Skip to content
Part 8 of 50 in the Series Sanadin Kenan by Sumayyah Abdulkadir Takori

Amina A Jami’a

Sakamakon bai dauki watanni uku ba kamar yadda ake yi a wancan lokacin, ya fito. Amina sai sam-barka ta lashe komai. Goggo ba ta yi wahalar banza ba. Babu jimawa ta samu gurbin da ta nema a kuma fannin data nema a ATBU a kananun shekarunta goma sha shidda, sakamakon (double promotion) da aka yi mata a karamar sakandire da firamare.

Tun daga shige da fice na (registration) da ta fara ta lura ta kuma amince tafiyar ba mai sauki ba ce, don haka ta kara ba da himma.

Manema kuma suka ce mata salamu alaikum, kamar da ma jira suke ta kare sakandiren ta fara jami’a. ba ta sauraron kowa, kuma ba ta barin Goggo ta gane tana korarsu ne tun kafin su biyo ta gida.

Lokacin da Amina ta shiga shekara ta karshe a jami’ar Tafawa Balewa inda ta ke hada B.Sc dinta a ‘Physiotherapy’, wanda ta kwashe shekaru biyar tana yi, Goggo Hauwa ta soma shiga damuwa a kan rashin kwakkwaran manemi ga Aminar, a lokacin ta cika shekaru ashirin da daya a duniya. Abin ya soma damunta sosai.

An tura su Amina ‘internship’ na shekara daya a asibitin koyarwa (Abubakar Tafawa Balewa Teaching Hospital), bayan kammala ‘B.Sc’ dinta, jininsu ya hadu da (consultant) dinsu Dr. Usman Turaki saboda kokarinta. Dr. Turaki na yabawa Amina sosai, yana kiranta ‘Young Doctor’, don duk cikin ‘team’ dinsu da ke karkashin Dr. Turaki ita ce karama.

Amina na girmama Dr. Usman Turaki don ta lura mutumin kirki ne mai tsanteni da mutuncinsa, ba shi da wasa ko kadan ga rikon addini. Duk sanda yake koyar da su da zarar an kira sallah, to fa zai katse ya yi umarni ga musulman cikinsu su je su yi sallah, sannan bai taba yi mata maganar banza ba, don haka tasu ta zo daya suke ganin mutuncin juna, duk abin da ya shige mata duhu shi ta ke samu, shi ya shige mata gaba ta ke samun (scholarship) daga gwamnatin jiha, ko da ba ta gaya masa komai da ya danganci (personal life) zahirin rayuwarta ba, ya lura iyayenta masu karamin karfi ne, an kuma taba gaya masa Babanta ya rasu, wannan ‘scholarship’ da ta ke samu duk shekara ba karamin taimakawa yake yi ba.

*****

Goggo Hauwa da aminiyarta Zulai Babar Ilya, a dakin Goggon suke tattaunawa a kan damuwar Goggon.

“Na rasa daga ina matsalar ta ke? Aminatu sam ba ta da niyyar aure a rayuwarta Zulai, boko dai, boko dai? Ina ki ka fito? Asibiti, ina za ki? Asibiti! Babu mashinshini ko daya, lamarin nan yana tayar min da hankali, mu shekarunmu goma sha hudu aka yi mana aure, yau Amina in watan nan ya mutu shekarunta ashirin da uku. Yaushe ne ta ke tunanin ajiye iyali na kanta? In na tambaya babu manemi ta ce babu, ga Hafizu da ta kora yanzu yaransa biyu, jiya suka zo shi da maidakinsa da yaransa ba ki gani ba abin sha’awa, ta san ta yi ta yin nan-nan da yaran wasu, amma ko miskala zarratin ba ta damu da itama ta yi ba, sai hidima da na mutane”.

Goggo Zulai ta gyara zama, “Kina nema wa yarinyar nan taimako kuwa? Yanzu ba wuya aljanu sun auri bil’adama su cire musu son aure a ransu, ga jifa irin na marasa imani dole ki mike tsaye”

Goggo ta girgiza kai, “In dai irin wannan mikewa tsayen ne ba zan taba mikewa ba, kullum na kai goshina gaban Ubangiji dare da rana, yini da safiya sai na roki Ya baiwa Amina miji na gari, addu’ar iyaye kuma karbabbiya ce a kan ‘ya’yansu, abin daga Aminar ne, na tabbatar korar maneman ta ke tun kamin su iso gida. Na yi fadan, na yi nasihar duka a banza.”

Zulai ta ce, “In haka ne sai ki daina damuwa ki jira lokacin da ijaba za ta zo, amma duk da haka ki sa a dinga rubuce mata alqur’ani tana shanyewa saboda shi maganin komai ne. zan yi wa masu rubutu magana a fara yi mata.”

Goggo ta amince da shawarar Zulai. Ta sa aka yi rubutun jarka guda tana takura wa Amina tana sha a gabanta.

*****

Amina zaune a gefen gado, Goggo a kasa, kitso Amina ke yi wa Goggo suna hira jefi-jefi. Amina ta ce, “Wai ni Goggo shekararki nawa ne? furfurarki ba ta da yawa.”

“Shekaru na hamsin.”

Goggo ta ba ta amsa.

“To Goggo me ya sa ba za ki yi aure ba, na ga dattijai ma da suka fi ki suna yin aure.”

Goggo ta sha kunu, sau tari Amina ‘treating’ din Goggo ta ke kamar kakarta.

“Sai ki kai ni bola ki yar in gajiya ki ka yi da ganina”

“Wuh!” In ji Amina tana dafe baki cikin dariya.

“Goggo na my life, my soul”

Goggo ta ce, “Idan ba za ki yi maza ki lallabe min kan nan ba ki kyale ni”.

Amina ta maida hankali ga kitso, amma bakinta ya kasa shiru,

“Goggo yaushe za mu je Sirrleone?”

Goggo ta yi mata shiru, sai ba ta ja ba, don ta san shirun Goggo na nufin ba za ta yi abun a lokacin da aka ba ta umarni ba.

Ilya ya shigo yana kakabin nan irin na ‘yan siyasa, “Sai Ji-qas, wallahi sai Ji-kas…!”

Ya yi tsalle ya dire ya shigo dakin Goggo yana ci gaba da fadin, “Sai Ji-kas, insha Allahu sai Ji-kas!”

“Mene ne Ji-kas?”

Goggo da Amina suka hada baki suna tambayarsa.

“Goggo ina rediyonki? Hira ake da Engineer Ma’aruf Habibu Ji-kas, dan takarar gwamnan Bauchi daga jam’iyyar NPC (Northern People Congress)”. Ya fadi yana ta kokarin murdo rediyon har ya samu radio Bauchi.

“Yaushe ka zama dan siyasa Ilya?” Goggo ta tambaya cikin mamaki.

“Ban zama ba Goggo, amma a kan Ji-kas zan zama. Daya tamkar da goma, mai son ci gaban matasan Bauchi, gagara-gasar masu gasa, bujimi uban matasa. Giwa an buga an barki, Ji-kas ikon Allah ke nan.”

Muryoyi suka soma fitowa tar-tar daga rediyon, na dan jarida da wanda ake yi wa tambayoyin yana ba da amsa cikin nutsuwa da wadatar ilmi, the programme is live (wato a lokacin ake yi).

Ba su ji farkon hirar ba, sai tsakiyarta.

“Mene ne babban burinku idan kun samu nasarar hayewa wannan kujera a garin Bauchi da kananan hukumominta guda ashirin?”

Ya dan ja lokaci kafin ya amsa, a hankali kuma ya soma bayani cikin Hausa mai tsafta wadda babu kalaman turanci a ciki.

“Babban kudirinmu shi ne gina matasa, saboda su ne shuwagabannin gobe. Za mu fadada samuwar aikin yi ga wadanda suka yi karatu, wadanda Allah bai ba su dama ba za mu samar da shirin koyar da sana’o’i, inda za a koyar da su duk sana’ar da suke so mu ba su jari wanda zai ishe su gina wannan sana’a, domin in ka lura akasarin matasan da ke samun kansu a shaye-shaye, daba da sauran laifuffuka rashin aikin yi da hanyar abinci shi ne sila, duk masu yin karatu a fannin kiwon lafiya (medicine), gwamnatinmu za ta dauki nauyin karatunsu. Wannan alkawari ne muka yi ga al’ummarmu da muke rokon Allah ya ba mu ikon cika shi.

A sauran bangarorin ma ba za mu bar ko daya ba, tun daga kan ilmi, ruwa da wutar lantarki, tsaro, cin hanci da rashawa, tituna da hanyoyin sadarwa, karawa malaman makaranta albashi, hakkin ‘yan pansho, tsaftar muhalli da sauransu, muna kira ga matasa da su fito wannan karon su zabi wadanda suke so su zama shuwagabanninsu ta hanyar aiki da hankali, kada su zabi wadanda za su zo suna da na sani…”

Dan jarida ya gamsu da amsar da ya samu, ya ce, “A karshe masu sauraro za su so su ji mene ne ‘Ji-kas’ da ya bi ya dabaibaye Engineer, har sunansa ya bace sai Ji-kas din?”

Murmushi ya yi mai sauti, kana iya jiyo sautin murmushin nasa ta rediyon.

“Ji-kas, kauye ne da ke karkashin jihar Jigawa, a karamar hukumar Gwaram, na san mutane da yawa za su ce ya ya dan Jigawa zai nemi kujerar Bauchi? To Ji-kas kauyen da mahaifiyata ta rayu a can ne saboda yanayin rayuwa, amma uslin iyaye da kakannina ‘yan kasar Bauchi ne, kuma a nan aka haife ni, sai dai na budi ido na gan ni a garin Ji-kas, da na isa shiga makaranta sai na baro Ji-kas na dawo Bauchi na ci gaba da zama da mahaifina.”

Dan jaridar ya ce, “Masu saurare da fatan kun gamsu? Bari mu kyale ka haka Hon. Ma’aruf Habibu Ji-kas. Ga sakonni suna ta shigowa na goyon bayan al’umma a gare ka, amma lokaci ba zai bari mu bi su daya bayan daya ba. A takaice wane sako ne gare ka ga dumbin masoyanka?”

Babu nuna kosawa cikin muryarsa, “Sako na ga jama’ata shi ne, ranar zabe kowa ya fito ya kada kuri’arsa don kwatar ‘yancinsa na dan kasa, kada a zauna a gida a ce su je su zabo mana alheri, a’ah, hakkin kowane dan kasa ne ya yi zabe don kar a yo masa zaben tumun dare. Sannan su ci gaba da addu’a Allah ya ba su shuwagabanni na gari, ba wanda suke so kadai ba.”

A nan hirar ta kare. Ilya ya yi zambarwa yana fadin, “Sai Ji-kas!”

Amina ta ce, “Hala cin hanci ya ba ka, wannan irin soyayya haka?”

Ilya ya ce, “Wallahi ko sisi. Kawai ina son mutumin. Ku ne ba ku sanshi ba, amma kaf garin nan waye bai san Engr. Ma’aruf Jikas ba? Takarar ma talakawa ne suka angiza shi saboda irin taimakonsa gare su, amma a da dan kwangila ne kawai bai da alaka da siyasa ko kadan.”

Zancen duk ya gundiri Amina, ta karasa wa Goggo kitsonta, ta mike ta yi waje don sake wanka ta tafi asibiti, tana da laccar karfe hudu na yamma.

A yanzu haka Amina na shirin gama ‘internship’ bayan kwashe shekaru biyar a jami’a, tana cikin shekaru ashirin da hudu, gabadaya shekarun gwamnati ce ta ci gaba da biya mata scholarship abin da Goggo ke kashewa ba yawa, don haka asusunsu cike yake taf da kudi da su kansu ba su san adadinsu ba.

An yi bikin yaye su Amina ranar wata asabar a matsayin cikakkun (physiotherapy proffessionals). Gabadaya danginta na kauye sun zo mata ban da kawu Sule, Hafiz da iyalinsa ma ba a barsu a baya ba. Goggo ta hada gagarumar walima a nan gidansu, an ci an sha daga abinci mai kyau da ababen sha masu kyau. (Ina ruwan mai abu da abunsa?) An yi taro lafiya an watse lafiya, Amina ta ci gaba da hutawa a gida kafin inda za a tuttura su hidimar kasa ya fito.

Bookmark
ClosePlease login

No account yet? Register

Rate the story.

Average: 4.5 / 5. Rating: 4

As you found it interesting...

Follow us to see more!

<< Sanadin Kenan 7Sanadin Kenan 9 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
3
Free daily stories remaining!
×