Na yi miki alkawarin kauna da soyayyahr zahiri ba irin ta mafarki ko imagination ba. Na yi miki alkawarin zaman aure na amana, zamu zamewa juna not only miji da mata but ‘yan uwan juna kuma abokan sirrin juna. I will make sure I made it up to you for the ten years you suffered. Come into my life Siyam, na miki alkawarin ba zaki nadama ba…..”.
Wannan karon da matukar fargaba da tangardar harshe Hamzah ya karasa maganar kuma duk yadda yayi kokarin gudun haduwar fatar jikin mu bai iya kasa tallafo fuska ta cikin tafukan sa ba. “I wish I could wipe away these tears with my tongue Siyam… I wish…..”. Na yi maza na janye fuskata daga cikin tafukan sa cikin tsananin kunya.
“Ba kyau, ka koma kan kujera”. Karo na farko dana yi magana tun shigowa ta falon cikin karfin hali. Ilahirin jiki na tsuma yake da tsumin soyayyah. Ya kwaikwayi maganata shima kafin yace “komai ba kyau komai ba kyau Siyam, har rarrashin ma?” Nayi wani irin harrr da idanu na na turo baki nace “ai baka biya sadaki ba ne”. Hamzah ya tura duka hannayen sa cikin sumar kan sa, yana fadin “Siyama ki bar ni in zauna lafiya da addini na, kafin ranar da zan mallake ki, in rungume ki yadda nake so in kuma tsotsi albarkar dake cikin dan bakin nan mai furta min ban biya sadaki ba, I will kisssss it in the way and manner da zan tabbatar masa da cewa sadakinsa mai matukar daraja ne!”
Da sauri na ja mayafi na na kara rufe fuska ta. Ya bi yatsun hannun Siyama da kallo wadanda bai taba ganin yatsu masu tsayi da kyawun su ba. Anya zai iya cigaba da zuwa zancen nan a sauran kwana biyun da suka rage? Ko dai ya roki Young Abba a daura auren a nan ba sai an je Najeriyar ba? Sai ya tuna shi kan sa Young Abban ba shi ya haifi Siyama ba, duk da cewa shine madaurin auren ta bai kamata ya yi kan gaban kan sa ba, tunda yana da na gaba da shi da kuma mahaifiyar su a raye.
Bai san meyasa ba amma tsoro yake ji, tsoron kada a je Najeriyar Kakar Siyama da Baban ta su ki shi, musamman in ya tuna akwai dan uwan ta da dukkan su suke so ta aura.
Wannan tunanin kadai ya fadar da gaban Hamzah ba dan kadan ba. Bai san sanda ya ce “Siyam, kin yarda Abban mu ya daura mana aure a nan? I’m sorry Siyam, ina tsoron haduwata da Abba da Ummati, ina tsoron su ji cewa da can ni ba musulmi bane, ina tsoron muje gaban su su raba mu, ko mu tarar da Omar ya dawo su bashi ke su hana ni.”
Ba muryar sa kadai ba, hatta siraran lebban sa rawa suke yi cikin rauni a lokacin da yake wannan hasashen (in despair) wato cikin fidda rai. Sai na ji nima tsoron ya mamaye ni, har fiye da wanda yake cikin kwayar idanun sa, Abba na mai wuyar sha’ani ne, tunda dama ba wai ya yafe min bane a kan kasar dana bada masa a ido, a yanzun haka kuma zan iya sunsunar abinda zai ce a kai,
“An guji Da na Omar da ba’a yi wa son soyayya, an komawa wanda ake so, abin dariya kuma ahlil kitabi. To Umma ta gaida Aisha.”
Na tabbata abinda Abba zai ce kenan. Ba zai sanya albarkar sa ba, in har ba Omar ne ya dawo gaban sa ba. Ummati kuwa ko duk duniya zata taru a kan ta ba na jin zata amince da Hamzah.
“Faduwar gaba asarar namiji ce in ji hausawa”. Hamza ya fada cikin murmushin karfafa guiwa. Ganin yadda kamanni na suka canja gaba daya har na fi shi tsoracewa. A hankali na runtse ido na ce.
“Young Abba ko ni ko kai babu wanda zai yi karya a kan background din ka, tunda kuwa albarkar su muke nema”. He felt relieved, daga nan ya roke ni kan mu koma bisa kujera guiwar sa ta gaji da durkuson neman soyayya. Wannan karon ma mayafi na na ja na kara rufe rabin fuska ta ina murmushi, na lura wannan kunyar tamu ta fulani da rufe ido cikin kallon So, na matukar impressing din sa.
“Yau hira zamu yi sosai irin wadda bamu taba yi ba Siyam, ki daina yi min wannan kunyar mun wuce wannan stage din. Adana min ita zuwa lokaci mafi dacewa. Because……because it’s arousing something in me..”. Ya fada kamar yana tsoron wani a bayan mu ya ji shi. Naga alama yau Hamzah so yake ya kashe ni da raina.
Bai damu da reaction dina ba ya cigaba da bani labari. “A can inda na yi makaranta (University of Jos) na sha haduwa da fulanin Taraba dana Adamawa, na dade Fulani suna burge ni, domin an ce sun fi kowa kunya a duniya. Unknown to me daga tsatson su zan samu ‘ya’ya na.
Da gaske ina son kunyar domin ado take zame muku. Kina matukar burge ni Siyam.” Hamzah ya fada cikin ravishing smile. Ya kara da cewa “ki cigaba da yi min wannn kunyar ina matukar son ta, amma please banda a gadon amarcin mu.”
Ai jin haka naji tamkar na nitse a kasa don kunya, na mike zan bar falon. Bayan na ambaci sunan sa in exclamation “Hamzah!”
Da mugun sauri ya sha gaba na “in ba so kike in yi abinda ba daidai ba don Allah ki koma ki zauna. Na tuba na bi Allah na daina!”
Wani kasaitaccen murmushi ya kwace min, he is always apologizing a inda ya kuskure, na koma na zauna, wannan karon a kujerar dake fuskantar sa shima ya zauna a opposite dina. Har ajiyar zuciya na saki, domin zaman sa daura da ni dazun ya maida ni uncomfortable ba dan kadan ba. Tasirin da Hamzah ke da shi a kaina mai yawa ne, mai girma ne, kuma mai ban al’ajabi ne.
Yau da yake durkushe gaba na wai da sunan neman amincewa ga auren sunnah tsammani nake yi cikin mafarkan nawa dana saba da su ne. In farka in neme shi in rasa, abin mamaki tun gani na da shi a zahiri ban kara ganin sa cikin mafarki ba.
Tamkar an yi ruwa an dauke. Haka komai ya tafi. Ban kara mafarkin HAMZAH MOWONMASE ba, sannan emotions da infatuations masu takura zuciya ta duk sun kama gaban su. A yanzu na fahimci shi kan sa Hamzan sukutum nake wa so na hakika ba son fantasy da infatuation na kuruciya ba, a’ah so ne genuine love irin na kowacce mace ga mijin da take burin ya zamo uban ‘ya’yan ta. Wanda ya hada duk abinda take mafarkin samu daga mijin auren ta.
Ina wannan lissafin na tsinkayi muryar sa a tsakar kunnuwa na.
“Tell me more about yourself and your past dreams, bayan wanda Nasara ta gaya mini?
Nima yau zan gaya miki ko wanene “Hamzah Mawonmase” bayan wanda kika sani a baya.”
Na ce “Duk abinda Aunty ta gaya maka shine hakikanin labarin Siyama. Bana jin Anti zata rage ko ta kara komai. Domin ta fi ni sanin kai na, tun daga ranar da ta dauko ni daga Mambillah ta ke studying komai a kai na. In fact, she’s my second lifestyle infleuncer bayan Aunty Wasila.”
“I can relate” in ji Hamzah, “wacece Anti Wasila kuma?” “my step-mother” “Oh! Okay. Amma shin don Allah Siyam wannan mafarkin naki ba na aljanu bane?” Dariya ce sosai ta kama ni, har tari ya sarke ni. Yayi maza ya zuba ruwa a tambulan ya mika min “sorry na sa kin kware, sorry. I’m extremely intrigued!”
“Akwai sanda step mother dina Aunty Wasila tayi hasashe kwatankwacin irin wannan, to amma Abba yasa an yi min ruqiyyah babu aljani ko daya a tare da ni. A Islam in aka yi wa mutum rukiyya in dai da aljani a jikin sa zai bayyana kan sa.” Hamzah yayi zugum! Yana duba na kafin ya ce “kuma yadda nake a mafarkin, haka nake a zahiri babu bambanci?”
Kunya ta kama ni, na kauda kai ina murmushi. Ban ce komai ba.
“Mr. Hamzah meyasa da tone-tone? Al’amari na da kai, nafi sawa a rai na cewa daga Allah ne. Because it is mysterious.
Nafi yarda da cewa Ubangiji na son ka da shiriya zuwa musulunci saboda kyawawan halayen ka da tsaftattacciyar zuciyar ka. Shiyasa ya salladoka cikin mafarkai na, ba don komai ba sai domin ya hada rayuwar mu wuri guda, ba zai yiwu a ce yadda nake ganin ka a mafarkin komai da komai haka na gan su a zahiri ba, amma kuma most of the appearances din da sautin muryar naka ne haka sautin in’inar ka. A zahiri akwai mutanen da Allah ke nunawa future din su cikin mafarkan su, na fi kyautata zaton ina daya daga cikin su. Tunda kuwa ba nake yi ba.
Tun farko ni na fara saka wa rai na ba zan auri farin mutum ba sai baki. Wai tunda ni fara ce sol. Sai na girma tare da wannan burin, wanda a hankali yayi developing into fantasy, daga nan ya koma imagination ba tare da na ankara ba.
Daga Fantasy and Imagination ne ya rikide ya koma min zuwa cikin mafarki. Ko ma yaya ne na wuce wannan jarrabawar cikin yardar Ubangiji, ina kuma kyautata zaton na haye ta da kyakkyawan sakamako tunda yau ga ni ga ka. Kuma daga ranar da muka hadu physically ban kara yin mafarkin ka ko sau daya ba, wanda ke nufin; Allah has fulfilled his mission on us (Allah ya gama ikon Sa a kan mu).
Na sha wahala mai yawa a kan ka Hamzah, na bata da iyaye na, na yi sanadin barin dan uwa na gida, na kusa salwatar da rayuwa ta duk a kan ka. Ranar da ka hada soyayya ta data wata diya mace ranar ne zaka karya min zuciya kuma ba zan yafe maka ba…”.
Hamzah ya taso daga mazaunin sa, ya dawo gaba na ya sake yin durkuso mai matukar ban sha’awa, yana leken fuskar dana ke boyewa sabida kunyar kishi na dana fiddo fili. Cikin tsokana ya ce “nima duk ranar da Yayan mu Omar ya dawo, kika canza min fuska a kan sa ko kika rage soyayyar da kike yi min Allah zai isar min Habeebty. Because I sacrificed a lot don na tsira da ke.
Yanzu haka Kakata wadda take makwafin uwa a gare ni bama ga maciji, she is about to disown me (gab take da tsine mini). Amma ji nake idan ina da ke a gida na Siyam, babu wani abu a duniya da zai kara daga min hankali.
Na shiga musulunci da zuciya daya a dalilin soyayyar ki. (Sorry), Abban mu ya ce ba’a shiga islam for any reason amma ni na shiga ne don Allah don kuma son da na tabbatar zuciya ta na yi wa Siyam, kuma ko Siyam ta juya min baya ba zan bar Islam ba, zan kare rayuwata a cikin Muslunci.
Maganar wasu matan kuwa Siyam, in na ce miki bani da ‘yammata nayi miki karya, amma wallahi babu wadda na taba takawa na je gidan su da sunan SO. Babu wadda na taba zuwa na nemi auren ta gaban iyayen ta, amma kullum baka raba su da hanyar gida na.
Ina fatan in sun ga mata ta Siyam a cikin gidan, babu wadda zata kara kuskuren zuwa inda nake.
Ba’a alkawarin rashin kara aure, amma ki tuna ni ban tashi na ga ana polygamy a tawa al’adar ba. I have found everything that I want in a woman in SIYAM!. She’s morethan enough for me.”
Na dube shi cikin cikin son tabbatar da gaskiyar furucin sa. Gesture din dana gani cikin idanun sa ya gama tabbatar da yana nufin abinda yake cewa. Sai naji tamkar Hamzah ya bani sarautar matan Najeriya. Ban san ina da tsananin kishi ba sai yau.
“Bari dai yau in baki cikakken labarin HAMZAH ALMUSTAPHA MAWONMASE. Kodayake duk abinda ya kamata in gaya miki na gaya miki shi rana ta farko dana kawo ki gidan nan. Ranar da zuciya ta ta gaya min na ga matar aure na. Amma a lokacin na fada miki a takaice ne, akwai kuma abinda a lokacin bai kamata in fada ba.
Zan baki labarin kabilar BIROM wato kabilar dana fito, wata babbar kabila ce a Najeriya da ake kira “BIROM”. Suna na asali MAWONMASE ma’anar sunan a yaren Birom shine “I Prayed and Received” (na yi addu’a na samu) da harshen hausa.
Mahaifi na Dr. Ezekeil Edward, ya fito ne daga masarautar Birom ko Berom (BIROM KINGDOM), kakannin – kakannin su sune tushen kabilar Birom wadanda aka kafa garin Riyom da su, bayan barowar su kasar su ta asali, wato Ethiopia.
Sabida haka akwai kakkarfar alaqa tsakanin iyaye na da masarautar Berom har gobe. Alaqar data sa har sarkin Berom mai ci a yanzu yayi wa Kakata tayin hada aure tsakanina da ‘yar sa Tina, taimakon da Allah yayi min na dade ina gayawa Grandma ba zan taba yin auren gida ba.