Sun isa Ji-kas lafiya, wadda ke karkashin karamar hukumar Gwaram ta jihar Jigawa. Maigidan Hajiya, Malam Halilu, shi ne babban limamin garin Ji-kas, saboda haka gidan na Hajiya ba boyayye ba ne. Ga kuma gyaran da Ma’aruf ya yi masa ya zama abin kwatance, in za a yi kwatance za a ce gidan Hajiya Saude farin Gida, kamar ita kada ke da gidan babu kishiya.
Hajiya ba ta kara haihuwa ba tun Ma’aruf, wannan kuma tsarin Allah ne, kuma hakan bai sa Malam Halilu ya taba canza mata fuska ba ko sau daya, don shi yana. . .
thank you