Skip to content
Part 7 of 73 in the Series Sakacin Waye? by Sumayyah Abdulkadir (Takori)

Tafiya Mabudin Ilmi

Tun ina karama nake jin Ummati na yawan fadin wannan zancen na hausawa, “tafiya mabudin ilmi” ban taba yarda ba sai yau da na fito daga alkarya ta ta ainahi wadda ban taba barin ta ba tun haihuwa ta, na ke keta garuruwa da jihohin Arewa maso gabashin Najeriya cikin lafiyayyar motar Abba (4-Matic) baka wul. Sanyin A/C ya addabe ni sai da na roki Ya Umar da ke tukin motar akan ya rage, Abba ne zaune a gefen sa yana karatun Al’qur’ani ni da Anti muna kujerar baya. Anti na ramuwar barci ni kuwa idanuna tangaran ko son kiftawa bana yi kada a wuce wani garin ban tambayi Ya Umar sunan sa ba. Shikuma baya gajiya da gayamin har da karin bayanin karamar hukuma ce ko kuwa jiha. Da sunan gwamnan garin mai ci idan ya sani. Tafiya sosai ta kwana guda da yini guda kafin mu isa FCT Abuja. A hakan ma mun tsaya a Kano ne mun kwana a wani gidan saukar baki (Tahir Guest Palace) washegari da safe muka dauki hanya.

Tunda aka haife ni ban taba fita daga garin Gembu ba sai wannan karon, hana rantsuwa na je Gashaka tare da Ummati wajen dangin mahaifiyata ba sau daya ba ba sau biyu ba dana yi wayo, don haka yau da na rinka ratsa jihohin arewa bude ido nayi kawai na yi ta shan kallo ina mamakin wasu gine ginen wadanda ban san da irin su a Najeriya ba. 

Da muka shigo Abuja kuwa manyan titunan ta masu fadi da gadojin sama da kasa su suka fi daukar hankali na domin cigaban dana tarar ya kai ya kawo. Sai yamma lis muka shiga wata kebantacciyar unguwa wai ita Jahi, inda anan gidan da Abba ya saya yake, gidan na mu ba wani babba bane kwatakwata (three bedrooms duplex) ne, dakuna uku kacal ke da gidan biyu a sama daya a kasa sai BQ inda anan Ya Umar zai zauna. Amma tsari da ilmin da aka zuba wajen tsara komai na gidan abin burgewa ne matuka. Ana kiran wadannan gidajen duplex, wadanda duk kusan iri daya ne cikin estate din, an kwaikwayo su ne daga gidajen kasar Sweden.

Dakin kasa Anti ta bar min, inda a can babban falon gidan yake, da main kitchen, ita da Abba suna sama, Ya Umar na daga waje shikadai a BQ sai maigadi a nasa dakin can a jikin gate din shigowa.

Kwana biyu kawai Anti ta bar ni na huta daga gajiyar mota daga ranar kuwa a gabanta nake wanka ina kuka ina komai ba ruwan ta, komai koya min take kamar ta samu katuwar jahila, tun daga alwallah har wankan tsarki, da wankan sabulu da yadda ake gyaran gashi, ta sayo min hand dryer ta koya min busar da gashi inna wanke, ta saya min shampoos ds conditioners samfurin Dr. Teal’s, komai na amfani na har man shafawa da bath foam dina samfurin (Dr. Teal’s) Anti ke zabar min, sati daya da zuwan mu ta kai ni H-MEDIX inda acan ta hada min set din su, daganan sai Grandsquare inda ta saya min undies farare sol sol da kayan barci kala biyar da dogayen riguna suma biyar biyar, Egyptian Jilbaabs kala-kala don zuwa islamiyya, maclean kuwa daga ni har ita dana Longrich muke amfani. 

Zuwa sati biyu na fara da rage kin shiga kitchen don kuwa Anti bata bari na in yi zaman banza irin wanda na saba a falon Ummati ina kallon talbijin, idan har zata shiga to dole ta biyo ta daki na ta sako ni a gaba, tare muke shiga safe, rana da yamma mu yi girki sau uku a rana. 

Aunty bata raga mini, ba ta sassauta min sai ta ga na yi komai daidai kamar yadda ta koya min shi a kicin. Haka da ta samu lokaci ta dauke ni muka je tayi min shopping kayayyaki na dinkawa kala kala atamfa, shadda, leshi da materials, ta bada a dinka min a gidan su bayan telan gidan su ya auna ni, sannan ta saya min kayan masarufi dana tsaftace jiki iri – iri, turaruka da deosprays masu dadin kamshi na Dolce&Gabbana, haka ta ke bata lokacin ta wajen nuna min yadda zan ke amfani da komai, yadda zan gyara fuskata, hatta shafa lipstick ita ta nuna min, kasancewar tana hutun aure bata zuwa aiki sai bayan wata daya.

Amma duk da haka ni kullum cikin jin haushin Aunty Wasila nake. Gani nake ta takura rayuwa ta ta canza ta iyakar canzawa, ta matsa mini.

“Me yasa ta damu da sai ta canza min tsarin rayuwa ta?”

Idan ina yi ma Ya Umar wannan korafin sai ya girgiza kai ya ce “nan gaba kadan zaki gane babu mai son ki a duniya bayan iyayen ki sai Antin ki, Wasila”. Nace “au kai baka so na?” Yace “ni ba na cikin lissafin su, soyayyar miji daban ta iyaye daban. Aunty wasila da Abba iyayen ki ne”.

Sai bayan ya fada yayi nadamar subutar bakin sa, yayi maza ya gyara da cewa “soyayyar Yaya daban take da ta kowa, kin ji? Ki daure ki daina korafi kan Antin ki, ki bata dukkan goyon baya da hadin kan ki. Bata nufin ki da komai sai tarin alkhairi. 

Ina tabbatar miki duk kudin da ta ke kashe miki ba Abba ne yake bata ba, hasali ma bai san tana yi ba. Don Abban namu Economist ne ba zai salwantar da kudi masu yawa har haka a kan ki wai don ki zama ‘yar birni ba.

Had you know how beautiful and radiant you have become now, da kin gode mata iyakar godewa. She is indeed your lifestyle influencer!”

Murmushi nayi.  Ban san takamaimai ma’anar kalmar da ya fada ta karshe a wancan lokacin ba, illa zuciya ta da ta fassara ta yadda ta ga dama, na san dai kawai Omar yana yabon kirkin Anti Wasila ne.

Da hutun Anti ya kare ta koma aiki sai na samu saukin ayyukan gida, ni kadai nake wuni a gidan, kuma sai naji gidan ya yi min fadi babu dadi kamar da, kewar ta ta dame ni. Kasancewar har zuwa lokacin admission dina bai fito ba daga ‘Regent College’ inda Abba ya nema min.

Ya Umar kuwa yanata zirga zirgar registration din sa tsakanin gida da Gwagwalada inda zai fara level 1 a tsangayar da Abban mu yayi nasa karatun wato tattalin arzikin kasa (economics). Don Abba so yake a komai Umar ya gaje shi tunda dai bai da dan da ya fi Umar din, amma shi a ra’ayin sa karatun likita ya so ya yi, likitan zuciya, amma tunda Abba yace ga abinda yake so ya karanta ya karba da hannu bibbiyu. Ko dama can shi mutum ne mai muhimmanta ra’ayin wanin sa a kan nasa, a haka kowa ya shaide shi.

Kullum Anti ta fita aiki zaka same ni ne ina gyaran gidan mu ciki da bai din sa, bani kicin bani falo bani saman bene har sai naga ko’ina yayi kal-kal, tsaf-tsaf, yana daukar ido, sannan in dora mana abincin rana, zuwa yanzu kam ba laifi na iya girki daidai gwargwado na zamani amma banda na gargajiya wadanda Anti su tafi koya min. 

Direban ofis din su Abba na zuwa daukar masa abinci karfe biyu daidai na rana kasancewar Abba tunda ya auri Wasila bai iya cin abinci a waje. Ya Umar in ya tafi Gwagwalada tun safe sai yamma yake dawowa, motar haya yake hawa don Abba motar shi daya ce tal Anti ma haka, ina ji rannan yana masa alkawarin idan ya fito da (first class) mota sai wadda ya zaba zai saya masa. Amma a yanzu ya fi so ya koyi rayuwar gwagwarmaya irin ta kowanne dalibin public university a Najeriya.

Ta hakan ne zai san muhimmancin wahalar neman ilmi. Ya iya tattalin abinda yake da shi. Sai a ka yi sa’a kusan duka halayen Abba irin na Umar ne, abin nufi anan  Abba da Umar-Faruq ko kadan basu dauki rayuwar duniya da zafi ba, suna tafiyar da ita a saukake, a duk yadda ta riske su. Sun yarda jin dadi da daukaka basa zuwar ma mutum ta sauki a lokaci guda sai bayan ya sha gwagwarmaya a rayuwa.

A tsayin watanni uku kacal na zama wata kasaitattar ‘yar hutu, budurwa ‘yar kwalisa mai aji da hankali na kwatance, mai nutsuwa mai kuma kyawun surar da yake samun gyara da attention din uwa, sannan da gani babu tambaya ka ga ‘yar gatan uwar riko da Abban ta.

Rayuwa ta ta canza min baki daya positively, jiki na ma ya samu canji, ya nuna samun hutu da tsabta. Abu daya ne kawai har gobe bai canza a tare da ni ba wato (strong fulfulde accent) din Mambila bai bar baki na ya iya furta kalaman turanci dana hausa sosai ba.

Ni kaina na san ina daga cikin ‘ya’ya masu sa’ar mahaifi a rayuwar su, wadanda basu taba neman wani abu daga mahaifi sun rasa ba. Wadanda maraicin uwa bai taba affecting walwalar su da jin dadin su ba, ko kuma don ban taba sanin ta bane?

Farkon zuwa na sabida yadda Anti ke faman takuramin da aiyuka bana samun lokacin kaina balle har in samu lokacin tuna mijin mafarki na ko yin mafarkin sa. Kusan kullum sai na kira Ummati a wayar Anti mun sha hira, don ni Abba ya ce ba zai mallaka min waya ba sai na gama sakandire amma ya baiwa Faruq bayan dawowar mu nan, kullum na kira Ummati sai na bata labarin duk abinda nake ciki kamar kawata aminiya, rannan Anti bata nan ta bar wayar a hannu na nake ce da Ummati.

“Oh! Ummati ban taba sanin haka tsafta yake da dadi ba, ashe da ba karamin cutar kaina na ke ba da nake zama cikin kazanta, ko’ina na tsami, yanzu fa Ummati da zan wuce ta gaban ki bazaki gane ni ba, gashi ke wayar ki Raka-ni-kashi ce (nokia) balle in yi hoto in turo miki ki ganni, ki ga yadda na koma, in kin ji irin kamshin dana ke yi kamar a kasar da ake sarrafa turare (Paris) din Faransa aka ahaife ni. Kai Allah dai ya yiwa Aunty Wasila albarka, ashe da can ni tantagaryar kazama ce ban sani ba Ummati?

Ummati dai sai dariya take tana jin dadi a ranta. Na cigaba da fada mata.

“Ashe Anti Wasila ba takura min take yi ba so na take yi da alkhairi kamar yadda Ya Umar ke yawan cewa? Ummati don Allah kullum kika yi sallah ki ke yi mata addu’a kin ji? Kice Allah ya bar ta da Abba na, Allah yasa ta haifa min kanne masu yawa.”

Kafin Ummati ta samu zarafin amsa min na ji tafi raf-raf a kaina. Daga kan nan da zan yi sai nayi ido hudu da Anti da Abba a bakin kofar shigowa suna kallo na suna tafa hannayen su, da alama sun gama jin duk abinda na gama fadawa Ummati na. Kunya ta kama ni, nayi saurin rufe fuska da tafuka  na. Nace.

“Abba da Anti, Allah ya hana labe.”

Dariya suka yi su duka.  Abba yace “mu bamu labe ba shigewa zamu yi muka ji ana ambatar mu. 

Sai in ce “Aamin to all your beautiful Du’as Siyama. Get ready for school tomorrow. Anti Waseelah zata sauke ki a Regent, kafin ta wuce nata aikin”

Na rasa murna zan yi yau ko bakin ciki, don dai na san a da can na ki jinin karatu kamar yadda na ki jinin mutuwa ta, amma wallahi yanzu ji nayi ina shawagi tsakanin farin ciki da doki, wadanda duka suka taru suka mamaye ni duka a lokaci guda. Na soma jerowa Anti tambayoyi.

“Amma dai makarantar basa duka ko Anti?”

Cikin rashin damuwa tace “in kin yi laifi me zai hana a duke ki?” Nace “ai ni matsala ta da makaranta Anti guda daya ce kin sani. Assignment/Homework da classwork, idan babu su to komai zai tafi lafiya kalau.

Idan kuma kin yarda kullum na dawo gida zaki dinga yi mini da kan ki shike nan”. Anti ta dubi Abba tana fadin “saidai Abba yayi miki ya fi ni iyawa”. Abba ya girgiza kai ya wuce sama yana fadin “Siyama har yanzu da sauran ki, bansan yaushe zaki girma ba.”

Washegari Anti ce ta taimakamin na shirya tsaf cikin sabon uniform dina na daliban Regent, nayi matukar kyau kamar ba ni ba, na kawo mini hijab kalar uniform din na dora a kai, kai bazaka taba cewa nice wadda ta zo daga Mambilan nan firgai-firgai dani watanni ukku da suka wuce ba.

Anti ta kai ni har makaranta ta karasa cike – ciken takardun da ya saura ba’ayi min ba, tukunna ta tafi ta bar ni cikin dalibai ‘yan uwa na, wadanda duka ‘ya’yan manyan ma’aikatan Abuja ne.

Na lura daliban makarantar kabilu sun fi hausawa yawa, hausawan kuma wadanda sune (minority group) duk ‘yan girman kai ne, don babu wacce ta kula ni, basu san ni nafi son hakan ba, don dukkan su da lafiyayyen turanci suke magana, wanda ko come din su bana ganewa sabida yadda suke furtawa a gwanance, nikuwa ko sentence guda daya kwakkwara mai kyau bazan iya hada miki a wannan lokacin ba. A hakan kuma wai na gama juniorclass a garin Gembu, nan kuwa a aji biyu na sakandire aka barni wato an maida ni baya.

Ana gab da tashi wata yarinya ta zo kaina ta tsaya tana min magana, da muryar ta mai sanyi, in zan girmeta to bazai fi da shekara daya ba. 

“Ke ya ba kya note?” 

Ta tambaye ni da Hausa, jin ta yi min husa sai naji dadi, na bata amsa da tawa hausar da ba fita take sosai ba,

“shai gobe jan yi?”

“Shaboda me? (Itama ta kwaikwayi baki na). Bata jira amsata ba ta cigaba da cewa “Idan Mr Kehinde yazo karbar Assignment gobe baki yi ba zai baki punishment”, “me ye kuma punishment?” Na tambaye ta, babu girman kai babu raini ta amsa min tace “horo, zai saki shara ko  wankin toilet din sa, ba ruwan sa da ko ke ‘yar waye a garin nan”.

Ban san sanda nace “ai gara min punishment din da wannan uban rubutun, hannu na ciwo zai yi, baya na ma qagewa zai yi, na dade ban yi rubutu ba gaskiya” na bata dariya sosai ganin yadda nake magana da iyakar gaskiya ta, ta ce, “da alama ke ‘yar auta ce” nace “ba wata auta fa, don kuwa Anti na tana da ciki yanzu haka. Kuma ta yi min alkawarin samun kanne duk shekara” na kara bata dariya tace “ya sunan ki don Allah? I like you” “sunana Aishatu Mamman Dalhatu Gembu” “ni kuma suna na “Azima Salim Ko’oje. Mu ‘yan Sokoto ne. Kina iya kira na Ko’oje. Aisha can we be friends?” Ta fada tana miko min hannun ta, na mika mata nawa muka yi musabaha irin ta muslunci, ta samu wuri gefe na ta zauna tace.

“Kawata dole ki cire kiwar rubutu da assignment if you really want to stay in Regent (idan da gaske kina so ki cigaba da zama a Regent) bazasu doke ki ba amma zasu sallame ki in kika ce haka zaki zauna ba kya rubutun class notes da yin assignment” cikin damuwa nace “to Azima kiyi min na yau don Allah, nayi miki alkawarin gobe zan fara da kai na, yanzu kam hutawa zan yi”. Tace to shikenan, kawo in miki.”

<< Sakacin Waye? 6Sakacin Waye? 8 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
1
Free daily stories remaining!
×