Skip to content
Part 7 of 50 in the Series Sanadin Kenan by Sumayyah Abdulkadir Takori

Ilyan Goggo da Goggo sun baje kudi a tsakar dakin Goggo suna ta lissafi, Ilya ya ware wasu gefe ya sanya a leda ya mika wa Goggo, “Ajiye wadannan a gefe, kudin makarantar Amina na shekarar karshe, Waec, Neco da Jamb kamar yadda aka ba mu list.”

Goggo ta amsa ta aje a gefe, ita ma ta ware wasu ta mika masa, “Wadannan kuma dubu sittin ga su, ka sayi sabon babur ka dinga amfani da shi, kada ka yi min musu, umarni ne ba shawara ba.”

Ilya ya sanya hannu biyu ya karba, idanunsa suka ciko da kwalla. Abin da zai ci sau uku a rana Goggo ce, suturar da zai sanya ita ce, Allah bai ba shi kwanyar karatu ba, amma Goggo ba ta barshi ya zauna cikin duhun jahilci ba, ta sanya shi dole ya shiga makarantar yaki da jahilci, ga albashi 10% da ta ke ba su duk wata shi da Talatu. Me zai yi ya biya wannan baiwar Allah ban da ya ci gaba da tsaya mata a kan kasuwancinta saboda Allah? Abin da yake fada cikin zuciyarsa ke nan.

Aka yi sallama aka daga labulen falon, Hafiz ne da kayan ma’aikatan MTN masu kalar yellow da baki a jikinsa, da gani daga aiki ya dawo ko gida bai je ba. Goggo da Ilya suka amsa, ya ce, “Inye! Hajiya Goggo da Ilyanta, zakka ake fitarwa ne?”

Goggo ta yi murmushi, Ilya ya ce, “Yaya hafizu ka lallashi Goggo ta yarda a bude mata (account) a banki tunda tana da abin da ya fi karfin abin da ta ke zubawa a dashi duk wata, ni ban ce ta daina dashi ba, amma abin da ya haura abin da aka zuba a dashin a sanya shi a banki.

Karatu Amina ba ta kare ba don ta gama wannan tunda jami’a za ta shiga, kuma likitanci ta ke so, an gaya min kuma ya fi kowanne karatu cin kudi”.

Hafiz ya samu kujera ya zauna, duk da Ilya ya ba shi haushi da ya ce Amina jami’a za ta shiga, ya danne bacin ransa.

“Goggo me ya sa ba kya son ajiya a banki?”

Cikin nutsuwa Goggo ta ce.

“Ba wani abu ba ne Hafizu, abu ne na rai da rayuwa, ka gama wahalarka ka zuba a banki, ka zo ka mutu wani naka bai san da su ba tunda rayuwar ba ta da tabbas”.

Jikin kowannensu ya yi sanyi. Da kyar Hafiz ya ce, “Ba wanda ya san gawar fari, amma mu ga mu, mun san kin yi ajiya a banki.”

“Idan dukkanmu muka fadi muka mutu fa?”

“Insha Allah Goggo ba za mu fadi lokaci daya gabadayanmu ba”.

Ilya ya kyalkyale da dariya, ita ma Goggon Hafiz ya ba ta dariya.

“Ga shawara”. In ji Ilya, “A bude asusun da sunan Amina, tunda komai aka saka na karatunta ne, duk abin da ya kama ta cira da kanta ta biya, mu sakawa ne aikinmu bayan mun ware uwar kudi, na cefanen gida da albashin ma’aikata.”

Goggo ta ce, “Na amince.”

A zuciyar Hafiz ya ce, ‘Wannan yaron Ilya kwakwalwarsa tana ja, da ya yi karatu da an ga kasuwanci’. Bai gama tunaninsa ba Ilya ya kara mamakantar da shi da cewa.

“Goggo za a kara jari fa, dazu mai kula da kantinan cikin asibitin koyarwa (containers) ya yi min magana cewa, mu dinga kai wa kantinan cikin asibiti, an yarda da tsafta da nagartar kayanmu, kasuwa za ta kara fadada da yardar Allah”.

Goggo ta ce, “Duk abin da ka ce Ilya na san wanda zai amfane mu ne, in na dau wannan dashin maimakon a kai banki, to a kara jarin. A bude asusun da abin da ke hannuna yanzu.”

Hafiz da ya ji ba su da niyyar sako zancen Amina ya muskuta ya yi gyaran murya.

“Ni Goggo ba gobe ne Amina za ta zo ba?”

Goggo ta maido hankalinta gare shi, “Eh, haka na ji a radiyo, gobe ne hutun ‘yan makaranta ko?”

“To Goggo ki yi zamanki ni da Ilya mu je mu dauko ta mana?”

Cikin girgiza kai Goggo ta ce,

“Ba za ta yarda ta biyo ka ba”

Shi ma sai ya yi shiru, don ya san gaskiya ta fada masa. Amina ba ta son shi ya sani kamar mala’ikan daukar rai ta ke kallonsa. Ya rasa abin da ya sa zuciyarsa ta kasa hakura da ita. Mata iri-iri binsa suke yana yakice su, amma Amina ce kadai ta samu nasarar tsayawa a kahon zuciyarsa.

Ba irin fada da zagin da mahaifiyarsa ba ta yi masa a kan ya rabu da gidan su Amina, don su suke magance shi yake son Aminar, don su shigo cikin arzikin ubansa da ya yi musu nisa, amma da ta gama zai karkade jikinsa ya tashi, hakan ba ya hana gobe in ya dawo aiki gidan su Aminar zai koma ya ci abincin rana.

Hafiz shi ne Da na farko a wurin kawu Sule da Atika, sai kanwarsa Tasnim, tana sakandire aji hudu da kadan Amina ta girme ta, sai Saifullah da bai wuce shekaru tara ba. Kamar yadda Baban Amina ya ce ne rashin yawan haihuwar na mahaifiyarsu ne, shi da Kawu Sule, su Kawu Bilya da Tasi’u uba suka hada ba uwa ba.

Ranar hutu Amina da kanta ta dawo gida ko hutun baya ma da kanta ta dawo, ta hana Goggo zuwa, ta ce su daina hidimarta haka (she is old enough), wato ta yi girman da za ta dinga daukar wasu (responsibilities) na rayuwarta. Yara suka sauke mata kayanta a tsakar gida ta bude jakarta ta ba su ashirin-ashirin, gidan ban da kamshin suyar kayan dadi ba abin da yake yi, Baba Talatu ce ke suyar Goggo na gefe tana kirgawa a cikin bokitan roba.

“Lale marhabin da ‘yar gidana”. In ji Baba Talatu.

Amina ta sunkuya ta dan rungume ta ta baya, kamin ta isa ga Goggo ta yi mata cikakkiyar runguma. Ta lumshe ido cikin farin cikin samun Goggonta lafiya. Ta sake ta ta dan ja baya ta sanya hannu ta dauki (meatpie) daya cikin daruruwan (meatpie) din da aka soya, ta kai bakinta ta gutsira ta soma taunawa, kunnenta ya yi wani irin motsi har can ciki sai da ta sa hannu ta sosa.

“Goggo mai kayan dadi!”

Goggo ta yi murmushi, “Ya hanya?”

“Hamdullah”. In ji Amina.

Da haka ta wuce daki don ta kimtsa, ta huta. Tunda ta yi sallar la’asar wani irin bacci ya dauke ta, sai yanzu ta san ta tara bacci da gajiya mai yawa a jikinta saboda jarrabawar da suka yi ta wucewa aji shida. Su Goggo suna ta aikinsu, ba su san bacci ta ke ba. Sanda aka kira sallar magriba duk suka mike. Goggo ta shimfida sallaya za ta tada sallah ne ta ankara da Amina da ke can karshen gadon katakonta tana bacci. Ta san baccin wahala ne ya kayar da ita, ba ta taba ganin yaro mai nacin karatu ba irin Amina, hakan ya sa duk sakamakon jarrabawa Amina ba ta wuce na daya ko na biyu.

Ba ta so katse mata baccin ba don da alama tana jin dadinsa. Ta dade tsaye a kanta tana kallonta tana yi mata addu’o’in nasarar rayuwa cikin zuciyarta, miji na gari, wanda shi ne abin da ya fi tsaya wa Goggon a zuciya tun sanda ta lura ta fara al’ada (jinin haila). Daga bisani ta tashe ta, ta yi wata irin doguwar mika da doguwar hamma, sannan ta mike don dauro alwala.

Ko sallar isha ba a idar ba Hafiz ya yi sallama, dukkansu suna tsakar gida kowa kan abin sallarsa daban suna bin jam’in masallacin da ke kusa da su daga nan inda suke. Sai ya karasa gindin famfo ya daura alwala, shi ma ya fita ya nufi masallacin.

Kafin ya dawo Amina ta cika ta yi fam! Tana neman wajen gudu a zuciyarta, Goggo Zulai ta je kauye kamar yadda Goggo ta fada mata, ga ta ita ba gwanar shige-shigen gidan makwabta ba. Ba ta gama tunaninta ba ta ji sallamar Hafiz, ya dawo.

Ya ja kujera ya zauna yana fuskantarta tana zaune a kan sallaya ko kunyar Goggo bai ji ba. Fuskar nan ta Amina ta kirne kamar wadda aka fasa wa danyen kwai a kanta. Goggo ta ce,

“An gama tuwo Hafizu”

“Bar tuwon nan yau Goggo, murnar ganin Amina ba za ta barni in ci ba”.

Ta shige daki ta rabu da su.

Amina ta mike tana kokarin bin bayan Goggo, Hafiz ya ce, “Don Allah, don Annabi Amina ki zauna, na yi miki alkawarin yau zan saurare ki in ji uzurinki da kalaman bakinki, in na gamsu da su, wallahi zan kyale ki, zan fita daga rayuwarki kamar yadda ki ke so’

Jikinta ya yi sanyi sakamakon yadda yake maganar (with a gesture), ya kuma nuna zai aikata abin da ya ce zai aikata din in har ta saurare shi.

Ta sake shimfida sallayar ta koma ta zauna, amma ba ta kallonshi, wani gefen daban ta ke kallo.

Ya dau mintuna biyu bai yi magana ba, ita ma ba ta nuna ta kosa ya yi maganar ba. Daga bisani ya ce,

“Tun ranar da Allah ya sa na fara ganinki duk da na sanki tun kina karama, ranar da na ganki a girmanki, Ubangiji ya jarrabe ni da ciwon sonki, kauna wadda nake fatan ta kai mu ga aure. Ban boye ba na nuna wa iyayena da Goggonki tun a lokacin. Amma minti guda ba ki taba ba ni don mu fahimci juna ba, duk da an ce labarin zuciya a tambayi fuska na fuskanci ba ki sona, kin tsane ni, ko me ya sa Amina?”

Amina ta hadiyi miyau, yau kam ta yanke shawarar ta bude baki ta magantu ko Hafiz ya shafa mata lafiya.

“Ni wallahi ban tsane ka ba”

Kamar daga sama Hafiz ya ji ta fada. Kamin ya farfado daga dadin da kalaman suka yi masa Amina ta ci gaba.

“Duk kusancina da mutum, duk kaunar da nake masa, in ya ce yana sona sai in ji duk duniya babu wanda na tsana irinsa. Kai dan uwana ne na jini, dole akwai kauna ta ‘yan uwantaka, da za ka janye kalaman soyayya ko aure a tsakaninmu, lafiya za mu zauna”

Abin ya kusa bai wa Hafiz dariya, wato wannan so na aure da yake furtawa shi ne ba ta so ba shi ba. To ban da abin Amina me ye amfanin zumuncin mace da namiji in ba soyayya ce a ciki ba?

Ya tattara kalamansa ya dunkule su cikin hikima, “Amina, me ya sa ba kya so a ce ana sonki?”

Kai tsaye ta amsa, “Saboda in Goggo ta samu tsayayye kwakkwara, aure za ta yi min, ba za ta bar ni in gama karatun da nake so in yi ba”

Hafiz ya girgiza kai, ya kuma fahimce ta, “To ke kuwa Amina wane irin karatu ne wannan da zai hana ki aure?”

Amina ba ta ce komai ba, don a ganinta wannan ba huruminsa ba ne.

Da bai samu waccan amsar ba, sai ya karo wata, “In na jiraki ki ka gama karatun da ki ke so ki yi din, a kalla nan da shekaru goma, in kin kare za ki yarda ki aure ni ko da a mata ta biyu ne?”

Amina ta mirgina kai, “Ban yi alkawari ba, saboda Allah shi Ya san gobe. Za dai ka shiga cikin manema in akwai su”

Hafiz ya rasa ta inda zai billo mata, yarinya na magana da cikakkiyar kwakwalwa kamar ta girme shi. Gara ya sanya wa ransa salama a kan Amina.

*****

Tun daga wannan ranar Goggo ta lura Hafiz ya dauke sawunsa daga gidanta. Ta sa Amina a gaba da fada kamar ta ari baki, ta tambaye ta ta gaya mata abin da ta yi masa, Amina ta ce, ita kawai ce masa ta yi ba yanzu za ta yi aure ba. Sai Goggo ta koma lallashi da nasiha, tana nuna mata ta daina wulakanta masu kaunarta, ta bi rayuwa a hankali, ta cire dogon buri.

Duk da Hafiz ya hakura da Amina bai fasa zuwa jefi-jefi ya gaida Goggo ba, lokacin Amina ta koma makaranta. A gefe mahaifiyarsa na ta yin nata kokarin wajen malamanta don a yi masa firraqu da Amina. Sanda Hafiz ya gaya mata ya hakura da Amina ta samo masa mata, don shi ba shi da idon kallon kowacce mace a duniya ba Amina ba, ta wani bangaren kuma ya matsu da ya yi auren ne a wannan dan tsukin ko ya samu nutsuwa ya fidda Amina a ransa.

Atika sai ta yarda kokarinta ne ya raba su, ta kara yarda da malamanta, ta kuma kara musu ihsani. Ta soma yi masa fafutukar auren ‘yar kawarta mai suna Siyama, wadda ta fito daga gidan da ya gamsar da ita, ba wadanda za su zame musu (liability) ba.

Lokaci ba ya jiran dan Adam, haka yake ta mirginawa cikin kudura da iradar Ubangiji. A yau Amina ta gama dukkan jarrabawoyinta na fita sakandire. Amina da Goggonta Hauwa sun yi godiya ga Allah da Ya nuna musu wannan ranar. Sun rabu ita da Hafsa kowa na sharar hawaye da alkawarin ziyartar juna in Mai duka ya yarda. Amina ta yi wa Hafsa alkawarin zuwa bikinta har Abuja idan Goggo ta amince, domin ba zai dauki lokaci ba, ita ake jira ta kare karatun nata, ga shi kuma an gama cikin yardar Ubangiji.

Amina sai zaman gida don jiran fitowar sakamako. Ta yi kace-kace cikin taimaka wa sana’ar Goggonta, duk karfin ayyukan ita ce don Allah bai halicce ta da kuiya ba.

Sun je ita da Ilya sun bude asusu da sunan Amina da bankin (firstbank), aka ci gaba da zuba ribar kasuwancin Goggo a ciki.

Bookmark
ClosePlease login

No account yet? Register

Rate the story.

Average: 4.2 / 5. Rating: 6

As you found it interesting...

Follow us to see more!

<< Sanadin Kenan 6Sanadin Kenan 8 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
3
Free daily stories remaining!
×