Ban san sanda na riko shi cikin hannaye na ba, sabida tsakanin Siyama da Hamzah sai Allah da ya halicce mu.
Cikin kuka nace “Ni fa baka taba yi min laifi ba Hamzah, koda da kuskure in dai Tsakani na da kai ne kullum cikinkyautata min kake. Idan ma ka yi min, wanda na sani da wanda ban sani ba, na yafe maka shi duniya da lahira.
A wasu lokutan mai kaunar ka da gaskiya yana tausaya maka azabar Allah, ya fi so ku tashi tare cikin inuwar al’arshin Ubangiji ranar hisabi. Idan makomar sa aljannah ce, ya fi so ya shige ta tare da wanda ya ke so dinnan, zai fi jin dadin zama a cikin ta har fiye da mazan aljannah ko su miliyan za’a bashi a madadin sa.
Ta ina macen da ke son mijin ta tsakani da Allah zata kasance cikin dadin rai, alhalin tana hango mijin ta an yi makamashin wutar jahannama da shi?”
“Yaa subhanallah!” inji Hamzah, “Siyama me yayi zafi? Ki fidda ni duhun da kalaman ki ke dada sanya ni”.
Na ce “kukan kurciya ne nake maka, kuma na san kana da hankali da tsinkaye (foresight) wanda ya sha banban dana mutane da yawa, in har hankalin ka har yau bai hango SAKACIN da kake yi da addini ba, to babu amfanin in yi asarar yawun baki na wajen tunasar da kai.
Saidai wani hanzari ba gudu ba Hamzah, na rantse da Allah da ya halicce ni ya halicci soyayyar dake zuciyata a kan ka, na fi son addinin musulunci da tsayar da dokokin ubangiji a kan son da nake maka, don na san soyayyar bazata amfane ni a lahira ta ba, musamman in ya kasance bana tare da kai a gidan aljannah”.
Da fadin haka na janye jiki na daga nasa, na mike na koma toilet din, alwallah na dauro na zo na sanya kayan sallata na shimfida darduma na tada sallah, na bar shi a cikin wani hali na kaka-nika yi da mutuwar jiki.
“Sakaci da addini!”.
Hamzah ya tuno kalaman Siyama, meye sakaci da addini? Ya shiga neman ma’anar kalmar ‘sakaci’ a cikin kan sa…. Kafin kakkaifar kwakwalwar sa ta halarto masa da amsa nan take.
Sakaci a turance yana nufin ‘negligence’. Kenan Siyama tana nufn tana fushi da shi ne sabida yana Sakaci da addinin musuluncin sa na yanzu, ya tambayi kan sa yaushe rabon sa da sallah? Wace rana ce bai sha giya ba tunda ya aure ta? Sai daidaiku. Ya san kuma bazata kasa ganewa ba.
Yana gani ita har azumin tadawwu’i take yi duk Litinin da Alhamis bai taba sha’awar gwadawa ba. Sai ya soma lissafin tuno daga ranar da yayi missing salloli, tun yanan kara’in su duka at a time in ya dawo aiki har kara’in ma ya gaji yaa watsar. Ya ga cewa renakun suna da yawa bazasu lissafu ba, ya mike a kasalance ya shiga toilet dina ya hau alwalah, yana ce da kan sa “Astaghfirullah”.
Saida duka kafafun mu duka suka dauka, ni nafilfili nake shikuma wai ramuwar salloli yake yi cike da nadama, abin zar takaici, na gama na kwanta na bar shi akan darduma yana ta fama.
Can kuma tausayi ya kama ni kamar ma yana yi yana barci ne. Ban san yaushe ya kwanta ba domin tuni barci yayi awon gaba dani, bayan na gama sake-saken yadda za’a yi Hamzah ya rike sallah a rai na.
Abin mamaki yau shi ya tashe ni da asubah muka yi jam’I, raina ya dan yi haske, ina addu’ar Allah yasa ya dore. Dadi na da Hamzah akwai tsinkaye da saurin fahimtar abu da kuma rashin girman kan yin repenting.
Mun koma mun dan kwanta zuwa gari ya dan yi haske mu samu mu yi wanka mu fita, ni ya sauke ni a school domin inada presentation na wani assignment karfe goma na safe shi kuma ya wuce office din su.
Sai ji nayi ya mirgino ni na dawo saman sa. “Siyam!”, Hamzah ya fada da taushin murya, “idan nace na tuba na bi Allah zaki yafe min? Wallahi ban san me yasa ba mantawa nake ban yi sallah ba, kin san abinda baka tashi cikin sa ba rana daya ka yi ‘adopting’ din sa. Sai a hankali……”.
“Sai a hankali….. kullum zancen ka kenan Hamzah, “sai a hankali, gradually”, umh. Shin yaushe wannan a hankalin naka zata zo maka? Shin itama mutuwa sai a hankali take zuwa?
Wannan fa tsakanin ka da Ubangijin ka ne ba da ni Siyama ba, duty na ne kawai in tunasar da kai a matsayi na na matar ka kuma masoyiya ta hakika, amma gaskiyar magana itace idan ka cigaba da SAKACI da addini watarana shi kan sa son da nake yi maka Hamzah na rantse neman sa zan yi in rasa…”.
Yayi maza ya toshe min baki da tafukan sa. “Kada Allah ya nuna min wannan ranar!”,
Ya cigaba da cewa, “kafin sannan har tabon sujjadah zai fito a goshi na, in Allah ya yarda”.
Sai ya maida akalar hirar zuwa irin wadda yafi so a yi, a kowanne lokaci a kowanne yanayi Hamzah romantic ne, ni kuma don in kara jan sa a jiki, kamar yadda Anti Nasara ta shawartar, zuciya ta kuma ta haqurqurtar, sai wannnan karon ban bashi mishkila ba.
Na barshi ya mori asubahin kamar ba gobe, kamar mu rike hudowar rana kada garin ya waye ya tafi nemo mana abinci, muka nishadantu, muka farantu, muka kuma gamsu da cewa, soyayyar da muke yi wa junan mu, wata ajiya ce daga Allah! Samun sabani ba ya taba ta, zukatan namu a sarke suke cikin na juna. Na yarda da cewar Hamzah da yace ‘we are meant for each other.’
Muna karya kumallo da safe bayan dukkan mu mun yi wanka mun sha ado cikin sababbin sutturah, ga kamshin turaren da kowannen mu ke amfani da shi ya kama dining din. Fuskokin mu cike da annuri kamar bamu ne masu takun sakar jiya ba. Zuwa can na aje cokali mai yatsu (fork) da ke hannu na bayan na cika bakina da ‘chips’ din da na cokalo a jiki, nace cikin rangwadar da kai.
“Shaheed, yaushe zamu je gida ne? Jiya na yi mafarkin na kaiwa Abba jariri ya kore mu ni da Babyn nawa, I was scared, it was a bad dream wanda ya tunasar dani cewa har yanzu Abba na yana fushi dani”.
Hamzah ya kurbi nescafe din sa ya aje a gaban saya dan tsura min ido, bai san meyasa ko kadan ba ya son Siyam ta yi maganar zuwan su gida Najeriya yanzu, don ji yake kamar idan ta samu shiryawa da Abban ta zai raba su ne ya aurawa Omar, ya dan girgiza kai kafin yace “please and please Siyam, ki yi hakuri, zan kai ki gida, zamu je Abuja da Mambillah Plateau, ‘but not in this condition’ da kike ciki. Nima kuma ba yanzu zan dau hutu ba sai watan haihuwar ki ya kama don in samu lokaci mu haihu tare.
Mu da zuwa Najeriya Siyam sai kin haihu. Ba zan iya barinki ki hau jirgi ba yanzu ba, I swear sai kin sauka lafiya.
In ya so kin ga sai mu kaiwa Abba babynmu, maiyuwa albarkacin sa yafi saurin yafe mana, in ya koro mu kuma, sai mu zauna a gate din gidan sa koda zamu shekara kullum ya fito ya bule mu da kurar motar sa, da haka da haka har sai ya huce. Zuwa lokacin kuma ni da ke mun daina fada” na ce “ni ai ka sani banida matsala da kai sai akan sallah Habeeby, in zaka dore daga canjin da na gani daga jiya zuwa yau, wallahi baka da matsala da ni kowacce iri. Komai bayan wannan zan masa uzuri da son da nake maka. Amma banda rashin sallah.
Taimaka min ka kai ni gurin Abba in neme shi da ya yafe mini, ko na samu cikar farin ciki da sukuni a zuciya ta, in yaso ko tsire mu zai yi yasa mashi ya tsire mu”.
Hamzah yayi min wata kasaitattar hararar SO, ya ce “idan duniyar ta ishe ki, dadin auren soyayya ya ishe ki, ni yanzu na saka damba a son su da jin dadin su, ki daina yi min fatan tsirewa”.
“Nace duk naji, amma kuma ba haka muka yi alkawari da kai ba Habeeby, kayi alkawarin kai ni gida da shirya ni da Abba na ASAP da yin auren mu. Yau gashi har muna neman shekara baka ko so in tada zancen”.
Yace har gobe alkawarin nan dana dauka yana nan Siyam. Kin wuce in miki alkawarin da na‘san bazan cika ba. Amma yanzu akwai abinda nake jira daga gare ki kafin mu kai da tafiyar. Bana so in ce miki kuma I’m afraid of Abbah’s decision, in ya ji cewa ‘I was not born in Islam”.
Wallahi tsoro nake ji, tsoron haduwata da Abba nake yi, haka Ummati sai nake hango rigimar ta irin ta Kakata ce, yanzu haka tana so ta bakunce mu, tuntuni nake so in gaya miki.
Amma ina tsoron kada ta zo ta tada maki hankali, kin san ba da yardar ta nima nayi aure da ke ba, I just ignored her, amma dai na sanar da ita. Siyam my Grandma is my everything, help me respect her.
Kada ki sako issue na addini a zaman da zata yi, addinin mu na gare mu, itama nata na gare ta. But always remember she is part of me! Bazan iya rabuwa da ita akan kowa ba”.
Duk da na hango matsala gagaruma na shirin samu na da tashin hankalin da zuwan nata zai iya zame mana, tunda da kan sa ya gaya min bata kaunar aure na da shi da irin yadda ta daga hankalin ta akan auren mu, har da su hawan jini ta gamu da shi da kwanciya a asibiti, a cewar ta gara ya kasha ta da hannun sa a kan ya auri musulma kuma bahaushiya. Amma me?
Sai na tuna ita din Kakar Hamzah ce wadda ta haifi wanda ya kawo min shi duniya, don haka ita makwafin uwa ce ga ‘Dream Husband’ dina. An ce Majnoon yana girmama hatta Karen da ya fito daga ahalin gidan su Lailah…. Balle KAKAR SA…. Wadda ita ta tsaya ta rainar mun shi a bayan rashin iyayen sa, ta kuma gina rayuwar sa positively har a yanzu na samu nake mora iya mora.
“GrandMa is most welcome. Kuma tunda bamu da dakin baki, ina ganin mu bar mata nawa dakin, in ya so ni sai in tattara abubuwan bukatata in koma naka dakin har zuwa komawar ta, ko kuwa ya ka gani?”
Hamzah ya sumbaci goshi na ya ce “to say I thank you, is not enough to express the gratitude”.
Sati biyu bayan haka na fara zuwa awo, bayan cikin ya riga ya girma, in the process, aka bukaci awon jini na dana Hamzah, a zaqule-zaqule irin na bature suka tabbatar mana yaro ko yarinyar da zan haifa zai iya zama sikila, aka tabbatar mana blood group dina dana Hamzah mai bada sickle cell children ne. Har likitar wadda ‘yar kasar Brazil ce take fadan don me muka yi aure ba tare da mun yi awon jini ba?
Har bayan mun bada baya ko gama fita daga ofishin bamu yi ba mukaji tana tattaunawa da likitoci ‘yan uwan ta cikin fushi tana fadin kadan daga matsalar ‘yan kasar Najeriya in suka tashi yin aure basa tsayawa su tabbatar da rukunin jinin su sai soyayya. Su haifi ‘ya’ya su a wahale ‘ya’yan a wahale har karshen rayuwar su. Idan ma an samu ‘ya’yan sun yi tsawon rai kenan.
Tashin hankalin da muke ciki ni da Hamzah shi ya hana maganganun ta na karshe su bata mana rai.
Ciki na irin cikin nan ne mai canza fasalin halitta,, duk na bude hanci ya kara girma. Ga wasu kurarraji da suka cika min fuska na babu gaira babu dalili don kuwa ni ba shafe shafe nake yi ba.
Hamzah tuki yak e a hanyar mu ta komawa gida but he cannot control his tears. Ni kuwa shiru na yi ina sauraron bugun da zuciya ta ke yi. To amma ya zamu yi da hukuncin Ubangiji? Na tuna nawa uban, ashe haka yake ji in aka ce bani da lafiya? Yasa hankaci ya tsane hawayen danun say a ce “a duk yadda Allah ya bani su ina son su, kuma a haka zan raine su. I wil make sure na soma tara kudi tun yanzu, na daina almubazzaranci, idan Allah ya raya min su ko su nawa ne zan biya ayi musu ‘Bone Marrow Transplant, I cannot endure to see any of my child suffering”.
Yana ta magana ni kuma ina tuno nawa Abban accordingly, maganganun sa sai suke ta zame min (a food for thought), na tsananin soyayyar da Allah ya sanya tsakanin Uba da Da, amma ni na sa kafa nayi fatali da soyayyar nawa Uban sabida son cika burin rai na da abinda zuciyata ke so.
Hawaye na na kara ninkuwa begen Abba da nadamar abubuwan da na yi masa na sake kama ni, wadanda a tunanin Hamzah ina fitar da su ne don an ce ‘ya’yan mu zasu iya kasancewa masu sickle cell anemia yace kuma ba zai tsaida haihuwa ba wai sabida zai haifi sicklers, duk abinda zai fito daga jiki na ko ba mutum bane yana so, sabida bashi da family bashi da wanda zai kira jinin sa bayan Kakar sa da abinda ke ciki na.
Cikin wannan damuwar muke duk mun rasa walwala a ranakun da suka biyo baya. Komai namu ya tsaya cak sabida damuwa. Har sai lokacin da Kaka Veronica ta iso United States. Ni da shi muka je dauko ta a filin jirgi Hamzah na rike da hannu na.
Daga can nesa na hango wata gyatuma gajeruwa cikin fararen kayan malaman addinin kirista, tana tafe rungume da Bible da sarka mai katon ‘cross’ a wuyanta wadda ta sauko har zuwa cikin ta. Ta saka farin gilashi mai kara karfin gani tana tafe a daddafe.
A zuciyata na shiga maimaita, “Amantu billahi rabba, wa bil Islama Deena, wa bi Muhammadur-Rasulullahi SAW Nabiyyan wa Rasoola!”. Sau tari, na kan maimaita imani na da addini na a zuciya ta, a duk lokacin da na ci karo da ‘yan sauran addinai a kasar nan, domin gasu nan birjit har da ‘yan addinin Buddu, wato ‘Budduism’, ‘yan Sikh wato ‘Sikhism’ da ‘yan Hinduism wato ‘yan addinin Hindu (masu bautar Saniya) ba irin wadanda bana gani a kasar ta Amurka.
Hamzah bai saki hannu na ba har ta karaso inda muke, idon ta a kaina bata ko kiftawa. Kasa gaskata kyawun halittar matar jikan nata tayi, gata fara tas jawur da ita kamar sai ka wanke hannu kafin ka taba, anya kuwa ‘yar Najeriya ce da gaske kamar yadda ya ce? A fili Kaka ta ce “Jesus christ! So this epitome of beauty is what snatch away my Grandson”. Kafin ta karaso ya saki hannu na ya karasa ya rungume ta amma bai karba mata Bible din hannun ta ba, sai akwatin kayan ta data ke ja da ya karba, ya iso inda nake tsaye ya bani akwatin sannan yace in gaishe ta.
Ni kuma hararar data ke ta zabga min ne ya dinke min baki ya kuma kasha min guiwa na kasa magana balle in yi mata sannu da zuwa, har muka zo shiga mota na kasa ce mata komai, sai da ta shiga gefen sa ta zauna na rufe mata kofa sannan na shiga baya.