Skip to content
Part 20 of 50 in the Series Sanadin Kenan by Sumayyah Abdulkadir (Takori)

Amina na dakin tantabarunta, bayan ta shirya tsaf, sallama ta ke musu tana fada musu za ta yi dan balaguro, amma ta wakilta Baba Talatu ta zuba musu abinci kullum, ta sauya musu ruwan sha.

Ilya ya zo zai sanyo kai gidan, wata luntsumemiyar Sienna na fakawa a kofar gidan Malam Mas’ud. Nan da nan ya gane motar daukar Dr. Ameena ce zuwa gidan gwamnati.

Ya danna kai cikin gidan da sauri, har yana tuntube saura kadan ya fadi.

“Tafi a hankali Ilyan Goggo”. In ji Baba Talatu.

“Ina Dr. Amina? In ce ko ta shirya, an zo daukarmu.”

Daga dakin tantabarun Amina ta jiyo shi, ba ta san sanda ta saki dariya ba. Wai an zo daukarsu, kai ka rantse da Allah tare za su yi aikin.

“To Ilyan Goggo ina zuwa, muna sallama ne da mutane na.”

Ilya bai san san da ya watsar da girman da yake bai wa Aminar ba, saboda haushin da ta ba shi, “Ke da Allah ki fito, Tantabarun me?”

Ya isa ga akwatunta guda daya da ke gefe ya dauka. Goggo ta fito daga daki Amina ta fito daga dakin tantabaru, wata ta biyota ta hau kafadarta ta kuwa sakar mata kashi a kafadar, Talatu ta goge mata, ta rungume Goggo da kyar ta sake ta suka rako ta har zauren karshe ita da Talatu, tuni Ilya ya kame a gaban mota.

Akilu ya fito ya bude mata ta shiga ta rufe kofar, ya ja motar a hankali suka bar unguwar suka dauki hanyar gidan gwamnati.

Kasancewar Akilu ke jan motar ba a tsaya yi musu dogon bincike ba. Ilya na gaban mota, Amina na kame a baya. Farin cikin duniya ya cika zuciyar Ilya, yau ga shi a gidan babban masoyinsa His Excellency Engnr. Ma’arouf Habibou Ji-Kas, ban da yi wa Allah godiya cikin zuciyarsa ba abin da yake yi.

Akilu shi ya yi musu jagora har falon shiga gidan na biyu. Nan ya ce su zauna zai kira Hajiya. Ya zaro wayarsa ya kira Hajiya, ya ce,

“Likitar ta iso?”

Hajiya ta ce, “Ka yi mata kwatance ta iso ko ka kira mai aiki mace ta shigo da ita.”

Mai aikin ya sa ta shiga da ita, nan Amina da ilya suka yi sallama, ta dauko jakarta, amma sai mai aikin ta karba suka wuce can ciki.

Akilu ya ce da Ilya su je ya maida shi.

Hajiya da Amina suna kwance cikin bargo, Hajiya ba bacci ta ke ba lazimi ta ke, Amina ce ke bacci. Mai aikin ta yi sallama Hajiya ta ba ta izinin shigowa, ta murda kofar suka shiga. Amina na binta a baya.

Hajiya Saude ta mike sosai ta janye bargon zuwa rabin jikinta, lullubin kanta yana nan bai fadi ba, ta zauna sosai tana kallon likita Amina kallo na kurillah, doguwar mace sambaleliya son kowa, kirar jikinta bata matan hausawa bace, tafi mata kama da mutanen Sirrleone, mai aikin ta ajiye jakar Amina ta tafi.

Amina har sai da ta ji wani iri da kallon da Hajiya Saude ke mata. Kamar tana son gano ta inda zata cutama jikarta. Ta tsugunna har kasa ta gaishe ta. Hajiya ta dan saki fuska ta amsa jin tayi hausa, kenan ba kedarar bace.

“Taso-taso ki zauna a nan kin ji ‘ya ta.”

Hankalinta ya kwanta yanzu tunda ba kabila aka dauko ba.

Amina ta samu gefen kilishi mai taushi ta zauna. Ba ta yarda ta hau gadon da Hajiyar ta yi mata tayin zama ba. Ta sadda kai kasa tana wasa da yatsunta.

Hajiya ta ce, “Ya sunan ‘yar tawa, ko in ce likitar tamu?”

Ta yi murmushi,

“Sunana Amina”

“Ikon Allah, sunanku daya da ‘yar taki. Allah ya yi albarka, Ya ba ki ikon kulawa da ita da amana”

Amina ta dago ta dubi Hajiya sosai da nutsatstsen kallonta.

“Kada ki ji haufi a kaina, ki sa a ranki Amina na hannun mahaifiyarta ne. Ni likita ce, marassa lafiyanmu bakidaya amana ne a hannunmu. Insha Allah zan yi iya kokarina a kan Amina, da yardar Allah za ta mike”

Hajiya Saude ta ji dadin kalamanta, ta bude bargon da ta rufe Amina,

“Zo ga ‘yar taki”

Amina ta yi murmushi ta mike ta isa ga gefen gadon ta zauna, ta kama hannun Amina ta rike cikin nata. Wadda ke bacci cikin kwanciyar hankali. Kyakkyawar yarinya wadda ko cikin lalura kyawunta bai jirkita ba. In ka ganta tana bacci abinta ba za ka yi zaton tana da kowacce irin lalura ba.

“Zan iya fara duba Amina yanzu?” Ta tambayi hajiya cikin sigar neman izni.

“Duba ta mana, ni na ji jikinta ma ya yi zafi.”

Ta mike tsaye, “Ni sallah zan yi. In kin gama ga makewayi nan”. Ta nuna mata kofar bandaki, ita kuma ta shige.

Amina ta janyo jakarta, ta fiddo wasu daga cikin kayan aikinta. Ta dauki ‘Stethoscope’ ta makala a kunnenta ta dora a kirjin Amina, ta ci gaba da caje ta ciki da bai. Har Hajiya ta fito ba ta gama ba. Ta juya tana tambayar Hajiya,

“Zan iya samun file dinta na asibitin da ta fara jinya?”

Hajiya ta ce, “Eh, toh. Bari Babanta ya shigo, ko in ba ki lambarsa ki kira shi ki fada masa.”

Gaban Amina ya dan fadi, ita fa ba za ta taba iya kiran Ma’arouf Ji-kas ba. Wane ita, wane mutum! Nan da nan dabara ta fado mata,

“Ki kira shi da wayarki Hajiya, ba lallai ya amsa kirana ba tunda bai san lamba ta ba.”

Hajiya ta amince,

“To bari na idar da sallah.”

Ita ma sai ta gyara wa Amina kwanciya ta ajiye komai ta nufi bandakin don daura alwalar sallar azahar.

Hajiya tana idarwa ta yi addu’a ta shafa ta dauki wayarta ta kira shi. Ba bata lokaci ya amsa.

“Likitar Amina ke son fayal dinta na asibiti”.

“Ba damuwa, zan yi wa Dr. Umar Bolori waya kafin la’asar zai kawo.”

Ga mamakin Hajiya, Dr. Amina na idar da sallah ta shiga bandaki ta hada ruwa mai dumi a Jacuzzi, ta zo ta dauki Amina ta yi bandaki da ita. Wanka ta yi mata mai kyau ta tsaftace ta da sabulai masu kyau na ruwa (Bathgel) ta wanke mata baki, ta tsefe kalbar kanta ta wanke mata kai da shampoo ta nado ta a babban shawul suka fito. Ta kwantar da ita ta shafe ta da kyau, ta sa mata kunzugun (pampers). Ta nemi Hajiya ta ba ta kayanta, ta nuna mata (wardrove) shake taf da kayan ‘yar gata Amina iri-iri. Ta dauki wata shirt da dogon wando kalarsu (Pink), ta sanya mata. Ta dora kanta a cinyoyinta ta soma yarfa mata kitso. Nan da nan Amina ta dawo kamar mai lafiya, ta yi (fresh) da ita, sai kallon Dr. Amina ta ke yi.

Da suka gama ta ce wa Hajiya tana son farfesun hanta da soyayyen dankalin turawa, Hajiya ta nuna mata abin da za ta dinga dannawa in tana son kiran ma’aikata mata da ke kicin din gidan, ba kamar gidansa na Fati Muazu ba nan sun tadda duk ma’aikatan cikin gida mata ne, da kuma wani madannin daban na masu tsaftace wuri. Ita ma Baban Amina ne ya nuna mata kafin ya fita. Amina ta yi yadda ta ce.

Wata mace mai tsafta ta zo, ta gaya mata abinda ta ke so ta kawo mata.

Ta ce, “Akwai su, bari na kawo”

Ba ta yi mintuna biyar ba ta kawo su da duminsu. Ta zaunar da Ameena a kan cinyarta ta marmarasa hantar cikin romon tana ba ta a baki. Dankalin ma marmasa mata shi ta ke, kuma ta karba tana ci sosai. Sai da ta koshi ta kyale ta, ta goge mata baki fes! Ta rungume ta a jikinta, ba ta ankara ba Ameena ta yi bacci a kirjinta.

Hajiya ta rika yi wa Amina tambayoyi a kan rayuwarta, tana ba ta amsa. Ta gaya mata Babanta ya rasu tun tana karama, mahaifiyarta ita ce komai nata. Ita ta tsaya mata ta yi karatu don haka ba karamin gumurzu aka yi ba kafin ta barta ta zo. Ta roki Hajiya su ma su yi kokari su kare mutuncinta a zaman da za ta yi da su saboda ba ta saba irin wannan rayuwar ba.

Hajiya ta yi murmushi ta ce, “Kamar wace rayuwa kenan?”

Amina ta nisa, kamar a ce komai sai an yi mata ita ba ta son haka, ta saba da kazarniya, ba ta so ta yi kiba. Ba ta so a dinga hada lamarinta da maza ko da masu aiki ne. She’s here for Amina alone ba ta son wani ya wulakantata, ko ya shiga shirginta.

Ba ta so komai sai an mata. A barta ta kula da kanta tunda tanada koshin lafiya.. Dakin da za su zauna da Ameena a bar mata alhakin kula da tsabtace shi, haka bayan gida. Sannan a bata kicin karami za ta dinga dafa abin da za ta ci, cimarsu ba daya ba ce. Itama Amina karama ba kowane abinci ya kamata ta dinga ci ba, sai wanda zai amfani jikinta da kasusuwanta, ita za ta dinga dafa mata.

Hajiya ta jinjina kai, a ranta ta ce, ‘ka ga wadanda daula ba ta sa wa su manta asalinsu, ba irin su o’oh ba’.

Da murmushi ta dubi Amina, “Ki rubuta duk abin da ku ke bukata ki ba shi. Na kuma yi alkawarin zan gaya masa duk abin da ki ka ce.”

Amina ta dauko jotter ta soma rubutawa.

Ya murdo kofar bakinsa dauke da sallama ya shigo. Sanye yake cikin ‘yar ciki da wando na farar shadda kal! Da alama ya cire ta saman ya ajiye kafin ya shigo. Wani irin daddadan kamshi ya surnano cikin hancin Amina. Muryarsa mai amo da karsashi kamar na kowanne babban mutum.

Bai kula da Ameena da ke rungume cikin jikin Dr. Amina tana bacci ba, kai tsaye inda Hajiyarsa ke zaune bisa sallaya ya nufa ya zauna daidai kafafunta kamar wani karamin yaro. Dr. Amina ba ta dago kai ba, ta ci gaba da yin rubutun da ta ke yi cikin jotter a cinyar Ameena.

Ya ce, “Hajiya, me ya sa ki nishadi haka?”

Ta ce, “Hira muke yi da Amina likitar Ameena.”

Ta yi masa nuni da ita a bakin gado. Da sauri ya juya ya dubi inda ta nuna masa din. Kan Amina na sunkuye ba ta dago ba, tana ta rubutunta. Ya dubi Ameena karama sosai, ya ga ta canza gaba daya ta zama kamar diyar Larabawa, daga fitarsa zuwa dawowarsa. Bai yi nasarar ganin fuskarta ba, amma zubin halittar jikinta da yanayin tsayinta da fatarta ya nuna ba cikakkiyar ‘yar Nigeria ba ce, ga ta nan dai kamar ‘yammatan kasar Sirrleone… Bai zurfafa kallon da yake yi mata ba, ya ce,

“A yi mata barka da zuwa”. Ya dauke kai daga gare ta.

Ta ci gaba da rubutun har ta gama, shi kuma yana magana da mahaifiyarsa. Ta mike don isa ga Hajiya ta bata takardar data kammala yin list na abubuwan da take so, tana faman kawar da kai wai kada ta kalle shi ko shi ya ga fuskarta. Ma’arouf ya juyo kenan sai suka hada ido a side din data mayar da fuskar, ya yi saurin dauke kai ya mayar wani gefen shima har ta mikawa Hajiya takardar ta koma inda ta tashi ta zauna.

Hajiya ta soma koro masa bukatun da Amina ke da su a zamanta da su, ta kuma mika masa takardar da ta rubuta kayan abinci zallah da ta ke so a sayo musu ita da Amina, kayan tsaftar bandaki da  na daki ciki da falo, har da su omo, mopper, jik, hypo, room freshner da sauransu. Ya kusa ya yi dariya amma ya gimtse, ban da abinta wadannan abubuwan da ta rubuta babu wanda babu a gidan nan, amma zai sa a tattaro mata a shirya mata kicin da toilet kamar yadda ta ke so.

Ya ce ba tare da ya dube ta ba, da murya ta girma, wadda yake amfani da ita wajen yin magana ga na kasa dashi ko kuwa ma’aikatan sa,  “Hajiya ki gaya mata, a bukatunta babu wanda ba za a kiyaye ba. Abubuwan da ta ke so babu wanda ba za a sayo ba insha Allahu!”

Hajiya ta maimaita kamar yadda ya fada…. “Amina bukatunki duk za’a kiyaye… abubuwan da kikeso duk zaa sayo su insha Allah..”. Hajiya ta ba ta dariya, ta yi murmushi mai fadi (broad smile) daidai lokacin da ya dago daga kallon Amina karama dake kan cinyarta ya dubeta kadan, wannan karon ya yi nasarar ganin fuskarta gaba daya. Ya yi saurin dauke kai saboda sun kara hada idanu ba da sanin su ba a karo na biyu, ga shi shi kuma ba ma’abocin kallon mata ba, ko matarshi ba ta ishe shi kallo ba.

A gaba dayan rayuwarsa ya tabbata bai taba kallon mace duk kyawunta sau uku ba ban da Aisha. Ita kadai ce baya gajiya da kallo.

Ya mika wa Hajiya file din da ya shigo da shi.

“Ga file din Hajiya, a ba wa Dr. Amina”.

<< Sanadin Kenan 19Sanadin Kenan 21 >>

1 thought on “Sanadin Kenan 20”

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×