Skip to content
Part 14 of 50 in the Series Sanadin Kenan by Sumayyah Abdulkadir (Takori)

Tenure dinsu ya cika sun sauka daga kujerunsu na ‘yan majalisar tarayya, ‘yan rikon kwarya sun hau. Ana gab da yin zabe.

Yana zaune shi kadai watarana yana tunani. Hajiyarsa kullum girma kara hawanta yake, mijinta ya yi masa karah da duk wata alkunya da ta dace, ya sallama masa matarsa don kula da diyarsa. Ga Amina babu ranar tashi sai sanda Ubangiji ya nufa. Zaman asibitin nan ya ishe su duka daga shi har Hajiya har yarinyar.

Gara ta dawo gida a ci gaba da kula da ita a gida ko su ma hankalinsu ya tsaya wuri guda. Hajiya ta dade tana cewa a koma maganin Hausa za ta mike kan kafafunta yana basarwa. Amma yanzu zai duba shawarar nan tata.

Kuma tunda ga Laila a gida ba ta komai, sai ta dinga kula da ita, zai gwada na Hausan tsayin wata biyu a gani, in ba nasara a sake komawa asibitin, don ba a hada duka biyun a lokaci guda in ji Hajiya. Inyaso Hajiya ta koma wajen mijinta ko na dan lokaci ne haka ta huta, jikin girma amma kullum bisa dardumarta ta ke kwana tana rokon ma Amina lafiya, uwarta gafara.

Sun yi wannan maganar da Hajiya, ta ce, “Ni ai da bakina ban ce maka na gaji ba”.

Ya ce, “Na san ba ki gaji ba Hajiya, ba kuma za ki taba gajiya ba in don ta taki ce. Magana ce ta dukkanmu muna da hakki a kanki. Ni, Amina, da Baba Liman. Bai kuma dace a yi ta take nasa ba alhalin ina da mata mai koshin lafiya.

Ga hadimai wadanda ba zaman kowa suke ba sai mu. A dauko masu maganin da ki ka yi magana su fara, Laila ta kula da ita da masu aiki, ke kuma ki koma gidanki ki huta. Yadda fa nake son Amina haka nake sonki Hajiya ta. Bana son kowannenku ya jigata, hakkin dan Adam za a ciccire.”

Sai ya ba ta dariya, ta ce, “To bari a kira masu maganin. Ita kuma Lailar zan yi magana da ita, amana zan bar mata Amina ba don na gaji ba.”

Laila rasa abin cewa ta yi sanda Hajiya ke mata wannan maganar, wai za a bar Amina karkashin kulawarta, ita ina za ta iya wannan wahalar? Gashi shagon kayan kawa na mata ta ke kokarin budewa. Cikin dan zamanta a Bauchi, da Abuja da ta ke bin Ma’arouf lokaci zuwa lokaci ta yi kawaye matan abokansa, idonta ya kara budewa har ta ke ganin karatu wahala ne in dai don a samu abin yi ake yinsa.

Ma’arouf ya ba ta jarin da ya yi alkawari, motoci sai wadanda ta zaba ta ke hawa, ga dankareren gida ita kadai a cikinsa tana juyawa yadda ranta yake so, ma’aikatan gidan duka, yanzu tsoronta suke don kuskure kalilan za su yi ta ci mutuncinsu. In danginta na kauye suka ce za su zo cewa ta ke ba ta gari, don ba ta da lokacinsu, har Innarta kuwa, amma tana mata aiken kudi da duk abin bukata, zuwa inda ta ke ne ba ta laminta. Wannan sai kawayenta matan ‘yan majalisa da matan ministoci, ba su da aiki sai maganin mata sababbin fitowa na suburban kudi kuma suna ganin alfanunsu tunda suna ganin yadda suke so daga mazajensu da dukiyoyinsu ba su da shamaki akan komai.

*****

Hajiya ta turo masu maganin gargajiya tun daga Maradi ta Nijar. Sun fara yi wa Amina magani a gida, har tsawon kwana goma. Amina dai ba ta mike ba, Ma’arouf ya sallame su suka tafi, aka samo wasu daga Kauran Namoda, suma sun buga irin tasu rawar ba nasara, amma dai bakin Amina da ya gicciye ya koma daidai. Su wadannan ya kara musu ihsani fiye da na baya. Haka kowa ya yi ta zuwa yana kwasar rabonsa daga wurare daban-daban har watanni biyu da Engnr. Ma’arouf ya diba wa masu maganin gargajiya akan Amina, don haka ya dakatar da zuwansu haka.

Tafiya ta kama shi zuwa Abuja a washegari ya bar Amina karkashin kulawar Laila.

Bayan tafiyarsa, Laila ta kira kawarta Nazi a waya.

“Wannan gawa-ta-ki-ramin ya dauko daga asibiti ya kawo min, uwarsa ta gaji da wahala balle ni, na kasa gane me yake nufi, in bar harkokin da ke gabana in zauna da ita ko ya ya? A pampers fa ta ke kashi da fitsari, ni ina zan iya wanke ta? Abinci sai an ba ta a baki, wanka sai an yi mata, brush sai an yi mata. Na rantse da Allah Nazi ba zan iya ba, ya ya zan yi ne?”

Kawartata ta tuntsire da dariya,

“Ki barta da masu aiki kawai, ki yi harkokin gabanki.”

“Masu aikin gidan nan duk maza ne, ga shi yarinyar mace ce (I’m confused), ki ba ni shawara.”

“Na ba ki ai kin ce ba haka ba, ina ruwanki da wani maza ne ko mata, ba biyansu ake su yi aikin ba? Kuma me za su dauka a jikin shanyayye? Ke ni rabu da ni ina da abin yi yau (container) ta za ta iso, taki sai jibi, mu wuni lafiya.”

Nazi ta kashe wayarta.

Laila ta tashi zuwa dakin Amina, wanda don matsayi yana kallon dakin barcin Babanta.

Ma’arouf yadda ya tsara gidansa na Bauchi babu (space) na karin mace. Katon falo ne shi da Aisha, ga dakinsa, ga na Aisha ga na yaran da za su haifa yana kallon dakin barcinsu. Kicin da store a kasan bene suke da wani katon falon a kasan. Sai bangaren ma’aikata a can waje kusa da (gate) din gidan.

Dakin Aisha shi ya zama na Laila, na yaran da ma can na Amina ne tun mahaifiyarta na raye, yanzu da ta baro gadon asibiti ma nan aka dawo da ita.

Laila ta daga ido tana kallon irin tsarin da aka yi wa dakin. Daki ne na ‘yan gata wanda aka kashewa dukiya ba kadan ba. Kamar na ‘ya’yan Turawa, ga wani gadon yara mai matattakala ga (teddy Bears) nan da can, ga (computer game), ga duk wani nau’in wani abu da yaro mai gata zai bukata. Fentin dakin da komai da ke cikinsa light blue and pink, toilet din kuwa ba a magana don kyau da ban sha’awa ko dakin dan shugaban kasa sai haka.

Ta jinjina kai, wani bakin ciki ya kule ta. Ta sa hannu ta shafi cikinta, ita har yau ko kyankyaso bai shiga ba da ta kawo su nan su ma. Ta daga kai ta dubi Amina a gadonta tana kwance. Kyakkyawar yarinya mai kama da ubanta kamar ya yi kaki ya tofar.

Tun safe ko ruwan shayi ba ta bata ba, ba ta canza mata (pampers) ba, ba ta dauko ta ta sanya ta a wheel-chair da Babanta ke sanya ta a ciki ya dan zagaya harabar gidan da ita ba, ko ta samu canjin iska.

Ta karasa gaban yarinyar tana kare mata kallo a yatsine.

“Ni ba zan iya wahalar da ubanki ke yi da ke ba, kakarki kanta ta gaji ta gudu shi ne ni za a hada ni da jangwam. Tashi ni su zo su wanke miki kashi.”

Ta danna kararrawar ma’aikatan gidan, nan da nan mutum biyu suka zo. Samari ne guda biyu masu share-share.

“Ku dauke ta ku kaita toilet ku yi mata wanka, ku cire mata (pampers) din tun dakin bai soma wari ba.”

Matasan biyu suka kalli juna kamar masu yin shawara, ta galla musu harara.

“Ko ba za ku yi ba ne?”

Da sauri suka ciccibo yarinyar, daya ya riko kai, daya ya riko kafafu suka yi toilet da ita, suka tube ta suka cire pampers za su soma wanke ta. Kamar an jefo shi, Ma’arouf ne ya shigo babu zato babu tsammanin Laila. Ya yi (missing flight) dinsa ne mai zuwa Abuja ba da son ransa ba.

Ashe da rabon zai ga bacin ran da bai taba shiga kwatankwacin sa ba.

Cikin matsanancin mamaki ya dubi Laila. Muryar sa kamarta wanda zai fashe da kuka.

“Maza balagaggu ki ka sa su tsiraita ‘ya ta haka Laila? ‘Yar tawa kwalli daya? Laila ko auren kiyayya ki ka yi da ni ba za ki iya taimakawa mara lafiya marainiya ba? Kina nufin su sanya hannu a (private part) din diya ta? Ban taba dukan mace ba, bana fata in fara a kanki. Ki je duniya ce, kuma in gaya miki wannan yarinyar ta fi min komai da duk abin da na mallaka a duniyar baki dayanta. Ke ma mace ce, kuma za ki haifa, ba ki san ya ya kaddara za ta yi da abin da ki ka haifa ba kina raye ko ba kya raye”

Kallo daya ya yi wa ma’aikatan suka saki (pampers) din da suke cirewa suka yi waje cike da addu’a a cikin zuciyarsu, kada Allah ya sa wannan ya zamo sanadin hanyar abincinsu. Su ma sun ji umarnin da aikin da aka sanya sun ‘odd’ to amma su me ye laifinsu? Salin-alin suka fice.

Laila ta rasa abin cewa, ba ta taba tsammanin zai dawo ba sai bayan kwana uku kamar yadda sukayi dashi. Ta kulla a zuciyarta ko ‘cangal’ ba za ta yi wa yarinyar ba har ya dawo. Maganganun da ya gasa mata ba su ta zata ba, ta fi zaton dan banzan duka daga gare shi in tayi la’akari da yadda ta lura yana son yarinyar.

Da sauri ya nade hannun riga ya wanke Amina, da kansa ya yi mata wanka da soso da sabulu mai kamshi, ya nado ta cikin shawul ya fito da ita. Har zuwa lokacin Laila a tsaye ta ke bakin (toilet) ta kasa ko kwakkwara na motsi, tana kallo ya shafe Amina da basilin, ya sanya mata sabuwar (pampers) da sababbin riga da siket masu kyau, sannan ya yi waya kicin a kawo masa ‘tea’ da ‘pankace’.

Da kansa ya rika bai wa Amina har ta koshi ta ture. Jiki ba kwari Laila ta wuce, don ganin yadda ya baiwa banza ajiyar ta ya yi kamar babu ita a dakin. Ya sumbaci Ameena a goshinta ya mayar da ita ya kwantar.

Ya fito ya zauna a daya daga ni’imtattun kujerun falon. Ya kai hannun damansa ya dafe kansa dake sara masa, ji ya yi dan son da ya soma yi wa Lailar na ‘decreasing gradually’ (raguwa a hankali). Zufa ta shiga karyo mishi da ya tuna kalamai na karshe na uwar Ameena.

“Ka kara kula da Ameena, ba don na raina kulawarka gare ta ba. She will need extra more!”

“Yes! She needs extra more Aisha, kuma in har ina raye, sannan kudi suna da amfani za ta samu kulawa Aisha. Da gaske kula da ‘ya mace sai mace. Na lura matar nan son kashe min Amina ta yi ko abinci ba ta bata ba har karfe daya na rana. Kuma ta sa maza su tozarta ta ba don Allah ya dawo da ni ba!”.

Ya san muddin ya gaya wa Hajiyan Ji-Kas wannan abin, cewa za ta yi za ta dawo ta kula da jikarta, bayan yanzun ta fara samun nutsuwa a gidan mijinta. Hankalinta ya tsaya wuri guda. Zai yi (finding solution) da kansa.

Babu wanda ya fado masa a rai a wannan lokacin sai abokinsa Dr. Usman Turaki. Classmate dinsa ne, tare suka yi sakandire a Science College Dawakin Tofa. Sun shaku sosai, yanayin karatu ya raba su. Kowa da jami’ar da ya wuce da fannin da ya zaba.

A take ya zakulo lambar Dr. Turaki ya danna masa kira. Ta jima tana kara kafin matarsa ta daga. Abin da ta ce shi ne, “Doctor is on call. A gida ya bar wayarsa”.

“O.k please, da ya dawo ki ce ya kira ni da wannan number din, Ma’arouf Ji-kas ne”.

“Insha Allahu”. Ta kara da cewa, “Sai Ji-kas, insha Allahu sai Ji-kas!”.

Murmushi ya yi, wanda bai shirya yinsa ba, wato matan aure ma ba a barsu a baya ba.

“Na gode. A gaida yara”

“Za su ji. Allah Ya tashi kafadun Amina!!!”.

Ji ya yi kamar ta yi masa addu’ar Allah ya sanya shi a aljannah. Wato komai na dan siyasa ba ya buya, kamar kasawa ake a faranti, kowa ya san matarsa ta lalle ta rasu, kuma yana da ‘ya mara lafiya.

<< Sanadin Kenan 13Sanadin Kenan 15 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×