar da nima zai iya yi min a rayuwa watarana ba.
Siyama ki amsa in ya kira amma sau daya kawai. Sabida shi bazaki bar karatun ki ba, bazaki bar addinin ki ba, sannan bazaki fasa rayuwa ba.
Ba don shi aka halicce ki ba. An halicce ki ne don ki yi bautar Allah ki tashi ranar lahira cikin al’ummar Annabi Muhammad SAW.”
A fakaice nasihar Anty; is a food for thought, tana kara tuna min cewa in tsaya a iya limit din da addini na ya bani tsakani na da wanda ba musulmi ba. Wanda kuma zuciya ta ke matukar son sa.
“Siyam, kina ji na?”
Muryar sa cikin sassarfar ta data rasa karsashi ta tambaya. Bai kuma jira abinda zan ce ba ya dora.
“Ki sa a ran ki baki yi mafarkin gaibu a banza ba, baki yi wahalar shekaru masu yawa cikin fantasy and infatuation a banza ba, baki bata da Abba a banza ba, baki bar Umar sabida ni a banza ba…. Hamzah must pay for all these, more than that, zan biya ki soyayyar ki ta shekara goma in a unique way that even myself HAMZAH i cannot express it. Amma lokaci zai nuna, gangar jiki na da zuciyata zasu nuna idan mun zamo miji da mata.
Siyam, na zabi karbar muslunci sabida ke, kuma zan shirya ki da Abba this is my responsibility. Da yardan Allah sai Abba yayi alfahari da ni a matsayin surukin sa kamar yadda zai yi alfahari da Yayan mu Omar.
Siyam, zamu dauki ciki tare, mu raine shi tare mu yi nakudar sa tare mu haifi ‘ya’yan mu masu albarka ni da ke. Mu yi musu tarbiyyah ta musulunci ….”. Kuka mai karfi ne ya ci karfi na, domin na hango wannan mafarkin nasa has a long way to go before it’s actualized, kamar yadda nawa mafarkin ya dauki dogon lokaci yana watangaririya kafin ya tabbata. Kawai sai na kashe wayar cikin rishin kuka da rashin sanin abin cewa.
Kafin kwana ukun daya alkawartawa Nasara ya gama yanke shawarar da yake ganin ita kadai ce zata sa ya samu Siyama. Wato ya koma nata addinin komai tsaurin sa.