Skip to content
Part 1 of 1 in the Series Sanadin Kaddaratata by Zarah Maitama

Bismillahir Rahmanir Raheem

Garin a lumshe yake kasancewar lokacin damuna ne kuma ga yanayin safiya, iska ce mai dadi take kada duk mutumin dake a waje harma da wanda yake a daki dan sosai ake iska.

Safiya ce sosai bayan Asuba kenan wanda sai a lokacin garin ya fara haske, mutane jefi_jefi na wucewa, wasu daga masallaci suke, wasu kuma harkar gabansu ce ta fito dasu.

Tafiya take yi babu tsagaita wa dauke da goyo a bayanta wanda ke daure da wani kyakkyawan farin towel, sai dai na kasa fahimtar a yanayin da take ciki, dan kuwa ita ba sauri take yi ba kuma ba a hankali take tafiya ba, wani lokacin idan ta wuce ta wani wajen wasu mutanen kan juya su kalleta su cigaba da harkar gabansu.

A hankali nakai kallo na zuwa kafarta da iska ta kada zaninta har hakan ya bashi damar dagawa, jini ne busasshe a kafarta ta, komawar zanin inda yake ya bata damar cigaba da tafiya ba tare data kalli ko mutum daya daga cikin masu kallanta ba, ba ta tsaya ko’ina ba sai da taje wajen wani tudun yashi dake aje waje guda sannan ta fara kokarin kwance towel din dake bayanta, hakan ne ya sake ba ni damar ganin jinin dake kwance akan fararen kafafunta, sai dai ita da alama bata damu da hakan ba dan kuwa cigaba tayi da kwanto abinda ke bayanta.

Daidai lokacin wasu mutane su biyu mace da namiji suka fito dattijai, dattijon na bayan matar.

“Ai dai kya yi da jiki mu isa da wuri. Kinsan dai..” Bai kai ga karasawa ba ya hangi wata matashiya na kwanto abu daga bayanta, kuri ya yi cikin hasken farin watan daya gama washe garin yana kallanta bakinsa na rawa ya furta” Jirani anan, yau nake ganin wani ikon Allah”  Ya fada yana yin gaba, kamar wanda aka tsikara sai kuma ya juyo ya kalli matar yace

“Aff! Kar na yi wani abun ya zama laifi, ki kula da matar nan don Allah, bari naje na sanarwa mai gari tukunna”.

Bai jira tace komai ba ya yi gaba, tsohuwar ta kalli garin babu kowa sai ita sai matar, sai ta mai da hankalinta kan matar wadda ta gama kwanto abinda ke bayanta, wata cute baby ce a cikin towel din wadda ke bacci calmly babu abinda ke damunta, bata kalli fuskar babyn ba bayan ta sakko da ita kawai ta ajiyeta a wajen sannan ta mike, tsohuwar tayi wani yunkuri ta yi baya tana kiran sunan Allah.

Hango jinin da ta yi a kafar matar kuma gashi ta aje jinjiniya a wajen and not minding ga wata halitta na kallanta, bin ta da kallo tsohuwar tayi harta wuce ta gabanta ta yi bakin titi sannan ta mai do da hankalinta kan yashin tana sakin wata gauruwar ajiyar zuciya, yayin da matar ta cigaba da tafiya abinta harta kawo titi, tana kokarin tsallaka titi, daidai lokacin da wata mota kirar taxi tazo wucewa and matar kuma na kokarin wucewa ta tsakiyar titin, me motar yayi iya bakin kokarinsa wajen ganin ya rike steering motar tasa, sai dai ina Allah ya riga ya kadarta, sai da ya yi gaba da matar wadda a lokacin ta fadi ƙasa warwas alamar babu rai a jikinta.

Cikin sauri wannan tsohon mutumin da suke tafe tare da yaron Mai Gari zuwa wajen da abin ya faru, tsohon na gaba yayin da yaron Mai Garin yake biye dashi har suka karaso wajen, basu tsaya ko ina ba sai wajen yashin nan, ganin alamar matar bata nan ya sanya Malam Inuwa (tsohon) ya kalli matarsa Gaje yace cikin rashin fahimta

“Ina matar take ?”

Gaje da tun dazu ta yi mutuwar tsaye, ga zafin ciwo kuma ga tsoratar da tayi sai a lokacin ta iya dagowa ta kalli malam Inuwa sannan ta tattaro wasu kalamai daga bakinta ta ce cikin in’ina

“Ta..tayi nan” ta fada tana nuna musu hanyar data bi ba tare data kalli inda take nuna musu ba, yaron me gari yayi gaba yana kallan inda gaje ta nuna wato hanyar titi, yayi iya duban da zai yi a titin shi dai bai ga kowa ba, sai mutane tsilla tsillah da suke wucewa suma kuma maza ne, tabe baki ya yi yana juyowa ya karaso ya kalli gaje da malam Inuwa ya ce

“Fisabillahi malam Inuwa da girmanku kuna irin wannan abun, yanzu ni gashi an tashe ni daga baccin da nake kokarin komawa ba tare…” Maganar tasa ta katse sanda wani sautin kukan jariri ya karade ilahirin wajen da suke, Sai ya zabura yana juyawa ya kalli inda yake da tabbacin daga nan ne kukan yake fitowa, Gaje ta hadiyi yawu da kyar tana fadin “wallahi matar ce ta ajiyeta, duk yadda aka yi aljana ce, malam kar kaje!!

Ta fada tana kallan malam Inuwa dake karasawa saman yashin, Bismillah malam Inuwa ya yi, yaron mai gari dai na biye dashi a baya yana kallan ikon Allah, malam Inuwa ya kai hannunsa inda yaga towel din da sake yin bismillah sannan ya dauko ta.

“Innalillahi! Innalillahi!” Yaron mai gari ya fada yanayin baya ganin da gaske jinjirin ne a hannun malam Inuwa sai tsandara kuka yake, Malam Inuwa ya kalli jinjirar dake cikin towel wadda a sanadiyar budewar da towel din ya yi yasa ya fahimci ko kaya babu a jikinta, sai ya dauke kai ya kalli gaje yace” kizo mu wuce wajen mai gari”.

Ita dai Gaje ba ta iya sake cewa komai ba, ta bari sai da su malam suka yi gaba sannan ta bisu a baya, bin su kawai take kamar wata doluwa bata cewa komai, motsi kadan sai ta dan leka ta kalli jinjirar da malam ke rike da ita sai ta cigaba da tafiya, shima dai yaron mai gari yana daga gefen malam tambayoyi fall a ransa, a haka har suka karasa gidan Mai Gari.

Yaron Mai Gari ya yi sallama a gidan, uwar gidansa da bata koma bacci ba kasancewar gari ya yi haske sosai tana tsakar gida tana hada wuta ta ji sallamar yaron mai garin, sai ta amsa sallamar tasa tana dorawa da fadin

“Abdullahi lafiya dai ko? Sai da yayi shiru kadan sannan ya ce

“Ehh toh, idan dai babu damuwa don Allah a taso mana Mai Gari”. Mamaki ya kara kasheta amma sai ta bar shi kawai tace

“To bari in masa magana, Allah dai Yasa lafiya” daga haka ta wuce dakin mai garin.

Suna nan tsaye a kofar gidan mai garin wanda wajen ya kasance rufaffe ne samansa. Gaje na gefe har lokacin kirjinta bai bar bugawa ba kawai dai karfin hali take, yayin da malam Inuwa shima har lokacin yake rike da jinjirar, mintuna wajen biyar sai ga Mai Gari ya fito daga cikin gidan nasa yana kallansu su duka, Abdullahi ya zube a wajen yana fadin

“Barka da safiya yallaɓai”.

“Barka ka dai Abdullahi” Mai gari ya fada yana kallan Malam Inuwa fuskarsa fall cike da alamomin tambaya, Malam Inuwa ya matsa suka gaisa cike da ladabi sannan yace, to ranka ya dade wata magana ce mai muhimmanci ta kawo mu, kaga wannan ‘yar? Ya fada yana sauko da ita daga kafadarsa sannan ya dora da yanzun nan mun fito zamu je asibiti, saboda muna so muyi sammako…”

“Kai Abdullahi, shiga ciki ka samo mana tabarma” Mai Gari ya fada yana kallan Abdullahi, Abdullahi ya mike ya shige gidan, can sai gashi ya fito da tabarmar ya shimfida ta anan kofar gidan kasancewar keɓantaccen waje ne, Malam Inuwa ya nemi waje ya zauna bayan Mai gari ya zauna, ita kuma Gaje dama tana gefe tundazu, Bayan Mai Gari ya zauna ya kalli Malam Inuwa ya ce

“Ina jinka” Jin haka ya sanya malam Inuwa dorawa da fadin“.

Ranka ya dade lokacin da muka fito sai naga wata matashiyar yarinya da goyo a bayanta ta hau kan yashin dake kofar gida na, to ranka ya dade kasan sha’anin garin nan, abinda yasa kenan nacewa mai daki na ta jira a wajen ni kuma zan zo in kiraka ko wani wakilinka, to da nazo shi ne na tafi da Abdullahi kasancewar an ce mana shigowarka gidan kenan, sai dai kafin komawarmu har ita yarinyar ta gudu tabar jaririyar, ga mai dakina can ita zata qarasa bayanin” Mai gari dai kallan malam Inuwa kawai yake cike da mamakin zancen nasa, se kuma ya kalli Gaje ya ce

“Bismillah” ya fada yana nuna mata kan tabarmar, a hankali ta karaso ta zauna kan tabarmar kanta a kasa ta fara magana

“Yallaɓai bayan tafiyar malam, ina tsaye ina kallan matar yadda nasan zata iya gani na, dan nasan idan ta ganni zataji tsoro ta fasa aekata abinda tayi niyya, sedae ga mamakina ko gezau batayi ba sanda ta ganni, ta ajiye jaririyar tayi tafiyarta, ranka ya dad’e abinda ya bani tsoro kenan yasa na kasa tsayar da ita dan nayi tunanin ko aljana ce” me gari yaja numfashi kafin yace

“Yah salaam, Allah yasa dai ba rabota aka yi da iyayenta a kazo aka yarda ita ba”

“Wa? Wallahi ranka ya dade wannan data yarda ita itace ta haifeta, zan iya dafa kur’ani akan abinda na gani wallahi, dan kuwa duk da na tsorata hakan bai hanani ganin jinin dake kafarta ba, ba sau daya ba ba sau biyu ba, kuma in dai ba karya na yi ba jinin haihuwa ne, dan da alama sabuwar haihuwa ce, yallabai duk yadda akayi irin masu haifar shegun nan ne suje su jefar dasu kafin kowa ya ankara da hakan shiyasa.”

“Ya isa haka” Mai gari ya dakatar da Gaje daga bayanin da take sannan yakai hannu ya karɓi jinjirar dake cikin towel tayi shiru abinta tana bacci hankali kwance, kyakkyawa da ita fara sol, duk da sabuwar haihuwa ce hakan bai hana dogon hancinta bayyana ba da dan karamin bakinta wanda ta kama kasan lips din nata a cikin bakinta, mai gari ya kalleta cike da tausayawa yana kallan yadda ko kaya ba a saka mata ba haka zalika ga bushasshen jini-jini a jikinta wanda hakan zai alamta maka da ba a dade da haifarta ba, haka kurum yaji tausayin yarinyar ya kama shi, yarinyar da ba taji ba bata gani ba, an haefeta da dattin zina, tunda yasan dae duk d’anda aka haifa na sunnah babu yadda za’ae uwar data haife shi ta yadda shi, sai dai waladiz zina din tunda ba sau daya ba ba sau biyu ba ya saba karɓar irin case din kuma daga baya idan aka yi bincike sai a gano cewa yaron shege ne, sai ya kawar da wadannan tunane tunanen ya juyo ya kallesu su duka yace

“Kuma ba kiga inda matar ta yi ba” Gaje ta girgiza kai

“Wallahi ranka ya dade, rudewa tasa banga inda ta yi ba amma dai tabbas titi ta yi” Mai Gari ya gyada kai yana jinjina al’amarin sannan ya ce

“Shi ke nan zaku iya tafiya, zan saka a bincika min, idan ba’a samu kwakkwaran abinda zamu rika ba to shikenan sai mu kai ta wajen ‘yan sandan cikin gari, duk suka amsa da “To Allah Ya ƙara girma” sannan suka miƙe suka wuce.

Me Gari ya shiga gidansa da sallama, har lokacin uwar gidansa na tsakar gida tana sarrafa musu karin safiya, cike da mamaki ta miƙe daga gaban murhun tana kallan Mai Gari sai dai ta kasa cewa komai, ganin yanayinta ya tabbatawa me gari tana bukatar ƙarin bayani ne dan haka cike da kulawa ya ce

“Ajiye abinda kike yi kizo ki ji” Ai bata koma ko’ina ba tabi bayan Mai Gari daya shige dakinsa ya nemi waje ya zauna, itama ta zauna, kafin tace komai Mai Gari ya yi mata bayanin duk abinda Gaaje ta fada masa, uwar gidan nasa ta girgiza da jin abinda ya fada din, idanunta har sun ciko da kwalla ta karasa ta karbi babyn tana kallanta cike da tausayi ta ce

“Kayya!Allah sarki baiwar Allah babu ruwanta anja mata, Allah Ya kiyaye ta daga gorin asali, yanzu me ye mafita malam ? Mai Gari ya aje numfashi sannan ya ce

“Yanzu dai zan saka ayi mini wasu bincike, idan hakan bai yiwu ba to sai mu mikata police station na cikin gari” Gyada kai ta yi kafin ta ce

“To Allah Yasa hakane mafi alkhairi”.

Bangaren Gaje kuwa asibitin da ba taje ba kenan, ba irin maganar da Malam Inuwa bai yi mata ba akan zuwa asibitin amma ina firr taki ta ce ita ta warke, ta zari jiki da sanyin safiyar nan zuwa gidan kawarta ta labarta mata abin da ya faru, to kun san tsofaffi akwai daukaka abu shi ke nan zance ya fara yaduwa cikin garin, kasancewar karamin gari ne, dadin dadawa kuma ƙauye yasa kafin azahar maganar ta baza lungu da saƙo na cikinsa.

“Wata mata ta yi cikin shege, a ranar data haife shegen taje tayar dashi, yanzu haka abinda ta haife din na gidan Mai Gari” kafin ka ce menene wannan maganar ta zama kamar wani topic of discussion, ko ina ka zaga zancen ake yi, wannan shi ne mafarkin kome.

“Malam lafiya dai ko? Naga ka shigo gida kamar a firgice” wata mata da ba zata wuce 30years ba ta fada tana kallan mijinta, Malam habu ya janyo kujerar dake kusa da ita ‘yar tsuguno ya zauna sannan ya ce

“Wallahi wani zance ne ya dauremin kae habi, kinji zancen dake ta yawo a gari kuwa” Sai ta saki wani miskilin murmushi ta ce

“Aff! Ai nan da kake gani na jiranka nake ka shigo in fada maka abinda na yanke akan maganar”.

“Aww, kin ji ma kenan ? Ya tambaya yana kallanta, Sai ta wani yatsine fuska

“To ban da abinka baban Ilyasu wannan maganar inane bata zaga ba a cikin garin nan, kasan dae halin ‘yan garin nan dae, ya aka ‘kare ma mutum bai yi abu ba ballanta ya yi? Ta karasa maganar cikin sigar tambaya, sai ya gyada kai ya ce

“Eh kuma hakane, yanzu dai fadamin me ya faru ? Gyara zama tayi akan kujerar da take tana kallansa tace,

“Wani hukunci na yanke kuma na san kai ma zai yi maka dadi” bata jira ya bata amsa ba ta cigaba da fadin

“So nake mu karɓo yarinyar da aka tsinta a gidan me gari mu ri’keta” Malam Habu ya wani zabura kamar wanda aka tsikara ya ce

“Kina nufin mu raini shegiya ?

“To ina ruwanmu, Allah Yasa tsinanniya ce ba shegiya ba mu dai in har burin mu zai cika ba shikenan ba ? Ta fada tana watsa masa wani kallo, kallan da kana ganinsa kasan babu mutunci daga wajen wanda yake yi din zuwa wanda ake aikawa

“To fadi in ji menene”.

“Yauwa, ba fa wai mu dauke ta mu rike tane haka kawai ba, a’a ina nufin mu san yadda za mu yi mu tausashi Mai Gari ya bamu ita mu raine ta yanzu, idan ta girma mu za mu more ta, dan kuwa za ta zame mana jari ne”

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×