Skip to content
Part 6 of 50 in the Series Sanadin Kenan by Sumayyah Abdulkadir Takori

A hutu na gaba da Amina ta zo, Goggo ta ce ta shirya ta tafi Shira ta gano kawun mahaifinta Bilyaminu, an gaya mata yana kwance ba shi da lafiya, ta kuma karasa ta gaida Baffa Tasi’u shi ma in ta dawo ta je gidan Kawu Sule shi ma ta gaishe shi. Amina ba ta yi wa Goggo musu ba, amma cikin zuciyarta mita ta ke yi, “Na rasa wace iri ce Goggo, sam-sam ba ta yin zuciya da mutanen da ba su damu da mu ba, dan gara-gara ma Baffa Tasi’un shi in an je inda yake yana yi wa mutane tarbar arziki ko da ba zai ba shi ko sisi ba. Amma Baffa Bilya da kawu Sule uhumm! Ba ta bukatarsu cikin rayuwarta, sai dai umarnin Goggo tilas ne a gare ta.

Ranar alhamis ba ta da islamiyya don haka ta shirya da safe, ta yi kwalliya da wata sabuwar atamfarta da Goggo ta dinka mata tana makaranta. Ta kawo wankakken hijabinta ruwan madara ta dora. Ta karbi kudin mota wurin Goggo ta yi mata sallama ita da Baba Talatu, Goggo ta kawo cincin mai sukari da daughnut cikin leda mai yellow da baki guda biyu ta ce ta kai wa kakannin nata da iyalansu.

Amina ta tari taxi (a lokacin ba Napep) ta kai ta tasha, daga nan ta hau motar garinsu Shira. Tunda motar ta soma tafiya Amina tagumi ta yi tana tunane-tunane a kan rayuwa. Ta rasa mahaifinta a daidai lokacin da ta ke tsananin bukatarsa, sai Allah ya share mata hawaye ya bar mata Goggo, ga shi ta cike mata kowanne gurbi na uwa, uba, kawaye da dangi. Shin ko ‘ya’ya mata nawa ne Allah ya ba su jajirtacciyar uwa irin Goggonta?

Dangin mahaifinta ba su damu da su ba, sun watsar da su, tun rasuwarsa wani nasa bai taba tako gidansu ba, amma Goggo ba ta yi zuciya ba, jefi-jefi tana tura Aminan. A cewarta, ‘Naka sai naka’ ko ta ina aka juya sune iyayenta, ita ba wani abu ta ke so su ba su ba, a’ah zumuncin Allah, wanda Allah subhanahu wata’ala ya yi umarni da a yi shi, Ya nesanta da mai yanke shi, Allah ka sa mu dace amin.

Ita kadai ta ke wadannan tunane-tunanen, har aka zo garin Shira. Ta dauko ledojin tsarabarta ta doshi gidan kawunnin nata.

Gidan su mahaifin Amina malam Mas’udu babban gida ne irin na Gandu, kowa an ware masa sassansa da iyalinsa. Bangaren Kawu Bilya daban, na Baffa Tasi’u daban, shi ma Kawu Sule yana da bangare cikin gidan inda yake sauka da iyalinsa idan ya zo. ‘Ya’ya da jikoki rututu don Bilya matansa hudu, Tasi’u mata uku, akalla kowannensu yana da ‘ya’yan da suka haura goma, kuma babu wata tartibiyar sana’a bayan noma, ita ma sai shekara-shekara, don haka duka matan kowacce da sana’arta don mazan ba wani abin kirki suke iya yi musu ba, karfin ciyarwa a wuyansu yake.

Uwargidan Kawu Bilya, wato Asabe sana’ar man kuli-kuli ta ke yi, ta biyun Sahura dinki ta ke yi, ta uku sakar huluna na maza, ta hudu Ramma danwaken sayarwa ta ke yi, ‘ya’ya kuwa ga su nan ba adadi don kowacce tana da kusan goma.

Bangaren Baffa Tasi’u shi da dan dama-dama, yana kokari a kan iyalinsa, duk ya kwashi ‘ya’yansa ya sanya a makarantar boko, babu wanda yake bari ya zauna a gida yana jiran a gama dahuwar abinci, sannan matansa akwai tsafta daidai misali, bai hana su yin sana’a ba shi ma kamar Bilya, sai dai yana wadata su da abinci, kuma suna zaman lafiya sabanin matan Bilya da kullum kamar su cinye kansu wajen tarewa ‘ya’ya fada.

Amina ta yi sallama ta shigo sassan kawu Bilya ta fara shiga. Ramma ce ta fara ganinta, ta dago da mamaki a fuska da muryarta ta ce, “Wa nake gani kamar Amina?”

Ta yi dan murmushi, “Ni ce Goggo Ramma.”

Ta tsuguna ta gaishe ta kafin ta bi sauran matan daki-daki su ma ta gaishe su, ta dawo dakin Ramma don duk ta fi su kirki, suka dan taba hira ta tambayi jikin kawun Ramma ta ce, “Babu sauki wai ciwon arne, mu je ki ganshi.”

Ramma ta yi mata jagora suka yi sallama a turakarsa, kallo daya Amina ta yi masa zuciyarta ta buga don sai ta ga kamanninsa da mahaifinta sun fito sosai. Yana kwance duk ya kare, sai tari yake yi. Amina ta gaishe shi, da kyar ya samu ya amsa sakamakon tarin da ke turnike shi.

Ya yafito Amina alamar ta zo gare shi, Amina ta matsa kusa, ya kama hannunta ya ce, “Ki yafe min uwata, na kasa zama kaka a gare ki saboda son zuciya irin tawa. Ba irin kyautatawar da mahaifinki bai min ba, amma na bi ta kai na take saboda son zuciya irin nawa. Ki yafe min ko Allah ya sassauta min zunubin yin wasarere da zumunci da maraicinki, ki kuma roka min mahaifiyarki yafiya don Allah”.

Hawaye suka cicciko a idon Amina, “Wallahi Kawu, Goggona ba ta taba rike ka a zuciyarta ba, ita ta umarce ni da in zo in duba ka, an gaya mata ba ka da lafiya. Ga wannan ma ta ce in kawo maka”.

Ta dire masa ledar da ta riko, ta ci gaba da cewa, “A nawa bangaren ni ma na yafe maka, Allah ya yafe mana bakidaya, Ya tashi kafadunka”

Ya dumtse hannun Amina cikin nasa, ya dinga sanya mata albarka, da kyar ya cika ta sakamakon wani tarin da ya turnuko shi.

Amina ta tambayi Ramma ko an kai kawun asibiti? Ramma ta ce, “Yo halin Sule wanne ne ba ki sani ba? Ana ta yi masa aike ya zo ya kai shi asibitin ya ki zuwa, tarin fuka ke damunsa in ji malamin asibitin da Tasi’u ya dauko, ya yi masa allurai ya ba da magunguna yana ta sha, amma ga shi nan kullum sai abin da ya yi gaba.

Amina ta ce, “Zan gaya wa Goggona mu zo da taxi gobe a kai shi asibiti”.

Ta yi sallama da su ta shiga sassan Baffa Tasi’u kowa a gidan yana lale maraba da ita har shi Baffan. Ta kawo tsarabar Goggo ta ba shi, shi kuma ya danka wa uwargidansa Azumi ta hau rabo, suna hira yana ba ta labarin ciwon yayan nasa, ya ce shi ya yi duk iya kokarinsa, ya dauko malamin kyamis ya duba shi ya yi masa allurai, bai san ya zai yi ya fitar da shi asibitin maraya ba, karfin nasa bai kai nan ba. Sule ne dama ya kamata ya kai shin, to an yi aiken duniya ya ki zuwa”

Amina ta ce, “A kyale shi Baffa, gobe za mu zo da mota ni da Goggo mu kai shi asibitin.”

Baffan ya yi ta sa mata albarka.

Ba ta jima ba ta yi sallar la’asar ta kamo hanya, kafin magriba tana gida. Ta kwashe komai ta gaya wa Goggo.

Goggo ta ce, “Allah ya kai mu goben, kin ga ai gara da ki ka je, da haka za su barshi a gida ciwo ya ci ya cinye shi, ai fuka ba ta da kyau, mugun ciwo ce, Allah ya ba shi lafiya.”

Washegari Ilya ne ya samo motar, aka tsadance zuwa da dawowa da wucewa asibiti, Goggo ta biya suka kama hanya. Da yake ba tsaye-tsaye ko jiran fasinja, nan da nan suka iso Shira.

Da ma tun kamin su iso Ramma ta kintsa mijinta cikin ‘yan kayansa masu haske, Ilya da babban dansa Hamza suka sanya shi a motar. Kai tsaye ATBU Teaching Hospital suka wuce da shi.

Likitoci sun karbi kawu Bilya, aka soma ba shi taimako bayan an ba shi gado. A binciken da suka yi ma bayan tarin fuka, akwai sugar tare da shi da hawan jini. Duk abin da suka nema Goggon Amina ta biya, suka ci gaba da ba shi kulawar da ta dace. Dansa Hamza ne yake kwana da shi, Amina na hidimar kawo abinci safe, rana, da kuma dare. Kwanansa uku ya soma murmurewa, sai kuma kunyar Hauwa’u ta hana shi sukuni. Da ya ganta sai hawaye da rokon gafara, yau bakuwar haure ita ta ceto shi daga cututtukan da suka kusa hallaka shi. Jininsa Sule ko oho! Balle ‘ya’yan cikinsa.

Kwanansa bakwai ya yi garau, likitoci sun kafa masa sharadi kan cimar da zai rinka ci ya ce, duk ya ji ya amince. Goggo ta sake biyan kudin mota Hamza da Ilya suka maida shi Shira.

Tun daga wannan abu da ya faru, Amina da Goggonta suka zamo shalele wajen dangin Amina na kauye. Kowa Amina- Amina, gidan Kawu Sule ma taje bata tarar da shi ba, wai yayi tafiya kasar Togo. Zuwan da  Amina ta yi da na sanin yinsa.

Tunda Hafiz babban dan kawu Sule ya ganta ya rikice wa uwarsa Atika shi fa ya ga mata.

A washegari sai ga shi gidan su Amina gidan da bai taba taka kafarsa ba tunda aka haife shi. In ran Amina ya yi dubu, to ya baci. Ta fashe wa Goggo da kuka tana fadin, ta shiga tsakaninsu, ba ta son maganganun da yake mata.

Goggo ta ce, “An taba shiga tsakanin ‘yan uwa ne Aminatu? Ki bi shi a hankali, ba wanda ya isa ya yi miki auren dole muddin ina raye”.

Hafiz fa da gaske yake, ya makalewa gidan Goggo, abincin ranarsa a gidan yake ci in ya taso aiki, ma’aikacin MTN ne. goggo ba ta taba nuna masa rashin goyon bayanta ba ko a fuska, Allah ta ke gaya wa cikin sallolinta Ya zaba wa Aminanta miji na gari, mai addini, wanda zai rike ta da maraicinta amana.

Amina da ta gane lokacin zuwan Yaya Hafiz gidan, da zarar lokacin ya kusa za ta sulale ta bar gidan zuwa gidan su Ilya wajen Goggo Zulai, tana taya ta gyaran zogale da dahuwarsa, sana’ar Zulai din ke nan, in ya tafi Ilyan Goggo zai zo ya gaya mata. Haka za ta koma gida tana yi wa Goggo mitar ita ta sakar masa har ya maida gidansu wajen zuwa. Ita fa ko maza sun kare a duniya ba abin da za ta yi da dan kawu Sule, balle ma mijinta ba a haife shi ba.

Goggo murmushi kawai ta ke yi, ba ta cewa komai. Da gaske Amina ta kullaci kawu Sule, duk da yadda ta ke nusar da ita. Kuma ba ta son kalaman Amina masu nuna ba ta da niyyar aure a rayuwarta.

A haka hutunsu ya kare, Amina ta koma makaranta.

Atika har gida ta zo ta tadda Goggo da kashedinta, cewa ta yi gaggawar kwance asirin da ta kulla wa Hafiz ta tura Amina gidansu da shi, domin ko mata sun kare ba abin da Hafiz zai ci da Amina, su ba su gaji fatara da talauci ba. Don haka a kiyaye tun Babansa bai ji ba.

Goggo ba ta ce mata komai ba har ta yi bambaminta ta gama, ta fita. Ta girgiza kai, a fili ta ce, “Rayuwa ke nan.”

Hafiz bai fasa zuwa gidan ba ko bayan da Amina ta koma makaranta, ita kuma Goggo ba ta fasa ba shi abinci ba in ya nema, sannan ba ta gaya masa mahaifiyarsa ta zo ta yi musu cin mutunci ba, ta bar komai a hannun Allah.

Cikin dumi irin na Hafiz yake gayawa Goggo babansa yake jira ya dawo daga Tokyo ya gaya masa zancensa da Amina, ya ce,

“Goggo na san zai yi farin ciki, zumuncin da ya gurgunce zai mike. Don Allah Goggo ki dinga nuna wa Amina na rasa gane kanta, ni dan uwanta ne, jininta. Zan fi kowa rike aurenta da daraja.”

Goggo kan yi murmushi, Hafiz gata ne ya yi masa yawa shi ya sa yake ganin komai yake so zai same shi da sauki. A ranta cewa ta ke, ‘ashe kun san kuna da ‘yan uwan na jini da ma? Wadanda jin dadin rayuwa ya hana ku san da su, sai yanzu da suka soma zama mutane yadda za su amfane ku?”

*****

Wannan zangon su Amina karatu suke ka’in da na’in, domin daga shi ne za su shiga aji shida na sakandire in sun dawo hutu. Ranar wata asabar suna labirare (library) ita da Hafsa, a gabansu tintimemen littafi ne an rubuta (Organic Chemistry) na ‘T.W Graham’, suna aikin wani (assignment). Hafsa ta ce, “Amina Mas’ud, me ki ke so ki karanta ne a jami’a?”

Ba tare da ta dago ba tana ci gaba da rubutun da ta ke yi, ta ce, “Ciwon da ya kashe Babana. Na ga yadda yake, ina tausaya wa masu fama da shi, domin rabin jikinsu ne a raye, rabi a mace. Sannan jinyarsu sai mai hakuri, juriya da sadaukarwa. Na jinjina wa Goggona da ta yi jinyar Baba babu korafi, babu gazawa. Ina rokon Allah ya sada su a inuwar aure a gidan aljanna”.

Hafsa cikin tausayawa ta ce, “Wane ciwo ne?”

Ta ajiye bironta a kan littafi ‘stroke’ Hafsa ta ce, “kina nufin za ki karanta Physiotherapy ne?”

Amina ta ce, “Insha Allahu”

Hafsa ta ce, “Amina kin rakito karatu mai tsayi, anya Goggo za ta barki? Maganar aure fa? Ko da wasa ban taba ji kin yi min maganar wani da sunan yana sonki ko kuna dating ba, ni na gaya miki har kudin aurena an karba, mahmud yana Russia yana nasa karatun, (family friends) muke da su, da ya kammala shekara mai zuwa zai zo daidai da mun kammala mu ma za a yi mana aure mu koma tare, in shiga jami’ar a can. Ki yi kokari ki fidda miji Amina, don in ki ka fara karatun likitanci ba za ki samu lokacin irin wadannan abubuwan ba. Gabadaya hankalinki zai afu ne ga cimma abin da ki ke son cimmawa, amma da aurenki in ki ka yi sa’ar abokin rayuwa komai zai tafi miki da sauki.

With someone aside who is always helping, supporting and encouraging your dreams will be realized (tare da wani a gefenki wanda kullum zai kasance mai taimaka miki, da ba ki kwarin gwiwa mafarkanki za su zamo gaskiya). Mace na bukatar namiji a gefenta (as soon as) ta kai munzali. Don kiyaye addini da mutunci. Ki yi nazari, karatu ba ya hana aure, haka aure ba ya hana karatu”.

Amina ta mike ta soma tattara takardunta don Hafsa ta ishe ta, ba ta da gamsasshiyar amsar da za ta bata, don Goggo ma abin da ta ke fada mata kenan. Ta bar mata wajen shi ne mafi a’ala a gare ta.

Hafsa ta jinjina kai tana murmushi, ta bi bayan Amina da kallo. Haka kawai Amina Mas’ud ke burge ta. Yarinyar ta san kanta, miskilar gaske ce, sannan wani bai isa ya canza mata ra’ayi ba komai kusancinta da shi, shi ya sa ba ta faye fadin ra’ayinta ba ma a kan abubuwa, sai dai ta yi a aikace a gani.

Ita ma ta mike ta harhada nata takardun ta bi bayanta.

Bookmark
ClosePlease login

No account yet? Register

Rate the story.

Average: 4.2 / 5. Rating: 6

As you found it interesting...

Follow us to see more!

<< Sanadin Kenan 5Sanadin Kenan 7 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
3
Free daily stories remaining!
×