Skip to content
Part 3 of 5 in the Series Sakamakon Zunubi by Fatima Rabiu

Tab’a tan da akai ne yasa da sauri ta tashi tana share hawayenta matsowa kusa da ita Hannah tayi tana sa hannunta ta dafa kafad’arta, cike da tausayin su ta ce “Amali lafiya dai na ganki a haka, ko dai mutanan gidan nan ne suka yi miki abunda suka saba yi ne?”. Wani murmushin k’arfin hali Amali tayi tana duba agogo, da sauri ta mik’e tana cewa “karka damu Hannah bari na je wajan Emily tana jira na, kinsan lokaci take badawa idan banje akan time komi zata iya min”

“Ai nima bari mu tafi tare zanyi mata wankin kaya”

Da sauri suka fice suna jawo k’ofar d’akin nasu.

Suna shiga kai tsaye part nata suka nufa, koda suka shiga tana waya ne da wani saurayinta, samun waje k’asa sukai suka zauna suna faman jiranta tana waya tana kurb’ar shayi.

Sai da ta d’au kusan minti 40 tana waya tukun ta aje wayar a nan ma sai da ta nuna kamar ba mutane bane a gabanta, sai da ta mula ta munl-mule. Ta d’ago tana binso da hararara. Suko dama duk zaman ya gunduresu babu yadda zasuyi ne.

Wani tsaki ta saki mtswwww tana ya tsine baki, a tsawace ta ce “ubanmi zanyi muku?, kuka wani zo kuka zaunawa mutane a nan, sai wani wari kuke kun cika min d’aki da wari”. Da sauri Amali tayi k’asa da kanta tana duba jikinta harda d’an shinshina jikinta koda wai zataji warin da aka ce suna yi, amma itakam bata ji wani wari ba. Tsawa ta kuma buga masu ta ce “keee Amali dubanni nan”. Da sauri Amali ta d’ago tana kallon Emily, sai dai d’ago war da zatai taji saukar ruwan shayin dake hannun Emily ta watsa mata shi a fuska. Runtse idonta tayi tana jin wani rad’ad’i na ratsa mata fuska. Wasu hawaye ne suka shiga zarya akan fuskar tata. Hannah dake kusa kuwa da sauri ta zaro ido, tana sa tafin hannunta ta tushe bakinta. Kallonta Emily tayi tana cewa “kee Hannah tashi ki bar wajan nan munafaka, kin wani zauna min a nan baki san aikinki bane?”. “Amma ranki ya dad’e ke ce kika ce idan na zo na rink’a tsayawa harsai kin ban umarnin farawa tukun sabo…. Katseta tayi a tsawace ta ce “dalla can rufe min bakinkin nan mai wari, munafuka kawai bagidaji zaki tashi kibar wajan nan ko sai na zamga miki mari?”.

Da sauri Hannah ta mik’e har tana tuntub’i tayi wajan b’an d’aki domin yin aikinta, jikinta duk a sanyaye tana waigen Amali dake zaune kanta a k’asa.

Emily ta dawo dubanta ga Amali ta ce “kee kuma yau ina so ke kad’ai zakiyi min abincin mutum ashirin da biyar, idan kin gama ki gyara Babban parlon gidan nan, zaki iya tashi kiban waje”.

Wata irin zabura da zare ido Amali tayi ta ce “ranki wannan aikin banzan iya yinsa ba ni kad’ai, ki tausaya min dan Allah”. “Ke rufe min baki zaki tashi kibar wajan nan ko saina miki shegen duka, kuma nanda minti goma idan na sakko baki fara aikin dana saki ba to tabbas horon da zan miki sai ya fi wadda nayi miki yanzu, dalla tashi kiba mutane waje”.

Emily ta idasa maganar tana bin Amali da wani banzan kallo na k’as-k’anci. Da sauri Amali ta tashi jikinta a sanyaye tayi waje.

Koda ta shiga k’aton kitchen d’in part d’in nasu Emily, tsabar girma da da fad’i kamar wani d’aki guda, bin kitchen d’in tayi da kallo kamar ganin babu kowa kenan duk an kori kowa ana nufin yau ita d’aya zatai duk wani aiki daya shafi abinci.

Da sauri ta fara aikin, tun tana yi da marmari, tana yi ta sauke wannan ta d’ora wancan, kanta harya fara juyawa tsabar yadda ta jigatu tasha bak’ar azaba kamin ta gama abinciccikan nan. Wani irin jiri take ji da kyar ta lallab’a ta fara gyaran k’aton parlon da kai girman wani gidan. Tana idasa kyaran ta zube, wajan a sume saboda wani irin bala’in jiri dake d’ibarta ga yinwa bata ci komai ba.

Emily dake sakkowa taci uban wanka an zubo gashin doki har gadon baya, ansha k’ananun kaya ana cin chingum ana taku d’ai-d’ai.

Jan birki tayi tana duban Amali dake yashe a k’asa, duk taga kamar ba k’alau take ba amma hakan baisa ta tausaya mata ba, da wata irin tsana ta nufi firiza tana d’akko ruwa mai sanyi tana zuwa kan Amali ta b’alle murfin ruwan ta fara kwarara mata shi a jiki. Wata irin zabura tayi har lumfashinta na shid’ewa tsabar yadda ruwan sanyin ya shigeta. Da sauri ta mik’e da kyar ta tsaya kan k’afafunta saboda kwata-kwata bata da k’arfi a jikinta. Emily tayi mata wani d’an iskan kallo tana cewa “uban mi kike a nan?”. Amali ta had’e wani abu mai d’aci a mak’oshinta ta ce “ranki ya dad’e babu komai banma san na fad’i a wajan ba”, “yen yen yen da anyi magana kin iya munafurci da iya zaro zance kega tsohowar munafuka, and kin gama aikin dana saki ko kuwa?”

Da sauri Amali ta ta bata amsar ta gaba d’aya, amsar data bata ce ta bata haushi ta ce ma Amali “kin taimaki kanki and zakiyi kwana uku kina min abincin nan fatan kin gane?”

Wasu hawaye ne suka cika idon Amali tana amsawa a ladabce. Tana tsaye saida tayi kusan minti biyar tukun Emily ta bata umarnin zata iya tafiya.

ISAAC AND NOAH POV

Zaune suke a wani lambu dake cikin estate d’in nasu suna shan lemo, Julia ce take ta sintirin kawo masu kayan ciye-ciye, tana yi tana gyara suturar dake jikinta domin ta lura da wani d’an iskan kallo da suke binta dashi. Allah-Allah kawai take ta gama aikinsu ta tafi, karda suyi mata wani mugun abun. Sai dai tana gaf wucewa har tana murnar ta gama basu mata wata maganar banza ba. Kawai taji muryar Isaac yana cewa “kee Julia kike ko kowa dawo nan”. Wani irin miyau Julia ta had’iye , ta juya ta nufi inda suke zaune ta duk’a k’asa, kanta a k’asa zuciyarta na wata irin bugawa tsabar tsoron daya dirar mata. Batai aune ba kawai taji Isaac ta jawota, sai ganinta tayi zaune akan cinyarsa yana k’ok’arin sa hannunsa a cikin rigarta. Da sauri ta rik’e hannunsa tana girgiza mai kai hawaye nabi mata fuska, kallonta yayi da haushi ya fisge hannun nasa yana kifa mata wani mari mai zafin daya sa ba shiri ta sakar mai hannun nasa. Bai tsaya komai ba yasa hannunsa biyu yana kamo gaban rigar Julia yajata da mugun k’arfi ji kake feeeet ta yage gida biyu. Wani irin marayan kuka ta saki tana sa hannunta domin k’are k’irjinta, sai dai Noah daya taso ya rik’e hannun nata ya jasa baya ya bank’are mata hannu ya jasa baya har sai da ya bada wani sauti k’as. Wani kuka ta sake saki. Wani kyalli Isaac ya d’akko ya d’aure mata baki dashi, sana Noah ya sureta yayi part d’insu da ita Isaac na biye dashi.

Koda suka shiga a tsakar parlon su suka ajeta suka cire kaya a gabanta su duka sai da sukayi anfani da ita, harda inda ya kusan sa zuciyarta bugawa, saboda harta duburarta saida sukayi anfani da ita, bak’in ciki ya cika mata zuciya kukan ma ta kasa sai sauke ajiyar zuciya take. Suna gamawa Noah ya tashi yana tufa mata miyau a fuska. Da sauri ta runtse idonta hawayen bak’in ciki da tsananin tsanar su na zubo mata ta gefen idon ta. Tsawar da suka buga mata ce yasa da kyar ta mik’e. Wurgo mata kayanta da suka keta su, sukayi masu fata-fata. Isaac ya ce “dallah tashi daga nan, kuma ki tabbatar kin kyara mana parlo ki tabbatar kin kyara wannan k’azantar”. Binsu kawai Julia tayi da kallo har suka haye sama, da kyar ta samu da d’angyanshi da rarrafe ta d’an gyara parlon, tasa kayanta ta nufi k’ofar fita idonta jawur da kyar take tafiya k’afafuwa duk a gwale.

<< Sakamakon Zunubi 2Sakamakon Zunubi 4 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×