Na yarda da ayar nan ta Ubangiji (S.A.W) domin kuwa ina kwance cikin duvet dina, ina faman rawar dari, na rufe kai na daga sama har kasa, hanci na kawai na bari a waje don shakar numfashi, a kokarina na boye wa al’ummar gidanmu halin da nake ciki na damuwa da tashin hankalin rashin dawowar Nasra a tare da su. Anti ta murdo kofar daki na ta shigo bakin ta dauke da sallama.
“Siyama kin yi barci ne?”
Kasa-kasa na amsa wa Anti cewa, a’a. Ta karaso tana taba goshina da hannayen ta ta ce, “Subhanallah, this is serious Siyama, shi ne ba za ki fada ba ki da lafiya a ba ki magani ba? Ki zo Abba ke son magana da ke”.
Ta taimaka min na mike na saka hijab, ta je ta kawo min paracetamol da gorar ruwa na sha sannan muka wuce falon Abba tare.
Abba na zaune a kan kilishin tsakiyar falonsa, tun dawowar su ba mu hadu ba sai yanzu. Kallo daya na yi masa na kasa tantance tsakanin ni da shi wa ya fi wani shiga damuwar rashin Nasra a gidan? Shi kam Abba har wata ‘yar rama ya yi, ga shayi a gabansa Anti ta hada masa amma bai ko taba ba.
Ina zama a gefen sa ya miko min kofin shayin, ya ce, “Amshi ke ki shanye tunda mai shanye min shayin kullum yanzu ba ta nan, uban ta ya nuna min ya fi ni son ta, tunda kuwa ya kwace abar sa cikin halin jinya. Ya bar ni da kewa”.
Sai na ji tausayin Abba ya kama ni kuma haushin Hamzah ya kama ni duka a lokaci guda, don ni kadai na san irin son da Abba yake yi wa Nasra, da irin shakuwar da ke tsakanin su, kullum tare suke cin abinci ba sa raba kwano.
Takaicin Hamzah ya ishe ni, na ce, “Don Allah Abba ka fidda ‘yar sa a ran ka, ka bar masa ‘yar sa ya ci abin da zai ci da ita tunda Alhamdulillah muna da yara fal a gidan nan”.
Abba ya yi dariya ya ce, “Siyama kenan, kowanne yaro da na ke da, ko jika, matsayin sa daban a raina, wannan ba ya cike gurbin wancan. Kowanne da gurbin sa da muhallin sa. Ba wannan na kira ki mu tattauna ba, domin kuwa Hamzah na da right na rikon diyar sa. Tunda ni ma na rike tawa na haramta masa alhalin Allah bai haramta masa ba.”
Kunya ta kama ni sosai, na ce, “Ba haka ba ne Abba, hukuncin da ka yi a kan hanya yake, don na ji wa’azin wani malami kwanan nan da ya ce da auren tubabbu gara barin sa. Domin da yawa suna yaudara da shiga musulunci su dauke mace su maida ta nasu addinin, in aka haifi ‘ya’ya su ma su mayar da su christianity. Malamin ya ce, “A fara tabbatar da musuluncin mutum tukunna, kafin a bashi aure. Kari cikin addini abu ne mai kyau, kuma muna maraba da shi, but iyaye has to be verycareful. Ba kowa ne zai zo ya ce ya musulunta ka dauki ‘yar ka ka ba shi ba tare da ka tabbatar da musuluncin nasa wane iri ba ne. Don haka ni Abba ban taba ganin beken ka ba a kan hukuncin da ka yanke min ba, illa ganewa da na yi duk da saba makan da na yi a baya, ba ka daina sona ba. Ka yi ne for my own survivalreligiously and morally, duk da na san Hamzah ciki da bai dinsa yana da bambanci da sauran tubabbu amma shima yana da nasa nakasun dana kasa gyarawa. Na san kuma ba shi da burin daukana ya kai ni cikin ahalinsa tunda shi ma ba shi da kowa cikin su yanzu.
Abba hukuncin ka shi ya kamata kowanne mahaifi na kwarai ya yi wa dan sa mai taurin kai iri na”.
Abba nata murmushin farin cikin jin abin da nake fadi, ya ce, “To yanzu Boddo, a misali idan na ce na ba ki zabi, komawa mijin ki ko yin sabon aure wanne za ki zaba?”
Na yi maza na ce, “Abba ba ni da zabi ni yanzu aure ma ba ya gaba na, ina jin dadin aiki na sosai, kuma ka ga rashin Hamzah ko wanin sa bai hana ni rayuwa mai kyau ba. Don haka idan ka ba ni wannan zabin sai dai in ce maka zabi na bar maka shi duniya da lahira a kan rayuwata ba zan kara maimaita irin kuskuren da na yi a baya ba”.
Na yi ajiyar zuciya ina cewa, “Abba ka kara yafe min don Allah halin da na saka ku a baya, a kan wauta, kuruciya da rashin hankali na”.
Abba ya ce, “Kin ce kin bar min zabi ko?”
Na ce, “Eh wallahi Abba, duk abin da ka zabar min ko tada kai ba zan yi in kalla ba sai dai in ce Allah ya sa shi ne mafi alkhairi a gare mu ni da ku bakidaya”.
Abba ya yi murmushi ya ce, “Shi ke nan Boddo, na gode. Je ki ki kwanta.”
Na kwana zuciyata cike fal da soyayyar Abba na da kewar diya ta. Amma in na tuna she’s now free from sickle cell disease sai zuciyata ta cika da godiyar Ubangiji, in roki Allah ya tsawaita rayuwar ta, ya sa ta yi aure da wuri ta samar wa mahaifin ta dangin da ba shi da su. Ina musu addu’ar doguwar rayuwa and prosperity a duk inda sunka tsinci kan su a duniya.
Sati biyu bayan nan Ya Omar ya dauke ni bias umarnin Abba muka je aka yi min finger print, bai dai yi min bayanin komai ba, amma ya ce, Abba ne ya sa shi, kuma na fahimci na yin visar Saudi ne, Omar ya ce, ni da Abba da Ummati ne za mu je umrah. Na ce, “Anti fa?” ya ce, “Ta ce ba ta samu leave daga office dinta ba, don ba ta dade da komawa daga annual leave ba”.
Muka wayi gari Ummati ba lafiya ta kira Abba ta fada masa, don haka Abba da kansa ya je Mambillah ya taho da ita don da ma yana da niyyar hakan saboda maganar umrah, ya kawo ta Abuja ta ke ganin likita akai-akai.
A daki na ummati ta sauka, ciwon kafafunta ke damun ta don haka kullum kafin mu kwanta sai na shafa mata maganin da likita ya bayar a kafafun, abincin ta na musamman ni nake mata da hannu na musamman tuwon acca, har zuwa lokacin da ta fara samun sauki.
Rannan ta ce, “Shin Azumi a ina ki ka kware da tuwon acca ne da kunun acca ne haka?”
Dariya na yi na ce, “Ummati, kin manta Baban yarinyar nan dan kabilar Berom ne? Kullum abincin sa ke nan sai ko in ya so cin basmati rice”.
Ummati ta yi jagale da baki ta ce, “Shin dangin sa ba su matsa miki ba a lokacin zaman ki da su?”
Nan nake bai wa Ummati tarihin Hamza da Kakar sa har zuwa mutuwar ta ta sanadin bugawar zuciya. Saboda bakin cikin ya musulunta. Ummati ta ce, “Kina nufin yanzu ba shi da kowa? Kuma zai iya rike ‘yar nan da ba lafiya ce ta ishe ta ba? Ni fa ban raba ki da mijin ki haka kawai ba sai don tsoron kada ke ma watarana su maida ki kirista, an ce suna guduwa da mata garin su su canza musu addini, amma shi kin ce ba shi da sauran dangi duk sai na ji ya ba ni tausayi, ga shi na ji abubuwa da yawa da ban zaci jin su ba daga bakin Baban ki da suka rikita ni.
Boddo ni kam zan yi istikhara a kan auren ki, idan na aminta da abin da na gani na kuma ji, to da sabon gini gwanda yabe, tunda dai har yau bawan Allahn nan ya kasa sakin ki, ya bar mu da daukar hakkin sa. Ni dai ki yafe mini Boddo, kada rabo ya kar ni, in kina son komawa gidan uban diyar ki zan kauda kabilanci daga raina, da ma ba shi ya fi damu na ba, addinin ki nake ji”.
Ni dai ban ce komai ba.
Haka washe gari ta samu Abba da sassafe hankali tashe, ta ce, “Mamman!”
Ya ce, “Na’am Ummati.”
Ta sake cewa, “Mamman!”
Ya ce, “Na’am Ummati.”
“Ka yi hamzarin mayar da Boddo ga mijin ta. Jiya na ga abin da ya ishe ni, domin kuwa na ga rabon ‘ya’ya rututu ba iyaka. Ni kam ban shirya tafiya lahira da hakkin kowa ba. Wanda na yi don kare addinin Boddo ne, amma kam na ga alkhairi da rabo mai tarin yawa a tarayyar su a istikhara ta ta daren jiya”.
Abba ya nisa, ya ce, “Ummati da ma ko ba ki zo ba ina da niyyar zuwa Mambillah a wannan satin in gaya miki abin da ba ki sani ba. Mijin Boddo dai da muke ta faman kira ‘tubabbe’ ya zama malamin musulunci, ko kin san tun barinsa gabanmu yana Saudiyyah yana karatun Fiqhu sabida ya yi zuciya, mun masa gorin kafurci? Kina da masaniyar cewa Jami’ar musulunci ta kasar Makkah wato Ummul-Qura University sun dauke shi aiki matsayin malami a jami’ar?
Ummati ni Mamman na ga aya, ina kan gani kuma kan wannan bawan Allah, a dalilin haka na daina kyamar tubabbu, na daina kiran wanda ya amshi musulunci da kafiri har abada wai don kabila ne. Na ji kunya ranar da ya ja mu sallah a asibitin Saudi German, na ji kunya ranar nan da na ji irin qira’ar Salah Bukarti a bakin sa, wallahi na ji kunya sosai, na kuma kara girmama iko da kudurar Allah. Ba a san dan aljannah ba sai ranar hisabi, in ba mu yi da gaske ba, duk hakki ne zai yi ta ba mu kunya tunda dai Boddo ta dawo hanya, ta tuba ta bi Allah ta bi mu.”
Ummati ta nisa ta ce, “Jiya ta kwance min duka tarihin sa, ashe Kakar sa zuciyar ta ce ta buga ta mutu saboda bakin cikin musuluntar sa. Yanzu haka bai da kowa nasa a raye. Maraya ne gaba da baya muke ta muzgunawa, abin da nake gudu a auren irinsu ba lallai ne ya faru da Boddo ba, tunda bai aje kowa ba, zuwan ta kasar haihuwarsa watarana in dalili ya yi ba zai zo da matsaloli masu yawa wadanda nake hangowa ba. Matsalar dai tana ga haihuwa, haihuwar ‘ya’yayen marasa lafiya abin dubawa ne. kullum ina ji likitoci na kira a radio a dinga kula, a dinga dubawa kafin a yi aure, amma su tantabaru sarakan soyayya babu ruwansu da wannan.”
Abba ya ce, “Ba laifinsu ba ne, wannan laifin na ga Adamu, shi duk bokon nasa bai gaya masa ya tabbatar da genotype kafin aure ba? Ko kuwa cikin irin gaggawar tasa ce ta son yi wa Boddo gwaninta don shi gani yake ya fi kowa sonta.”
Suka koma caccakar Young Abba, inda suka ce tun yana yaro shi mutum ne mai gaggawa, Ummati tana cewa, kuma a karshe ya zo ya fi mai kora shafawa, wai ba ya so Boddo ta haifo ‘ya’ya sikila ta bata musu jinin zurri’a.
A karshen tattaunawar su, Abba da Ummati suka yanke shawarar idan sun je umrar wannan shekarar tunda dai Siyama ta yi biyayya, ta kuma ba su wuka da nama kan aurenta, to za su baro ta a hannun mijinta uban ‘yar ta ba tare da sun gaya mata shirin da sukayi ba. Sauran al’amuran na haihuwar ‘ya’ya suka bar wa Allah. Tunda a cewar Ummati sauran mutanen da ke auren AS-AS bisa kaddara da rashin sani ko ajizanci na dan Adam (mantuwar gwaji) su ma ba su fasa rayuwar aure da haihuwa ba.
“Allah shi ne mai rayawa kuma shi ne mai kashewa”. In ji Ummati, “Allah ya ba su yadda za su yi da su”.
Duka shawarwarin nan da suke yi tsakanin su biyu ne babu na uku. Sai daga baya ne Abba ya kira Ya Omar ya gaya masa abin da suka yanke shi da Ummati na baro Boddo a wajen mijinta idan sun je umrah. Cikin farin ciki Ya Omar ya ce, “Abba mun gode Allah ya kara girma”.
Ya Omar din ma kuma bai gaya min komai ba, har ranar tafiyar tamu, ya dai jaddada min in kula da Ummati a masallaci shi ba zai bimu ba.
Jirginmu ya daga zuwa kasa mai tsarki, kai na a kafadar Ummati tsohuwa mai ran karfe uwar Gidado, uwar Mamman da Adamu, kakar Boddo da Omar, surukar Wasila da Nasara, Allah ya kara nisan kwana.
Kafin jirgi ya sauke mu a Jidda ba irin tunanin da ban yi ba, ko Nasra har yanzu tana Saudi-Arabia tare da Babanta in je in ganta ko da sau daya in Abba ya yarda? Ko sun koma Turkiyya. Ko kuwa ya koma VOA din? Sai kuma na tuno irin sababbin abubuwan da Ya Omar ke fada a kan rayuwar Hamzah ta yanzu cewa he moved on a new life, shi din yanzu islamic scholar ne a Ummul-Qura University not that popular media celebrity.
Na daga kai sama ina tuno kudura da buwaya irin ta Ubangijin sammai da kassai. Mai juya al’amura da rayuwar bayinsa duk ta yadda yake so. Na tuno artabun da na sha da Hamzah a kan addini amma da yake shiriyar ba a hannuna ta ke ba Allah bai nufe shi da shiriyar a sanda muke tare ba, sai bayan Abba ya sa power dinsa na uba mahaifi ya raba tsakanin mu.
Wannan kadai in aka duba zai sa a yarda cewa, babu mai shiryar da wani sai Allah, haka babu mai batar da wanda Allah ya shiryar. Sannan shiriya da bata duk a hannunSa suke.
Subhanakallahumma wabi hamdihi nashhadu laka wa natubu ilaika.
Tnx
Sakacin waye