Hajiya da Ameena sun dade da yin bacci, har sun soma minshari. Sun kashe fitilu baccin gajiya kawai suke yi.
Ya kai hannu ya kunna wutar dakin, nan da nan dakin ya gauraye da haske. Da sauri ya isa gaban gadon ya russuna da gwiwoyinsa ya kama hannun Amina yana tattaba ta kamar wani abin ne ya same su na cutarwa.
Hajiya ta bude ido ta ganshi cikin wani yanayi da ta kasa fassarawa. Ya kuma ki bude baki ya yi magana, so yake ya ce da ita.
“Wace irin kara da kiyashi ki ka aura min haka ne Hajiya? Wace irin annobar mace ce haka ki ka kawo min cikin rayuwa ta?”
Hajiya ta yi gyaran murya, don ta lura ba zai yi magana ba. Yana cikin bacin rai bayyananne wanda ta gane ba na komai ba ne, na masaukin da aka yi musu ne.
Ta ce, “Ka zo ka kunna mana haske muna cikin bacci, ko me ye ba za a yi masa lamunin gobe da safe ba? Kai kanka a gajiye ka ke, ka je ka kwanta a bar wa gobe in Allah ya kai mu.”
Sai kawai ya mike ya ciccibi Amina, ya kuma samu bakinsa ya bude.
“Taso Hajiya mu je.”
“Mu je ina a wannan dare? Ka yi hakuri ka barmu mu kwanta tunda dare ya yi, ni gobe zan juya Ji-kas, amma ina tantamar in ba da Amina zan juya ba. Don ni ban ga wata likita da ka yi min zance ba.”
“Amma kin ce min kwana uku za ki yi, me ya sa ki ka canza shawara? In ba ranki ne ya baci ba Hajiya, don Allah ki taso mu je na ajiye ku a inda hankalina zai kwanta. Ina jin motsinku. Kwata-kwata wannan ginin na baki ne, bakin ma na nesa.”
“Ai mu ma bakin ne, don kuwa gobe za mu juya.”
Ya gama fahimtar bacin ran Hajiya a kan kamilalliyar fuskarta.
“Idan har za ki juya gobe Hajiya, sai in tare za ku juya Ji-kas.”
Hajiya ta tashi ta zauna sosai ta gyara zaninta.
“Ni da wa kenan?”
“Ita waccan yarinyar da ki ka aura mini. Ai na gaya miki auren ya yi gaggawa, daga ni har ke har Baba Liman ba mu san halinta ba, amma da yake kuna taya ni son siyasar da nake so ku ka kasa yin bincike akanta…. Don haka dukkanmu ke da laifi wajen aurenta…?”
“Ya isa! Ya isa!!”
Hajiya ta dakatar da shi, akalla ta samu ya amayar mata da bacin ransa yau. Ta ji sanyi a ranta, shi ma ko yayane ta san ya ji sanyi.
“Ka yi mata uzuri, cikin mulki ta fada. Kuma ni ban raina inda aka ajiye ni ba. Me ye laifin wajen nan saboda Allah? Yi hakuri ka yafe mata in don ni ce, don Allah don Annabi.”
“Zan yafe mata only in kin taso mun koma cikin gida….”
“Ba ka tausaya min doguwar tafiyar nan? Da nisa fa!”
“Hajiya, bari to in kai Amina sai in dawo in dauke ki.”
Hajiya ta yi dariya tana saukowa daga gadon, tasan kadan da aikinsa.
“Me ya yi zafi? Mu je in hakan shi ne kwanciyar hankalinka. Amma tafiya ta gobe ba makawa, kuma tare da Amina.”
Bai ce komai ba, farin cikinsa Hajiya ta huce tunda har ta yarda ta biyo shi. Ya santa in ta yi fushi ba dama, shi kansa ya yi mamakin rashin daukar zafinta a kan Laila, don ba ta daukar raini. A ransa ya ce, ‘Watakila don ita ta kawo abarta ne, ba ta da bakin korafi.’
Dakin da ke kallon nasa ya bude musu. Wani hadadden bedroom na tashin hankali, komai da ke cikin dakin ‘Royal colour’ ne. Don haka da ya kunna fitilar dakin ya wadata da haske, sai ya zama kamar dakin shugaban kasa. Asali dakin shi ne nasa, ya barshi ne ya dauki ‘smart’ din (British bedroom) don ba ya son abu mai daukar idanu.
Hajiya ta ce, “A wannan ranar za mu yi bacci?”
Ya karasa ya shimfidar da Amina a tsakiyar luntsumemen gadon, ya danna wani dan abu jikin gadon, fitilu shudaye na bacci suka maye gurbin masu hasken. Hajiya ta karasa ta kwanta kusa da Amina. Sai yanzu ne ya ji hankalinsa ya kwanta, wata nutsuwa ta shige shi. Suka yi sallama da Hajiya, ya juya ya fita ya jawo musu kofar.
Ya shige nasa dakin ya rufe da mukulli, maimakon kwanciya bacci, wanka ya yi sannan ya daura alwala ya yi nafilfili masu dama, ya shigar da bukatunsa da godiyarsa ga Allah a bisa wannan jagoranci da Ya ba shi, ba don ya fi kowa ba sai don Ya zabe shi. Ya roke shi Ya ba shi ikon sauke hakkin talakawa da ke kansa, Ya ba wa Amina lafiya, Ya kara wa iyayensa tsawon rai su ci gaba da zama sanyin idaniyarsa, kuma fitilarsa masu haska masa rayuwa da ankarar da shi a duk lokacin da zai yi kuskure, da kauna ta fisabilillahi gare shi, wadda babu algus ko tasirin abin hannunsa a cikinta wannan sai iyaye.
Ya yarda wanda duk zai so shi, ko ya girmama shi, ko ya rabe shi a wannan lokacin zai yi ne saboda dukiyar al’umma da ke hannunsa, ban da Hajiya da Baba. Ya ya kuwa za a yi ya bari wani ya nuna su da dan yatsa bai karya dan yatsan ba? Balle wata banza Laila, wadda ba don Hajiya ta nema mata afuwa da kanta ba, yau sai ta bar gidan gwamnati inya so a ce ya yi auren siyasar. Sai me? Ta ci albarkacin wadda ta fi kowa alfarma a rayuwarsa.
Da wadannan tunane-tunanen barci ya dauke shi, amma rashin samun barcin da wuri bai sa ya kasa tashi sallar asuba a kan lokaci ba. Ma’arouf Ji-kas kenan.
WASHEGARI
Wajen karfe tara na safe ya fito a shirye, ko karin kumallo bai yi ba, Laila ta kai masa har daki ko kalla bai yi ba.
Ta ce, “Ina kwana?”
Ya ce, “Lafiya kalau.”
Ya wuce ta ita da abincin nata.
Ya yi sallama ya murda dakin Hajiya, ta amsa, ya sanya kai ya shiga. Ya same ta da jaka a gaba da lullubinta na tafiya, har da takalminta a kafarta. Ta shirya Amina tsaf har hijabi karami ta sanya mata, daga ganinsu za ka gane fitowarsa kawai suke jira.
“Hajiya rigima!”
Ya fada ciki-ciki. Ya yi kamar bai gane ba, cikin taushin murya ta lallashi ya ce,
“Hajiya karin kumallonmu ya kammala, mu uku na sa a shiryawa ni da ke da Aminata.”
Muryar tashi ta fi kama da ta lallashi, a wani bangare nuna tsantsar kulawa ga wanda ake matukar kauna. Idan Hajiya ta ki dandana gidan gwamnati mene ne amfaninsa gare shi? Wannan ya nuna har yanzu tana fushi da abin da matarsa ta yi mata, to shi me ye nasa a ciki? An ce ya yi aure dole, ya yi babu bata lokaci, babu nazari, babu bincike. In Hajiya ta ki zaman gidansa saboda abin da Laila ta yi mata ba ya nan ba ta yi masa adalci ba.
Duk da haka ya ji ya gani ya dauki laifin, fatansa ta amince ta zauna kamar yadda ta yi niyya da farko, kuma ta bar Amina da likiciyar da ya daukar mata ta ji da kanta da kananan lalurorinta na ciwuwwukan da girma ke haddasawa da nauyin mijinta. Ya kuma fi son duk sanda ya shigo ko zai fita ya ga Amina cikin gidan, ya san halin da ta ke ciki kullum, ko da babu ci gaba a lafiyarta. Ganinta da sanin kowanne motsinta kusa da shi shi ne kwanciyar hankalinsa.
Hajiya ta ce, “Toh! Sabon salo, namiji da suyar naman sunan matarsa. Mu je mu ci sai ka kira min Akilu mu kama hanya.”
Ya yi dariyar abin da ta ce. Waya ya yi wa amintaccen kukunsa. Nan da nan ya zo ya shirya komai a gabansu a kasa kan kilishi, saboda Hajiya da Amina ba masu hawa tebir ba ne.
Da kansa ya zuba wa Hajiya romon bindin saniya da ya dahu ya yi lugub. Ya hada mata shayi mai dadi, ya zuba mata gasassar hanta da koda, ya gutsira mata biredi mai laushi. Hajiya ta soma ci sai ya koma kan Amina a baki ya ba ta ‘tea’ da ‘cake’, don abin da ta fi ci kenan. Ya zuba romon kaza a dan ‘bowl’ yana ba ta da cokali, sai da ta ture sannan ya ci nasa.
Da suka kammala ya mike ya fiddo waya zai yi magana, Hajiya ta ce,
“Akilun za ka kirawo mana?”
Nan da nan dabara ta fado masa.
“Ni ba Akilu zan kirawo ba, Dr. Turaki zan kirawo, wanda ya kawo likitar da za ta dinga kula da Amina. Yau muka yi da shi za ta zo.”
Hajiya ta yi shiru, a ranta ta ce, ‘na ga mai sa ni in bar Amina a nan a wulakanta min ita.’
Ya kai wayar kunnensa suka yi magana da Kwamishinan nasa.
“Tura address din wayar Akilu ba wayata ba ya je yanzu ya taho da ita.”
Ya kashe wayar ya sanya a aljihu. Ya dubi agogon hannunsa na danyar azurfa karfe goma saura kwata, goma zai shiga office wanda ke nan cikin gidan nasa. Ba zai iya tsayawa jiran isowar likitar ba.
Ya zauna yana fuskantar Hajiya cikin lallashi da taushin murya.
“Hajiya abin da ya sa nake so ki zauna tsawon sati guda, don ki nazarci likitar Amina ne, don ni yanzu mata tsoro suke ba ni. Duk da Turaki ya ba ni tabbacin nutsuwarta dari bisa dari, akwai bukatar ki dan sa mata ido irin na manya cikin hikima, ki kuma ganar da ita abubuwan da suka shafi Amina, kamar abincin da ta fi so, abin da ta ke so da wanda ba ta so. Abubuwan da ta ke yi a da can kamin ta samu lalura da sauransu. Ki kuma nazarci cewa, za ki iya bar mata amanar Amina ko a’ah?
Shi ya sa nake so ku zauna tare na akalla sati guda, na kuma riga na fada wa Baba Liman, ya ce ya yi miki izini.”
Hajiya ta nisa, “Shi kenan zan zauna.”
Ya sumbaci hannun Hajiyar ya mike, “Ni zan wuce office sai azahar zan shigo.”
“A dawo lafiya.”
Ya juya zai fita ya ji Hajiya na tambaya, “In ce ko ba kedara ba ce?”
Ya dan daga kafada, “Ba na ce ba, amma na san ba zai kawo kabila ba, ki yarda da shi, shi ne babban abokina na kuruciya, ba zai kawo wadda za ta cuci Amina ba. Na yarda da shi Hajiya.”
“Shi kenan, je ka za mu dan kwanta kafin ta zo. Amma wane daki ka tanadar musu su zauna in na tafi? ka dan nesanta su da kai saboda matarka, in har da gaske ka yarda ba za ta cuci Amina ba, ka dan raba su da nan.”
“Ba matsala Hajiya, a nan (down stairs) dakin yara yake, sai su zauna a ciki. Zan sanya a zuba musu komai da za su bukata. Amma yanzu ku zauna a nan din tare zuwa tafiyarki. Kwamishina ya tura wa Akilu adireshinta ya tafi ya dauko ta.”
“Shi ke nan, je ka kada ka bar jama’a na jiranka don kai ne shugaba, babu dadi sam”
“Toh Hajiya”
Ya cika hannun Amina mai lafiya, ya fita.
Bai dade da fita ba Laila ta yi sallama, bayan ta ma’aikata ne da manyan ‘trays’ suka shigo tare.
“Hajiya ga (breakfast)”
“Ai mun karya Laila.”
Ta juya ta kalli kwanukan ko kwashewa ba a yi ba.
Ta mike, cike da haushi, wato ya ki cin nata yazo nan ya ci da uwarsa da ‘yarsa, ta daure tace
“Mu wuni lafiya to, ina da taro ne da hukumar makarantun firamare, ban san lokacin da zan shigo ba.”
A ranta tana fadin, ‘Tunda na ji kamshin mutuwa a kanki tsohuwar nan gara in lallaba ki mu rabu lafiya.’
Hajiya ta ce, “A dawo lafiya”
Tana fita Hajiya ta ja Amina suka kwanta. Ma’aikata suka fita da komai, suka gyara wajen, suka fita su ma.
Babi Na Takwas