Skip to content
Part 4 of 5 in the Series Sakamakon Zunubi by Fatima Rabiu

“Adam wato ba zaka daina shiga harkar da babu ruwanka ba ko?”

“Amma Mami kina ganin irin cin fuskar da suke ma wannan yarinyar Amali kuma ace ba wadda yayi magana”

Kallon sa Mami tayi tana k’ara cewa “to ina ruwanka a ciki? Miye matsalarka da ita? Hakan ai shine ya dace da talaka tunda dama bauta ce ta kawota dole kuma tayi hakuri tunda a k’ark’ashin wani take, kaga kuwa dole a juyata”. Zai sake magana ta d’aga mai hannu ta sake magana ta ce “kaga dakata Adam daga yau duk abunda zai faru bana so kana tsuma bakinka, indai abu bai shafeka ba”. Ba yadda ya iya kawai ya fice daga part d’in nasu yana jin wani iri a ransa.

Yana fita Mubeena tayi sallama tare da k’awayenta su uku suna tafe suna rufa mata baya Mami ce tayi murmushin ganinsu, Mubeena ta d’an tsaya tana kallon Mami ta ce “Mami yana ganki haka?” “Uhmm” sauke lumfashi Mami tayi tana jawo hannun Mubeena ta zaunar da ita ta ce “nida Yayanki ne mana ya cika shiga abunda babu ruwansa a ciki”

Tab’e baki Mubeena tayi tana mik’ewa ta ce “ai Mami indai Ya Adam ne ya saba da hakan dan haka ki daina ma damun kanki, amma nidai kam dama kowa ya sani bana shika shirgin family d’in Estate d’in nan tamu kowa yayi harkarsa, sai idan kaine ka shiga tawa harkar nanne fa za’a sha kallo danni kinsan Mami bana son raini a rayuwata”

“Ai Mubeena ke ni ce kika biyo duk wasu halayanki amma banda Adam sai kace an canza min shi wallahi”

Kiss kawai Mubeena ta kai mata ta juya ita da k’awayenta da suka gaida Mami ta amsa fuska a sake, suka fara haurawa sama Mubeena na tafiya tana cewa “Mami wai yaushe su Abbiey zasu dawo ne sunfa dad’e?”

“Eh kinsan dama idan suka tafi harkar kasowancinsu da harkar siyasar nan sai a hankali amma cikin satin nan zasu dawo shima naji Sir Benjamin sai tafi k’asar India cikin satin nan”

Da sauri Mubeena ta waigo inda Mami take ta ce “shin wai shi Daddyn su Henry ba zai hakura da siyasa ba wannan zab’enma sai ya ce saiya tsaya takara, da alama neman asiri zaije India dan kinsan ba wadda ya kaisu iya asiri da sihiri wallahi”

“Kinci gidanku ina ruwanki idan basa irin haka an gaya miki zasuci zab’en ne ki wuce kawai ku shiga ciki, wannan zancen ba naku bane”

Shuru Mubeena tayi tana d’an d’aga kafad’arta irin ko a jikinta d’in nan.

Ayat dake zaune akan kujerun parlon su tana kallon wani film, taji Amma ta tab’a ta tana cewa “da alama ba kallon nan kike ba, domin tun d’azo nake ta miki magana amma baki ji ba hankalinki na wani waje, mi yake damunki ne?”

“Tabbas Amma akwai matsala ina son Captain Henry amma Asma tana shigarmin hanci da k’udundine wallahi”

“To kina buk’atar fiddota kenan?”

“Tabbas Amma haka ne, ina so na shirya mata wani tugun da zata rink’a kwasar takaici”

Murmushi Amma ta saki tana k’ara dafa k’afadar Ayat ta ce “karki damu mudun ina lumfashi Asma ita da uwarta bazasu tab’a mallakar wani abu mai daraja ba, ke dai kawai ki cigaba da k’ulla masu munafurci ni kuma zanje ga boka na d’an mukyakis zai min wani aiki akansu”

Wani tsalle Ayat ta saki tana rungume Amma tana cewa “shi yasa a bana jinki Amma, Amali zan had’ama tarko domin itama na tsani yarinyar da ace nan part d’inmu take aiki da tuni nasa an koreta daga estate d’in nan, domin idan kika lura yarinyar nada wata baiwar kyau mai fisgar mutum, tare da wata baiwa duk namijin da yayi katari da ita dole sai ya kalleta ya sake kallo, wai a haka ma cikin wahala take inaga ta samu waje, ai ba’a san yadda zata koma ba”

“Kashhh wannan ma ki daina tunaninta, domin bazata bamu matsala ba, idan kuma zata bamu ai baza tai wahalar kawar da ita bama a duniyar gaba d’aya, wa take da shi?, waye gatanta a duniya?, waye ubanta? bata da kowa bare har ta d’au kanta wani abu baiwace kuma y’ar aiki kuma a haka zata cigaba da zama”.

Murmushi kawai Ayat take saki tana sauraran Amma.

Tashi kawai Ayat tayi ta d’au wani k’aramin mayafi tana nufar k’ofar fita daga part d’in, da sauri Amma ta ce “ina zuwa kuma Ayat muna magana kawai zaki tashi?” “Karki damu Amma yanzu zan dawo kinsan da zafi-zafi ake bugun k’arfe ina zuwa”. Tana idasa fad’ar haka tayi waje.

Fitowarta kuwa ta hangi Amali dake fitowa daga part d’in su Emily, wani murmushi cin nasara tayi tana kwalama Amali kira. Amali dake tafiya a hankali saboda aikin da Emily ta sata da kyar take tafiya, tana k’araso, ta ce “ga ni ranki ya dad’e”

Wani banzan kallo Ayat ra wurgama Amali kamin ta ce “ina kiranki kina min wata yanga, ubanwa zakiyi ma yanga a nan wajan iyeee?”. Wani abu mai d’aci Amali ta had’iye a mak’oshinta cike da takaicin mutunan gidan gaba d’ayansu ta ce “kiyi hakuri bana jin dad’i ne”. Tab’e baki Ayata tayi tana cewa “ki biyo ni”.

Tana fad’ar haka ta juya tayi cikin part d’in. Bin bayanta Amali tayi, har suka shiga cikin parlon gidan basu tsaya parlon Amali taga sun nufi kitchen, tana zuwa taga Ayat ta d’akko wani lemo da wasu kayan ciye-ciye tasa a faranti tana mik’ama Amali ta ce “ungo nan kije part d’in Henry ki kai mai”

Zaro ido Amali tayi tana kallon Ayat ta kasa amsar farantin, wani banzan kallo ta bita dashi tan cewa “kee ni sa’arki ce zance kiyi kaza, ki tsaya kina bina da kallo, zaki amsa ki wuce kije ko kuwa sai na ci miki uwa?”. Wani irin abu taji ya rik’e mata k’irji dan taji zagin da Ayat d’in tayi mata ta tsani a zagar mata iyaye, cike da jin haushin Ayat d’in ta amshi farantin bata k’ara cewa komai.

Ta juya zata tafi taji muryar Ayat na cewa “saura kuma idan kika je baki gansa ba ki juyo ki taho baki basa ba, ki tabbatar ya ganki ya amsa da kansa, kinji na gaya miki?” Wasu hawaye ne Amali taji sun tarar mata a cikin ido, da sauri kuma ta mayar dasu, bata dai ce komai ba ta fice kawai.

Tana fita daga part d’in ta tsaya cak tana duban masu tsaro kota ina a cikin estate d’in sai shawagi suke bare a k’ofar part d’in Sir Benjamin, shine yafi kowane part girma a gidan, da tsoro da komai ma, duk da yana d’an siyasa bai zauna gidan gwammanati ba, yafi son zama a cikin estate d’in, tana tunani tasan idan ba tana y’ar aikin gidan ba ita ai bata isa koda taka inda d’an president yake ba bare harta sa president d’in a idonta tasan komai sanadi ne, ji yadda ake basa tsaro shida y’ay’ansa kai duk wadda ke cikin estate d’in ma idan zai fita cikin gari haka zakaga ana mai jiniya tare da motoci nabin bayansa.

Tana tunani harta k’arasa inda part d’in Henry yake, duk haka sai da masu tsaron part d’in suka dakatar da ita suka duba abunda ta d’akko tare da dubata ko ta taho da abun cutarwa, duk sunsanta sun san ma’aikaciyar gidance, amma haka k’a’idar take, idan shiga goma zakai sai an cajeka.

Koda ta shiga k’aton parlon, wani k’amshi yayi mata d’irar mikiya daya sa sai da ta lumshi idonta tsabar yadda k’amshin turaran ke shiga ta k’ofar hancinta. Sauke ajiyar zuciya tayi, tana tsaye ta rasa inda zata nufa da kayan dake hannunta.

Gargad’in da Ayat tayi mata, ba yadda ta iya ta haura sama inda take d’anjin motsi.

Koda ta shiga yana zaune ya d’ora k’afa d’aya kan d’aya, yana aiki a computer sai wani mutum dake tsaye gefensa yana masa bayanin wasu takardu yana nuna mai. Jin shigowar mutum da sallama yasa mutunan dakatawa da yimai bananin, tunda ya kalleta sau d’aya ya maida dubansa ga computer, sai mutunan data ji ya kira da suna Osman, ne ya kalle ta yana cewa “ranka ya dad’e kaine kasa a kawo ma abinci ne?”.

Sai da aka d’au minti talatin kamin yad’an motsa bakinsa kamar baya son magana ya ce “No, I don’t know about him, to be honest”,

Shine kawai ya ce ya tsuke bakinsa, wani haushi ne ya cika Amali jin yadda ya amsa, to ita ina ruwanta dashi cewa akai ta kawo mai kawai.

Osman ya ce “zaki iya ajewa ki tafi”

Da sauri Henry ya dakatar da ita, shuru sukai Amali ta cigaba da tsayuwa su kuma suka cigaba da aikinsu. Amali tun tana tsayuwa da marmari harta gaji ta rasa ta inda zata fara magana ma. Har sai da Osman ya gama mai bayanin komai ya sallameshi ya tafi Amali na tsaye kamar wata g’unki, bak’in ciki ya gama cikata sai harararsa take tana murgud’a mai d’an k’aramin bakinta. Duk yana kallonta ta k’asan ido wani miskilin murmushi ya saki yana dubanta maganarsa bata fita sosai saboda jin kai ya ce “Who brought me food and it’s not your job?”

Sai da ta murgud’a baki sana ta ce “ni nasa kaina”

Baiji mi ta ce sosai ba saboda itama kamar rad’a maganar ta fito, kallonta yayi na wasu y’an mintina tukun ya ce “am taking to you”

Sauke ajiyar zuciya tayi ta sake cewa “ni ce nasa kaina”

“Who told you that I need food?”

Wani haushi ne ya kamata bata k’ara magana ba, shima shuru yayi, ya k’ara barinta a tsaye har saida Amali tayi danasanin fad’ar haka, yafi hawa d’aya yana aiki a computer kamar wani injin ko gajiya baya yi. Tukun yayi mata nuni da hannu ta aje kayan.

Tana ajewa zata juyawa ta tafi taji muryarsa yana cewa “I told you to go?”

Wani irin takaici ne ya rufe Amali, har bata san sadda ta fara bubbuga k’afa ba tana tab’e baki alamar tana gaf sakin kuka. Shi ko kallonta take ta k’asan ido yadda tayi kamar zata mai shagwab’a shi dariya ma ta bashi, amma ya maze, idan ka kallesa saika rantse da Allah ba ita yake duba ba. Ci gaba yayi da safgar gabansa, sai da Amali ta k’ara kusan mint ashirin harta fara hawaye, tukun taji saukar muryarsa mai kamar busar sarewa ya ce “You can go, from today you can do the work that has not been released”

Harara ta b’alla mai ta juya ta tafi, tana masifa a zuciyarta, au duk tsayuwar da tayi dama babu abunda zatai mai tsabar mugunta ce dama gashi ba wani jin dad’i take ba, ai ko kyar take taka k’afarta saboda yadda sukai mata nauyi saboda yadda tasha tsayuwa..

<< Sakamakon Zunubi 3Sakamakon Zunubi 5 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×