Skip to content
Part 28 of 50 in the Series Sanadin Kenan by Sumayyah Abdulkadir Takori

Ga abin da ya ce da ubangidan nasa, a lokacin da ya zo masa da bukatarsa na ya shige masa gaba ya auri likita Amina.

Turaki bai yi masa shakiyanci ba, ko tuna masa yadda suka yi a baya, ko don yanzu ubangidansa ne? Oho! Sabanin da kafin ya hau kujerar Gwamna sanda suke abokan makaranta. Da hannu bibiyu ya karbi maganar, amma in ya tuna yadda suka yi da Ma’arouf a baya sai dariya ta shake shi.

“Zan taimaka, kuma zan shige gaba Yaa Maulaya, to amma sai ka yi min alkawarin ba za ka kara tunkarar Amina ba, ta waya ta ido da ido ko ta aike sai bayan kwana goma sha hudu.”

Ma’arouf ya zaro ido, “Idan kuma wani ya riga mu fa? Me ye hikima cikin hakan? Kai kamar ba ka tausayi na Turaki? Sati biyu? Yau kwana uku dubi yadda na koma ina ga sati biyu? To amma ban san me ye a zuciyarka ba, me ye hikimarka cikin hakan? Na san dai (your brain is sharp) fiye da ni ko a makaranta.

Haka ya kamata ka tambaye ni, ba idan wani ya riga mu ba. Do you think a yanzu Amina za ta iya auren wani ba kai ba?”

Ma’arouf ya dube shi idanu a russune na neman karin bayani. Ya yi murmushi, “Ita ma tana sonka Yaa Maulaya, babban alamun so sune kunya da jin nauyi. Za ka iya hada yadda Amina ke mu’amala da ni da yadda ta ke yi da kai? Kwata-kwata daina tunanin wani zai riga mu, sai dai a riga mu a fatar baki, amma ba a riga mu a zuciya ba.

Hikima ta a nan shi ne, a sati biyun nan ta huta, ba daga komawarta gida sai neman aure ba. Sannan a sati biyun nan za ta shiga cikin kewarka da damuwa da rashinka za ta yi kyakkyawan tunani ba na hanzari ba. Yadda da mun je za ta amshi bukatarmu don soyayyarsa da ke zuciyarta ta yi zafi har ta fito fili. Sai dai na tabbatar maka ba za ta iya fada wa mahaifiyarta ba a dai halinta da na karanta. Sai dai mu mu sanar da ita. Bayan sati biyun ka san yadda ku ka hadu sau uku ka ji amsarta, ku tattauna daga nan sai mu shiga neman aure.”

Dole kam ba yarda zai yi ya amince da shawarar Turaki, amma fa sati biyun nan ya gansu kamar shekara goma sha hudu. Sai ya kirkirarwa kansa tafiye-tafiyen kauyuka duba ‘projects’ har zuwa sati biyu.

Ranar da sati biyun nan ta cika Amina ta shirya za ta tafi Shira, gaido Baffaninta, don ta tabbata in ta koma aiki ba za ta samu lokaci ba. Ilya ke janta a karamar motarta Kia Picanto kasancewar hannun nata bai gama fadawa ba.

Gida-gida ta bi ta gaishe su, kowa sai murnar zuwan Dr. Amina yake yi don an san ba ta zuwa hannu rabbana. Haka kuwa, ba wanda bai samu rabonsa daga Amina ‘yar Mas’udu ba, Baffaninta kuwa jari, ta ba su na makudan kudade ta ce, su kara a gona ko su bude tireda. Amina ta sha albarka har ta gode Allah. Da la’asar suka kamo hanyar dawowa.

Goggo ta jaddada mata lallai ta je gidan Kawu Sule ma, don haka da suka shigo cikin gari ta gaya wa Ilya su je.

Amina dai sai da tambaya suka gane gidan Kawu Sule saboda yadda ya bi ya bushe kyamas ba shuka ko daya, ya ratattake ya lalace ba maigadi ba motoci. Haka dai suka boye mamakinsu suka shiga.

Ashe cikin gidan har ya fi wajen lalacewa. Kai! Atika Babar Hafiz wadda ita ma duk ta canza wahalar rayuwa ya bayyana a jikinta ta yi musu iso dakin Baffanin nata Sule. Yana kwance a kan wata tsohuwar kujera.

Ta gaishe shi cikin ladabi ya amsa sai kuma nan da nan ya kama kuka yana rokonta gafara a kan yadda ya yi watsi da rayuwarta. Ya ce, yanzu alhakin zumunci ya kama ni, dubi yadda karayar arziki ta rufto mini. Na hada duk abin da na mallaka nasa a wani sari na auno kaya jirgin ruwan da ya dauko su ya nutse.”

ya ci gaba da sharar hawaye yana rokonta gafara, fadi yake, “Ban kyauta wa Yaya masa’udu ba idan na mutu ba ki yafe min ba, ba ni da abin da zan iya uzuri da shi ga dan uwana, son zuciya kai da rudin abin duniya”.

Ta tabbatar masa da cewa, da ma ita da Goggo ba su kullace shi ba.

Ya ci gaba da gaya mata, “Ba don Hafiz ba, da abin da za mu sanya a bakin salatinmu ma babu. Ga shi shi kuma mace ta mallake shi, sai dan abin da ta ga dama ta ke sa wa ya ba mu. Ba kuma ya nan yanzu an canza masa wajen aiki zuwa Adamawa”.

Haka Amina ta baro gidan Kawu Sule bayan ta yi masa ihsani mai yawa. Suna tafe a mota suna tattauna al’amuran rayuwar duniya masu ban tsoro. Ta tausaya wa Kawu Sule, ta koka yadda al’umma muka yi watsi da martabar zumunci, kuma a haka wai muna burin shiga aljannah. Bayan duk martabar zumunci da darajja shi da Allah (S.W.T) ya yi, Ya yi mana umarni da mu kyautata shi, yana daga cikin manyan hanyoyin shiga aljannah. Allah ya sa mu dace, amin.

Ba su iso gida ba sai karfe takwas na dare. Wata mota ce ‘yar karama mai duhun gilasai ‘tint’ a kofar gidan Goggo, ta dan fara tsufa kuma ba a shaida wadanda suke cikinta saboda bakaken gilassan.

A daidai sanda Ilya yake kokarin sanya motar a inda ake ajiye ta. Amina ta ce, “Hala Goggo ta yi baki ne?”

Ya ce, “Ko kuma sabon saurayi ki ka yi ba?”

Ta harare shi ta bude kofar bangarenta ta fita. Kanta tsaye ta shiga cikin gida, ta baro Ilya a waje.

Sanya kanta falon Goggo ke da wuya ta ji wani sassanyan kamshi, wanda a cikin kanta ta dade da saninsa, ta yi (marking) dinsa a matsayin kamshin mutum daya, domin bayan shi ba ta kara jin mai irinsa a ko’ina ba, kai ka ce kamfanin da ya yi shi mutum daya ya yi wa shi, ya kuma gargade shi kada ya rabar da shi da sauran al’umma.

Gaban Amina ya yi wani irin faduwa, saura kadan dunduniyar dogon takalminta ta kayar da ita garin cirewa. Ba don mutane ukun da ke falon sun dago sun dube ta ba da tabbas ta juya ta bar gidan. Mutum na farko da ba ta taba sanya wa a ranta za ta gani tsakiyar dakin Goggonta ba.

Sanye da kaftan na shadda mai taushi, fara kal. An yi aikin zarenta da zare silver, hular kansa ma fara ce kal, a hannunsa na hagu agogon (rolex) ne mai farar fata. Ya saya kwayar idanunshi cikin farin gilashin ido, siriri mai garai-garai wanda ya kara fiddo ilhama da cikar zatinsa. His Excellency Ma’arouf Ji-kas ne.

A kusa da shi kwamishina Dr. Usman Turaki ne. Shi kam ya sha ‘suit’ ya tsuke abinsa, har da ‘neck-tie’. Da shi ta fara hada ido don shi ke fuskantar kofa. Ma’arouf din bayansa ke kallon kofa. sai da ya juyo jin karar takaminta da ta kusa kayar da ita, sannan ta ga fuskarta.

Goggo ta sha lullubi da katon mayafinta ta takure  can gefe, Dr. Amina ta samu kanta cikin rikicewa, ta rasa me za ta yi? Shiga za ta yi ko fita za ta yi? Sallamar da ta fara yi ma makalewa ta yi a makogaronta ta hadiye abarta. Ta kasa gasgata abin da ta ke gani; Ma’arouf Habibu Ji-kas shi ne ya tako da kafafunsa ya zo neman aurenta.

Dr. Turaki ya fahimci halan da ta ke ciki na razana da rashin sanin abin yi saboda ganinsu unexpected. Ya dauko murmushin karfafa gwiwa da sanya (courage) irin na Malami ga dalibinsa ya shimfida a kan fuskarsa.

“Shigo Dr. Amina, shigo mana, ai mu ba baki ba ne. Ko kuwa baki ne?”

Ta girgiza kai, sannan cikin sanyin jiki ta cira kafa kamar wadda kwai ya fashewa a ciki ta shiga falon. Ta tsugunna gaban Dr. Turaki ta gaishe shi, ta wuce dakinta wanda ke kusa da dakin baccin Goggo mai ban sha’awa. Abin da ta kashe wa dakin baccin Goggo bai kai wanda ta kashe wa nata dakin ba.

Wannan abu da Amina ta yi, ta gaida Turaki ba ta gaida Ji-kas ba ya fusata Goggo, har kunya sai da ta ji. ya kuma tabbatar mata da abin da suka fada mata, akwai kauna da soyayya a tsakaninta da mai girma Gwamna, wanda ita da ma tuni ta sanya wa zuciyarta akwai din. Ta dauka Aminan ce ba ta sani ba, ko ba ta fahimta ba, ashe ita Amina ke wa kallon sakarai, Allah ya ba ta mijin da ta ke hana idonta bacci tana roka mata har a dakin Allah, ta tattara maganar ta zuba a kwandon shara yadda ta saba.

Bayan alkawarin da ta yi mata kafin ta barta ta fara aikin nan, na cewa, duk wanda ya zo na farko za ta bar komai ta yi aure, yau me raba ta da Amina sai Allah.

Sun dau tsawon lokaci tare da Goggo, har karfe goma na dare. Amina ba za ta ce ga abin da suke tattaunawa ba. Ta kwanta ta yi rigingine a gadonta ta ja bargo mai laushi ta rufe jikinta, kirjinta in ban da dukan tara-tara ba abin da yake yi. Shi kenan ta faru ta kare, wai an yi wa mai dami daya sata, tunda zance ya zo kunnen Goggo, ta lissafa kanta cikin AMAREN BANA in ji Aziza Idris Gombe. An zuba wa Goggo magani a kan ciwon da ya addabe ta.

Ba ta san yaushe suka tafi ba, ta dai bude ido ta ga Goggo tsaye a kanta tana bubbuga ta sabida barci ne ya dauke ta ba da saninta ba, mai cike da mafarkai marasa kan-gado, wai Goggo na zane ta da wayar rediyo. Tana bude ido kuma ta ga Goggon tsaye a kanta tana huci.

Da sauri ta mike zaune, ta koma bakin gadon ta sunkuyar da kai.

“Sannu, sannunki likiciyar duniya.”

Amina ta yi shiru, kai a kasa.

Goggo ta ce, “Alkawarin da muka yi da ke kenan? Yaushe ki ka koma boye min sirrikan rayuwarki Amina?”

Amina ta soma hawaye, “Wallahi Goggo ba abin da na boye miki”.

“Daina rantsuwa, kin gaya min Baban Amina ya yi miki maganar aure? Kin gaya min ya ba ki kwanaki uku ki yi shawara da ni?”

Amina ta yi shiru tana share hawaye.

Goggo ta ce, “Ba da ke nake magana ba Amina?”

Ta saki kukan sosai, “Goggo na kasa ne, maganar ta yi min nauyi a baki”.

Goggo ta ji zuciyarta ta fara hucewa. Ta zauna gefen gadon ita ma, “Amma kin san burina ki yi aure ko Amina? Duka naki burikan na lamunce miki kin cika su, ni me ya sa ba za ki cika min nawa ba in samu cikon farin cikina, bayan na haihuwar ‘ya ta gari da Allah ya ba ni, idan na mutu ban ga aurenki ba alhalin Allah ya ba ki min auren, ke ce ki ka shure ba zan yafe miki ba Amina”. Ita ma ta soma kuka, ta sanya fuska cikin mayafinta.

Hankalin Amina ya yi kololuwar tashi, ta sauko da hanzari ta durkus a gaban Goggo, ta dora hannu a kan cinyoyinta. Hawaye na zuba daga idonta.

“Don Allah ki yi hakuri Goggo, wallahi ko gobe ki ka ce na yi aure zan yi. Na tuba na bi Allah na bi ki…”

Sai da Goggo ta yi kukanta mai isarta, sannan ta daga Amina daga durkuson da ta yi a gabanta tana neman gafara.

“Na yafe miki duniya da lahira. Kin amince za ki iya auren Baban Amina saboda Allah ba don wani dalili ba, ko don ‘yarsa Amina?”

A hankali Amina ta daga kai ta kalli Goggo.

“Goggo duk da ina jin nauyinki, amma a yau zan gaya miki, na dade ina son Baban Amina. Amma Goggo ba kya tunanin jama’a za su ce kwadayi ne ya kai ni ga aurensa, ko wani abu makamancin hakan? Ga kuma matarsa wata irin halitta mai mugun hali da in ba mutum mai tsananin hakuri da kauda kai ba ne kamar shi (Ji-kas) babu mai iya zama da ita”.

Goggo ta yi murmushi, “Amina in ki ka ce za ki daka ta mutane ko abin da za su ce a kanki, ba za ki taba kulla wa rayuwarki wani abin alheri ba. Ke dai komai za ki yi, to ki yi shi don Allah da neman yardarSa. Ki tsarkake niyya da zuciya. Ki yi don neman falalar Ubangiji, ki rabu da mutum wanda ko Ubangijinsa ba ya iya masa. Maganar matarsa, ki nemi da ya raba muku gida…”

“Hakan ba zai yiwu ba Goggo, har sai ya sauka daga kujerarsa, ma’ana sai (tenure) dinsa ta cika, saboda tsaro”.

Goggo ta ce, “To ai ni ban san yaushe ki ka koyi tsoro ba. Aminata da na sani mai dabarun zamantakewa ce. Duk da halin nata da ki ke kokawa kin taba ko musayar yawu tare da ita?”

Da sauri Amina ta girgiza kai, “Ko sau daya ban taba ba. Mafiya yawan lokuta ma ni dariya ta ke ba ni, saboda abubuwan da ta ke yi na marasa hankali ne da tsinkaye”.

“Madallah!” In ji goggo, “Ci gaba da zama da ita yadda ki ka zauna da ita tun farko. Na tabbatar miki ranar da ta gaji da kanta za ta neme ki da ku zauna lafiya”.

Amina ta ce a sanyaye, “Toh Goggo”

Hajiya Hauwa ta kawo murmushin lallashi kan fuskarta, “To tunda mun yi shawarar da ya ba ki kwana uku mu yi ba ki gaya min ba sai yau, bayan kwana goma sha hudu da ya gaya min da bakinsa. Mun kuma tsaida shawarar, kin amince wa auren bawan Allah irin Baban Ameena, sai ki kira shi ki gaya masa amincewarki, saboda yana cikin damuwa na rashin ji daga gare ki. Ki kuma yi masa gaisuwar da dazun ba ki yi masa ba ki ka wuce shi kai a sama…”

Amina ta turo baki, kamar kankanuwar yarinya, “Don Allah Goggo ki bari sai in shi ya kira, na yi miki alkawarin zan dauka. Ai sai ya ga kamar neman kai ki ke yi da ni.”

Goggo ta danna mata harara, “Da me nake yi ba neman kan da ke ba? Kin ga bana son iya shege, ta bakinki suke jira Ilya ya raka Turaki Shira, da wajen Sule. Cikin wata mai kamawa suke so a gama komai ki tare a dakinki.”

Ta yi ficewarta ta bar Amina tana kakabi da sambatu ita kadai, “Wata daya Goggo? Sai ka ce wata ‘yar tsana?”

Bookmark
ClosePlease login

No account yet? Register

Rate the story.

Average: 4 / 5. Rating: 4

As you found it interesting...

Follow us to see more!

<< Sanadin Kenan 27Sanadin Kenan 39 >>

1 thought on “Sanadin Kenan 28”

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
3
Free daily stories remaining!
×