Skip to content
Part 11 of 50 in the Series Sanadin Kenan by Sumayyah Abdulkadir Takori

Sun kulle sun dunkule sun zama abu daya, abokan sirrin juna, masoyan juna, kuma ‘yan uwan juna, kasancewar dukkaninsu ba su da wanda za su kira dan uwansu na jini, sai junansu.

Aisha na shara a tsakar gida wani yaro ya shigo, “Wai ana neman maigidan”.

Ba tare da ta juyo ba ta ce, “Ya tafi wajen aiki, sai karfe daya da rabi zai dawo.”

Yaro ya fita, can kuma ya dawo da ambulan mai fadi a hannunsa,

“Wai ga shi a ajiye masa, sako ne daga ‘post-office’. Aisha ta ce, “Toh”

Ta karba ta kai daki ta ajiye a kan talabijin dinta ta fito ta ci gaba da ayyukanta.

Da ya dawo ba ta ba shi takardar ba, sai da ya gama komai na al’adar rayuwarsa, ta dade da kashe fita kofar gida karatun jarida don a cewarta da haka zai kallo wata tunda kallon masu wucewa yake ba karatun jarida ba. Ya  kan ce,

“Ki yi abin da ki ke so dole a bi, ko ana so ko ba a so.”

Tare suke hirarsu na abubuwan da suka shafe su, ko al’ummah. Inna Luba ta dade da shafa mata lafiya.

“Au! Ka gani na manta, dazu aka kawo maka wai daga post-office.”

Ya karba yana juya ambulan din mai dauke da tambarin kamfanin ‘Lange&Grant’, ya ciro ya bude yana karantawa.

Bai san sanda ya mike tsaye ba,

“Aisha, alheri zai same mu, kirana ake yi intabiyu. Na dade da neman aikin wajen shekara guda ke nan. Sai dai ga bikin zuwa babu zanin daurawa”

Ta ce, “Kamar ya ya?”

“Eh, toh!. Sai na je Lagos. Ga shi babu kudin mota. Wata ya zo karshe, kuma gobe-gobe ake so in shiga Lagos jibi in shiga intabiyu din”.

Aisha ta mike ta shiga dakinta, ta jawo abu daga kasan gadonta. Sai ganinta ya yi ta fito da bankin kasa, ta tika shi da kasa, sai ga kudi fululu.

Da mamaki yake kallonta, “Wannan fa?”

“Naka ne”.

“Kamar ya ya nawa?”

“To an ce da kai haka ake ba wa iyali kudin cefane kamar ma’aikata? Ko an ce maka maigida ba zai dinga adana komai ba a kudin cefane yake karewa? Ko kuwa mu hudu ka ajiye da ka ke ba ni tsabar kudin da ka ke ba ni kullum? Karbi ka shirya ka tafi”.

Shi dai ya kasa magana, sai binta yake da kallon kauna.

“Ba zan karba ba sai kin yarda rance za ki ba ni”.

Da ta ga zai bata mata lokaci wajen ja-in-ja, ta ce, “Na yarda”

Sannan ne ya soma kirga kudin. Za su kai shi har karshen Nigeria su dawo da shi Bauchi lafiya.

A daren ta hada masa kayan da zai bukata, sun shirya da asuba zai fita. Ya yi sallama da Baba tun a daren ranar ya ce suna fitowa daga masallaci zai nufi tasha. Baba ya yi masa addu’a sosai.

Ya gamu da wahalhalu irin na matafiyi, har Allah ya kai shi garin Ikko lafiya.

Ofishin Lange&Grant na nan a 53 Akanbi Onitiri, Eric Moore Road a Surulere cikin jihar Lagos. Bai sha wuya ba ya riski kamfanin kasancewar yana da adireshin a rubuce.

Su suka ba shi masauki, washegari suka yi masa intabiyu da (screening) din takardunsa. A take suka dauke shi cikin manyan ma’aikatansu, saboda kyawun takardunsa.

Sun ba shi sati daya ya koma gida ya shirya ya dawo ya shiga office.

LANGE AND GRANT kamfani ne mai zaman kansa da ke karbar kwangilar gine-gine construction company na abubuwa da dama, sannan suna daukar nauyin ma’aikatansu da tura su kwasa-kwasai kasashen da suka ci gaba, babban ofishinsu yana nan a jihar Lagos. Samuwar aikin nan ga Ma’arouf ba karamar sa’a ba ce a gare shi, da duk wani mai kaunarsa.

Ya dawo gida cike da farin ciki, ya sunkuci Aisharsa yana juyi da ita a tsakar daki.

“You are a blessing Aisha. Tunda na aure ki nake cin karo da farin ciki iri-iri, da ci gaba ta kowane fanni. I really love you. Pack our belongies (harhada mana kayayyakinmu). Mun zama ‘yan Lange&Grant.”

Murmushi kawai Aisha ta ke yi. Ita ba za ta iya gaya masa adadin kaunar da ta ke masa ba, kuma ba za ta gaya masa kullum ta yi sallah addu’ar ci gaban rayuwa da gamawa da duniya lafiya ta ke masa ba.

Baba ma ya yi farin ciki. Ya sa Aisha ta shirya ta je ta yi wa mahaifinta sallama. Har matan baban ta gaisar ta yi musu sallama, ta gaya musu za su koma jihar Lagos da zama. Ba wadda ta damu da me ta ke ciki, don haka suka bi ta da ‘a dawo lafiya.’

Tare da Baba suka tafi Lagos ya je ya gano muhallinsu. Madaidaicin gida mai dakuna uku da falo. Komai na bukatar rayuwa akwai shi a gidan daidai bukatar kowanne dan Adam.

*****

Shi kansa shugaban ‘Lange & Grant’, Mr. Timothy Emmanuel na mamakin (talent) irin na Ma’arouf, kullum cikin kawo musu sababbin ‘discoveries’ da ‘ideas’ yake. Tunda ya zo bangarensa na ginin titunan mota da jiragen kasa kara inganta yake, sai samun abokan ciniki suke. Ma’arouf ne ya sa suka yi kokarin da suka soma karbar kwangila daga (Federal Government), hakan ba abu ne mai sauki a gare su ba a da (before), amma da zuwan Ma’arouf sai ya maida shi mai saukin. Suka soma samun kwangila daga gwamnatin tarayya.

Cikin shekaru biyu da shigowar Ma’arouf kamfanin, ya samu ci gaba a dukkan bangarorinsa, don haka shi ma ogansu Mr. Timothy ya kara masa promotion, da daraktansu ya yi (retire) ya dora ma’arouf a kujerarsa. Ya zamo daya daga cikin (board of directors) na kamfanin, da tafiya ta yi gaba ya zama mataimakin Mr. Timothy.

Abin da ke bai wa Mr. Timothy mamaki da Ma’arouf ya ki zuwa kowanne (course) da suke tura shi Amurka, bai yi shiru ba, kuma ya yi masa bayani, ra’ayinsa ne, tsarin rayuwar da ya yi wa kansa ne ba shi ba fita waje. Shi ma sai ya kyale shi, sai dai ya ga abokan aikinsa na fita, su kuma hakan na musu dadi. Saboda suna kishin daukakar da ogan ke masa a kansu, shi da ya zo a bayan-bayansu, amma har ya isa kololuwa.

Zuwa wannan lokacin duk wani rufin asirin rayuwa da dan Adam mai ilimi ke nema, Ma’arouf Habibu Ji-qas ya same shi. Falla-fallan motocin hawa har guda biyu, ya gina (smart mansion) dinsa a Fati Mu’azu Links cikin Bauchi, ya bige gidansu ya yi wa Baba ginin da ya ja hankali a unguwarsu, ya doke na Baban Aisha.

A kauyen Ji-qas ya yi wa mahaifiyarsa da mijinta gida na gani a fada, wanda duk kauyen babu kamarsa. Haka yake dauko ta ya kawo ta Lagos ta yi kwanaki ta huta tare da Aisha. Suna son juna ita da Aisha suna girmama juna, suna kiyaye mutuncin juna.

A cikin wadannan shekaru Aisha ta goge, ta waye, ta zama cikin wayayyun matan Arewa a Lagos. A Lekki suke da zama. Ta shiga (Unilag) ta yi digirinta a kan (Accountancy) ta yi hidimar kasa a nan Lag ta adana takardunta a karkashin gado don Ma’arouf bai yarda da aiki ba, ko da ya barta ita ba ta da ra’ayi, burinta kullum ta kula da Ma’arouf ta janye idanunsa daga sauran mata masu auren maza don abin hannunsu.

Sai kuma ta yi sa’a shi Ma’arouf din akan karan-kansa ba mai ra’ayin aure-aure ba ne. Sannan iyayensa a tsaye suke a kansa wajen yi masa addu’a da ba shi (azkar) iri-iri yana yi duk inda zai shiga.

To da ma Ubangiji ba ya barinka haka ba tare da ya jarrabe ka ta wani bangaren ba. Hakan ce ta faru da Ma’arouf da Aisha, ko batan wata Aisha ba ta kara yi ba, tun wannan barin data yi a cikin jirgi, haihuwa sun neme ta sama ko kasa Allah bai ba su ba. Shekara biyar ke nan da aure.

Tebirin likitoci iri-iri a Lagos da Abuja babu inda ba su tsugunna ba. Duk amsar daya ce, dukkaninku lafiyarku kalau, Allah ne bai nufa ba. In suna da damuwa a rayuwarsu, to wannan ce. Har taimakon magungunan Hausa Hajiyan Ji-qas ke kawo wa Aisha, amma shiru, kamar an aiki bawa garinsu.

Mr. Timothy wanda da zuciya daya yake kaunar Ma’arouf ya zauna yake tunani, shi ga shi shekaru sun tura, ya san kuma yadda dukkan ma’aikatansa ke kishi da Ma’arouf, idan ya yi (retire) ko ya mutu yanzu Ma’arouf zai ga ba daidai ba a ‘Lange & Grant’ ga yaron ya taimaka masa ya tara dukiyar da shi kansa bai san iyakarta ba cikin shekaru biyar kacal, kuma an ce dadewa a bauta ‘yanci ne, ya kamata ya taimaka masa ya tsaya da kafafunsa.

Don haka ya wari wani kaso na dukiyarsa ya tura ‘account’ din Ma’arouf, abin da ya firgita Ma’arouf ya zo ganinsa har gida afujajan.

Sun kulle kansu a dakin ganawa da bakinsa na musamman, a nan Mr. Timothy ke yi masa bayanin kudurinsa a kansa. Cewa daga yau ya bar ‘Lange & Grant’ ya zama (contractor) mai zaman kansa, zai buda masa hanyoyin karbar kwangilar gine-gine daga kwastomominsa. Wannan godiya ce a gare shi na wahalta masa da ya yi da zuciya daya har kamfaninsa ya kai matsayin da ya ke da shi a yanzu.

Ba shi da abin cewa sai godiya, don ya san halin ogan nasa, ba ya niyyar yin abu ya fasa, amma da ya ce masa zamansa karkashinsa ya fiye masa dadi, kuma (remuneration) din da yake samu a karkashinsa ya ishe shi. He is contented with his life as such… Amma an ce ba a maida hannun kyauta baya. Kuma a yadda ya san abin da Ogan nasa ya mallaka, wannan ba wani ‘big deal’ ba ne a wajensa (babban abu).

Don haka ya dauko Baba da Hajiyan Ji-qas da Alhaji Mansur (surukinsa) suka zo har Lagos suka je suka yi wa Mr. Timothy godiya. Sai ya hau Ma’arouf da fada, (how dare…) ya kwaso dattijai haka ya ba su wahala. Ba zai kira shi a waya su yi maganar ba (a lokacin waya ta shigo, amma rike ta sai wane da wane).

Shi ma ya sayar da duk kadarorinsa, filaye da gonaki biyu da ya saya a Bauchi, ya hada da ‘capital’ din da ubangidansa ya ba shi, ya gina kamfanin kwangilar gine-gine mai zaman kansa, kuma da yake ya san kan harkar, idonsa ya riga ya bude da ita. This is the beginning…

Da wannan ‘JI-QAS CONSTRUCTION COMPANY LTD’ ya kafu, mai hedikwata a Abuja da Lagos. Ya dauki karantattun ma’aikata ya zuba, suka soma karbar kwangilar gina wani (oil-refinery) a jihar Ondo, daga gwamnatin tarayya, da abin ya yi gaba ya dawo gida Bauchi yana karba daga gwamnatin jiha, makarantun firamare ne, gadoji ne, tituna ne, gyaran Dams, hydro-electric power, da sauransu. Allah kuma ya sanya albarka a ciki.

Ma’arouf in ya zauna yana tunani a kan kansa, yana kididdiga arzikin da ya samu cikin dan lokaci kalilan, sai ya ga ya kamata ya soma wani tallafi ga matasan jihar Bauchi, wadanda ke zaman banza, da wadanda ke da zuciyar neman ilimi babu damar yi, wadanda suka yi karatu babu aikin yi, da ilimin yara kanana a jiharsa Bauchi ganin yadda gwamnati ta yi wasarere da su saboda abin ya yi mata yawa ita kanta gwamnatin, hakkin masu hannu da shuni ne su sanya hannu a gudu tare don ci gaban al’umma, amma fa masu zuciyar taimakon kadai.

    Ya fiddo da wani tsari na gina matasa mai suna (Ma’arouf Foundation), ya sa aka rika cigiyar matasa a kafofin yada sadarwa masu matsalolin can da ya ambata a baya.

    Matasan Bauchi da iyayen yara talakawa suka amsa kiransa da gaggawa, ya dora ma’aikata masu amana, aka soma yi wa matasan maganin matsalolinsu daga cibiyar MA’AROUF FOUNDATION. Ya gina katuwar makarantar firamare ta kyauta, wadda gwamnati ta san da zamanta.

    Allah kadai ya san adadin matasan da suka samu kwalin digiri daga aljihun Ma’arouf a jihar Bauchi. Su gama ya yi musu hanyar samun aiki daga gwamnati ko (private sectors), ilmin firamare mai kyau (free) ga kananan yara, masu zaman banza an sanya su (6-week orientation) sun koyi sana’o’i ana ba su wadataccen jari. Sai a hankali sunan Ji-qas ya fita a Bauchi har ake masa kallon wani babban dan siyasa ne. Har zuwa yanzu (foundation) din na ci gaba da gudana.

    Wannan ne ya janyo ra’ayin matasan Bauchi na son ya tsaya musu takarar gwamna na kara yaduwa. Sun yi gangami sun bayyana masa ra’ayinsu na son ya shiga siyasar ya taimaka wa jiharsa, su kuma za su tsaya wajen yi masa kamfen babu ko sisinsa. A lokutta da dama hakan ta faru babu wanda ya samu gamsasshiyar amsa daga bakinsa.

    Daga baya jama’ar suka bi ta kan surukinsa wanda an san ba ya ketare shawarwarinsa a gare shi. Sun zauna ya yi masa nasiha, cewa ya rungumi alherin da mutane suke so da shi, ya tsaya takarar ya barsu da kokarin komai na Allah ne. Mahaifinsa kuwa addu’ar da ba ya fasa yi masa kullum ita ya yi masa, yana fadin, “Allah ya yi jagora, Allah ya zaba mafi alkhairi”.

    Hajiyan Ji-kas, kusan ra’ayinsu daya da Baba, cewa ta yi idan siyasar alkhairi ce Allah ya yi riko da hannunka”.

    Aisha ce kadai ba ta son zancen siyasar nan. A cewarta yanzu haka sai in dau lokaci ban sa ka a idanuna ba, kana nan kana can, ina kuma ga ka shiga siyasa? Ina kuma ga ka zama gwamna?”

    Ita ma ba ya ba ta amsa, murmushi kawai yake yi.

    Yau da gobe ba ta bar komai ba, kwadaita masa siyasar da kowa ke yi da goyon bayan da ya samu daga sama da kasa ya sa ya amince, ya shiga siyasa karkashin jam’iyyar (NPC) wato ‘Northern People Congress’. Bai tsaya takarar gwamna ba, ta dan majalisa ya tsaya mai wakiltar Bauchi ta Kudu don ya kara bude ido da yadda al’amuran siyasa ke tafiya.

    Ai kuwa da gudu ya haye, suka koma Abuja shi da iyalinsa. Su Baba kan je, Hajiyan Ji-kas kan je ta yi hutu duk sanda ta so, su ma kuma suna zuwa ganinsu akai-akai.

    Ashe da kafar dama suka fada siyasar, domin a shekarar ne ciki ya billo a jikin Aisha. Murna da godiyar Allah gurin ma’auratan da iyayensu da duk wani mai kaunarsu abin ba a cewa komai. Sai shukrah ga Lillahi.

12

Aisha ta sauka lafiya a ‘National Hospital’ ta samu ‘yarta mace, santaleliya mai kama da ubanta a komai. Ranar suna Baba ya sanya mata suna Amina. A cewarsa babu sunan da ya kai wannan albarka (Aminatu mamar Manzo) haka yake kiranta.

Amina ta taso cikin gata da soyayyar iyaye da kakanni. Hajiyar Ji-qas Abuja ta dawo kacokam tana musu jego, yanzu kam Aisha ta dade da zama tauraruwa a cikin ‘yan uwanta, kowa nan-nan yake da ita saboda ita Allah ya rufa wa asiri fiye da su. Ba ta ki su ba, kuma ba ta hana su rabar arzikin da Allah ya yi mata ba. Dogon hannu gare ta, kullum cikin mikawa kowa abin alheri ta ke. Don albashi gare ta mai zaman kansa cikin (account) dinta, duk wata Ma’arouf ke zuba mata, ba ruwansa da me za ta yi da shi.

Yanzu shekarun Amina hudu ke nan a duniya, ta dade da shiga makaranta. Ma’arouf (tenure) dinsu ta kusa cika, sun yi nisa da yawon kamfen da shirye-shiryen zabe mai zuwa ba da jimawa ba. Shi ne dan takarar da jam’iyyarsu ke tinkaho da shi, kuma dan takara mafi rinjayen magoya baya.

*****

Jirgin gab yake da sauka a filin jirgin zaman Abuja, idanunsa a lumshe, fuskarsa rufe cikin hular kansa, kan nan sumul ya sha saisaye irin na su na masu madafun iko. Za ka yi tsammanin tunda ya zauna cikin jirgin bacci yake yi, sai yanzu da aka ce ya yi fasten belt jirgi zai sauka. Ba bacci yake ba (flash back) ne na gwagwarmayar rayuwarsa ya gilma masa.

Ya ja dogon numfashi ya sauke. A hankali ya bude idonsa, ya cire hular daga fuskarsa ya mayar da ita mazauninta. Ya mike ya fito daga cikin jirgin inda dumbin jama’arsa ke jiran fitowarsa.

Daya bayan daya yake mika wa jama’arsa hannu suna musabaha, kamin su dunguma su shiga motocin da suka zo a cikinsu. Motar sakatarensa Idris ya shiga suka shiga cikin birnin Abuja, sai da suka kai shi har gida sannan suka juya. Gidansa na Abuja a ‘Apo’ ne. Tuni kukun gidan ya kammala komai na abincin rana a tebirin cin abincin falon ya gaida ogan ya fita.

Sallah ya fara yi, sannan ya ciro wayarsa daga cajin da ya sanya ta. Cike da mamakin me ya sa Aisha ba ta kira shi ba, in shi jama’a da rashin cajin waya sun hana shi kiranta.

Kunna wayar ke da wuya ya tadda ‘missed calls’ har ba adadi, sai (text messege) na Aisha guda uku, su ya fara budewa.

‘Mun kusa isowa, da fatan ka sauka lafiya, I’ll miss you beyond expression Baban Amina…’

Murmushi ya yi, Aisha ke nan, me ya kawo maganar ‘missing’ kuma (kewa) bayan waje daya za mu kwana? Ya bude ‘text’ na biyu.

‘Ka taya ni kula da Ameena, ba don na raina kulawarka gare ta ba. She will need extra more…’

Na uku, kuma na karshe, mafi gajarta,  ga abinda Aisha ta rubuta;

‘Lots of love, Aisha Mansur’.

Lumshe ido ya yi. Ya zauna a dandaryar ‘tiles’ yana dan nazarin kalaman nata. Kafin ya danna mata kira.

Ya yi-ya yi iya kokarinsa layin ya ki shiga, sai ya danna ta direban Aisha wanda ya dauko su daga Bauchi.

Iya kokarinsa ya yi, Malam Bukar bai daga waya ba, alhalin kuma ga ta nan tana ta ringin. Kamin ya yi wani yunkurin kiran bakuwar lambar da ya gani ba adadi da ya kunna wayarsa ya sake shigowa.

A ka’idarsa ba ya amsa kiran lambar da bai sani ba, amma sai ya ji gabansa ya yanke ya fadi, zuciyarsa ta tsinke daidai shigowar wannan kira, don haka a sanyaye ya latsa (accept button).

Abin da aka gaya masa shi ne abu mafi tashin hankali a kafatanin rayuwarsa, kuma tun daga lokacin rayuwarsa ba ta kara komawa yadda ta ke ba.

“Sun yi accident, matar da direban sun rasu, yarinyar na ICU na ABUTH”.

Rasa abin da zai ce ya yi. Ban da zama a dandaryar ‘carpet’, wata irin zufa ta shiga keto masa har daga dan yatsansa na kafa. Daga bisani kamar wanda aka yi wa wahayi, ya soma ambaton, ‘Innalillahi wa’inna ilaihi raji’un.’

Duk wata basira ta bace masa. Idanunsa sun yi jajawur, amma hawaye ko digo daya ya kasa fitowa balle ya ji dan sanyi. Ji yake kamar an gumbuda masa barkono a idanunsa. A haka ya shafe awa daya a zaune.

Ma’arouf Ji-qas bai dauki Aisha da soyayyarta nan kusa ba. Har dai da ta haifa masa sanyin idaniya AMEENAH. Tunda ya aure ta bai kaara kallon mata da sunan so ba. Ta kankane ta toshe duk wata kafa da zai bukaci karin mace. Da gaske dan sandan nan yake? Aisha ta bar duniya bari na har abada?

Da sauri ya rarrafa ya isa ga wayarsa, ya budo ‘texts’ dinta da ya gama karantawa yanzun nan.

‘I will miss you beyond expression Baban Amina.

Ka taya ni kula da Ameenah ba don na raina kulawarka gare ta ba, she will need extra more…

‘Lots of love, Aisha Mansur’

A wannan karon ne wasu zafafan hawaye suka zubo wadanda sun fito ne tun daga karkashin zuciyarsa.

“Ashe Aisha bankwana ki ke mini? You are bading a farewell?”

Sai kuka mai tsanani.

Wayarsa ta ci gaba da ruri har ba adadi, dole ya daga, dan sandan dazu ne yake masa tuni su yi gaggawar zuwa ABUTH su tafi da gawarwakin, sannan yarinyar na bukatar kulawa ta musamman.

Cikin hawaye mai tsananin yawa ya latso lambar Baba.

“Baba wai Aisha sun rasu, suna ABUTH, mu je mu dauki gawarsu. Ba zan iya kiran Baba Mansur……..”

Baba ya kidime, “Me ka ke fada ne? Ba na fahimtarka sosai…”

“Su Aisha sun yi ‘accident’ sun rasu Baba”.

“Innalillahi wa’inna ilaihi raji’un”. Baba ya ambata, kamin dif! Ya kashe wayar.

Mikewa tsaye Ma’arouf ya yi da wayar a hannunsa, ya latso lambar Hajiyan Ji-qas.

“Sun rasu Hajiya!” Abinda ya fara furta mata ke nan, yana mai share ambaliyar hawayensa.

“Su wa?” Hajiya ta tambaya cikin tashin hankali.

“Su Aisha!”

Hajiya ta debo salati ta dire, “Ma’arouf saurare ni, kada ka yi tuki da kanka, nemo direba. Bauchi za ku wuce da su.”

Kamar wani karamin yaro ya ce da Hajiya, “Toh”.

Wayar Anas direbansa ya kira, da ma yana harabar gidan. Nan da nan ya fiddo mota suka kama hanyar Zaria.

An basu gawar Aisha da direbansa na Bauchi malam Bukar, da Amina wadda ta jikkata sosai a (ambulance) suka kama hanyar Bauchi.

Suna isa Bauchi aka wuce da Amina ATBU Teaching Hospital, su kuma suka isa unguwar Yalwa, ainahin gidan iyayensu. Inda aka yi wa mamatan suttura zuwa gidansu na gaskiya.

Idan Ma’arouf ya zauna yana tuna yadda da hannayen nan nasa ya sanya Aisha cikin kabarinta, sai hawaye su tsattsafo mishi. Ya kara yarda rayuwa ba komai ba ce. Kamar matafiyi ne ya tsaya don ya huta ya ci gaba da tafiya. Sai ikhlasi ya kara cika zuciyarsa. ‘Memories’ na rayuwarsa da Aisha ya dawo masa sabo fil.

Ya ki zama wajen karbar gaisuwa koyaushe yana asibiti gurin Amina, wadda ba ta farfado ba ma balle a san hakikanin ‘injuries’ dinta. Likitoci dai sun tabbatar tana numfashi da taimakon (oxygen), ta kuma karye a dukkan kafafunta.

Aisha tamkar ruhi ce a gare shi. Ya tabbata ya yi babban rashin da ba zai taba maidawa ba. So zama ana mishi gaisuwa ba abin da zai rage na daga radadi da zugin da zuciyarsa ke yi na rasa ta, sai dai ya kara. Don haka ya zabi da ya yi nisa daga amsar gaisuwar.

Kwanan Aisha bakwai da rasuwa wanda ya yi daidai da kwanan Amina bakwai a asibiti, cikin matsananciyar kulawar likitoci numfashinta ya daidaita. Aka cire (oxygen) aka ci gaba da bincike ta. Daga baya likitocin suka kira Ma’arouf don gaya masa halin da diyarsa ke ciki.

Ma’arouf wanda komai na duniya ya fice masa a rai, burinsa a yanzu tashin kafadar gudan jininsa, ya yarda Aisha ta tafi, inda ba za ta taba dawowa ba. Ya karbi wannan kaddarar da hannu bibbiyu, fatansa Allah ya tashi kafadar Ameena ya samu mai taya shi yi mata addu’a.

Likitan ya kalli kyakkyawar fuskar wadda ta karade talabijin da sauran hanyoyin yada Campaign irin su ‘posters’ a garin na Bauchi, ya mika masa hannu cike da kauna. A fili ya ce,

“I solute, Ma’arouf Habibu Ji-qas, sai ka yi. Insha Allahu!!!”

Ba kamar da ba da in an fadi hakan yake murmushi. Yau bai yi ba, cike yake da son jin matsalolin diyarsa. Hannu kawai ya mika wa likitan, wanda a jikin aljihun farar rigarsa aka rubuta “Umar Bolori” suka koma suka zauna a tare. Gani yake likitan wanda aka kira Umar Bolori, bai damu da damuwarsa ba sam, ta siyasa yake, wadda a halin yanzu shi ba ta gabansa.

Ganin kallon da Ma’arouf ke masa na zakuwa kamar zai matse bakinsa ya fada masa makomar lafiyar diyarsa, ya sanya Dr. Bolori kintsa kansa. Ya zauna yana fuskantarsa kana cikin nutsuwa ya soma yi masa bayani yana karantowa daga takardun gabansa.

“Yarinyarka Ameena Ma’arouf ta samu karaya guda biyu, a dukkan kafafunta.

Babbar matsalar ita ce gefen jikin Amina ya mutu, abin da muke kira ‘paralysis’ (shanyewar barin jiki). Wadannan sune matsalolin Ameena, sai ciwuwwuka haka ba a rasa ba, da kukkujewa a wurare da dama.”

Zufa ce ta kara keto mishi, (she is the only hope he had in this life), ban da ita jinsa yake ba shi da komai. Wane taimako ko kokari zai yi don ceto lafiyarta shi ne bai sani ba.

Idanuwansa sun kada sun sanja launi zuwa (brown), wannan shekara ya yi (marking) dinta matsayin shekarar bakaken kaddarorinsa. Bayan shekarun da ya shafe cikin fararen kaddarori, da farin cikin rayuwa mara yankewa. A matsayinsa na cikakken musulmi wanda ya yarda karbar kaddara mai dadi ko mara dadi na cikin rukunin cikar imani, dole ya mika hannu ya amshi kaddarorinsa da hannu bibbiyu, ya fuskance su a duk yadda suka zo masa.

Numfashi ya zuka ya fitar, ya dago ido jazur ya dubi likitan, shi kansa likitan ya karanto matsananciyar kaunar yarinya Amina daga wadannan idanun. Ya kuma tausaya a zuciyarsa. An dauki mintuna kafin Ma’arouf ya bude baki ya yi magana, shi kuma bai nuna kosawa ba, kullawa yake a zuciyarsa yadda zai kula da yarinyar nan ba don kobon ubanta ba, sai don kaunarsa da yake yi ba, tun yau ba, in bai manta ba, kannensa matasa uku ne suka yi digiri daga tallafin ‘Ma’arouf Foundation’.

Ma’arouf ya katse tunaninsa da cewa, “To yanzu wane taimako za ku ba wa Amina?”

Dr. Umar Bolori ya ce, “Za mu fara bata taimakon farko na wadanda suka gamu da lalurar ‘paralysis’ a sakamakon hadarin mota wato ‘resuscitation’, sannan muyi attacking bleeding din data ke yi, a samu ta dawo hayyacinta, sannan muyi mata dorin kafafunta guda biyu, sai sun hade za a fara ba ta kulawar masu shanyewar barin jiki (paralysis).

Mu dai fatanmu ka yi hakuri kada ka ce za ka canza mata asibiti ko za ka fidda ta waje, is all a waste, za mu yi iyakar kokarinmu a kanta, sai dai ka san ba abu ne da za a ce yau ga karshensa ba, lalurar (paralysis) tana bukatar hakuri da rashin kosawa har a samu lafiya”.

Da wannan suka kawo karshen zaman nasu

*****

An yi wa kafafun Ameena dori a washegari, duk da cewa ba cikin hayyacinta ta ke ba, ta nuna azabar ciwon da ta ke ciki. Ma’arouf da kansa kwanan asibiti yake shi da Hajiyan Ji-qas, gani yake ko ya ya ya yi nisa zai dawo ya ga babu Ameena kamar yadda babu Aisha. Kodayaushe kanta na bisa cinyoyinsa a kan gadon asibiti yana share mata hawayen da suke fita daga idanunta.

Ba ta iya cewa komai, kuma idonta a bude, amma shi tana gane shi, don yana ganin yadda ta ke rike hannunsa da nata mai lafiya. Hajiya ta yi-ta yi ya bar mata jinyar ya fuskanci ayyukan da ke gabansa amma ya ki, suna da yawon kamfen kananan hukumomi na Bauchi guda (20), amma ya daga fitar saboda lafiyar diyarsa wadda yake jin zai iya sadaukar da duk abin da ya mallaka in har za ta sake taka kasa da kafafunta.

Lokacin da kashin ya soma hadewa Ameena ta soma rigima saboda azaba. Wanka da canza sutura ke maida shi gida, sallah kuwa dama a cikin asibitin yake yinta. Har sai da karayar ta hade likitocin suka koma kan babbar matsalarta ta shanyewar barin jiki, sannan ne Ma’arouf ya soma dawowa hayyacinsa.

Sun fita (campaign) garuruwan Ganjuwa, Itas, Katagum, Misau, Toro, Ningi, Darazo, Jama’are, Warji, Dass, Tafawa Balewa cikin kwana bakwai. Inda duk tawagar Ma’arouf ta gifta masoya ne ke kwararowa ta inda shi kansa bai sani ba. Sai dai kuma rade-radi ya soma yawo, ai ba shi da aure, ta ya ya zai zama gwamna babu iyali?

Wannan rade-radi ya zo kunnen Hajiyar Ji-qas domin an ce ita magana tafiya ta ke da kafafunta.

Dawowarsu ke nan daga garin Jama’are ya zarto asibiti wajen su Hajiya. Yana tare da Amina har tsayin rabin awa. Kallo daya Hajiya ta yi masa ta karanto matsananciyar yunwa a tare da shi. Ta jawo sundukan abinci na alfarma da ke gefe ta zuba masa masah mai taushi da dadin gani a ido da baki tasa miyar ganye akai ta jawo tebir ta daura masa akai. A gefe lemon tuffah ne na kwali ta aje da kofi,

“Kyale Ameena, sakko ka ci ka gama magana za mu yi”.

A duk sanda ya ga Hajiya cikin wannan yanayin maganar da za ta yi mai muhimmanci ce. Ya bi umarninta. Cikin dadin rai ya soma cin abincin don kuwa ya manta rabonsa da abinci mai dandanon gishiri cikin kwanaki biyun nan, sai (caffinated drinks) da (snacks) da yakan ci in ya samu dan lokaci.

Sosai ya ci masar, har da yi wa Hajiya godiya, lemon kwali guda haka ya shanye shi. Ya tattara hankalinsa ya mika wa Hajiya don ya fuskanci hakan ta ke so.

Ita ma nata hankalin ta bashi.

“Kana sane da cewa ka tsaya siyasa ba ka da iyali?”

Da sauri ya dago ya dubi Hajiya. Ita kuwa ta tsare shi da idon.

“Ba ka da iyali ta ya ya za ka shugabanci al’umma alhalin kai kanka ba ka da abin shugabanta?”

Ya bude baki zai yi magana ya kasa, to me zai ce? Ya manta da wannan shaf! Kuma a da bai dauke shi da muhimmanci ba tunda ya san yana da su, Allah ne ya yi hukuncinsa, yanzu ya tuna wannan (decree) ne mai zaman kansa a sharuddan shugabanci.

Hajiya ta gaji da shirunsa, “Ba ka ce komai ba”

Da kyar ya hadiye miyau ya kalato sauti.

“To Hajiya ni me zan ce?”

“Me za ka ce? To gaya min ta ya ya za’a ba ka shugabancin?”

Ya dan kifta ido, don shi ma yanzu ya kwadaita da siyasar, don ita da ma haka ta ke, wuyarta ka dandanata sau daya. Yana kuma tuna wahalar da ya ke ta yi a kai shekaru biyu ke nan a ce ya bari don ba shi da aure? Auren wata wahala ne da shi? Ba kamar siya ake a kasuwa ba?

Hajiya shirunsa ya fara bata haushi, “Ka kyale ni ina ta magana, in ba ka yarda da abin da na ce ba ne ka tashi ka yi tafiyarka, zan tada sallah”

Ya dan muskuta ya gyara zama.

“To Hajiya gani na yi abin ya yi kusa. Kwata-kwata yau kwanan Aisha arba’in da biyu da rasuwa, kawai kuma a ji na yi aure kamar dama jira nake ta kauce in yi aure?”

Hajiya ta girgiza kai.

“Wannan ne daidai lokacin da Manzo (S.A.W) ya umarce ka da ka yi auren. Ba don kana neman kai da Aisha ba, sai don cikar mutuncinka da kamala a wurin Ubangiji da idon al’umma”

Ya zuki iska ya fesar, cikin kankanuwar murya kamar ba tashi ba.

“Na amince Hajiya ki yi duk abin da ya dace. Nawa zan bayar?”

Hajiya abin ya ba ta dariya, ta lura ya dauki auren kawai matsayin wani abu da za a sa kudi a sayo a kasuwa, a duk sanda ake so. Sai ta biye masa.

“Naira ishirin ya isa”

Ya dube ta da sauri, don shi da zuciyarsa daya ya tambaye ta, sai kuma ta jefe shi da gatse.

Ta kalle shi cikin ido ita ma.

“Ka kalle ni mana tunda ka dauki auren abin siyarwa”.

“Ki yi hakuri Hajiya”

“Ban yi fushi ba. Ka ba ni kwana uku in je Ji-qas in cigita cikin ‘ya’yan ‘yan uwa ko abokan arziki. Kada gaggawa ta sa mu yi aikin shaidan.”

Da wannan suka gama tattaunawar tasu ta ranar, ya sumbaci Amina wadda ta yi bacci ya tafi gida.

Da hajiya za ta tafi Ji-qas ta ke gayawa likitocin Amina za ta yi tafiya ta kwana uku, wa zai kula da Amina? Saboda ba ta so ta kirawo matan Baban Aisha don ba zumunci na jiki sosai ne tsakaninsu ba, haka ba ta son cewa Baba ya kawo Inna Luba duk da rayuwa ta koya mata hankali yanzu ta zama mutuniyar kirki, ga Babanta yana Abuja ba ta gaya masa lokacin da za ta yi tafiyar ba, don duk muhimmancin abin da ke gabansa haka zai ajiye shi ya ce shi zai zauna da Amina.

Dr. Umar Bolori ya ce, “Hajiya kada ki damu, akwai (nurses) dinmu da za su kula da ita, mu ma muna tsaye fi-amanallah. Insha Allahu”

Da wannan Hajiya ta shirya sabon direbansa na Bauchi Akilu ya dauke ta zuwa Ji-kas, hankalinta a kwance don ta san ta baro Amina a kyakkyawan hannu.

Bookmark
ClosePlease login

No account yet? Register

Rate the story.

Average: 4 / 5. Rating: 4

As you found it interesting...

Follow us to see more!

<< Sanadin Kenan 10Sanadin Kenan 12 >>

1 thought on “Sanadin Kenan 11”

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
3
Free daily stories remaining!
×