Henry yana cin abunci kad’an kamar baya son ci, yana ci yana d’an danna wayar dake hannunsa. Wata budurwa dake kusa dashi, ta juya ta d’an tab’o y’ar uwarta dake kusa da ita sosai, d’an kasa tayi da murya ta ce “Asma guy d’in nan fa yayi wallahi dama Abbu zai barni na aure shi ni ba ruwana da wani ba musulmi bane, and tunda Daddynsa duk abokai ne ina ganin kamar ba zai ki ba”
Wani murmushi d’ayar ta saki tana cewa a zuci “hmm Ayat kenan idan kinga na barki kin mallaki Henry to bana durun duniya ne, amma babu wacce ya dace ta ita sai ni”. Amma a fili sai ta d’an saki wani murmushin yak’e tana cewa “ke kuwa miye zaki yi da Henry kin manta a addininmu ba’a haka, da dai shine musulmi ke ce wacce ba musulma bane za’a iya hakan”.
“Amma ta tabbas Asma zan shawo kansa ya musulinta su Abbu ma suna so Daddy Benjamin ya musulinta shida iyalinsa”. Tab’e baki Ayat tayi tana harara Asma k’asa-k’asa.
Wadda suke ta maganar domin shi ma tuni ya mik’e yana yana hawan bene rik’e da waya manne a kunnansa.
K’arar fad’uwar wani abu da suka ji a saman yasa ba shiri suka mik’a su duka, Emily ce ta zaro ido tana nufar kan benan inda Henry yake rik’e da wata matashiyar yarinya wacce bazata wuce shekara goma sha takwas ko sha tara, da ka kalle ta zaka shaida y’ar aiki ce domin sanye take da wani yadi kalar sararin samaniya uniform, riga da wando rigar ta kai mata har gwaiwarta, ganshin kanta ya rufe mata fuska. Zero ido tayi cikin tulin gashin daya rufe mata fuska, ba abunda k’irjinta yake sai lugudan bugawa, na tsananin tsoro, domin kawai tana sakkowa ne kanta a kasa tana son barin parlon kamin wani ya lura da ita. Domin tasan halin gidan gaba d’ayansu basu cika mutumci ba, duk wani wadda yake aiki a k’ark’ashinsu su wulak’antaka ba wani abu bane a wajansu, na kirkin y’an kad’an ne daga cikin su. Tunanin ta ne ya katse jin an fisgota daga jikinsa sai dai taji saukar mari tasss tassss kake ji k’arar marin ta karad’e gaba d’aya babban parlon.
Saukar maganar Emily taji a kanta da masifa tana cewa “ke Amalil Islma wacece ke? har kin isa had’a jiki da brother na kina y’ar aiki dake k’ask’antacciya dake k’azama, to kin jama kanki mummunan horo a waje na, shashasha bagida jiya kawai”.
Wasu irin hawaye ne suka shiga zuboma Amalil dake tsaye tana duban yadda Emily take surfa mata ruwan rashin mutumci, tana da tabbacin ta girmeta amma talauci da rashin galihu yasa tana wulak’antaka, yaya zata yi dole ne zama a k’ark’ashin su tunda tunda ta taso a gidan kawai ta ganta, wasu daga cikin y’an aikin suna yawan bata labarin Mahaifiyarta ai wajan haihuwarta ne ta rasu kuma ta barta a gidan, ta d’ora da bautar da Mahaifiyarta tayi can baya.
Da sauri taja himar d’in dake sanye a wunta ta gyara gashinta daya fito tana had’e wani abu a zuciyarta. Hakuri ta cigaba da bata amma yadda kasan ana zuga Emily yadda take ruwan masifa, shi ko wadda ake abun danshi tuni yabar wajan.
Bak’in ciki duk ya cika Amali data bisa da kallo kenan ma ma zai tsawatarma k’anwarsa ba? Duk tasan halinsa ko mi za’ai indai bai shafesa dole ba baya ma sa baki bare har ya shiga harkarka miskili ne na bugawa a jarida.
Marin da aka k’ara kaima Amali ne ya dawo ta ita daga bin Henry da kallo da tayi. Bin Asma tayi da kallo data mareta ta cakumo mata wuyan riga tana janta kiiiii tana nufar waje da ita tana cewa “kee mayiya uban mi kike kallo a jikinsa?, au dama kina sane kika fad’a jikin nasa kenan?, kega karuwa y’ar iska, to ki bud’e kunnanki kiji da kyau kinsan suwaye mu kinsan Henry yafi k’arfin ki nesa ba kusa ba, bakin rijiya ba wajan wasa makoho bane, ki kiyaye koda kallonsa ne idan ba haka ba, na rantse saina yi sanadiyar nakasa idon naki”
Shiru wajan ya sake d’auka, Adam na so yayi magana amma Maminsa tayi mai mugun gargad’i da ido, sauran samarin gidan kuwa ko a jikinsu saima komawa su kai suka ci gaba da cin abincin su hankali kwance.
Banko k’ofar parlon da akaice yasa Amali sakin kukan dake taso mata tun d’azo, tana kuka ta nufi part d’in y’an aikin gaba d’aya estate d’in da yake waje guda aka ware masu. Duk da kowanne d’an aiki da gidan da yake aiki na cikin estate d’in guda shadda dake cikin estate d’in.
Koda ta shiga b’angaran nasu babu kowa duk sun tafi inda suke aiki, shiga d’akinsu tayi wadda yake d’auke da jerin gadaje kusan guda goma, saboda k’aton d’aki ne, babu abunda ba’a sa musu ba harda fankar sama data k’asa sai toilet guda uku dake a cikin d’akin duk da d’akin bashi kad’ai bane akwai kusan guda biyar dake jere da juna kuma ko wanne d’aki na d’auke da gajen guda goma da toilet uku a cikinsu, part mata daban na maza ma daban, duk yawan su ko wanne da irin aikin da zakiji yana yi wani wanki da goga wani wanke-wanke wani girkin abinci, wani goge-goge, wani ma gogar takami ne kawai aikinsa, kai kowa dai da abunda yake yi. Ita Amali tana d’aya daga cikin wadda suke aiki shashinsu Emaily, kuma abinci take girkawa, suna shan wahala sosai dan a rana sai suyi abinci ya kai kala goma koma fin haka, mutunan gidan suna ji da milki da isa suna gadara da kud’i.
A can parlon su kuwa Emily dake kallon Asma tana murmushi ta ce “hey sister kinyi dai-dai wallahi, ai ki barni da ita, saina gyara mata zama ne, shegiya kodan ta ganta da kyau?”
Wani yatsine baki Asma tayi tana amsa da cewa “har wani kyau ne da ita ni banga kyan ba gaskiya mi take dashi?”
Duk abunda suke Ayat na kallo tana sak’a wani abu a ranta, wani murmushi ta saki tana tono yadda zata rink’a amfani da Amali tana k’unsa ma Asma bak’in ciki akan Henry, tabbas za tai amfani da ita, ko dan ta jefi tsuntsu biyu da dutse d’aya, zata sa a k’ara tsanar Amalin, sai kuma Asma da zata rink’a kwasar bak’in ciki.