Skip to content
Part 1 of 5 in the Series Sakamakon Zunubi by Fatima Rabiu

Jerin motoci ne suke shara uban gudu kamar za su tashi sama, duk wasu ababan hawa sun tsaye gefe, an tara uban gosulo a tsakiyar titin.

Motocin sun fi guda ashirin dake ta wuce wa kamar ba za su k’are ba.

Wata magana na ji daga wata kekenafef, mutanan daya d’akko wata mata, matar ta d’an saki wani tsaki ta ce “fisbilillahi miye hakan anzo an tara mu a nan duk rana na dukan mu akan wani can zai wuce shine za a wani tsayar da bayin Allah”.

Mai nafef d’in ne yayi d’an murmushi yana cewa “haba Haj kike wannan maganar ba ki ga number dake jikin motacin da suke wucewa ba?, baki ga kalar motocin ba ansa BB No 1. Ai ɗan ɗan Sir Benjamin kenan ba wadda bai san su k’asar nan ba, suna tare da manya-manyan y’an siyasa wadanda suke fad’a aji a k’asar nan, saboda tsananin kud’in da suke dashi. Mahaifinsa yana da abokai su Uku ne suka had’a wani katafaran Estate tare da gidanjansu kantama-kantama, suka ware kansu daga cikin jama’ar gari, yanzu haka da nake gaya miki wannan wadda ya wuce ɗa ne daga cikin wa’innan mutane, yazo k’asar ne domin shi ba mazauni ba ne, matukin jirgin sama ne”

“Yanzu duk wannan uwar jiniyar da ake mai au ba ma uban ba ne d’ansa ne?”

“Kware kuwa Haj ai kad’an ma kenan daga cikin irin kud’in da halalinsa suka mallaka, family d’insu suna d’aya daga cikin masu kud’in duniya. Da yawan mutane sun d’iga ayar tabbaya akan su, domin ba wadda suke so ya rab’e su daga nasu sai nasu”.

Jinjina kai kawai matar ta yi, daidai motocin sun gama wucewa, aka bude ma sauran ababan hawa hanya.

Motocin kuwa har yanzu sun miƙa titi ga mamaki na, sunyi tafiya mai nesa da cikin gari sosai ba kad’an ba. Tukun naga sun d’auke wata hanya da yi cikin wani k’urk’urumin daji, mai duhun gaske da yalwar bishiyoyi, wata hanya suka mik’a a cikin jejin wadda ta kawo su wani katafaran Estate dai-dai bakin get d’in Estate d’in motocin suka d’an dagata. Idona na zaro d’aga kan da zanyi sai da zuciyata ta buga ganin irin tsaruwar get d’in kansa daga zama an rubuta BILLIONAIRE’S ESTATE.

Wasu maza masu k’irar sadaukan yak’i sunkai su shadda dake tsoron kafcecen get d’in, sanye suke da bak’ak’en kaya da gilas manne a idonsu tsaye suke k’am ko motsawa basayi.

Ganin motocin ne yasa da hanzari suka wangale katon get d’in gidan. Sakin baki da hanci nayi ganin kamar gari ne guda a gaba na. Jerin motocinne suka fara kutsa kansu cikin katafaran Estate d’in. Gabad’aya kaina ya kwance saboda irin had’uwar estate d’in gidaje ne jere part 6 a ciki, sai k’aton hospital dake ciki ga bishiyoyi masu mugun kyau da suka zagaye ko wanne part dake cikin estate d’in, sai garden Gym area, Swimming pools area, da wurin shak’atawa kai in tak’aice muku harda home beauty saloon, asibitin dake cikin estate d’in na kai idona a kai shima a samansa ansa BILLIONAIRE’S HOSPITAL. Sai wajan saloon shima an saka BILLIONAIRE’S SALOON, Komai daya danganci estate d’in ansa inkiyar gidan a jiki.

Tunani nane ya katse lokacin da jerin motocin da suka tsaitsaya a harabar estate d’in, kusan gabad’aya mutanan dake estate d’inne suka fiffito domin tarbar Captain Henry daka kalli yadda mutanan gidan suke farin ciki kai kasan ba k’aramin d’an gata bane gaba da baya.

Sakin baki na sake yi lokacin da aka bud’e bayan wata mota, sai da aka kai mintina kusan biyar kamin wata k’afa mai d’auke da wani matsiyacin takalmi ta fito daga cikin motor, shi kansa takalmin daka kallesa zaki shaida ba k’ananan kud’i aka kashe ba wajan sayensa, kamin gaba d’aya ya fito daga cikin motor. Alk’alamina ne na kusan yadda sa saboda kyakkyawar halittar Ubangiji da idona yayi tozali da ita. Kyakkyawan matashi ne Captain Henry fari ne tas yadda kasan bature, k’aramin bakinsa yad’an motsa wadda ya d’auke da jan lebe ja jir kamar na jiriri, sai kwayar idonsa ce ta k’arasa rud’ar dani kalar idonsa bulu shar dasu daga tsakiyar su kamar na mage, idan yana kallon mutum kamar mai jin bacci, wadda da yawa y’an mata na sasu cikin wani yanayi. Wani irin miyau na had’e lokacin daya saki wani murmushi na gefen baki, yana bin family d’insa da kallo da sauran y’an uwansa. Kai tsaye wajan wata mata wadda kallo d’aya zakai mata ka shaida mahaifiyarsa ce, ya nufa, yana zuwa ta rungumesa tana shafa kansa tana cewa “Wow my son Henry miss you so much”, wani murmushi ya sake sakar mata wadda daga gani kasan ita d’aya ake ma irinsa.

Wata matashiyar yariya ce ta taho da gudu tana anbatar sunansa a hankali ya anbaci sunanta itama da cewa “Emily” ya idasa maganar yana rungume ta itama. Murmushi ta saki mai k’ayatarwa tana zuba mai surutu. Bai wani kulata ba gaba, d’aya suka rank’aya sukai wani part wadda ya gaji da had’uwa.

“Ai fa Boss ya dawo yanzu zai hana mu shak’atawa wallahi and banso dawowar shi ba. Gashi an kawo wata y’ar aiki zazzafa nake gaya maka ina so na d’anata wallahi”

Cewar wani matashin saurayi, ya idasa maganar dai-dai sun zauna akan wasu kujeru dake zagaye da k’aton parlon da suka shiga.

Wadda yake ma maganar ya kallesa ya ce “wato Noah da kai da Isaac baza ku daina halin lalata y’an aikin da duk aka kawo estate d’in nan ba kenan ko, sai kun jawo mana wani bala’in ne wai”

Wani tsaki Noah yaja yana basarwa ya ce “kaifa Adam kana da matsala wallahi daga gayama abunda ke cikin raina minene a ciki to”

“Minene a ciki fa kace duk da ku ba musulmai bane and ko addinin naku bai yarda da irin abunda kuke yi ba, ba addinin daya ce ayi haka, idan kuma k’arya nake ka musalta mana”

Sosa k’eya Noah yayi yana tashi hango d’an uwansa yana wani ciccin magani. Isaac ya k’araso wajan yana basu hannu yana cewa “mi ake tattauwana ne kar ayi babu ni”

“Uhmm nida wannan Adam d’in mana shima kwata-kwata baya son harkar shak’atawa”

Isaac ne ya kai dubansa wajan Adam ya ce “anya Adama kana da ishashshiyar lafiya miye jin dad’in rayuwar to?, idan babu mata a kusa ina bazan iya rayuwa ba mace kusa dani ba”

Wani murmushi Adam ya saki yana cewa “shi yasa ma Henry yake birgeni da yake hanaku wasu abun ma yayi dai-dai wallahi, ayi dai mu gani Allah ya shirye ku”

Tab’e baki sukai suna amsawa da amin.

Dai-dai Henry ya gama shiryawa a part nasa ya sakko, yanzu sanye yake da wata riga har kasa mai k’aramin hannu bak’a ce tayi mai kyau sosai saita k’ara haskaka farar fatarsa, gaba d’aya y’an matan gidan wadda suka gaji da had’uwa da mazan da suke ji da kuruciya da gayu suka zauna akan wani darning mai d’auke kusan mutane goma sha biyar zuwa da ashirin ma, ko wanne ya nutsu yana cin abinci, da yawan y’an matan dake zaune a wajan ko wacce hankalinta naga Henry da Allah yayisa da farin jinin y’an mata ko cikin family y’an matan gidan nasu suna mugun sonsa, ko wacce burinta ace ita ce yake so, dama tunda aka fad’a yau zai sauka k’asar ko wacce ta dage da gyara jikinta.

Takaitattacan Tarihin Billionaire’s Family.

Hamshaƙan masu kudi wadanda sunan yi yayi sura a fadin duniya, sun shahara A idon duniya, Asalin kafuwar family din mutun ukune tushen shi, wadanda suka kasance aminnan junane, tankar shakikai, amintarsu ta faro tun daga kuruciya har izuwa girman su, kafin samuwar wadatar arxikin su, Almajirai ne marasa galihu muggan takalawa fakirai, jajircewarsu da kwazon su wurin neman nakansu yasa a hankali suka fara kasuwanci wanda daga bisani suka tsunduma a cikin siyasa, Har Allah yakaisu ga matakin da basu ta6a tsammani ba, harta al’umma sun yi mamakin Yadda bayin Allahn nan suka ha66aka a fadin duniya, shin su wanene wadannan Aminnan? Mutun nafarko daga Cikinsu Shine Sir benjamin former president na nigeria, kuma shine mutun mafi wadata arxiki a nahiyar africe, Ya kasance dan kabilan Yoruba ne, sannan mabiyi addinin kristan, yana da mata mai suna Dr Catherine suna kiranta da Mimi. Da yara guda hud’u Capitan Henry shine d’ansa na fari matok’in jirgin sama ne, bai cika zama a Nigeria ba, ya kasance miskili ne na sosai, bai cika shiga harkar daba shafe shi ba, idan kaga yayi magana mai d’an tsawo to tabbas abun nada mahimmanci ne a gare shi, duk cikin familyn billionaire’s ana ji dashi, danshi kansa shima ba k’ananan kud’i ya tara ba, sai ko y’an biyu maza Noah, da Isaac, basa jin magana kwata-kwata sune lalata duk wata yarinya da aka kawo aiki a gidan, saboda sunga bata da wani gata gaba da baya. Sun lalata yara da yawa sun maida su kamar matansu. Ga d’an shaye-shaye da suke afawa. Sune yawo can sune can, ga kashe kud’in tsiya kamar mi suna da wulak’anta mutane bare wadda yake k’asansu. Sai kanwarsu Emaily and itama itama dai tana wulak’anci bare ga y’an aiki bata da k’irki ko kod’an, amma duk ciki Henry yafi ji da ita. Sai masu aiki a part nasu akwai Hannah, Amali, Julia, Abigail, sai maza masu goge da share-share.

Bayan Sir benjamin mutun nagaba Alhaji Mu’azzam Gidan Dala, Shine mutun na biyu, ya rike mukamai da dama na yan siyasa, Ya kasance Hausa fulani ne, Yana da tarin arziki naban mamaki Yana da mata biyu ta farko mai suna Haj Saratu wacce suke ma lak’abi da Amma tana da yarinya d’aya mai suna, Ayat sai sai kuma matarsa ta biyu mai suna Haj Shuwa, suna ce mata Ammi, itama tana da yarinya mace Asma, sun kasance suna Matuk’ar son Henry suna kishin junansu akanshi basu cika junatuwa da juna ba saboda ko wacce burinta ace ita ce wacce Henry zai aura, a tsakanin iyayan nasu ma basa wani jutuwa ko wacce burinta ace d’iyarta ce kan gaba ga komai, suna yawan had’ama junansu munafurci saboda ba k’aramin kishi ake bugawa tsakanin Haj Shuwa da Haj Saratu ba. Suna y’an aikin part nasu kowacce nada y’an aiki hud’u biyu maza biyu Mata, Mutum na karshe daga cikin su sunan shi Alhaji Habu ana yi mashi lakabi da Barumaye, yana mata mai suna Haj Binta wacce suke kira da Mami tana da yara guda uku na farko Adam, Adam ya kasance yaron kirki ne duk da shima ta wani b’angaran baya da yawan fara’a, amma duk haka idan kuka zauna tare dashi baya son marar son gaskiya duk inda gaskiya take saiya fad’a koda za’a tsire shi ne, sai kuma Aziz shima dai ba daga baya ba wajan rashin jin magana, shima yana shaye-shaye da d’an lab’ewa da yaran masu kud’i y’an mata yana masu b’arin kud’i yana holewarsa dasu. Sai kuma autarsu Mubeena, itama dai akwai d’agawa da nuna ita wata ce, but bata shiga harkar ko wanne part na Estate d’in nasu rayuwarta kawai take, akwaita da son rayuwar k’arya da yawan k’awaye. Tana da k’awaye kusan su uku halinsu kusan d’aya ne da juna Hana Layla da Amira, suma akwai son rayuwar k’arya duk da iyayansu ba wasu hamshak’an masu kud’i bane, shi yasa suka mak’ale ma Mubeena domin tana basu duk wani abo da suke so, shi yasa kullum suna Estate d’in su Mubeena nar su baro cikin gari su taho. Suma suna y’an aiki kusan hud’un, ko wanne d’an aiki yasan part d’in da yake aiki, da kuma irin aikin da yake yi. Duk y’an aikin part d’in su Emaily sunfi shan wahala da kyara, sai kuma y’an aikin su Ayat b’angaransu Haj Shuwa, suma dai suna shan tsangwama, y’an aikin part d’in su Adam ne kawai basa wani shan wulak’anci sai a wajan Maminsa itama ba daga baya ba, bata da son mutane ga nuna d’agawa da nuna ita wata ce.

Tasha shiga cikin su Haj Shuwa tana d’agawar ita mai gidanta bai isa yi mata kishiya ba bare har taita b’ab’ato da wata aba wai kishiya. Suna matuk’ar jin haushinta sosai.

Sakamakon Zunubi 2 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×