Skip to content
Part 72 of 73 in the Series Sakacin Waye? by Sumayyah Abdulkadir (Takori)

Murfi

“Without you life is progressing tremendously, yet incomplete and at times boring!”

Bai san me yasa yake yawan son sauraron wannan wakar ta Ba-Sudane Sharhabil Ahmed ba, wadda asali shahararren mawakin yayi ta cikin harshen larabcin yammacin Sudan ne, shi kuma Jenny Mayhem yayi shigen ta a ma’ana da balagar harshe da harshen Bajan na kasar Barbados, dalilai da yawa na saka shi sauraron wannan ‘cool Arabic music’ din, wato wakar larabci mai sanyin amo ta Sharhabil Ahmed. Yana yi yana fassara manufar kalmomin a zuciyar sa da turancin da yafi sabawa da shi a can baya, watakila soyayyar sa da wakar mai tushe ce, kuma mai harshen Damo ce. Hakan ba zai rasa nasaba da kasancewar abinda wakar ke dauke da shi yayi daidai da halin da yake ciki ba, akan matar sa uwar ‘yar sa abar son sa wato Siyama! A iya sanin sa rayuwar sa ta yi kyau ta fuskar addini har fiye da burin Siyam a yanzu.

Amma ya rantse ko zai tsufa yayi furfura babu Siyama tare da shi ba zai taba zuwa ‘Biko’ ko ban hakuri ga iyayen ta ba (ba kuma don girman kai ba). Hasali ma shi kalmar girman kai baya cikin vocab bank din sa (vocabulary bank). Sannan ba zai taba sakin ta ba, har duniya ta nade. Amma zai kasance mai yi wa hukuncin iyayen ta biyayya saboda girman su a idanun sa na haihuwar Siyamah, hukuncin su na ya bar musu ‘yar su a bisa hujjar su ta shi tubabbe ne kuma kabilar da ba hausa fulani ba.

Yana rokon Allah idan ya tashi daukar ran sa ya dauke shi yana a matsayin mijin Siyamah, wata kwayar mutum guda daya data yi masa silar tsira daga duhu zuwa haske, daga shirka zuwa kan tafarki madaidaici, wadda dukkan burin ta a rayuwa shine ya zama mutum nagari yanda yake a yanzu; wato cikakken musulmi mai tsaida sallah da kiyaye iyakokin Ubangiji. Yau ga burin Siyam ya cika Hamzah ya zama Hamzah, ba Mawonmase ba a lokacin da suka yi wa juna nisa.

A iya sanin sa bai yi musu laifin komai ba, tsana ce kawai da gani-ganin addini irin wanda bafillace/bahaushen mutum ke yi wa tubabbu da yare ko kabilar da ba tasa ba cikin Najeriya, da kallon da ake musu na rashin cikar addinin su ko da sun tuba sun bi Allah guda daya.

Bayan tahowar sa daga Mambillah kalaman Ummati da na Abba ne suka zame masa motivation and a food for thought, sannan suka jagoranci canza rayuwar sa ko ba don su maido masa Siyamah ba.

Ya tsaida shawarar cike wannan gibin na gani-ganin addini da ke tsakanin sa da iyayen Siyam, ta hanyar canza rayuwar sa kacokam da juyawa giya baya, ko ba don a maida masa Siyam din ba, sai don inganta addinin sa da gyara kurakuran sa a idanun Ubangiji, da kuma kore gani-ganin kafirci da ke idanun iyayen Siyam a kan sa,  ita kanta har suka rabu bata daina saka shi a hanya ba, bata daina roka masa shiriya ba. Yana so ya canza tunanin mutane daga kan mutane irin sa wadanda suka tuba dama al’ummar duniya baki daya dake ma wadanda suka samu rabauta da Shahada wato tubabbu a kalmar hausa kallon basu tuba ba. Ko sun tuba din ba zasu dore a cikin addinin musulunci yadda ya kamata ba. Dole a komai akwai exemption. He wants to be an exempted

Da wannan ya ajiye career din sa ta sama da shekaru goma wato International Media Broadcasting, ya rungumi sabuwar rayuwa a kasa mai tsarki. Ya bar Amurka ya bar Turkiyya da niyyar ba zai sake komawa ba tunda har Jami’ar Ommul Qura sun rungume shi.   Ba tare da Siyam ba ya cimma nasarori masu yawa na canjin rayuwar sa daga SAKACI da addini (kamar yadda SIYAM ke cewa) zuwa RIKO DA ADDINI, ya samu nasarori masu girma iri daban daban a cikin shekaru ukun da baya tareda Siyama.

Muhimmi a ciki shine ya bar giya/barasa tun kafin shigowar sa Ommul Qura. Salloli biyar ba ya yin su shi kadai a gidan sa, sai a masallaci tare da jama’a a Haraam ko Masjidnabawy (idan yana Madinah kenan). A ganin sa raba shi da Siyam da Abba Dr. Mamman Gembu da Ummati suka yi, koma da wanne nufi sukayi hakan ya zame masa blessing upon blessing, kuma silar alkhairori masu yawa ga rayuwar sa, domin shine mujazar data bude masa ido ya canza rayuwar sa positively zuwa irin wadda ta dace da kowanne musulmin kwarai, koda asalin sa bai canza ba, yaren sa bai zanza ba, kabilar sa bata canza ba, ya kuma san bazasu taba canzuwa ba.

Bai san me yasa hausawa da Fulani basa karbar shahadar wanda ba yaren su ba, wanda ba koyarwar addinin musulunci bace. A karshe ya gane cewa; Ashe ko babu soyayyar mace a gefe, namiji in ya amsa sunan sa na namiji zai rayu, rayuwa mai kyau da tsabta a kan tubalin abinda ya fuskanta, zai kuma rayu cikin ruhin ita waccan soyayyar kamar tana tare da shi, zai yi rayuwa mai nagarta wadda babu damuwar komi a cikin ta banda KEWA wadda sabo ke assasawa.

Ita kan ta kewar ba koyaushe take zuwa ba sabida yadda ya maida kan sa busy da rubutun (PhD research) din sa har Allah ya taimake shi ya kammala a cikakken lokacin da Jami’ahr Ommul-Qura ta deba masa.

His PhD thesis (dissertation) ya rubuta shi ne a kan sahihancin tuba (Taubah) a cikin ilmin Fiqhu “The Authenticity of Repentance in Jurisprudence”. _ Hamzah Mustapha (PhD).

Dr. Hamzah Mustapha (Mawonmase), kodayake inkiyar sunan sa na asali na “Mawonmase” ya dade da bace masa yanzu, tun bayan tahowar sa Saudi Arabia “Hamzah Al Mustapha” ya maye gurbin sunansa na al’ada wanda Kaka Veronica ta sanya masa wato “Mawonmase”, duk da har gobe sunan yana jikin takardun sa (qualifications) amma ba wanda ya san shi da wannan inkiyar a Ommul Qura.

A wani dare mafi tsayin darare a rayuwar Dr. Hamzah Al-Mustapha, sabida yadda ya kasa runtsawa ya kuma kasa mikewa don ragewa kan sa nauyin da kan danne kirjin sa a irin wannan lokacin. Sau tari, jikin sa bakidaya ya kan dauki zazzabi ne idan ya tuno wasu abubuwan, a irin wadannan dararen ya kan kasa barci ne da tunanin ta, barci kan gagare sa sai juyi a kan gadon sa, ya kan fadawa kansa a fili kamar tana gefen sa, ko bisa kirjin sa “INA KEWAR KI BODDO_SIYAMAH!

Siyam, uwar Nasra Masoyiyar da babu irin ta a duniyar Hamzah Mawonmase. Amma bai sani ba ko SAKACIN sa ne yasa ya rasa ta, ko kuwa biyayya ya yi wa Abba? Ko zuciya yayi? A kan korar da iyayen Siyam suka yi masa fata-fata?

“Ni dai na rantse babu saki tsakanin mu har abada Siyam, sai dai mu kare rayuwar mu cikin kewar juna da yi wa juna takaba idan ta Allah ta kasance a kan dayan mu. Siyam you are my Hurul’een a duniya da lahira.”

Hamzah baya barcin safe yadda ya kamata a duk ranar shirye shiryen Aisha-Siyama Mamman Gembu sabida dakon sauraron muryar ‘yar mutanen Gembu, daga gidan radion British Broadcasting Corporation (BBC) na sassafe wanda sauraron muryar ta ya zame masa abin karya kumallon safe kullum, duk wasu tactics nasa na broadcasting a sanda yake VOA Siyam ta naqalta ta kuma iya su kuma dasu take amfani a nata broadcasting din with so much enthusiasm and very passionate ga career din ta. Ya kan saurara da murmushi, da tagumi, da dariya wani lokacin da tsatstsafowar hawaye cikin almond shaped idanun sa cikin tuna abubuwa masu yawa a baya.

Wanda Takori ta ce wai TUNA BAYA SHINE ROKO! Ya shafa kan ‘yar sa Nasra wadda ya kan kira da suna ‘diyar SO’ wadda ke kwance bisa ruwan cikin sa tana barcin ta peacefully. A darare masu yawa irin wadannan da kyar yake iya barci said ai ya saka Nasra a gaban sa in tana nata barcin yayi ta tunanin mahaifiyar ta. Gashi dai ya samu dukkan abinda yazo nema a Saudiyyah wato ilmin addinin musulunci zallah amma kuma a lokuta irin wadannan da kowanne magidanci yake bukatar iyali yana kare su ne a zubda hawaye.

Bai taba nadamar fitowa daga kabilar sa ta asali ba tunda a nan Allah ya ga damar halittar sa, amma yana kuka in ya tuna background din sa wanda ba zai taba canzuwa ba, ya kuma tuna a kan sa ne aka raba shi da Siyama ba tareda ya cika alkawura da yawa da ya daukar mata ba. Ciki Banda na soyayyar gamayyar jiki data zuciya daya bata bai zame mata irin mijin data ke so kuma take mafarki ta fuskar addini ba. Siyama na son soyayyar Hamzah amma fa tareda addini da tsarkin musulunci a tare da shi. Yau gashi ya zama duk abinda Siyama ke so, har ma fiye,  unfortunately babu Siyamar da zata mora tayi appreciating tayi warkajami cikin soyayyar Mawonmasen ta, wadda tsarkin addini da hasken da ke cikin sa zai jagoranta.

Da gaske ne da ake ce “opportunity comes only once in life?”

Ni Kuma TAKORI na taya Hamzah cewa a’ah. Dama ba sau daya take zuwa a rayuwa ba, sabida rahamar Ubangiji ga bayin sa bata da karshe. Rahmar Allah is infinite.

Shirin da Siyama ke gabatarwa kullum da safe on current affairs na kasar Najeriya. A yawancin shirye shiryen ta tana yawan sako advocacy a kan a karbi zaman lafiya a kasar Najeriya a ajiye kabilanci. Tana bayar da Misalai akan kasashen da suka cigaba sun kauda rikicin kabilanci da na addini ne a tsakanin sus ai kyautatawa juna, sun baiwa kowanne bangare damar gudanar da addinin sa. A fakaice tana advocating a kan muhimmancin peaceful coexistence between Nigerians of each ethnic group. Dalilin ta na yawan son daukar wannan Maudhu’i (topic) dinne yake da ayar tambaya a kai mai Sanya shi murmushi. Her voice is even cooler now than before.

“Abba Moya!”

Wato “Abba zan sha ruwa”.

Nasara ta katse masa tunanin bayan ta tashi barci da asubahi. Yana zaune a gefen gadon sa ya hada kai da guiwa shi ba kuka ba, shi ba barci ba.

Mika hannu yayi ya dauko gorar ruwan da yake ajiyewa a bakin gado saboda ita. Ya kafa mata a baki tana sha da sauri domin kishi ne ya tada ita.

“Abba Boddo za ni” Nasra ta fada da muryar son fashewa da kuka. Ta sake cewa “Abba Boddo!”.

In da sabo ya saba da rigimar daren Nasra a kan son tafiya wurin mahaifiyar ta tun bayan fitowar su daga asibiti. Shi kuma ya yi rantsuwa ta zo kenan, kada watarana ace mata “’Yar tubabbe”.

Wannan kalma ta Ummati in ya tuna a kullum tana masa ciwo. Saidai a kullum yana yi wa Ummati uzuri ya gayawa kansa reality din rayuwar sa kenan wanda bazai kankaru ba. Kuma a hakan Dan ta na karshe wato Young Abba ya nuna masa kowacce kalar kauna ta duniyar nan. A yanzu da baya shan barasa bashi da false perceptions, bashi da da false beliefs kuma bashi da temper a kan kowa. He is cool now. Yana daga illolin ta gayawa ma’abocin shan ta cewa komai aka yi da manufa mara kyau a ka yi. Yanzu dai kam ya dade da neman gafarar Young Abba a bisa mummunar fahimtar da giya tasa yayi masa a baya kuma suna waya ko da yaushe, duk abinda yake ciki a Macca Young Abba ya sani.

A kullum da sabon hope din da Young Abba zai ba shi na a kara hakuri, a bar Abba da Ummati da duk hukuncin da suka yanke da yardar Allah shine mafi alkhairi.

Ya kan ce “na daina gaggawa akan komai Hamzah, domini ta gaggawa daga shaidan ce, na daina yanke hukunci da ka, ba tare da bincike da istikhara ba, domin ni na saku cikin matsalar haihuwar yara sickler da kuka samu. Amma Allah ya gani ban yi da niyya ba sai da niyya mai kyau ta samar da kari cikin addinin musulunci da kuma son farantawa Boddo.

Kuma bawa baya hada sani da Allah shi kadai ya san me ya boye a cikin wannan auren naku mai tarin KALUBALE.

Duk wani kalubale kuma a rayuwa in an yi hakuri watarana yanada karshe, komai ma yanada karshe banda ikon Allah”.

Wadannan sune kalaman Young Abba da a kullum in ya tuna suke kara masa karfin guiwar cewa challenges din su shi da Boddo, tunda sun barma Ubangiji da iyayen su to hakika kuwa zai iya musu.

<< Sakacin Waye? 71Sakacin Waye? 73 >>

1 thought on “Sakacin Waye? 72”

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×