Skip to content
Part 18 of 50 in the Series Sanadin Kenan by Sumayyah Abdulkadir Takori

Amina ta shiga gida da sallama, ta tadda Goggo da Ilya suna aikin nasu na kirga ciniki.

Talatu mai aikin Goggo ta karbi katuwar jakar hannunta, wadda duka littattafai ne a ciki da farar rigarta ta likitoci sakale a hannunta na hagu.

Ilya ya yi mata sannu da zuwa cikin karramawa don shi fa yanzu Amina ta zama uwardakinsa, tunda albarkacinta ya tabbata watarana sai ya ga Ji-kas ido da ido, sai ya taka kafarsa cikin gidansa ko da sunan kai wa Dr. Amina sako ne. Yana rokon Allah ya cika masa wannan burin.

Ta zauna ta na fadin “Wash, na gaji wallahi.”

Goggo ta ce, “Ai shi aikin sa-kai haka yake.”

Ilya ya yi magana cikin muryar rashin jin dadi.

“Goggo, yaushe za ki daina yabawa Amina magana mara dadi ne a duk sanda ta fada miki wani abu da ya shafi aikinta? Mijin nan fa ba ita ta hana kanta ba, Allah ne bai kawo ba. Shi auren ina ce lokaci ne? Koda a da Amina ta hana kanta aure ni shaida ne akan cewa banda yanzu. Don Allah Goggo ki dinga tausasa kalamanki gare ta.”

Goggo tana mamakin soyayyar da Ilya ke yi wa Ma’arouf  Habibou Ji-kas, alhalin shi bai sanshi ba, shi ma bai sanshi ba. Bai san yana yi ba. Ga shi har ta shafi Amina. Ta lura tun ranar da aka yi zancen aikin Amina a gidan Ji-kas ta fahimci Ilya wani girma da kulawa yake baiwa Amina na musamman, ada kuwa ai kullum si an raba su fada, ta kuma san ba don ya ba shi komai ba ne, fisabilillahi yake kaunarsa, irin kauna ta talakawa ga wasu tsirarun shuwagabanninsu.

Ta nisa, ta dubi Aminar da idon rahma.

“Sannu, ki je ki kwanta ki huta, akwai farfesun kaza da gurasa da muka yi na zuba miki cikin flask dinki in kin tashi ci.”

Amina ta ce, “To Goggo.”

Ta wuce su, Ilya ya ji dadi har ransa.

Da daddare Amina na tsitstsince abubuwan amfaninta, ta gaya wa Goggo gobe ne tafiyar, direba zai zo ya dauke ta.

Goggo Hauwa ta ji wata irin kewar Amina tazo ta lullube ta kamar garin za su raba bakidaya, koko shekara za ta yi ba ta ganta ba. Amma ta daure ba ta bari ta gane ba, don ta san halin Amina sai ta ce ta fasa. Ta taya Amina harhada wasu abubuwan nata, ta zuge a jaka. Amina ke ba ta labari suna aikin wai an ce kada ta dauki kayan sanyawa.

Goggo ta ce,

“Dauki abinki, idan kuma wando da riga zasu baki fa? Kwashi zannuwanki kinji na gaya miki.”

Amina ta yi dariya, tana nun ke zannuwanki tana jerawa a jaka ta ce, “Goben da Ilya za mu tafi ya ga waje, ko ya ji dadi.”

Goggo bata ko amsa ba, ita kadai tasan me take ji a zuciyar nan tata mai cike taf! Da kewar Amina. 

Government House Bauchi

Tun yammacin jiya Akilu direban Ma’arouf na Bauchi ya dauko Hajiya Saude da jikanyarta Amina daga kauyen Ji-kas zuwa gidan gwamnati. Zuwan Hajiya na farko kenan tun bayan tarewarsu. Tun daga bakin gate ganin irin tsaron da gidan ke da shi da irin rundunar sojojin da suke wucewa kafin su shiga ciki, Hajiya Saude ta rika tasbihi a zuciyarta in ta tuna wai duka don kare lafiyar danta kwaya daya suke wannan zaman. Da aka shiga da su falo na farko, wanda daga shi za su bi har su tadda sassan masu gidan Hajiya Saude kasa daure farin cikinta ta yi, sai da ta yi hawaye, ta share da habar zaninta. Tana ganin gidan Ma’arouf na Fati Mu’azu karshen daular duniya, ashe gaba da gabanta wai aljani ya taka wuta.

Tafiya kamar ba za ta kare ba, har dai suka iso bangaren Laila. Tana hakimce cikin kujerar kasaita tana waya. ta ci ado har ta gaji, ta dace kwarai da a kira ta matar gwamna, don ko can baya ita kyakkyawa ce, ma’abociyar ado, balle yanzu da ta ke kan kololuwar ni’imar rayuwa.

Shigowar Hajiya da Amina, Akilu na turo ta cikin wheel chair dinta bai sa ta katse hirar da ta ke yi a waya ba, ci gaba ta yi har tana kyakyala dariya, ta dai yi wa Hajiya nuni da kujerar zama da hannunta, nufinta ta zauna, ita kuma ta ci gaba da hira da kawarta, tana gaya mata at last ya yarda ya amince da kafa ‘Family Support Programme’ din, sauransu fidda tsare-tsare su wawaso miliyoyi na tashin hankali.

Hajiya ba ta sa wa hirarta kunne ba, sai dan tabuwa da zuciyarta ta yi ganin irin karbar da Laila ta yi musu. Ko kallon Amina ba ta yi ba har Hajiya ta fiddo ta daga ‘Wheel chair’, ta kwantar a kujera bacci ya dauke ta. Ta zauna ta yi tagumi tana jiranta ta gama. Sai da Laila ta kwashe minti talatin tana hira, sannan suka yi sallama ta ajiye wayarta a gefe. Ta dubi Hajiya tana dariya.

“A’ah mutanen Ji-kas ne, sai yau? Har mun so mu yi fushi tunda muka tare ba ku zo ba.”

Hajiya ta yi murmushi fuskarta ta dan canza, da gani zuciyarta an taba ta.

“To ga mu nan dai sai yau Allah ya nufa. Masha Allahu da sabon muhalli, Allah ya sanya albarka.”

“Amin-amin Hajiya, bari a kawo muku abinci, wanne iri ku ke so?”

Mamaki yana kara shigar Hajiya, ta ce, “Kin ganmu nan a koshe muke. Har a cikin mota mun yo guzurin abinci. Nuna min bayan gida dai in yi alwala, in yi wa Aminatu wanka.”

Laila ko a jikinta, ta danna kararrawa wani ma’aikaci ya shigo sanye da (uniform) dinsu na ma’aikata, ya tsuguna gaban Laila.

“Mukullin dakin saukar baki na farko yana hannunka ne?”

“A’ah, yana hannun Amos shi ke kula da bangaren saukar baki.”

“To ku je da Hajiya da shi Amos din ya bude muku ka shigar da kayansu.”

Laila na kallon Hajiya tana ciccibar Amina da ke bacci, tana kici-kicin sanya ta a ‘wheel chair’ kamar za ta fadi sabida jikin girma da nauyin yarinyar. Amma ko ta motsa daga inda ta ke zaune balle ta taimaka mata. Ma’aikacin ya kama ‘wheel chair’ din zai tura, Hajiya ta dakatar da shi.

“Barshi ni zan tura.”

Sai ya dauko mata jakar kayanta ya shiga gaba suka bi shi a baya.

Bangaren saukar bakin daga can wajen ginin da Laila ta ke ne. Tsararrun ‘apartment’ ne iri daya sun fi guda hamsin. Amma in aka kwatanta shi da ginin da Laila ta ke ciki kamar gida ne da baskwatansa.

Ma’aikacin ya yi wa Hajiya sallama ta fita, bayan ya nuna mata wayar da za ta kira in tana bukatar wani abu. Hajiya kasa shiga bandakin ta yi, ta zauna bakin gado ta zuba tagumi tana mamaki, ba wai don ta raina muhallin da aka kawo ta ba, a’ah, mamakin canzawar Laila ta ke farat daya kamar wadda tunda aka haife ta cikin rayuwar da ta ke kenan. Ba ta yi mamakin karbar da ta yi musu ba, tunda da ma masu iya magana sun ce, da ka zama uwar Gwamna gara ka haifi matar Gwamna. 

Amma anya fisabilillahi ita din ta cancanci tarbar da ta yi mata? Ina ta kuskuro a kan yarinyar nan, da me ta rage ta tun bayan da ta hada aurenta da Ma’arouf? Na kulawar suruka ga surukarta? Da ta yi mata wannan tarbar da bakon da ba ka sani ba za ka yi wa? Lallai mulki akwai giya a cikinsa.

Ta tuno rayuwarta da Aisha Babar Amina, wadda nata dakin shine masaukinta, sai hawaye suka sakko mata shar-shar! Ta kwance habar zaninta tana sharewa. Ba za ta iya tafiya ta bar Amina a hannun wannan yarinyar ba, sai dai Baba Liman ya hakura da auren nata.

Da wannan ta mike tsaye, sai ta ji jiri ya kwashe ta ya mayas, ta koma ta zauna da sauri tana fadin.

“Hasbunallahu wa ni’imal wakeel’.

Har ta ji komai na jikinta ya koma daidai.

Ta shiga bayin ta dauro alwala ta samu wuri ta rama sallolinta a zaune, don ta kasa tsayuwar sabida bacin rai da motsuwar zuciya.

Ta bude jakarta karama ta dauko (panadol) ta sha da ruwan da ke cikin firij. Bayan mintina goma ta ji karfin jikinta ya dawo, ta dauki Amina ta shiga bayi da ita, ta hada ruwa mai dumi ta tsarkake ta ta yi mata wanka fes, ta fito da ita ta shafe ta da mai, ta sanya mata kaya da sabuwar pampas, ta ja ta jikinta suka kwanta a gado, don huta gajiyar zaman mota da suka kwaso. Tana ta jan carbinta tana hailala. Fadi take cikin zuciyarta. Allah ya sa ba zaben tumun dare ta yi wa Ma’arouf ba, don ta san halinsa kowanne hali yake ciki ba zai fada mata yana da damuwa a kan kowa ba, balle iyalinsa. Sai dai ita ta ganewa idanunta.

Karfe goma na dare ya shigo gidan a matukar gajiye. Ko ruwa bai sha ba, ko zama baiyi ba don ya huta, sabida zuwan Hajiya da Amina da ya tura a dauko su yau yana makale a ransa.

Laila tuni ta kule a (bedroom) dinta ko dai ba ta yi bacci ba, to ta kashe fitila ta yi linkim a gadonta na alfarma, shigowarsa kawai ta ke jira. Da shigarsa falo ko zama a kujera bai yi ba ya kunna wayarsa ya kira Hajiya, shi kansa ya san da kyar zai same ta a waya, don da ta yi isha’i ta ke kashewa sai gobe kuma.

Ya kira sau uku tana kashe. Ya shiga sauran dakunan da falon ya kunsa wanda dukkansu (self-content) ne, bai gansu a ciki ba.

Ya kira direban da ya dauko sun. Da sauri Akilu ya daga.

“Ka dauko Hajiya da Amina kuwa?”

“Ranka ya dade na dauko su tun da yamma, na kawo su har falon uwargida.”

“To ya ya aka yi ban gansu ba? Duka dakunan nan, na sassan nan ba sa cikinsu.”

Akilu ya rasa me zai ce? Shi dai ya san ya damka su hannun uwargida, daga nan kuma ya fita, ya gama aikinsa.

Jin Akilu bai ba shi amsa ba, ya gane ba shi da abin ce masa, tunda ya ce ya damka su a hannun matarsa.

Shi sai a lokacin ma ya tuno da ita, sau tari yana mancewa ya ajiye mace a gidansa, sabida amfanin Laila kalilan ne a cikin rayuwarsa. Ita kanta ta san hakan, amma ba ta damuwa, to saboda Allah me zai dame ta?

Duk wani burin ‘ya mace ta same shi a rayuwarta har wanda ba ta taba mafarki ba. Me ye nata na shisshigi a inda ya nuna ba ya bukatarta?

Da sauri ya juya ya shiga dakin nata. Ta kashe mai haske ta bar mai duhu, koriya sharr, ta yi linkim cikin ni’imtaccen bargo a dankareren gadonta. Ita kanta katifar gadon tausa ta ke yi mata.

Ya kunna fitila, dakin ya mamaye da haske. Ta dan fiddo kanta daga cikin bargon tana kallonsa, a zuciyart ta ce, “Yau ina da amfani, ga shi kuma ba za a samu abin da ake nema ba, hutawa nake son yi’. Don ita har ga Allah ta manta da wata Hajiya balle rami-ta-ki-gawar ‘yarsa.

Akasi ga tunaninta, abin da ya tambaye ta daban ne, cewa ya yi,

“Ina Hajiya da Amina?”

Ta dan baiwa kwakwalwarta aiki na wurin gani, aikin  tuno mata wadanda yake nufi da gaggawa. A take ta tuno mata, ta ji dan darr! Amma ta dake ta ce, 

“Na sa a raka su ‘guest house.”

Ma’arouf ya tsura mata ido, ya kasa ko qiftawa, idanun nasa har wani kankancewa suke yi. Ji yake kamar ya fizgo ta daga gadon ya jefa ta waje ta taga. Ya bude baki zai yi magana ya kasa, babban burinsa a rayuwa kada ya daki mace har karshen rayuwarsa. Albarkacin uwar data kawoshi duniya ta raineshi har ya zama abinda ya zama. Amma a yau ba abin da yake son yi  fiye da hakan.

Hannayensa biyu har kyarma suke yi cike da kai kayi suna so ya basu damar yin abinda suke so, bai san sanda ya isa inda ta ke ba ya damko wuyan rigarta ya mikar da ita ba. Idanuwan Laila duk suka yo waje, domin shaka ce ba ta wasa ba, ta namijin da ya amsa sunan namiji.

Saki uku yake so ya furta mata yana danne harshensa, yana lallashin zuciyarsa.

Laila ta soma kakari tana rokonsa ya cika ta, muryar ba ta fita.

“Kada ka yi kisa Ma’arouf, a’ah!” Wani bangare na zuciyarsa ke lallashinsa.

Ya cika ta ta fadi a wajen rikicaaaa! Rike da wuyanta tana ta tari kamar wadda ta shaki tiyagas don wahala.

Da sauri ya juya ya fita daga dakin, shi bai ma san ina ne hanyar sassan bakin ba. Jefa kafa kawai yakeyi, daya fara nutsuwa ne ya kira Amos a waya yace ya zo ya raka shi inda aka kai mahaifiyarsa.

Bookmark
ClosePlease login

No account yet? Register

Rate the story.

Average: 5 / 5. Rating: 4

As you found it interesting...

Follow us to see more!

<< Sanadin Kenan 17Sanadin Kenan 19 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
3
Free daily stories remaining!
×