Na bararraje na gwaggwafe kafafu a kasa ina baiwa Ummati labarin yadda na shiga uku hannun Antin Abba yau, na ce “wato Ummati Anti Wasilan nan ba karamar muguwa bace ta bugawa a jarida, kina ganin ta wata sumui-sumui muguntar da ke kunshe cikin bakin ta ta fi bakin ta girma.
Ummati baki na yau har jini ya yi, sabida dirzar muguntar da ya sha a hannun ta…”
Sai na ji gyaran muryar ta tana tahowa ta ce “UMH! Sai kuma ta daga labule ta shigo kamar dama tana labe a kofar dakin, ta ce.
“Ummati ke da kawar ki Siyama hira ake haka? To ga ‘meat balls’ kuna yi kuna taunawa, hira zata fi armashi”. Ta ajiye kyakkyawar roba a rufe a gaban Ummati, na faki idon ta na jefa mata harara, Ummati ta janyo akushin gaban ta ta bude ta dauki kosan naman kaza guda ta luntsuma a baki, dadin sa ya ratsa har kwanyar ta, bata san lokacin da ta ce.
“Ai wato zaman nan da kika ga ta yi kamar Rakuma a gabana, ba abinda ta ke yi sai kwashe miki albarka!”
Na zaro ido na ce “Ummati ki ji tsoron Allah ce miki fa kawai na yi na yi mata girki”. Sai kuka irin na borin kunya. Kunyar duniya ta lullube ni. Shiyasa na nannade ta da kuka. Ba abinda ya fi a kama ka kana gulma kiri-kiri, gulmar ma ta wanda ya kama ka red-handed.
Anti Wasila tayi wani lallausar murmushi ta ce “ai kafa ta kafar ta zuwa Abuja Ummati, kawancen namu nida ita yanzu ya fara”. Ban san lokacin da na saka kukan da karfi ba ba ina fadin “idan wasa kike yi ki bari, in kin ga na bar Mambila to gidan bakinhadaddenmijin mafarki na zani a wani garin daban, amma ba zani gidan ki ba. Ba wanda zai raba ni da Ummati ita bata takura mun”. Anti ta wani dube ni shekeke! Tace “da wannan annakiyar kazantar taki da gashi fal hammata hadadden mijin zai zo? Lallai fa hadadden miji a mafarki! Ai sai a mafarkin kam! Allah tsinewa uwar mai karya, hatta Umar aka bashi ke a haka an takaice shi, kuma sai na gaya masa ya sayi shavingcream ya ajiye duk sati ya saka ki a toilet ya sullube ki da kan sa….”
Tashi na yi ina kumburi kamar kububuwa na bar mata dakin don na tsani Anty Wasila yanzu.
Ummati na jin mu banda aika lomar ‘meat ball’ ba abinda take yi, na gama lura Anti ta gama saye Ummati da nau’in kayan dadin ta kala-kala kullum da abin dadin da zata sauya mata na makulashe ashe dama don ta raba mu ne don yanzu haka Ummati ta fi jin maganar Anti a kan tawa.
Da daddare bayan sun gama cin abinci ita da Abba ta kwashe komai ta dawo ta same shi cikin kissa irin tata sai ta ce.
“Baban Siyama amma dai da Siyama zamu koma Abuja ko? Tunda Umar ma komawa zai yi gara suna tare yadda suka taso nima kuma in ke jin motsin mutum a kusa da ni don wallahi bani da ra’ayin ‘yan aiki.”
Abba kamar Anti ta shiga ran sa ta sosa masa inda ke masa kaikayi don ya gama yanke shawarar kai ni makaranta mai kyau don kamar bana koyon komai a makarantar mu ta nan Mambila, cikakken sentence wannan na turanci bazan iya hada maka daidai ba, kawai yana shayin rigimar Ummati ne.
Anty bata fito fili ta gaya masa dalilin ta na son tafiya da ni ba amma shima Abba ya san wasu, musamman rashin kwaba ta da Ummati bata son yi, sannan Umar yana yawan kokan ta masa abubuwa da yawa da suke damun sa akan irin goyon Kaka da Ummati take min.
Sai Abba ya ce “I thought as much. Amma Ummati bazata yarda ba.”
Anti ta ce “ka bar komai a hannu na, I assure you zata yarda idan ni nayi mata magana.
Tsakanina da Allah da kuma kaunar da nake maka Dr. nake son gyara rayuwar Siyama, hakika tana bukatar mentoring na uwa a wannan stage din na puberty da take ciki, ka saka a ranka tamkar Siyama na hannun mahaifiyar ta mai rasuwa a zaman da zamu yi tare ni da ita. Allah ya jikan ta da gafara.”
Abba bai san sanda ya bude ma Wasila hannu ba ta yi azamar shigewa ciki ya rungume ta yana shi mata albarka.
*****
“Watakila dai matar nan har tsayuwar dare ta yi wa Ummati ta mallake ta!” Haka na gayawa Ya Omar cikin kuka da ya tabbatar min Ummati ta amince gobe da Anti Wasila ta cika wata guda a Mambila zamu wuce Abuja tare bakidayan mu har da Abba da ita Antin. A kofar gida na dawo daga islamiyya ya tare ni yake gaya min wai maza in je in hada kaya na da sassafe zamu kama hanyar Abuja.
Da kuka na wiwii na shiga gida domin kuwa a karo na biyu Ya Omar ya sake gwabje min baki wai na raina Anti Wasila da nace ta yi tsayuwar dare ta mallake Ummati.
Kan Ummati na fada da kuka na “Ummati da gaske kin yarda a tafi da ni a raba mu? Ummati nice fa Azumin ki, Boodon ki, Asshenki, Siyamar ki”. Ummati tayi azamar ture ni daga kan kafafun ta tace
“Allah yasa Sabira ce ba Siyama ba. In kin zauna wace tsiyar kike taimaka min da shi? Banda ki nade kafa a gado ki ci ki tashi hatta kwanon da kika ci abinci sai ni zan dauke miki, idan kuwa kashi kikayi sai dai in kora miki, hayya ratata Allah ya raka taki gona, Wasilar ce abin tausayi ba ke ba, sabida yadda zaki je ki maida mata daki matattarar kazantar ki. Faruqu kawai zan yi kewa.”
Gefe na koma na saka kai cikin cinyoyi na na soma gunza kuka, na ki hada kayan na ki yin komai, maganganun Ummati sun bakanta min ba dan kadan ba, sai ga Antin ta yi sallama tana tambayar Ummati wai na kammala hada kayana? Abba ya na jera su a trunk din mota ne tun yanzu da daddare, don da assubah zamu kama hanya sabida sai mun kwana a hanya.
Ummati ta ce “gata nan sai kuka take wai bazata bi ku ba” Anti ta karaso inda nake ta tsugunna cikin lallashi tana cewa “Oh ni Wasila bakin jinin nawa har ya kai haka gun Siyama?! To ki sha kurumin ki duk hutu da kaina zan kawo ki Mambila ki yi hutun ki tare da Ummat.i”
Na dago idanuna jajir, jagab dasu da hawaye na dube ta “kada ki kara tube min zani, babu kyau wani ya ga tsiraicin wani, in kin ce in yi ko menene zan yi, sannan don Allah kada ki kara saka ni girki” Anti tace “kece kika yi gardama in da kin yi salin alin ba zan yi miki da kai na ba, girki kuwa sunnar kowacce mace ne”. Na yi sharbe na ce “ai ba dole bane, tunda ni din bana so, kuma kada ki kai ni makaranta, bana so bana son karatu wallahi.”
Anti ta yi dan jim! Kafin ta ce “ban yi wannan alkawarin ba, sabida ba ni ke iko da ke ba, alkawarin da zan yi shine ko iya sakandire kika yi zan roki Abba ya kyale ki ba lallai sai kin je jami’a ba, sai ku yi auren ku da Omar ki yi ta sullubowa Ummati kyawawan tattaba kunne.”
Ummati mikewa tsaye ta yi don lallashin da Anti Wasila ke ta faman yimin ya fara bata haushi tace “da ke da mijin naki da tattaba kunnen naki da Antin naki duk ku tattara ku bar min daki kafin in miki tabon sallama da Mambila a kan farar fatar ki, ki koma birnin da dabbare-dabbare, kin san dai ban taba gwada kai hannu na jikin ki ba kada kisa mu yi sallama da shi yau (duka).”
Anti tace “yi hakuri Ummati, kukan sallama take miki, bari in hada mata kayan da kaina.”
Anti ta shiga dakina tana hada min kaya amma ko nisa bata yi ba da ta ci karo da wanduna masu busashshen menses a jiki ta watsar ta fito tsigar jikin ta na tashi, tana ce da Ummati.
“A tattara kayan Siyama duka a wanke a bada sadaqa Ummati” “to me zata saka in kuka tafi?” Ummati ta tambaya cikin mamaki, sai Anti tace “babu matsala zan diddinka mata wasu.”
Shi kam Ya Omar sosai yake murnar komawar sa Abuja sabida jami’a da zai fara a can, nikadai nake bacin rai na da fama da kuncin zuciya. Da asubah muna idar da sallah muka kama hanyar barin Gembu, Gembun Mambila, Gembun da ta tattara duk wani dabdalar kuruciya ta. Zuwa birnin da ya bude sabon shafi na rayuwa a gareni, wanda mafarki na na shekara da shekaru ne yayi min sanadin sa.
Da gaske Aunty Wasila has become my lifestyle influencer…. ta yi nasarar mai da ni MUTUM!
Na farko ta raba ni da rayuwa mara ma’ana dana ke yi a baya. Amma da na san actualizing mafarkin dana ke faman yi shi ke jira na a birnin da ko kusa ban yarda na bi Wasila ba, gara na dauwama a dakin Ummati na, cikin kwarkwata da amosani da kirci, doyi da hamami na da gashin hammata ta. Hausawa suka ce wai zama lafiya ya fi zama dan sarki ta kowanne fanni.
Abu daya nake tunani akan hanyar mu ta zuwa Abuja yake nutsar da bacin raina na rabo ni da Mambila da Wasila ta yi; watakila in hadu da shi…… Watakila silar haduwar mu kenan da mijin mafarki na, tunda na tabbata ba a Mambila yake ba, da a can yake, da tuni na ganshi a tsayin shekarun dana dauka ina mafarkin sa.
Bai yi kama da Mambilawa ba ya fi kama da ‘Black-Nigerians’, don haka kila kaddara ta da shi ita ke sarrafa kanta a kaina. Na kuma tabbata kaddarar ce har ila yau ta sa Wasila fizgoni daga mahaifa ta zuwa birnin gamayyar ‘yan Najeriya. Domin na yi amanna da cewa Allah na nufin wani babban al’amari a tsakani na da shi wanda ba’a mafarki zai kare ba.
Wanda kuma ban san farkon sa ban san karshen sa ba. Addu’a ta guda daya bazata taba canzawa a kan sa ba ta Allah ya bayyana min shi. Ya hada fuskokin mu ko da sau daya ne in gan shi a zahiri don cire kishirwar ganin sa da ke addabar idanu na dare da rana, in gaya masa tsahon shekarun dana dauka ina mafarkin sa…da mafarkin zamowar sa miji a gare ni. In kuma gaya masa cewa ba zan iya rayuwa ba tare da shi ba.
Hakika an halicci zuciyata sarqafe da tasa ta yadda na ke da assurance na cewa zukatan mu are undoubtedly connected, an yi min jarrabawa mai girma a kan sa tun kan in gan shi, tun kan in san shi, tun kan in mallaki hankalin kai na.
Masha Allah