Skip to content
Part 1 of 50 in the Series Sanadin Kenan by Sumayyah Abdulkadir Takori

Sadaukarwa

Littafin ‘Sanadin Kenan’ sadaukarwa ne ga duk makaranta littattafan Takori, wadanda na sani da wadanda bansani ba. Ina son ku, ina alfahari daku. Allah ya kara zumunci.

Don Tunawa Da

Domin tunawa dake marigayiya Kakata kuma Goggo na HAJ. HAWWA ABUBAKAR WALI.

Gargadi            

Ba’a yarda a karanta ko a rubuta littafin nan a kowacce kafar sadarwa ba, gidan radio da sauransu ba tareda izinin marubuciyar sa ba. Yin hakan zai jawo gurfana a karkashin shari’a insha Allahu.

Tunasarwa

Littafin SANADIN KENAN! Kirkirarren labari ne don fadakarwa da nishandantar da mai karatukamar sauran littattafan TAKORI. Bashi da nasaba dani ko wani nawa ta kowacce fuska, SANADIN KENAN! Kirkirarren labari ne don haka a kiyaye.  

Jinjina

Littafin SANADIN KENAN! Ya jinjina miki AUNTY ZULAIHA ZUBAIR (Mrs late Tafidan Kano Hakimin Kura,  SANADIN KENAN! Ya jinjina miki saboda gudummuwarki gareshi. Aunty Zulaiha Madallah Allah ya kara lafiya da nisan kwana.

Shimfidar Labarin

Yayi missing flight dinsa ne mai zuwa Abuja ba da son ransa ba.

Ashe da rabon zai ga bacin ran da bai taba shiga kwatankwacin sa ba.

Ta danna madannin kararrawar dake jikin bango ta kiran ma’aikatan gidan, nan da nan mutum biyu suka zo, samari ne guda biyu masu share-share da goge-gogen gidan, ba wanda bai wuce shekaru ashirin a cikinsu ba.

“Ku dauketa ku kaita ‘toilet’ kuyi mata wanka, ku cire mata ‘pampers’ dinnan tun dakin bai soma wari ba.”

Matasan biyu suka dubi juna kamar masu yin shawara, ta galla musu harara “ko bazaku yi bane?” Da sauri suka ciccibo yarinyar, daya ya riko kai daya ya riko kafafunta sukayi bandaki da ita, suka tube ta suka cire ‘pampers’ zasu soma wanke ta.

Kamar wanda aka jefo ya shigo babu zato babu tsammani. Yana so ya gaya mata jirgin ya tashi ya barshi sakamakon wasu muhimman baki da yayi suka tsaida shi. Saidai ya jira na yamma insha Allah.

Idonsa bai sauka akan komai ba sai kartin maza kabilu rike da Amina sun tube ta, idanunsa suka kada sukayi jawur, zuciyarsa ta rika wani irin tafarfasa, hakan bai sa yayi magana cikin fada ko bacin rai ba, a sanyaye ya zuba mata ido na ‘yan dakiku  kafin ya soma magana.

“Maza balagaggu kika sa suka tsiraita ‘ya ta haka? ‘Yar tawa kwalli daya Lailah?? Ban yi zaton ko auren kiyayya kika yi dani ba Lailah bazaki iya taimakawa mara lafiya marainiya ba!

Kina nufin su sanya hannu a (private part) din diya ta? Ban taba dukan mace ba, bana fata in fara a kanki, kije duniya ce, kuma in gaya miki wannan yarinyar ta fi mun duk abinda na mallaka da rayuwar baki dayanta. Kisa a ranki kema mace ce, kuma zaki haifa, baki san yaya kaddara zatayi da abinda kika haifa ba kina raye ko bakya raye”.

Kallo daya ya yiwa ma’aikatan suka  saki ‘pampers’ din da suke cirewa suka yi waje. Cike da addu’a a zukatansu, kada Allah yasa wannan ya zamo sanadin hanyar abincinsu. Suma sun ji umarnin da aikin da aka sanya sun ‘odd’ to amma meye laifinsu? Salin-Alin suka fice.

Da sauri ya wanke Amina da kansa yayi mata wanka da soso da sabulu mai kamshi, ya nado ta cikin shawul ya fito da ita. Ya shafe ta da vaseline ya sanya mata sabuwar ‘pampers’ da sababbin riga da siket masu kyau. Sannan yayi waya kicin a kawo masa ‘tea’ da ‘pancake.’

Da kansa ya rinka baiwa Amina a baki wani na shiga wani na dawowa yana goge mata har ta koshi ta ture. Jiki ba kwari Laila ta wuce don ganin yadda yayi kamar babu ita a dakin. Bata taba tsammanin zai dawo a yau ba sai bayan kwana uku kamar yadda ya ce. Ta kulla a zuciyar ta ko ‘cangal’ bazata yiwa yarinyar ba har ya dawo.

Maganganun da ya gaya mata ba su ta zata ba, tafi zaton dan banzan duka daga gareshi yadda ta lura yana son yarinyar tasa. Kafafunta ba kwari ta nufi dakinta.

Ya sumbaci Amina a goshinta ya mayar da ita ya kwantar ya gyara mata pillow, ya fito falo ya jibgu a kujera mai tsananin taushi. Ya kai hannun damansa ya dafe kzźansa dake tsananin sarawa. Ji yake dan son da ya fara yiwa Lailar na ‘decreasing gradually……..(raguwa a hankali). Zufa ta shiga karyo masa, da ya tuna kalami na karshe na uwar Amina…..

“Ka kara kula da Amina, ba don na raina kulawarka gareta ba, she will need extra more…”

Yess! Tana bukatar karin kulawa, kuma zata samu insha Allah in har ina raye kuma kudi suna da amfani zata samu kulawa. Da gaske kula da ‘ya mace sai mace. Na lura matar nan son kashe min Amina tayi ko abinci bata bata ba har karfe biyu na rana. Kuma tasa maza su tozarta ta ba don Allah ya dawo dani ba.

Ya san muddin ya gayawa Hajiyarsa wannan abun cewa zatayi zata dawo ta kula da jikarta. Bayan yanzu ta fara samun nutsuwa a gidan mijinta da nata koshin lafiyan, hankalinta ya tsaya waje guda. Zaiyi ‘finding solution (nemo mafita) da kansa.

Babu wanda ya fado masa a rai sai tsohon abokinsa Dr. Usman Turaki. Consultant a asibitin koyarwa na Tafawa Balewa teaching hospital.

Tare sukayi sakandire, sun shaqu sosai a wancan lokacin, yanayin karatu a gaba ya raba su, kowa da jami’ar da ya wuce da fannin da ya zaba.

A take ya zakulo lambar Dr. Turaki,  ta jima tana kara kafin matarsa ta daga. Abinda tace shine “Doctor is on call. A gida ya bar wayarsa” “ok. Please da ya dawo kice ya kira ni da wannan no.din. Ma’arouf Ji-qas ne”.  “Insha Allah zan gaya masa”

“nagode agaida yara”

“zasu ji. Allah ya tashi kafadun Amina”.

Ji yayi kamar ta yi masa addu’ar Allah ya sanya shi a aljannah. Wato komai na dan siyasa baya buya. Kamar kasawa ake a faranti ana terere da shi. Kowa yasan yana da ‘ya mara lafiya.

Dr. Turaki na komawa gida matarsa Zainab ta isar masa da sakon abokin nasa, ko abinci ta kasa bari ya ci. Balle ta barshi yayi wanka, amma tayi kokari ainun wajen boye azarbabinta da murnarta na yau ta yi magana da Ji-qas. Tauraron taurari a wurin al’ummar Bauchin Yakubu.

“Zan kirashi gobe dana shiga ‘office’

“Haba kai kuwa Baban Aadil, ka kirashi yanzu mana muji menene? Ka sani ko kujerar Makkah  ce?” Dr. Turaki ya tuntsire da dariya,

“Zainab mai idon cin naira, ki bari Allah ya bashi kujerar Bauchin, Makkah kinje kin dawo insha Allahu.”

Ita dai Zainab ba haka ta so ba, ta so ya kirashi tana zaune taji kwaf!  Ko samu ne.

Kamar yadda ya cewa matarsa, yana shiga ofis washegari ya bude tagogi Ji-qas din ya fara kira.

A lokacin yana baiwa Amina ‘golden morn’ ya dakatar ya daga kiran Turakin.

“Sai yanzu kaga damar kira na?” “Afuwan Yaa Maulaaya, lokutan likita a kididdige  suke” yayi murmushi, ba raha ya kira shi suyi ba kamar da, da ya bashi amsa don haka kai tsaye ya zarce da gaya masa makasudin kiran.

“Akan ‘yar ka Amina ne. Mun bar gadon asibiti don dukkannin mu ba zamu iya ba ni da Hajiya, saboda wasu muhimman uzurirrika musamman ni da yanayin rayuwata ba na tsuguno bane a wuri guda. Sai na tsaya nayi tunani akan abinda yafi kawai inyi ‘hiring professional’.

Ina son hayar (physiotherapist) da zata cigaba da baiwa Amina (treatment) a gida da kula da komai nata bilhaqqi, zata bar aikinta na asibiti ta zauna da Amina a gida ta cigaba da kula da ita tsahon shekara daya mu ga abinda Allah zai yi.

Zan ninka mata albashin data ke karba a asibiti sau hudu a kowanne karshen wata.

Saidai Turaki ba kowacce ba, shi yasa ma na biyo ta kan ka ban bi ta kan likitocin Amina ba. Ina son wadda akwai sanayya ta sosai a tsakaninku, ka yarda da ita, ka yarda da tarbiyya da amanar ta. Mata tsoro suke bani Turaki. In kana da kudin da zaka basu babu mai zama da kai tsakani da Allah. Yau na firgita na tsorata da al’amarin mata yadda baka zato.  Sun karya min zuciya sun kara sa ni kewar Mahaifiyar Amina. Mata irin ta tsiraru ne a cikin al’umma.”

Dr. Usman ya ja numfashi, babu wadda ta zo masa a rai sai likitar da ya raina da hannunsa, ya kwashe shekaru bakwai zuwa takwas tare da ita, ya lakanci dukkan halayen ta; Dr. Amina Mas’ud  Shira!

Dukkan  suffofin da Ma’arouf ke so (proffessional) din ta kasance dasu Amina ce ta mallake su. A dai likitocin wannan bangaren nasu (physiotherapy) da ya sani a duniya.

“AMINA MAS’UD SHIRA!”

Ya furta da sauti mai dan kauri  (husky) kuma a hankali, kamar a zuciyarsa ya fada,  Ma’arouf din ma bai ji sosai ba.

“wacece haka?”

Suna ne na likiciyar data dace da komai daka ambata ne. Dalibata ce, ni na raine ta, physiotherapist ce”.

“Ka yarda ta hada duk abubuwan dana lissafa a sama?” “har ma ta zarta. Proffessional ce data san kan aikinta at a very young age. 

Bayan lakantar aikinta harda baiwa cikin al’amarin ta. Ta karbi ‘award’ shekarar baya na ‘Best Physiotherapist in Africa’. Sannan ‘yar babban gida ce, by saying this, ba ina nufin gida na masu kudi ba a’ah, gidan tarbiyya da mutunci. Ka fahimce ni? ”.

“Na fahimta. Ka yi mata magana toh. Cewa zan dauketa kwangila na tsawon shekara daya in bata da aure. Ta kula min da mai sunanta paralysed diya ta. Zan ninka mata albashin ta sau hudu in ta amince. Duk karshen mako sai ta tafi gida, nikuma zan maida kwana biyun lokutan zamana da Amina in cigaba da kula da ita har ta dawo….” “…….excuse me please….” Turaki ya katse shi da wani irin tune mai kama da tun zura a muryar sa, “meye amfanin matarka idan har bazata iya kula da abinda ka haifa ba ko da na kwana biyu a sati?”

Murmushi yayi, zuciyar sa ta hasko masa yadda karti biyu suka tube Amina a bandaki a bisa umarnin Laila, tana gefe toshe da hanci, idanunsa suka wani irin rine sukayi jajawur  da kyar ya bashi amsa.

“Ban aureta don in sa ta jinya ba. Yaushe zaka yi magana da likitar?

“lallai” Inji Dr. Turaki. Ya san zurfin cikin Ma’arouf din bazai barshi ya zurfafa zancen ba, haka Allah ya halicce shi, amma jikinsa ya bashi akwai wata a kasa. Ya kyale zancen shima ya bashi amsa.

“insha Allahu gobe. Yau tana off. Sannan sai ka dan tsahirta ta rubuta (leave without pay) that’s in har ta amince kenan. Zanyi kokari a bata  (leave) din don ba kowa ake baiwa ba. In kuma bata amince ba sai mu nemi wata….” “no please. Ita kadai na aminta da. Idan bata amince ba I will find another solution”. “Jikina yana bani zata amince saboda tana ganin girma na kuma bata yi auren fari ba”.

Da wannan suka kawo karshen tattaunawar tasu.

Bookmark
ClosePlease login

No account yet? Register

Rate the story.

Average: 4.2 / 5. Rating: 46

As you found it interesting...

Follow us to see more!

Sanadin Kenan 2 >>

17 thoughts on “Sanadin Kenan 1”

  1. Masha Allah aunty sumayya a kullun a dauki takardar ki sabbin abubuwa ne zakaci karo dashi salon da ban ne da alamar labarin Amina da Dr ta ga carrying uba jikas da matar uba wacce narasa da sunan da zan kirata allah yakara jagora

  2. Masha Allah anty sumaiyyah Allah ya kara basira da kwarin ido dukkan rubutunki bnida haufi akanso akwai darasi ga nishadi ga uwa uba muhimancin zumunci Allah ya kara lfy

  3. Ah lallai laila bata da kirki, yarinya mara lfy marainiyar Allah. Allah Ya sa amina ta yarda. Masha Allah anty sumy Allah Ya qara basira, ban taba karantawa ba kuma tun daga page one nacsan novel dinnan yayi iya yi gsky

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
3
Free daily stories remaining!
×