Flashback
Amina da Goggonta, tare da Inna Zulai da Goggo ta kirawo don ta taya ta jin wannan almara, ko kuwa rashin kan-gado da Amina ta zo mata da shi.
“In ban da rashin kan-gado irin naki Amina, ina hankalina zai kwanta kina kwance wani muhalli daban da nawa, alhalin na san ban yi miki aure ba?” Goggo ta fada cike da damuwa, muryarta a sanyaye.
Goggo Zulai ta ce, “Da ma a ce aurenki zai yi ne don ki kula da diyar da ya fi armashin ji.”
Amina ta jefa wa Inna Zulai harara ta gefen ido, ganin tana tufka tana kara warware mata.
Amina ta gyara zama, “Goggo a kan aikina nake. Mu ne Proffessionals din da ake ‘hiring’ har gida mu kula da mai lalurar shanyewar barin jiki, ‘If a person can afford (idan mutum zai iya biya), sannan ban bar aikina na gwamnati ba, za a bada arona shekara daya ne in daina karbar albashin gwamnati in karbi na wadanda suka haye ni.
Ki kwantar da hankalinki Goggo, duk karshen sati zan taho gida in koma lahadi da yamma. Sannan fa akwai matar aure a gidan, kuma Goggo ai gidan gwamnati ya wuce duk yadda ki ke tsammani. Girmansa da fadinsa in ba kai ka nemi mutum ba babu abin da zai hada ku. Albashina za a ninka sau hudu Goggo, ba da jimawa ba Allah zai cika min burin da na ke da shi a kanki. Ki barni na yi aikina Goggo in har kin yarda a kan kanki cewa, kin ba ni tarbiyya yadda ya kamata.
Duk inda na shiga zan iya kula da kaina Goggo, zan nuna tarbiyyar da ki ka yi min da yardar Allah ba zan ba ki kunya ba. Hakan ba zai yiwu ba ba tare da na samu goyon baya da kwarin gwiwarki da albarkarki ba Goggo.
Shekaru bakwai ina karatu a jami’a, ba ki taba samun wani abin Allah-wadai daga gare ni ba sai don zan je aiki na shekara daya duk karshen sati ina tare da ke? Da zan yi hidimar kasa Gombe na tafi, duk ba ki nuna damuwa ba Goggo sai wannan?”
Goggo ta nisa, “Amina, mutane da halayensu canzawa suke kamar wahainiya in suka samu daular duniya. Ina tsoronki da shiga daular nan Amina, kada halayenki da tarbiyyarki su canza…”
Kamin Amina ta ce komai, Ilya ya yi sallama ya shigo. Amina ta gode Allah a zuciyarta, ta tabbata mai taya ta wannan battle (yakin) da wadannan dattijan masu tsoron duniya da abin da ke cikinta ya zo.
Ita ma tana yarda da abin da suke hangowa kawai tana kare kanta ne don ta yarda da kanta kuma tana son yin aikin ko burin da ta ke da shi a kan Goggo ya cika. Ba tana son yi don amfanin kanta ba ne, za ta yi ne don ta cika burin da ta ke da shi a kan Goggonta tun tana karama, wandadaga ita sai Ubangijinta sai suka san me take son yiwa Goggon.
Goggon da ba ta yi karatun zamani ba, amma ta tsaya (against all odds) ta cika mata burinta, har ga shi yau al’umma na amfana da ita, ya kuma zame mata hanyar samu na har abada, ya zama silar dogaro da kai a gare ta.
Kullum ta dauki albashi cikin asusunta sai ta tuna Babanta, sai ta ce, “Ina ma kana raye Baba? In rashin kudi ne ya sa ka sha wahalhalun da ka sha a rayuwarka, yau ga kudin na samar maka ba ni da abin da zan yi da su. To bari in yi ta tara su, in yaso Goggo ta amfana a karashen rayuwarta. Ni ba abinda zanyi dasu, Goggo ta min komai, tana kan yimin, Alhamdulillahi! Goggo is a blessing, from almighty Allah to Amina!!!”
Ilya ya shigo ya zauna a gefe, “Wai me ku ke tattaunawa ne ana ganina aka yi wani gumm?”
Goggo ba ta tanka ba, don ta san shi sarai, muddin ya ji a kan aikin wa ake wannan takaddamar Amina ta yi nasara akansu ta gama, don kaifin bakinsa wajen yarje mata sai ya fi na kowa.
Inna Zulai da bata san waye Ilya ba ta dan soma harhada masa abin da ta fahimta.
“Wai Gwamna Ji-kas ke son daukar Amina aiki, ta kula da diyarsa mai shanyayyen jiki, amma dole sai ta koma gidansa don ya rabo yarinyar da gadon asibiti, zai dinga ninka mata albashinta na asibiti sau hudu duk wata, Goggo ta kasa amin……”
Ilya ya kasa tsayawa ya ji karshen zancen, ya daka tsalle ya dire ya ce, “Tabdijan! To shi ne ku ka sa Dr. Amina a tsakiya kuna son yi mana sagegeduwa? To ke Amina yanzu wai me ki ke ce musu sun ki yarda? To ke Goggo in wannan damar ta wuce Amina anya kin yi wa kanki adalci ganin wahalar da ki ka ci kamin Amina ta zama likita? To wai ma in tambaye ku, ina ruwan Ji-kas da Amina in ya dauke ta aiki cikin gidansa? An ce maku ba shi da mata ne, ko manemin mata ne? To in SANADIN hakan ne Allah zai bai wa Amina miji sai ku sa kafa ku shure alherin Allah? Kai ban taba jin Goggo kin ba ni takaici irin na yau ba. Kin biye wa Inna Zulai kifin rijiya kuna ta bata yawun bakinku a kan alherin da ya zo har gida ya same ku.
Shin wai an ce muku Amina ita ce kadai likitar mataccen kashi a jihar Bauchi? Don kun samu Allah ya zabo ta cikin dubu ya ba ta shi ne za ku tsaya kuna kasa ta a kan faranti tana lallashinku kuna togewa? Dr. Amina, adana yawun bakinki zai yi miki amfani a gaba, bar ni da su. Ku gaya min duk abin da ku ke gujewa na shigar Dr. Amina gidan gwamnati…”
Amina ban da dariya ba abin da ta ke, Goggo da Inna sun kirne fuska sai jifansa suke da harara. Shi kuwa ya kai hannuwa kirji ya harde shi a dole jira yake su ba shi amsa.
Inna Zulai ta ce, “Sannu ubanmu. Matse bakunanmu in muka ji zafi sai mu gaya maka abin da muke gujewa din na zuwan mace babu aure wani waje ta kwana”.
Ilya ya gyara murya, ya dafa kirjinsa da hannun dama.
“A inda babu uba komai kankantar namiji uba ne. Don haka, ni Ilya uban Amina na amince diya ta Amina ta je aiki gidan Engineer Ji-kas. Da ta ke kwana a asibiti binta ku ke? Kai ni ba don kar a ce na yi rashin kunya ga iyaye ba, da sai in ce ban taba ganin gidadawan mutane irinku ba, ana kiranku gidan gwamnati kuna cewa ba za ku je ba……”
Goggo ta dauki kofi a gefenta ta jefa masa a baki. Inna Zulai da ta fi kusa da shi ludayi ta kai wa bakinsa ya kauce.
Amina cikin sassanyan muryarta ta ce, “Haba Yaya Ilya? Maimakon ka gyara duk ka kara damalmala al’amarin.
Goggo ku yi hakuri ni dai na gaya muku a kan aiki na nake neman amincewar ku inje gidan gwamna, da kuma wani kebantaccen uzuri da nake da shi a kan ki Goggo. Amma in ba ki amince ba na hakura Goggo, zan je gobe in fada wa Dr. Turaki ban samu amincewarki ba.”
Jikin Goggo ya yi sanyi, ta san Aminanta har ga Allah ba ta da kwadayi. Ba ta nemi komai ta rasa ba, Amina gudun maza ta ke ba son kai kanta gare su ba. Amina na son aikinta fiye da komai a rayuwarta, a cewarta yana sanya mata nutsuwa, yana sa ta nishadi, yana sa ta farin ciki, yana raba ta da damuwa. Duk ta yarda da wannan, kawai burinta a yanzu Amina ta yi aure shi ne kwanciyar hankalinta, ba wai ba ta sonta da aikinta ba ne. Kuma ta yarda Amina yanzu ba ta korar masu sonta, sune suka dauke kafa.
Goggo ta nisa ta dubi Amina, Zulai da Ilya da duk suka zuba mata ido. Kowa ta bakinta yake son ji don a yanke maganar haka kowa ya huta.
“Amina, na yarda ki je aikin ‘yar gwamna, amma a bisa alkawari guda daya”.
Amina ta dago da nutsuwa a kan fuskarta.
“Wane alkawari ne Goggo? Insha Allahu zan cika miki shi muddin bai fi karfina ba”.
“Ki je ki yi aikin na amince, amma idan kafin ki gama Allah ya kawo miki mijin aure za ki bar aikin ki yi aurenki. In ya so in mijin ya amince sai ki ci gaba”.
Amina ta yi murmushi har gefen kumatunta biyu suka lotsa.
“Ai a bisa wannan alkawarin muke Goggo har gobe. Wallahi ba ni nake korarsu ba, su suke korar kansu. Amma na kara yi miki wannan alkawarin, ko yau na fara aikin gobe mijin ya zo, zan bar aikin na yi aure, ko wane ne shi.”
Ilya ya ce, “A’ah Dr. Amina daina cewa ko wane ne, idan kuturu ya zo ko gyartai ba ruwan Goggo fa, ke za ki zauna da shi.”
Goggo ba ta san sanda ta yi dariya ba, duk zukatansu suka yi dadi, don ba sa son ganinta cikin damuwa ko ya ya, walwalarta ita ce tasu.
Inna Zulai ta yi musu sallama, ta tashi tana fadin, “Kin bari sun kalallame ki da dadin bakinsu Goggo, ni na yi nan, tunda ko na sake cewa komai ma ba tasiri zai yi ba”.
Ilya ya ce, “Haka ne Hajiya Inna. Gara ki adana yawun bakinki. Sai Ji-kas! Wallahi sai Ji-kas!! Insha Allahu sai Ji-kas!!! Ba mu fada a banza ba, ba mu sha rana a banza ba, ga shi tun ba a je ko’ina ba ni da Amina mu za mu fara shan inuwar gwamnatin Jikas, mu ne har cikin gidan gwamna.”
Washegari Amina da kwarin gwiwarta ta doshi ofishin (consultant) dinta Dr. Usman Turaki.
Sai dai kash! Ofishin Turaki a kulle. Wani masinja ke gaya mata ai Dr. Turaki an ba shi kwamishinan lafiya ya bar asibitin, shi da asibiti sai nan da shekaru hudu.
Allah ya so tana da lambar wayarsa, a lokacin waya ta fara cika duniya. Duk wani babban ma’aikaci yana da ita.
Ta kira shi akan ya kwatanta mata sabon ofishinsa sai ya ce zai turo direba ya kai ta yanzun nan.
A wata ni’imtacciyar mota da Amina ba ta taba shiga irinta ba aka kai ta (Ministry of health) inda ofis din kwamishina Turaki yake.
Amina ba ta bi dogon layin da ake bi wajen ganin kwamishinan ba, kai tsaye aka sadar da ita gare shi.
Amina ta shiga da sallama cikin nutsuwarta kamar yadda ta ke a kullum, irin wadda zuzzurfan ilimin boko ke gadar wa mai shi.
Ta gaishe shi, ta kuma yi masa murnar sabuwar kujerarsa. Ya yi godiya sannan ya tambaye ta ta yi shawarar? Iyayenta sun amince?
Amina ta ce, “Goggo ta amince, amma a bisa sharadin in miji ya zo kafin lokacin kwangilar ya cika zan bar aikin in yi aure.”
Dr. Turaki ya yi murmushi mai kama da dariya, yadda tayi maganar ne ya bashi dariya kamar auta kamar kuma ‘yar fari,
“That’s good.”
Yace da ita.
Wani tunani ya darsu a zuciyarsa a kan Ma’arouf da Amina, amma da ya tuna halin mutumin nasa, sai ya yi gaggawar goge tunanin daga zuciyarsa ya janyo na abin da ya tara su.
“Ki yi parking yau, duk da mai girma gwamna ya gaya min ba kya bukatar daukar komai, amma mutum ba ya rasa abin amfaninsa. Kayan sanyawa ne ba kya bukatarsu, yau za a maido takwararki gidan daga kauyen Ji-kas.
Don Allah Amina ki kula da ita yadda ya kamata. As a doctor na san ba kya bukatar a tuna miki yadda za ki yi da (patient) dinki. But wannan ‘patient’ din ‘need extra more’ saboda marainiya ce. Sannan lafiyarta ‘matters alot to her Dad.’
Zai nutsu ne kadai wajen aikin al’ummarsa in ya tabbatar Amina tana a kyakkyawan hannu, kuma tana cikin koshin lafiya koda bata taka kasa da kafafuwanta.
Daga yau zan bar zama jakada a tsakaninku, kai tsaye za ki dinga magana da ‘His Excellency’ in kuna bukatar wani abu ko sanar da shi wani abu na ci gaba ko akasin haka da ya danganci lafiyar diyarsa. Be the best doctor and best physiotherapist as we know. Kawo wayarki in sanya miki lambar tasa…”
Amina ta miqa masa, ya sanya ta yi ‘saving’. A ranta ta san ta karba ne kawai amma ba za ta taba iya kiran Ma’arouf Ji-kas ba! Wani kwayan mutum guda daya da ko sunansa bata taba kwatanta fada ko da a zuciyarta ba, shi din dai, (Turakin), za ta ci gaba da bai wa jakadancin ko yana so ko ba ya so.
A sanyaye ta ce, “Sunan yarinyar AMINA?”
Dr. Usman ya amsa, “Eh, AMINA ‘yar AMINA koh?”
Duk suka yi murmushi,
“Allah ya ba ta lafiya”.
Ya amsa, “Ameen.
Allah kuma ya sa ta hannunki za ta samu lafiyar. Ina addu’ar tukwicin hakan ya zamo naki ne Dr. Amina”
Ta yi murmushi.
Har gida direban ya kawo ta, ya kuma ce in ta gama shiryawa gobe ta kira shi, shi zai zo ya shigar da ita gidan Gwamnati.