BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM
Da sauri Juwairiya ta dawo ta rungumshi da hannunta ɗaya, ɗayan kuma ta na shafa mishi ruwa, ajiyan zuciya ta sauke mai ƙarfi ganin ya buɗe ido, don hankalinsu ya tashi maƙura gani suke kamar mutuwa zai yi ganin yadda idanunsa suka ƙaƙƙafe.
Juwariya ta miƙe ta na faɗin. “Tun da ya farfaɗo bari na je na naimo mishi magani.”
Miƙewa ta yi ba ta jira amsar da Mama zata ba ta ba ta fice da ga cikin gidan ta na sharar hawaye.
A hankali ta ƙarasa shiga cikin shagon na sa ganin yadda ya haɗe rai tun da ya hangeta ta na tahowa, tamkar an aiko masa da mala’ikan mutuwa ya haɗe ransa babu wani walwala. Jikin ta ya yi sanyi sai ta tsaya a bakin ƙofar ta kasa mishi magana kuma ta ƙi ta tafi duk da kallon kora da hali yake mata.
“Lafiya ki ka yi min tsaye kofar shago kamar na saki ki? Ya faɗa ransa a ɓace. “Don Allah ka taimake ni Bala kasan mai ya kawo ni a karo na biyu, wallahi suna cikin wani hali na rantse maka wannan karon zan naimi kuɗin ka na baka.
“Ta faɗa da muryar kuka fuskarta bayyane da damuwar halin da take ciki.
“Ni ina ruwana na gaji da baki bashi kuma ba kawo min kike ba, sannan na nuna miki hanyar da zaki bi mafi ɓulluwa kin nuna a’a wai ke ustaziya, to sai kije can amma ko maganin biyar ba zan baki ba. “Tamkar zai kai mata duka yake magana ganin haka sai kawai ta juya, dan ta saka a ranta yau ba zai bata ba.
“A’a Juwairiya tafiya zaki yi.” Ya faɗa da sanyin murya ganin ta kama hanyar fita, sai kuma ya ƙara matso da fuskarsa gurin ta yace.”Kin cika kafiya ki yadda ki amince ko sau ɗaya ne, Allah zan baki duk abinda kike so. Kin san ina son ki Juwairiya na san babu yadda za’ai na same ki, wannna dalilin ya sa nake so ki amince min kar soyayyata ta faɗi a banza.”
Ƙarashe fita ta yi da ga shagon dan abin da yake so bazai samu ba. Mahaifiyarta kullum ta na mata nasihar ta tsare kanta da ga aikata zunubi mai girma wanda Allah yake fushi da wanda ya aikata, kuma ya yi hani ga bayinsa muminai na ƙwarai.
Gidan ƙawarta Mariya ta wuce ta same ta zaune akan tabarma a cikin falo ta na gugan kayan ta da dutsen guga na gawayi, sallama kawai ta yi ta zauna a kan tabarma ji take kamar zatai hauka.
“Juwairiya lafiya kike mai ya faru?” Mariya ta jera mata tambayoyin da ta kasa ba ta amsa ba, sai ta janye hannunta da Mariya ta kama tare da share hawayen da ya gangaro mata.
Mariya ta ƙarashe share mata sauran hawayen ji take ita ma kamar ta saka kuka, ta ɗago idanunta da suka kaɗa suka yi ja ganin ƙawar ta ta na kuka tace. “Ki yi min magana Juwariya! Kin san ba na jure ganin ki a cikin wannan hali, abin da ya sa naƙi dawowa kin san halin Baba Sani na rasa yadda a kai ya takurawa rayuwar ki baya son kowa ya raɓe ki, dan haushin koron da yake yi nake ji irin kullen da yake miki ko fa yaran sa baya yi mawa, lamarinsa akwai ayar tambaya ,dan ina tunanin akwai lauje cikin naɗi!”
Ta ja fasali ta na kallon Juwairiya da kukan ta ya tsananta, tuna yadda ya tsane ta yake azabtar da rayuwarta. Mariya ta ci gaba da magana cikin ɓacin rai ta na cewa.
“Ina jin takaicin halin da kike ciki amma ki sani bawa bai isa ya canza ma wani rayuwar sa ba,kin ga da Baba Sani baya miki kulle sai na sama miki aikatau ni bashi nake yi ba hankalina kwance.
Juwairiya ta sauke ajiyar zuciya duk da baƙin cikin da take ji na ƙin barta ta yi aikatau,wanda mahaifinta ma ya amince amma ƙememe ya hana ta da ta na yi ƙila da basu shiga cikin uƙubar rayuwa ba,gashi tun da ta gama sakandiri ya hana ta karatu amma yaran sa duk sun yi.
Duk da lamarin na ci mata tuwo a ƙwarya amma ba ta ce ƙala ba,sai dai zuciyar ta cinkushe take da damuwa tare da tunani iri-iri.
Mikewa Mariya ta yi ta shiga kicin ta zuba tuwo da miyar kuɓewa ta kawo mata ta na faɗin.”Gashi tun ɗazu na so na kawo muku amma ina tunanin wannan Baban naki,kuma Auwal tun da ya tafi islamiya bai dawo ba balle na bashi ya kawo miki.”Ta miƙa mata tare da kwance ƙullin zaninta ta ciro naira ɗari biyu ta miƙa mata.
Tsabar murna sai kawai ta rungumeta tare da fashewa da kukan murna,Mariya na taimakon ta ƙwarai ta na fatan Allah ya bata ta taimaka mata.
Rako ta ta yi ta siya magani sannan ta kaita dai-dai kwanar lungun gidansu.Da sauri Mariya ta saki hannunta ta na faɗin.”Na shiga uku wallahi gashi nan duk da ƙin kaiki gida da na yi amma ya na nan ya na sa ido ya san ki fita,ke Juwairiya wannan ko mijin ki ne sai haka.”Ta ruga da gudu har ta na tuntuɓe bayan ta gama maganar don Allah ya saka mata tsoron shi,bashi da mutunci in dai akan Juwairiya ne.
Juwairiya da jikinta ya fara rawa ji ta yi kamar ƙasa baza ta iya ɗaukar halintar ta ba,ta tsorata iya tsorata zabura ta yi kamar zata ruga sai kuma ta fasa ta na karanta wallahu galibun ala amrih ganin ya tunkaro ta.
Ya ƙaraso ya na mata wani irin kallo da shi kaɗai yasan ma’anarsa.”Ina kika je?”Ya tambayeta da murya kakkausa tare da saka ƙafafunsa ya take mata ‘yan yatsun kafar,ta rintse ido ta na jin wani iri madarar azaba ya na taso wa daga kan ‘yan yatsun na ta ya na zagaye ilahirin jikinta,taso ta matsa domin akoda yaushe ya tsaya kusa da ita ta na ƙalubantar yadda yake matsowa daf da jikinta.Amma hakan ya ci tura ganin yadda ya take kafarta ya hana motsinta.
“Bana hana ki yawon maula da uwarki ta koya miki,bayan Yayana bai rage ku da komai ba.”Ya faɗa ya na ƙara kusanci da ita fiye da na ɗazu.
“Don Allah kayi haƙuri bani ta yi wallahi ban roƙe ta ba,kuma Ibrahim zan bawa.”Tace yayin da taƙi shaƙar numfashi ba ta son ta shaƙi iskar hucin bakin sa da take jin sa a fuskarta.Ya ɗa ga kafafun na ta ya na ƙare mata kallo hakan ya bata damar shirin arcewa ko takalminta bata ɗauka ba,dan ya zame lokacin da ya take ƙafarta.
Da gudu ta ruga amma sai ta faɗi ƙasa yayin da miyar tuwon ya zube,amma duk da zafin da take ji bai saka ta yadda tuwon ya zube ba,ta zabura ta miƙe hanyar gida dai dai sanda ta ji ya na faɗin.”Ni da kene a duniyar na baza ki taɓa jin daɗi ba matuƙar ina raye,haka kawai na yi sakaci har tunanina ya faru mu zu ba mu gani.
Juwairiya na shiga cikin ɗaki ta fashe da kuka mai tsuma zuciyar mai sauraro,a ranta ta na jin baƙin cikin halinsa bata san mai ta tsare mishi ba,amma ya saka ma rayuwarta ƙahon zuƙa.
Koda ta shigo Mama ba tace komai ba har ta sha kukanta ta ƙoshi don tasan mai ya faru,tunna babu abin da za ta iya shi yasa bata tanka mata ba,sai ta jawo kwanon tuwon ta ba Ibrahim sannan ta bashi magani ragowar taci ta ragewa Juwairiya duk da babu miya kuma ta ji ƙasa-ƙasa a tuwon.
Bayan ta gama kukan taji sanyi a zuciyar ta dama kukan shi ke sanyaya mata zuciya,duk lokacin da ya yi mata hakan don babu wanda yake ko tari a cikin iyayenta,su kansu tsoron sa suke yi duk da mahaifinta shine babba.
Miƙewa ta yi ta ɗauro alwala ta yi magariba sai ta yi zamanta ta na jan carbi yayin da hawaye ke zuba fuskarta,wani gefe na zuciyarta ta na hasaso mata lamura sosai game da Baba Sani.
Baba Sani ya yi tsaye a gurin bayan tafiyar ta ya na tunani sannan ya ƙarasa dakalin ƙofar gidan ya zauna ya na gadin masu zuwa gurinta,ko da ka kira sallar isha’i ya yi sannan ya dawo ƙofar gidan ya ci gaba da gadin gurin.
Sai misalin tara na dare mahaifin Juwairiya ya yi sallama ya shigo da ƙullin leda mai ɗauke da garin rogo gwangwani biyu da siga.Mama ce ta amsa sallamar ta ƙarbi ledan tare da shinfiɗa mashi tabarma,lokacin har baccin wahala ya fara ɗaukar ta don yunwa take ji matuƙa kuma kamar zazzaɓi yake son kama ta.
Jin sallamar ya sa ta buɗe idanu ganin leda a hannun Mama ya sa ta miƙe tare da ƙarban ledar bayan ta yi mishi sannu da zuwa ta fice dan ta jiƙa garin.Ya kalli Ibrahim dake kwance ya na bacci ya shafa fuskarsa ya na faɗin.” Ya jikinsa?Ina can amma hankalina ya na nan kin san jiya ƙafarsa ta bani tsoro.”Yace ya na lasar bushashshen bakinsa dan rabon sa da abinci tun jiya da yamma da suka girka taliya leda ɗaya gashi ya wuni ya na faskare.
“Da sauki amma ya kama ta a maida shi asibiti gaskiya,yau ya bani tsoro ina ki kamar zan rasa Ibrahim saboda halin talaucin da muke ciki.”Tace sai kuma ta rushe da kuka ta na fyace majina.
A sanyaye Juwairiya ta ije garin da ta jiƙa ganin Mama ta na kuka ta koma gefe ta zauna ta na jin zafin Baba Sani dan ita gani take shi ya takurawa rayuwarsu da ya hana ta naimi aiki,in da ace ta na aiki rayuwar su ba ta yi muni haka ba,ga Mariya da take aikin suna jin daɗi kuma matar ta na taimaka musu.
“Ki bar kuka dan Allah da kin san halin da na wuni da kin tausaya min!Na dage tuƙuru ina faskare sai da na gama Malam Aminu yace bashi da kuɗi sai gobe,daƙyar na samu ya bani naira ɗari biyu wai shima kwana biyu ba cinikin iccen.
Shuru sukai cikin jimamin rayuwar su kowa ya na takaicin yadda suke tsotsan tsamiya,ganin Baba ya dawo Juwairiya ta miƙe tare da yi musu sai da safe ta tafi ɗakin da take kwana.
Washegari da safe misalin bakwai da rabi ta shafa addu’a,sannna ta miƙe ta nufi waje dan wanki zatai da aka kawo musu da safe kuma ana so anjima,murna sosai ta yi dan aka wo kuɗin wankin za su sami su yi girki.
Da sauri ta ƙarasa ta na faɗin.”La Mama har kin fara.”Bata ce mata komai ba sai botiki da ta miƙa mata ta ibo ruwa a randa.
Basu gama wankin ba har misalin tara da rabi bayan sun gama Juwairiya ta fita tayo musu cefanen taliya suka dafa da mai da yaji.Bayan ya dawo daga sallar asuba ya kwanta don ji yake ko ina na jikin sa ya na ciwo,bai tashi ba sai da aka gama girki shi ma sai da Juwairiya ta tashe shi,dan tasan yunwa ce ke damunsa.
Bayan yaci abincin ya miƙe tare da fita ya na son ya ga kanin nasa,akan maganar komawa da Ibrahim asibitin da kamar yadda likitocin suka faɗa.
Ya na ƙoƙarin shiga shashinsa suka yi kicibis saura kaɗan su yi karo,Baba Sani ya matsa ya na kallon ɗan’uwan nasa ya ce.”Lafiya yaya baka da lafiya ne?Ji yadda ka koma kamar wanda ake iban shi ana miya.”Yace da maganar shi ta izgilanci ya na karkaɗe jakar zuwa aikin shi,dariya kawai ya yi mai kama da yaƙe yace.”A irin wannan rayuwar ka na sane da halin da nake ciki ni da iyalina,yanzu ko taimakon da kake yi min ka daina.”Ya ƙarashe magana da takaicin yadda ɗan’uwan nasa ya daina taimaka mishi tun tsawon shekaru da irin butulcin da ya yi mishi.
Hannun shi ya watsa ya kalleshi ya na kallon agogo.”Sauri nake yi yaya kaga na yi latti kuma kasan yanayin aiki na,yi sauri ka faɗi abinda ke tafe da kai.Kuma da kake maganar ba na taimaka maka nauyi ne ya yi min yawa kowa ya ji da kansa.”
“Haka ne Allah ya shige mana gaba,amma ya kama ta ka duba rayuwar Juwairiya kaga ni bani da shi da zan saka ta a makaranta,kuma kace ba aure zakai mata ba baka da ƙuɗin auren da ita.”
“Haka na ce don ni yanzu ba ta aure nake ba,sabon gidana nake son na kammala.Ya bashi amsa a taƙaice sannan ya ɗora da ce wa.”Kuma da kake maganar na saka ta a makaranta baka ga yadda take mara kamun kai ba can zata dinga watsewa da mutane,ka na sane da irin ƙorafin da nake maka a kanta ni nasan halinta da nake zaman gida.”
Shuru ya yi ya na takaicin abinda ya faɗa ransa ya yi zafi,shi dai yasan kawai ya tsaneta ne amma yasan wacece ‘yarsa wani irin hali take dashi.
“Yaya na fa gaya maka aiki zan tafi amma ka tasa ni gaba kana ta wasiƙar jaki,ina sauri ne in kima baka da abin faɗe na tafi imna dawo saimu tattauna.”Ya ce dashi ya na ƙoƙarin fita da sauri ya tare shi sannan ya ce.”A kan maganar komawa da Ibrahim asibiti ne,kuma gashi bani da kuɗi dan Allah ka taimaka….”
“Haba yaya kasan fa bani da ƙuɗi nima hidima tayi min yawa kowa yaji da kansa,amma ga dubu ɗaya kuje Allah ya ba da lafiya.”Ya miƙa mishi ‘yan ɗari biyar guda biyu ya fice ya barshi a tsaye kamar sanda ya na tunanin butulci irin na ƙanin nasa.
A sanyaye ya shigo cikin sasan sa ya zauna akan turmi kamar babu laka a jikinsa,bai ce komai ba har zuwa wani lokaci sannan ya ja numfashi ya na kallon Mama dake ninke kayan da suka wanke har sun fara bushewa.
“Lailai ɗan adam butulu ne.”Yace cikin raunanniyar murya sannna ya ɗora da cewa.”Wai yau ni Sani yake wulaƙanta wa kan kuɗi ya manta yadda na wahala dashi dan ya sami ingantacciyar rayuwa.Mama ba tace mishi komai ba sai gyaran murya da ta yi,dan babu wani abu sabo a cikin halinsa duka sananne ne a gurinta.
Juwairiya na kwance bayan ta tashi ta yi sallar nafila ta yi addu’a ta koma ta kwanta,idanunta babu alamun bacci sai juyi take yi ganin haka sai kawai ta janyo carbi ta na ja,idanunta a rintse zuciyar ta na fatan samun maslaha a rayuwar su tunannin ta inda za’a sami kuɗi a mai shi asibiti,don likitocin suna tunanni aiki za’ai mishi a ƙafar.
Kawai sai ta ji ana ƙoƙarin buɗe ƙofar ɗakinta tsoro ya kama ta,tunawa da ta yi ta manta bata saka sakata ba da ta fita zuwa alwala.Tsananin tsoro ya kama ta ta rintse idanunta ta na tunani ta ya ya kai wani ya shigo cikon gidan su,dan Baba Sani ya gyara gidan kuma akwai ƙofa na masu kuɗi mai ƙarfi gidan.
Ba ta gama wannan tunanin ba ta ji mutum ya shigo ya nufi makwancinta,ta buɗe baki da nufin ta yi ƙara sai kawai taji an toshe mata baki da wata irin murya da nufin a ɓatar da tunanin mutum ga sanin mamallakin muryar aka ce.”In kika yi ihu saina kashe ki?Ya faɗa tare da soka zungureriyar wuƙa dai dai cikinta,amma ta yadda bazai cutar da ita ba.
Wani irin tsoro da tashin hankali ya ziyar ce ta taji tamƙar numfashinta zai yi balaguro zuwa wata duniyar wacce take da banbanci da wacce take rayuwa a cikinta.”Da gaske abin da sautin amon kunnnuwana suke gaya min muryar Baba Sani take amo a cikin dodon kunnuwana?To mai ya shigo dashi cikin ɗakina a wannan sulusin daren?”Irin tarin tambayoyin da suke ta bijiro mata a cikin zuciyar ta wacce ba ta samu ko da amsar ɗaya ba.
Kar dai ku manta sunan labarin “SAKACINA KO HALIN MAZA” Mu haɗu a shafi na uku dan har yanzu shinfiɗa ne har ba’a fara ba. Ga masu buƙatar shiga cikin group ɗina na whatsapp ga numba 08144072423_.
Kuma a buɗe take na ƙorafi gyara ko ƙarin bayani ga zakakuran marubuta, har yanzu ni mai koyo ce.
Kar dai ku manta da wannan lintafin sadaukar wa ne ga zaƙauran marubuciya, kuma ƙawata, Sumayya Na’ige. Allah ya ƙara fasaha ya sa ki fi haka, ina alfahari dake a cikin marubuta da irin taimakon da kike bani.
FOLLOW, READ, COMMENT, SHARE
an interesting novel